Idon Naira 23

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*

23

Babbar 'yar SSG Yar kimanin shekaru goma Sha bakwai ce tashigo bedroom din mahaifiyarta riqeda wayarta a hannunta da alama kome nene yakawota dakin mahaifiyarta a Acikin wayar yake sbd yanda ranta yake bace.


Nafeesat dake zaune tana waya da babbar aminyarta Kuma Yar uwarta Bilkees wadda duka duka batafi wata ukuba zuwa hudu da dawowa kasar da Mijinta da yarta sai uwar Mijinta...


Dagowa tayi tana kallon 'Yar tata batareda ta Gama wayar datakeyiba tace,


"Amrah lafiya?

Menene ranki yake a bace haka?


Miqa Mata wayar hannunta dake daukeda kyakkyawan hoton AMAL da kyanta ke bayyanuwa sosai kamar wadda ta hada jini Arab.,tace,


Mummy duba kigani maganar auren daddy da wannan karuwar dangin karuwai da Yan daudu ya tabbata sai yadawa akeyi a social media 

School ma kusan koina zancen suke tunda ansan AMAL din da zafin Kai da  ajin banza tana familyn karuwai.


Zubawa screen din wayar idanuwanta tayi zuciyrta na bugawa da qarfi,

Kyakkyawar fuskar Amal ta zubawa idanuwanta dake Neman qanqancewa da tashin hankali da baqin ciki tareda tafasar zuciya.


Ko tana so ko bataso kamai Hassada da baqin cikinta Akan Amal tasan kyakkyawace Wanda hakan yake qara mata baqin ciki da tsanarta harma da tashin hankali tunda tasan yanda mijinta ya gama Mutuwa akan kyan bayako duba da qazantar karuwanci dake tattareda zuriarsu


Jin shirun nafeesat din yasa bilkes da itama taji abinda Amrah ta fada ta cikin wayar,

A dan hasale tace,


“Nafee meyesa wai kinaji kina gani da ranki da lafiyarki zaki bar Mijinki ya auri karuwa? Karuwar ma wadda tayi Gadon abinta ta uwa da uba da dangin uwa Dana uba tunda kince yayan uwarta ma Dan daudu ne na musamman mai zaman Kansa.,


Wace masifa ce wannan Zaki zauna kina kallo ta shiga rayuwarki?


Kinkuwa San babbar masifar dakika shiga wasa ce idan har wannan Idon Nera da ake fada tashigo gidanki??


Gaskia nafee kinada sake a komai,


Ni Aminyarki karkiji yanda zuciyata ke shiga tashin hankali da tisishi tareda daukan zafi idan na kwantanta halinda kike ciki ma kawai,


Gaskia Nafee banbaki shawarar barin SSG ya auro Yar IDON NERA ba kamar yanda naji sunan koina aka fadesa dai shedar daya ce.


Cikin Jin zafi da qunci Mai tsuma nafee tace,


"Inda ma ace irin karuwan Nan ne qanana marasa galihu da suka tuba zaa rufa musu asiri a aura sai suzo suyita yimaka biyayya......


A qule Aminiyar tata ta katseta da cewa,


"Ba tubabbiyar karuwa ba ko Tubabbiyar malama ce Karki yadda a auro Miki Dan babu gwara fa a kishiya,


Nafee kinji abinda nakeji kuwa ko sunan kishiya aka ambatarwa wani bare ke da kike Taredani,

Nidai gaskia banaji Miki alkhairi a wannan lamarin gwara musan abinyi tunda har barazanar rabuwa dashi kinyi ko gwada yaqi fasawa.


Hawayen baqin ciki da radadin zuciya me suka gangarowa Nafee tana kasa riqesu tace,


"Bilkees Hayat fa ya Gama shallake duk wani tunanina,

Yariga yayi Nisan da sai Allah Amma na tabbatarda Idon Nera Basu barsa Haka ba Dole akwai abinda sukai Masa,

Qarin abin baqin cikin da takaici basa zaman auren fa,

Tana shigowa zata mallaki fiyeda Rabin arzikinsa ta rabu da auren taje ta auri wani Wanda ya fisa a kudi takuma aura,

Auren uwarta Dana 'yar uwarta baya kirguwa fa, yanzu gashi zaa hada da nawa Mijin gurin qirgan auren muguwar zuriar tasu.


Wani zazzafan numfashi Bilkees ta sauke tana sake jinjina lamarin,


Innalillahi wainna ilayhi rajiun,ita Kam duk ranarda nata Mijin yace zaiyi aure Kila bugawa zatayi uwa uba aure irin wannan na SSG din da dangin da kaf babu Mai kunya bare kawaici bariki sai wadda suka manta.....


Inaaaa,Astagfirllh, Astagfirllh, Allah yaci gaba da barmin mijina da kamewarsa da nisancinsa da Mata.


