Idon Naira 8


 *_Arewabooks@Mamuhgee_*


8

Da farko Jin tafiyarsa Zainab tashiga damuwa sosai saidai kuma Tunda karatu ne zaije,

Qaruwarsa ce hakama duk cigabansa tanaso Dan haka sai ta danne damuwarta kawai ta boye a ranta Tunda kafin zuwansa duniya cikin kadaici take rayuwarta batareda kowa Dan haka yanzu dinma zata iya idan Allah ya yarda.


Dayake Yana karantar yanayinta Kai tsaye kwana biyu duk yanda take dannewa ya gane Tana cikin damuwa da kadaicinsa tin yanzu Dan haka sai shima yaji damuwar barin nata ita kadai din.


Kwana biyu yafara tunani da neman yanda zaiyi da lamarin Dan kuwa bazai taba iya tafiya yabar Mamin cikin damuwa da kadaiciba Kuma Hakanan zuciyarsa takasa nutsuwa da barin nata...


Ficewa tafiyar tafara yi daga ransa sbd ita,

Jin yake zai iya hakura da tafiya wata qasar ya zauna yayi karatunsa anan sbd ita

 Amma Tunda Haj maryamah tafara fahimtar abinda yake Shirin faruwa na sauyin raayinsa dayake Shirin Yi take Hankalinta ya tashi sosai Kuma ranta yayi mummanan baci Dan kuwa wannan karon batajin zata sassautawa Aqeel din bare Zainab idai akan tafiyarsa ne.



Farko Kai tsaye ta tarasu a babban palonta da Aqeel da Zainab din wadda take zaune a kujera jiki amace


Ita kanta zaman kujerar sbd Aqeel Yana gurin ne take zaune akai Dan tuni yayi Hani da Zamanta a qasa Dan bazai iya yarda Yana ganinta zaune a qasa ba shi Yana kan kujera 

Haka Haj maryamah tanaji Tana gani ta dauki wannan dokar tasa ta barin zaman Zainab din a kujera a palonta idan suna tare sbd kaucewa bacin ransa.


A yau din ranta bace yake sosai Wanda kusan su dukansu sun shaida Hakan 

Dan haka palon yayi tsit suna jiran abinda zata fada musamman Zainab data Gama sanyi akan ko wane irin laifine tariga tasan itace zaace ta aikata Tunda akai kiranta.


Take jikinta ya sake mutuwa Dama kwanakin sai ahankali Tunda maganar tafiyar 'dan nata ta tabbata takasa gane kanta Dan Jin takeyi idan ya tafi kamar sun rabu kenan...


Kai tsaye Zainab Haj maryamah ta kalla kafin ta maida kallonta akan Aqeel Wanda ya kalla Maminsa yaga yanda duk tayi sanyi take zuciyarsa tayi Dan nauyi Dan haka ya dauke kallonsa daga gefenta ya gyara zamansa tareda hade dogayen fararen yatsun hannuwansa guri daya Yana Dan lumshe fararen idanuwansa cikin Yar damuwa da rashin Jin dadi.



"Aqeel maganar tafiyarka UK nakeson nasake Jin raayinka Dan kasan yanzu Kai ba yaro bane da zan zauna muna Abu daya koyaushe akan tafiyarka karatu,

As you can see manyanci yariga yaxomin Dan haka Dole zaka maida hankali kan karatu Dan is dakemun wannan nauyin na Aiki da kula da komai Nima nasamu na huta na fuskanci gyaran gobe na.. so me kace gameda tafiyar???


Ahankali ya sauke idanuwansa akanta tareda Dan sauke idanuwansa qasa Dan girmamawarsa ga manyansa itace Sam baya iya kallon idanuwansu ko tsaida kallonsa akan fuskarsu Dan haka Bayan ya kalleta kadan saiya sauke idanuwansa..


Muryarsa data fara zama budaddiya irin na mazan dasuka amsa sunansu maza yace"


Umma inaga zanyi karatun anan hankalina zaifi kwanciya....


Katsesa Haj maryamah din tayi da cewa"


Sbd Zainab kake ganin karatun naka anan zaifi??


Baya qarya kwata kwata sbd ilimin addinin daya ratsasa yasan illarta barema ba halayyarsa bace Dan tarbiyar da Zainab tayi Masa Sam Babu gurbatacciya a cikinta Dan haka ka tsaye yace"


Eh harda ita a dalilin.....


Ajiyar zuciya Haj maryamah ta sauke zuciyarta na wani irin nauyi da 'daci tareda mutuwar jiki 


Bata iya cewa komaiba ta juya ta kalli Zainab cikin sanyin murya tace"


Kinji da kunnenki ko?


Haka kikeson rayuwar tasa ta qare batareda karatun dazai Gina Kansa ba dama mu gabaki daya..

Haka kikeso ko Zainab??


Kasa magana Zainab tayi saidai AQEEL dinne ya duba umman cikin nutsuwarsa yace"


Umma Mami batasan da wannan tunanin nawa Dana yanke ba...


