Idon Naira 25

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*

25

Lokacinda SSG ya samu cikakken bayanin abinda ya faru harma da matakin da Haj Zainab ke Shirin dauka akan matarsa da matar Aminin nasa Wanda yama fisa

mutunci a idanuwan mutane sbd kamewarsa da Kuma Arzikin dayafisa uwa uba Yana cikin manya malaman addini sosai wainda duniya kewa kallon zallan mutunci da girmamawa..


Cikin bacin Rai da damuwa ya sallami Jameel daya isar Masa da sakon,


Sake kallon wayarsa yayi a karo na babu adadi Yana tunanin yanda zai tinkari Haj Zainab da ban hakurin janye matakin datake da niyar dauka din sbd mutuncinsu su duka Bai Kamata zasu hada zuria ba duniya tajisu tun yanzu suna daukan matakai akan junaba...


Ta wani bangaren kuwa shakkar tinkararta da maganar yakeyi sbd antaba 'yarta ne Kuma kowa yasan 'yayanta sune rayuwarta Bata Wasa da lamarinsu ko daya.


Dafe goshinsa yai Yana sauke numfashi Mai dumi bacin Ransa akan halayensu Nafeen Yana qara sosa Ransa.


Wane irin kishi ne wannan se sakasu yin abinda zai kawo fitinar da baasan ya zata qare ba.


Ya debo shekaru Yana bibiyar AMAL Idon Nera yasamu ta aminta da aurensa gashi sune neman lalata Masa auren tun kafin ayi.


Cikin bacin Rai da damuwa ya soke duka schedules dinsa na ranar ya fito da yamma kai tsaye the IDON NERA's ya nufa wato gidansu kenan da ake Kira da hakan.


Daga haj Zainab har uncle Lulu babu Wanda ya sama a gida mutuniyar tasa Kuma Daman a abanza ma tayi aji barema an tabata gata Bata daukan reni Kona Wasa bare irin wannan.


Siddi kawai yasamu damar gani ta sanar Masa babu kowa sai masu aiki Amal Kuma tace Bata buqatan ganinsa..


Bai tsaya ba Dan yasan bazata fito dinba tunda tafada gashi Bata daukan wayarsa,

Uncle Lulu da haj Zainab ma duka basa daukan waya da alama suna guri Mai mahummanci.


Daukan dumi Kansa yayi sbd Allah ne kawai zai Hana auren Nan samun matsala,

Nafee sun lalata Masa komai,


Wani irin bacin Rai mai tsanani yake ji

Abin mamaki Kuma Yana Isa gidan yatadda Nafee tadawo..


A karo na farko da Nafee taga mummunan bacin Ransa da Bata saniba,


Ita kanta Bilkees Saida ta tsorata da kalmarsa ta karshe dayace matuqar aurensa da Amal ya lalace akan wannan abin dasukai abakin igiyar aurenta 'daya Kuma wlh saiyayi wani auren Koba Amal ba tunda yayi niya.


Bilkees a duniya babu kalma mafi Muni da tsoro gareta kamar kalmar kishiya da saki sbd duk inda sunan kishiya ya tabba to saki na kusa idan ba Allah ya rufa asiriba,


Kukan da Nafee keyi Sosai yasa balkees sake shiga damuwa da mamaki mai tsanani,


"Yanzu sai Hayat ya iya sakinki akan wannan yarinyar??


Wlh tallahi ba dauka lamarin Nan yakai hakabama,.


Rabuwa fa yake nufin yayi dake idan Bai samu wannan din ba,


Duk 'yaya da shekarun da kukai Bai dubaba yake iya furta Miki wannan kalmar akan karuwa¿


Menene wannan yarinyar take dashi da Hayat ya haukace Haka kamar Wanda Bai taba sanin maceba ciki da Bai sai wani rawar jiki da mutuwar zuciya yake akan wannan..


Nafee Bata iya cewa komaiba bayan kukan datakeyi na qunci da tsoro,

Allah yagani tanason Mijinta sosai,


Kuma zuwa wannan lokacin ta fahimci idan namiji yaso aure idonsa ya rufe a auren kaikuma kace baka yardaba karshe naka auren ne zaiyi rawa.,


Da daddare ta samesa Dan suyi magana Amma har lokacin Ransa a matuqar bace yake Bai saukaba..


Abinda takasa ganewa shine ba iya fashin auren yakejiba matakin dasu Idon Nera din zasu dauka na saka qarar ko wani Abu akanta akan abinda tayi din.


***Amal kuwa gabaki daya kashe wayarta tayi sbd ko sunan Hayat din Bata buqatan gani,

Idan Dama baifi qarfin matarsaba Baya iya controlling dinta Kuma ita yayi Mata alkawarin babu inda zasu hadu bare matsala ta biyo baya gashi sunje itada mahaukaciyar kawarta suna son saka Mata ciwon kai tun Bata auresaba.