Hawayen Nafee dasuka koma sheshekan kuka yasa Dole suka katse wayar hankalin Bilkees a matuqar tashe da wannan masifar data fara isarta akan wannan Idon Nera din.


Ajiye wayarta tayi tana kokarin tunanin yanda zasu bullowa lamarin,

Dan tsananin kishinta akan nata mijin yasa ko Wanda tasani taji kishiya akansa ta ringa zullumi da damuwa kenan bare Aminyarta guda Kuma Yar uwarta uwanta zaayiwa wannan babban lamarin.


Hameeda dake gefenta zaune tana duba waya ta dakata da duba wayar ta kalli mamar tata cikin Jinjina lamarin itama tace,


"Umme idan Kikaga AMAL IDON NERA din sai hankalinki yafi tashi fa,

Gaskia mummyn dasu Amrah na cikin  babban tashin hankalinda su kadaine zasu iya fadar abinda sukeji,


Hameeda bana buqatan ko ganin hotonta wlh,

Idan bana son Abu to ko inda Zan gansa bana zuwa,

Karki nunan hotonta Dan ko ahakan karkiji tsana da qyanqyamin danake musu bare Nafee da zaa aurowa,

Tana zaman zamanta a kwaso musu jaraba da cutittika da komaima,

Tazo karshe ta haihu yayan Nafee sun hada jini da yayan gidan karuwai fa kenan...ya Salam,wlh Nafee na cikin mummunan Hali,.ya Allah ka lalata wannan auren ka hanasa ka wargaza zancen can taje ta samu wani ta aura badai SSG dinba.


Amin umme fatar kenan,

Can tasamu Wanda zai aureta..


Adduoin fashin auren da gaggawa suka ringa jerowa cikeda tsana Mai tsanani ga sunan IDON NERA din gabaki daya..


Dan kusan kamar sunfi su tsanar lamarin gabaki daya sukeji... musamman Bilkees Jin takeyi kamar ta zama uwar SSG ta tsine Masa idan ya yarda yayi auren.


Ita Kuma mufeeda takaici da tsanar AMAL din tafi ji sbd irin Yanda ake kuranta kyau da ajinta tareda Basarwarta ga maza tana tinkahon Arzkin da suke dashi Wanda yake na qazantama...


Ta gogewa Allah takuma ta gode Masa da yasa daddy dinta kwata kwata baya sabgar da zata hadasa ko huldan business ko aiki da masu irin wannan qazantacciyar rayuwar mai abin qyama sbd batasan Yaya zatayi da rayuwartaba idan akace itace daddynta zai aura AMAL din wadda so daya ta taba ganinta Amma taji Sam Bata kaunarta sbd ta tarwatsa gidan uncle SSG dinsu.




*****AMAL tunda ta aminta da auren na SSG duk da ba lokacin zaayiba Amma tini momynsu tafara gyaranta ahankali ahankali shikuwa yasake bude musu kofar aljihunsa..


Har alokacin Amal Bata wani doguwar soyayya dashi Amma ba kamar dah ba yanzu Yana Dan samun kanta.


Siddi kuwa yafe komawa Abuja tayi Kiri Kiri saidai Sweetheart din nata yakoma shine yake zuwa akai akai sbd shima ba qaramar mutuwa yayi akan Yar babyn tasa ba bare Daman Acikin mugayen shaidar da akaiwa IDON NERA shin duk Wanda ya aura 'yayanta saidai iyalansa su yafesa.


Tako Ina gyara da tsimin yarta takeyi Haj Zainab sbd Koda lokacin auren zaizo basa buqatan wani dogon gyara 

Koba komai tsimin ahankali ahankali yafi shigar mace maimakon na sai gabanin auren Sam wannan baya wani aikin dazai dauki lokaci mai Nisan tsayi ajiki.



Kasancewar AMAL din bamai son wainnan abubuwanba sai suka taqaita aka rage Amma dai still kullum sake rikida takeyi tana qara Kyau da kyan fata,


Dama AMAL komai nata Mai aji ne Koba yanzu ba fatarta lafiyayya ce sbd hutu da tsadaddun natural body products datake amfani dasu.




******Ta bangaren familyn SSG kuwa komai ya qarasa rikicewa matarsa da Aminiyarta Yar uwarta Bilkees wadda kusan ta fita shiga tashin hankali da damuwar wannan halin datake ciki,


Auren sai qara tabbata yakeyi sbd kudin auren da ake Shirin Kaiwa miliyoyan kudi uncle Lulu da baya qasar kawai ake jiran dawowarsa akawo kudin.


Tashin hankali akayi sosai tsakanin Nafee da SSG akan kudin dataji zaa kai na tambaya.


Da farko da Kansa ya Bata zabin kota zauna ta hakura kokuma ta tafiyarta Idan bazata iyaba yabata Dama.