Cikin qosawa da halayensu Haj maryamah ta katsesa da cewa"


Tashi kaje nagama maganata dakai.


Miqewa yayi ba musu ya fice a natse Yana Dan rufe idon wasu halayen na iyaye Dole sai kana musu uzuri da kuwa sun wuce ka tsaya gardama ko sainsa da su.


Bayan fitarsa ahankali Zainab ta dago cikin sanyi ta Dan kalli Haj maryamah tace"


Anty wallahi bansan da wannan tunanin nasaba,

Koda nasani Anty wlh kinsan bazan taba barin ya zaba abinda zai daqile cigaban rayuwarsa ba....



Kasa magana Haj maryamah tayi sai data dafa goshinta dake sarawa Yana saka kanta wani matsanin ciwo Dama gashi rayuwarta gabaki daya tagama juyawa Tunda tazama itace komai hatta hawan jini na wahalar Aiki da tunanin duniya duk ya kamata gashi acikin gidanma Aqeel da Zainab na neman sake Dora mata wani hawan jinin akan Wanda take fama dashi.


Cikin sanyi tafara fada ranta amatuqar bace Dan ko energy din fadan sosai batada Amma ranta yayi bacin da Zainab din tajima Bata ganiba Dan haka takasa cewa komai sai hawaye datakeyi masu zafi da ciwo Dan kuwa maganganu ne masu 'daci da zafi take fada Mata akan ba itace ta haifi Aqeel dinba shiyasa zata lalata Masa rayuwa..


Tun Tana hawaye karshe wata irin sheshekar kuka takeyi Wanda yake bayyanarda tsananin zafi da ciwon harma da 'dacin da maganganun suke Mata a zuciya.


Ita kanta qarshe Haj maryamah din kukan tafara wandata jima batayiba Dan kuwa kusan komaima Yana cin zuciyarta gameda Zainab,


Har cikin ranta tarasa yanda zatayi ta karba Zainab cikin zuciyarta,


Tanajin dacin yanda suke rayuwar saidai shedan a kafirar zuciya irin tata yasa komai nasu yaqi gaba bare baya kullum suna tsaye guri daya

Dukkaninsu rayuwarsu Tana guri guda a tsaye.


Koda Zainab ta fita Jin tayi zuciyarta na Kara daukan 'daci da nauyi Dan haka umma takira ta sanar Mata komai tareda bada tabbacin matuqar Aqeel bai tafi karatun datakeso dinba Zainab zata bar Mata gidanta.



Hankalin umma ya tashi sosai da hukuncin Haj maryamah din sbd ko yayane batason su rabu gwara dai suna taren wata ran kila su hade kansu duk da dai kusan kaman an qurewa Hakan Tunda manyancin ya fara shigowa musamman maryamah da manyancin Kam yariga yazo ita kanta Zainab ta girma ai tafiya sawun Yan Mata ma.


Umma tsufa yazo batajin zata iya doguwar tafiyar da zata zo gurinsu.



Kwana biyu akai gidan bbu Mai dadin Rai sbd Haj maryamah ta dauki zafi sosai Kuma ko Aqeel din Bata bawa damar zuwa gurintaba bare ya lallabata yabata hakuri...


Zainab ma sosai ta bawa zuciyarta hakuri ta fara janyewa daga Aqeel din sbd kaucewa fitina da bacin rayuka kamar Hakan Dan umma ta kirata a waya tayi Mata fada sosai Dan haka duk sai taji a Karo na farko rayuwar tafara fice Mata arai.



Lamarin dai sai qara munana yakeyi sbd Kai tsaye Aqeel yasake tabbatarda bazai tafiba yabar Mamin tasa Dan haka Kai tsaye Haj maryamah itama ta sanar masa ko yatafi ko Mamin tabar gidan...


Shock suka shiga kusan shida Mamin tasa Dan kuwa Babu Wanda ya taba kawo Hakan zata faru.


Zainab tayi kukan data jima bataiba,

Tayi baqin cikin wannan rayuwar,

Tayi kukan rashin uwa da Uba,

Tayi kukan rashin sanin dangin uwa harma Dana uban,

Tayi kukan rashin samun mijin aure Wanda Koda baida komai idan har zai iya zama da ita cikin mutunci da mutuntawa.


Aqeel ma kwata kwata bai dauka lamarin zaije can ba hankalinsa ya tashi matuqa da yanayin da Mamin ta shiga Dan haka shida Kansa ya Kira umma yasake fada Mata komai Dan ita kadaice zata tankwasa Mahaifiyarsa,


Hakama ya Kira hajiya Kaka mahaifiyar Dadynsa itama tazo tabawa haj maryamah hakuri Amma dai itama Tana Bayan Aqeel din yatafi karatu Bata yarda da karatunsa anan ba.


Rigima dai Bata qareba saida umma ta taso daga Cameroon tazo aka zauna akai magana tareda tone tone inda anan Aqeel yaji asalin matsayin Maminsa ba 'yar aikin gidan bace qanwar mahaifiyarsa ce Uba daya.