Sidda ma takaicinta da mamakinta duka yaqare akan yanda matar Hayat din tasamu guts na aikata wanna rainin hankalin da rashin hankali.


Ita dai Amal ta tattara Hayat din da lamarinsa ta watsar tukuna sai idan taji zata iya saurararsa tukuna tasake bi takan maganar neman auren nasa.***Kwana biyu Nafee ta dauka fushinsa da bacin Ransa Mai wucewa ne Amma sai abin ya shallake tinaninta sbd tafiya ma yayi kusan sati daya kafin ya dawo Kuma still babu wani sauyi a yanayinsa.


Tayi kukan,tayi adduar tayi fushin itama Amma duka babu sauki bare sauyi Dan Haka ta tattara makaman yaqinta tafara zubarwa sbd mafita dai Bata samuba sunyi sunyi Amma babu alamar samun mafitar Dan Haka tafara saduda akan lamarin Dan batason rabuwa da Mijinta,


Shikuwa daqyar yasamu ya kwantar da Kai gurin Haj Zainab da uncle Lulu aka janye zancen sukai hakuri saidai baisan ya makomar zancen aurensa yakeba da AMAL amma tunda Haj Zainab da uncle Lulu sun sauko yasan komai yawuce sauran gimbiyar yasamu ta sauko tayi hakuri.Nafee kuwa nuna Masa tayi ta sauko gabaki daya ta hakura da auren nasa da AMAL Amma ta bayan fage itada Bilkees din Basu saki komai dukaba sunata fafutikan yanda zasu samu auren daya fara lalacewa ya qarasa lalacewa afasa gabaki daya.


Dukkanin mafita da hanyar neman lalata auren sun rasa face daya wadda kusan itace suka gwada farko saidai wannan karon babbar Kara zasu saka malaman addini su saka IDON NERA's a kotun musulinci Dan harga Allah barnar dasuke yadawa da koyarwa tayi yawa ga alumma,

Babban gidan karuwan da IDON NERA takedashi a garin yafi wasu makarantin girma nesa ba kusa ba.


Bilkees ce ta bada wannan shawarar Dan harga Allah cikin tsakiyar ranta takejin tsanar duka ahalin IDON NERA shiyasa har lokacin ko hotonsu babu Wanda ta kalla Dan ma kada ta zuciyarta tasake 'daci da kyansu da ake zuzutawa Wanda ya zama na banza tunda ya qare a rayuwar banza da wofi.
****Ajiye wayar hannunta tayi bayan tagama sauraron duka bayanin Barr Salahudeen,


Kallonta uncle Lulu keyi Yana jiran Jin  abinda zata fada.


Numfashi ta sauke ahankali tana qarasa ajiye wayarta gefenta ranta na Dan neman baci tace,


"Qara ce aka Kuma sakani Kuma Wai malaman musulinci a kotun musulinci...


Bansan wannan karon waye zai Kuma yin wannan yunqurin ba,


So nawa Wai akeson ganin bayana da ahalina?

Kusan komai na irin wannan rigingimun sun kwanta Amma Kuma yanzu ko wane me tsaurin Ido da zafin kan ne ya sake Kai sunana???


Uncle Lulu mayar da bayansa yayi ya Jingina da kujerar dayake Kai Yana Dan hade fuska yace,


"Ko waye wannan banajin yasan illar abinda ya aikata,

Me suke nema da wannan familyn ne dako yaushe ake Mana barazana da kotun musulinci.,

Yanzu me su Barr Salahudeen din sukace???


Wani numfashin son watsar da zancen kada ya dameta ta sake kafin tace,


"Zasuyi abinda zasuyi Amma bazani kotun ba idanma malaman sun tsananta ne zanje muyi magana Amma baa kotun ba,,shine abinda Barr yafada.


Amal ce tashigo palon sanyeda Riga da skirt na cotton lace Mara nauyi da ado sosai,

Ba dankwalin kayan a kanta sai qaramin gyalen data daura iya kanta da qaramar bvlgari handbag a hannunta sai key na motarta..


Siddi siddi ce a bayanta suka qaraso tsakiyar palon tareda zama Amal na cewa,


"Uncle barka da yamma.

Mommy Yaya dai Naga fuskanki a yamutse??


Siddi datake maqale kusada mommyn batama lura ba ta dago ta kalleta cikin kulawa tace,


"Mommy All ok right????


Numfashi haj Zainab din ta sauke tana kallon Amal kafin ta kalli Siddi tace,


"Yes baby,

Kan Amal datake kallonta har lokacin ta maida kallonta sbd Ko kadan Amal Bata Wasa da damuwar mummyn Koda mummyn tace babu komai Amal Bata yarda idan taga alamar damuwa ko tunani atareda ita tana ganewa Dan haka take nuna tata damuwar har sai mummyn ta cire komai duk da basuda wata damuwar  sai irin wadda baa rasaba data danganci sanaoi da huldodinsu mummy dashi uncle Lulu din.