Wannan kalmar tasa ta kawo mummunan tashin hankali a tsakaninsu sabo harta tattara kayanta da 'yayanta uku ta tafiyarta gidan iyayenta.



Hankali tashe Bilkees ya sameta gidan  jikinta a mace.


Kamar zaman makoki ta tadda gidan sunayi sbd mahaifin Nafee din baya Nan yayi tafiya mahaifiyarta Kuma lamarin yafi karfinta sbd tasan bazasu taba iya Hana Hayat aureba to Amma Kuma abin baikai ya Koro nafeesat din gida ba.


Amrah kuwa tayi kuka sosai har idanuwanta sun kumbura sbd bazata taba kaunar iyayenta su rabu ba har abada,


AMAL IDON NERA ta zamar musu masifa da balain da zai tarwatsa gidansu su rabe tun iyayenta sunada sauran kuruciya a auren nasu.


Cikin tashin hankali da firgici Bilkees tace,


"Wannan balain tun Bata shigoba kenan,

Idan sun shigo sai Yaya kenan?

Ki dubi yanda ta rabo yara da gidan ubansu tana neman raba musu uwa da uba 

Ji Amrah yanda duk ta fice hayyacinta sbd kukan baqin ciki.


Anya kuwa DR SHAYKH yasan wannan danyan hukuncin na SSG kuwa??


"Umme gaskia banajin Daddy ya sani da bazai Bari komai yayi nisa hakaba ki fada Masa Dan Allah yayi wani abin cikin gaggawa nidai wlh banason uncle din ya auri wannan AMAL din Sam Sam rayuwarsu babu abinda yake ciki sai qazanta da datti.


Nafee ce ta Hana a sanarwa Babban Aminin Hayat din wato DR SHAYKH mijin Bilkees sbd Bama zai iya shiga zancen wainnan qazaman karuwanba..


Ita kanta Bilkees Dama fadane kawai tayi Amma bazata taba barin ko sunan IDON NERA yashiga kunnensaba Mai tsafta bare ya saka bakinsa harma ya iya ambatar sunan.


Har kusan dare a gidan kafin su balkees suka tafi gida sbd Nafee na cikin mummunan halinda yasa duka jikinsu yayi sanyi Matika.


Bayan isarsu gida tsaban basa cikin dadin zuciya daga ita har Yar tata mufeeda babu Wanda ya iya shiga gurin umma ya gaidata Kai tsaye part dinsu suka nufa zuciya da Rai a cunkushe.


Washe gari hakama kota bangaren umman Basu bi ba suka fice gidan zuwa gidansu Nafee sbd Amrah data kwana da zazzabi Mai karfi hardasu amai so Acikin daren suka nufa asibiti fa ita.


Ayanda ta tadda Nafee da Amrah sun jangwame a asibiti kamar wainda sukayo hijira sbd damuwar dake zukatansu take Bilkees ta kwatanto hakan akanta da mafeeda take tafara jero istigfar tana girgiza kai da sauri tana cewa ba akainaba"cikin ranta.


Mufeeda ma Jin tayi Ina bazata iya dauka ba...


SSG din shima tunda safen ya iso asibitin cikeda kulawa da damuwa da Yana tsananin so da kaunar yayansa harma da ita kanta Nafee din Amma dai son Amal IDON NERA Yana Ransa daram guri na musamman.


Ya Jima a asibitin kafin yatafi sbd babu fuska ko kadan daga Nafee din,

Itama Bilkees kasa sake Masa tayi Kamar dah sbd harga Allah mutuncinsa ya zube Mata kwata kwata mutiqar ya auri wannan IDON NERA din.


Bayan tafiyarsa aka sallamesu suna kokarin shiga mota saiga motar gidan SSG din tashigo asibitin.


Shine da Kansa ya dawo asibitin batareda driver ba da Kansa yake Jan motar babu Wasa a fuskarsa yace Amrah ta shigo su tafi.


Cikowa idanuwan Amrah din sukayi da hawaye ta kalli mahaifiyarta zatayi magana Dad din ya sake cewa tashigo motar cikin Dan babban sauti Mai girma.


Motar ta nufa ta shiga jiki a mace tana hawaye Dan kamar rabata da mahaifiyarta ne zaayi tunda tasan gida zai tafi da ita.


Suna kallo ya dauki yarsa yabar asibitin yabarsu tsaye cikin zallar mamaki da sanyin jikin komai na sake daukan dumi kenan.


Gidansu Nafee suka Isa suka tadda acan dinma ya Aika driver ya dauki qannan Amrah din an tafi dasu gida..


Ta tabbata kenan auren Nafee da SSG rawa yakeyi a karo na biyu duk akan wannan lamarin.


Yau Kam ita kanta Bilkees din da wuri suka tafi sbd Nafeen dake cikin mummunan yanayi ayau din na 'yayanta da SSG ya karbe kenan baida niyar janyewa.

##MAMUH#



*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.