Innalillahi wainna IlayhirRajiun......

Wani irin fitinannen tsoro da mamaki ya shiga na wannan mummanan alaqar da iyayen nasa Mata biyu suka gudanar tun qananun shekaru har manyanci....


Tsananin tausayi da sabuwar kaunar Maminsa ne ya shigesa Wanda a gabansu saida ya zubda qwallar wani irin 'daci da raunin da zuciyarsa ta samu na Jin wannan babban lamarin.


Kai tsaye ya amince da barin qasar zuwa UK Dan kuwa bazai taba barin sbd shi Mamin tabar gidanba Dan kuwa yasan batada gurin zuwa.... Amma a gabansu ya shimfida wani kyakkyawan alqawari Mai girma na cewa duk ya dawo zai dauki Maminsa har abada nauyinta zai dawo kansa yadauke musu nauyinta tun daga na jini harna jiki.


Da farko Haj maryamah Bata fahimtaba saida umma tasake nuna Mata illar Hakan da gaba zaa samu Dan haka tace Bata yardaba 

Zainab qanwarta ce a hannunta zata zauna sai aure idan tanada rabon yinsa kenan.


Kalmar ta Sosa zuciyar Aqeel yakalli Mamin wadda take zaune batada abin cewa sai yanda akai da ita.


Take wani ciwo da daci yakuma mamaye zuciyarsa Dan haka baice komaiba aka bar zancen ahakan.


Umma sai datai kusan wata daya kafin ta tattara ta koma Cameroon tabarsu Bayan tayi musu Yan nasihu Amma dai kusan kowa yanzu zuciyarsa ta cire Rai daga Dan uwansa.


Zainab gabaki daya yanzu tasake zama wata iri tayi sanyi sosai fiyeda baya Dan an ankarar da ita ko zaman datakeyi gidan alfarma ce akeyi Mata

Batada wani amfanin da zaa mutunta Dan shi saima tunatar da ita da akai ita din ba kowa bace face Yar Aiki a gidan wadda zaa kora aduk lokacin da akaso.



A yanzu gidan Bayan Aiki da abinda aka sakata Yi Babu abinda takeyi 

Data Gama take komawa inda dakinta yake ta zauna ta kame kanta.


Shi Kansa Aqeel yanzu tsakaninta dashi sai idan yazo dakinta da safe gaidata kamar yanda ya saba Amma duk wani alaqarta dashi ta Dan ja baya dashi.


Wannan sabon halin data shiga ya sakasa damuwa shima Amma Kuma shima cikin nasa yanayin na damuwar yake Dan haka kowa dai yazama sai ahankali gidan.



Ta bangare daya karatunsa na addini da malaminsa Kuma ubansa malam Sanda yayi zurfi,


Malam Sanda A yanda yakejin Aqeel shima tamkar shine ya haifesa musamman Dama baida da ko daya ba taba haihuwaba,


Asalinsa Dan Billiri dake gombe karatun almajiranci ne ya kawosa cikin gombe daga Nan aka ringa kaisu garuruwa almajirancin qarshe ya tsaya anan Jigawa harya girma yafara Dan sirkawa Dana Biko kadan kadan haryayi karatun secondary Amma daga Nan bai Dora ba saiya Dan ringa kasuwanci Yana karatun addinin sosai har Allah yasa ya Dan Yi suna a karatun Addininsa.


Tunda iyayensa suka rasu ya rage zuwa gida haryazo Yana jimawa sosai baijeba Dan kusan dangin kowa tayita kansa.


Anan yayi aurensa na farko kusa shekararsa bakwai da matar Allah bai Basu haihuwaba qarshe ta rasu sanadin breast cancer batareda ta haihuba..

Tun daga lokacin bai Kuma aureba haka yake zaune Yana cigaba da yiwa addini hidima.


Alh Asad shine kusan komai na malam Sanda Dan kuwa ko dawainiyar jinyar matar malam din shine ya dauki nauyi har qasar India sukaje Amma Hakan dai Allah yayi bamai warkewa bace.


Tsakanin malam Sanda da Alhaji Asad akwai kauna da shakuwa tareda mutunci sosai kamar Yan uwan jini haka suka dauki juna...


Alaqarsu tasaka malam Sanda cusawa Alh Asad kaunar addini Mai tsanani gashi Hakan yazo har Dan sa Aqeel Wanda kusan ayanzu yafi mahaifinsa daya rasu akidar karatun na addini gashi shi yanada kuruciya Kansa a bude yake sai ya zama har yanafin malam din riqe wasu abubuwa idan malam din ya Dan tsaya.



Farko Kai tsaye sha'awar aurarda Maminsa ga malaminsa Yashigesa Amma Kuma lura da su dukan kamar iyayensa ne sai bai fidda maganar kai tsaye ba sbd yanason fara Jin raayin Maminsa Dan bazai iya Mata abinda batasoba.

##MAMUH#

#LOVE

#AQEEL ASAD

#IDON NERA




*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo



Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.