Cikin basar da yanayinta dake nuna ciwon kan da ake neman saka Mata da sabon lamarin daya bullo da batasonma su Amal su sani Dan dukkaninsu zafi zasu dauka.


Tana kyakkyawan murmushi Mai Fadi akan fuskarta tace,


"Sweetie babu komai kaman yanda nafada Miki ki Dena kallona Haka Mana.


Dariya siddi tayi tana kallon fararen idanuwan Amal din akan mummy tace,


"Mummy Nan gaba Amal ce zata ringa Miki juyamu duka.


Wani kallo Amal din tayiwa siddi zatayi magana uncle Lulu ya katseta dacewa,


"Karki biyeta sweetie idan na nutsu zuwa gobe idan kin dawo makaranta zanyi magana dake.


Ok Uncle" Amal din tace cikin muryarta me tattarreda rashin rawar Kai ko hayaniya.


Kallon Haj Zainab tayi yace,


Zanyi magana dasu Salahudeen anjima da kaina

Zan sanar dake duk yanda muka Kai qarshen zancen.


Miqewa yayi ya fice daga palon zuwa bagarensa dan yasamu magana dasu Barr cikin nutsuwa tunda acan basa son su Amal su San da zancen zasu kashesa batareda kowama daga familyn ya saniba tunda Daman an Saba ba yauba suke kashe case bataredama ko sunansu an Kuma maimaitawa a idan aka fadesaba.Tashi Amal tayi ta nufe bedroom dinta Kai tsaye bayan ta cewa Bilkisu ta dafa Mata Noodle daya da carrot kawai sai dafaffen kwai.


Tana shiga bedroom din Jakarta da key na mota dake hannunta ta ajiye gaban mirror ta zare kayanta ta nufi toilet tana zare band dake daure da manyan kalban kanta masu tsayi.


Wanka tayo ta fito da bathrobe ash ta nufi gaban mirror ta shirya sharp sharp sbd sallar dake Kanta ta laasar da bataiba sbd fitowarsu lectures kenan ta dawo gida.


Skirt da hijab na sallah ta saka tayi sallah tana idarwa Bata tashiba akai magrib ta miqe tayi tana idarwa tayi adduointa ta miqe tareda zare kayan ta maida closet ta janyo wata doguwar Riga Mata hannu ta saka ta nufi comfortable resting kujeran dake dakin nata ta zauna ta janyo wayarta daketa haske alamar Kira.


Hayat ne me kiran,

Qaramin numfashi ta furzar tareda maida wayar ta ajiye tana miqewa ta fice dakin.


Kitchen ta nufa Dan duba idan an dafa mata abinda tace din sbd batason abinci Mai zafi Sam shiyasa tace a dafa din kafin ta fito ya rage zafi.


Tana shiga ta tadda an dafa Mata din Dan Haka anan kitchen ta zauna kan dan qaramin dining din ciki tanaci tana Dan fira sama sama dasu Bilkisun Dan Dama kusan gidan itace tafi sakewa dasu bayan mummy wadda ta dauki duka masu aikinta kamar 'yayanta ko qannenta tunda a qarqashinta suke.


Siddi ce Sam Bata wani sake musu Amma Kuma bata wulaqantasu,

Uncle Lulu kuwa babi abindama yake hadasa da masu aiki idan ba masu gadi da securities dinsuba na gidan Suma Kuma baya wani zama bare yasan yanda zaiyi treating nasu unfairly barema suna aikinsu yanda ya Kamata Dan Haka Yana musu ma yakeyi duk lokacinda yasamu damar tsayawa dasu din.


Fareedah ce take Dan wulaqanta masu aikin gidan sbd ta taso gidansu basusan darajar masu aikinba Amma Kuma ahankali ta tattara ta Dena itama ta Dena kyararsu sbd anan basa hakan

Tana denawa din itama saitaji ta raba kanta da wahala sbd wani lokacin wahalarda Kai ne da sakawa Kai ciwon Rai faman ihu da wahalarwa ga masu aikin.Karfe bakwai da rabi sukai dinner dinsu gabaki dayansu Kamar yanda suka Saba 

Suna gamawa kowa ya nufi inda yake so 

Wasu sukai dakunansu wasu Kuma palon sama suka nufa Dan acan suke fira iyasu familyn kawai baqi basa zuwar dasu palonsu na sama.


Amal dakinta tanufa sbd tanada abinda zatayi.Uncle Lulu kuwa yayi magana dasu Barr Salahudeen sun basa tabbacin lamarin yazo da Dan tsauri Amma dai zuwa gobe zasu kashe zancen kwata kwata inshallah.


Sanarda IDON NERA yayi tace Gaskia Dole su kashe zancen zuwa gobe Dan har tafiya takeson Yi Amma wanna qarar zata tsaida ita ta Bata Mata lokaci.

#MAMUH#

#PURELOVE#MARRIAGE#

DS AQEEL ASAD#AMAL IDON NERA#

#SISTERS
*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯

Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯

Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*πŸ”₯

No comments

Powered by Blogger.