Idon Naira 20

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*

20

Rayuwarsu a Lagos da gwagwarmaya da wahala suka Kai matsayinda suke a yanzu,


Mutane babu ruwansu da wahalarka,.da zufanka, da gwagwarmayarka, da dararrakun baqin cikinka Amma daga ranar da aka gano kuskure daya atareda Kai zaa fassaraka,zaa bika da zantukan gaskia da sabaninsu,hakam zaa bika da tsinuwa da kalamai maka mantansu,....


Daga ranar da aka haifi siddi ta gano hakan Kuma taji hakan daga gurin  'yar uwarta, jininta Dan Haka duk abinda duniya zata kirata dashi kokuma ake kiranta dashi Bata damuba sbd ko tace aa babu me shedarta......


Kowa Yana aikata kalar nasa laifi ko sabo tsakaninsa da ubangijinsa ne

Dan Haka itama wannan shine nata laifin,


Ta zabi aurarrakin datakeyi ne akan karuwanci Wanda mutane suka kasa rabasa da karuwancin sbd abinda takeyi din karuwan ma sunason samun damar Yi Amma Basu samu ba Dan basuda kamar hajiya Lulu Wanda shine sanin manyan gwamnati na gida Dana waje....


'yayanta tuni akai musu tambari da sunan shegu basuda uba Dan babu wadda akasan ubanta acikinsu,


Taji ta gani takuma dauka saidai Kuma nerarta na sake zaunuwa Ana mantawa da yayanta shegu ne kamar yanda ake fada...


Ta badawa yaranta gata da Jin dadin da duk wani Mai uwa da uba zai nema,.


Rayuwar yayan hutu da gata sukeyi tareda abinda ransu yakeso sbd mahaifiyarsu da yayar mahaifiyar tasu Haj Lulu sun tsaya musu yanda ransu yakeso...


Karuwai mutanensu ne haryanxu akwai Amana tsakaninsu dasu Dan kuwa sune mutanen dasuka karbeta alokacinda batada kowa batada komai batada gurin zuwa,


Allah shine gatanta Kuma shine ya qaddara yankewar wahalarta acikinsu dan haka duk inda suke Bata qyamarsu tana musu kallon nata me shiyasa ta zama tamkar uwar karuwai a garin lagos,.itada Lulu sun sun tsaya musu sun zama gatansu,...


Babbar qungiyar karuwai Mai zaman kanta akeda a garin Mai sunanta,


Lafiyayyun tsayayyun manyan Mata da Yan mata ne dasuka Sanku suka amsa sunayen Mata Kuma sukeda manyan connections a qungiyar,


A garin duk wata babbar Mai zaman kanta Yar arewa harma daba Yan arewan ba a kungiya suke duk da kowacce tanada gidan kanta da ikon kanta Amma suna tsayawa junansu,


IDON NERA ta tsaya musu,

Tasan manya,

Tayi auren manya,

Tana hulda sosai dasu

Dan Haka duk Wanda yake qarqashinta baya wulaqantuwa a hannun hukuma sbd wannan wani ciwo ne dake ranta da bazaso kowace mace ta wulaqanta a hannun hukuma ba sbd tashiga taji daci da ciwon hakan Kuma har abada bazai fita ranta ba.Duk arzikin dasukai Basu taba raba gida ba da Dan uwanta,Rabin jikinta Lulu saidai kowa da babban sashensa Amma tare suke zama dining gabaki dayansu cin abinci as a lovely and happy family...


Babban quality din dasuke dashi a rayuwarsu shine suna tsananin so da kaunar juna tareda tattala juna,,,,,wannan din itace ta tsaya ta saka musu wannan aqidar sbd har abada bazata so 'yayanta su dandani kowane bangare na rayuwar data dandaba.


A yanzu datake Haj Zainab IDON NERA baya ita da Lulu babu wanda ya taba sanin ba itace ta haifi ba,

Haka daga AMAL har siddin basusan ba uwa daya uba daya sukeba kamar yanda babu Wanda yasan da IDON NERA din da Lulu ba uwa daya uba daya sukeba,...IDON NERA shine Kamar family name dinsu kokuma ace Surname dinsu sbd kaf dinsu da Idon NERA suke amfani a komai nasu idan aka cire AMAL da ita kadaice takeda qarin sunan sanda Acikin nata sunan....


Passports, credentials da komai nasu Surname dinsu shine IDON NERA,


Da wannan sunan duniya tasansu,

Ta San arzikinsu,

Ta San su din asalin hamshaqan uwayen karuwai ne masu zaman kansu ne....


Yawanci tafiye tafiyenta qasashe da yayanta takeyi duk da karatu sukeyi Amma yayanta sune sanyin idaniyarta Bata cika tafiya ba taredasuba..
******Haj Zainab IDON NERA a yanzu hamshaqiyar kanta ce datake da abin kanta taci ta tada wuya a Jin Dadi da arzki bakuma wai an Dena abinda aka Saba din bane saidai aji da komai ke qarawa da girma....


Kyakkyawa ce duk da zamanta babbar mace Amma har lokacin fes take qyam Kamar babar yayarsu AMAL ba mahaifiyarsuba Dan Haka take zuba lokacinda Acikin manyan mutane,


Baya bayan Nan wani hamshaqin balaraben Sudan ta aura shi nasa auren ya Dade tunda tayi shekara biyu dashi a Kuwait zaune kafin suka rabu inda arzikin data samu agunsa ya kere na Koda yaushe take gabaki daya tagama miqawa ta wuce sanin wasuma daga cikin manyan mutanen dasuka santa,Babban abinda yake qara kusancinta da manyan hamshaqan masu dollar shine duka manyan Matan dasuke taredasu a qarqashinta suke,.


Itace take toshe duk wata hanyar da zaasan suna neman Mata sbd kada mutuncinsu ya zube,


Itace sirrinsu na boyewa ko toshe musu duk wata matsalar da zata taso data danganci bacin suna Haka Kuma itama Bata barin Ana cin zarafi ko tozarta duk wata macen Dan ana Mata kallon karuwa Dan Haka sai takeda connections tako Ina da matsala zata bullo.


Yayanta sun girma sun zama Yan Mata masu tsananin farin jini ga manyan mutane sbd kyau da ajinsu tareda gatan dasuke dashi koina 

Sbd itama ta zama babbar mace Mai arziki kusan da Dama wasu na yiwa yayansu shaawarsu wasu Kuma kansu Kuma bawai qananun mutane ha manyan masu NERA a hannu..


Tanada kyakkyawan buri akan yayanta da Haka Bata taba shaawar aurar dasu Dan kudi ba tunda kudin ba matsalarta bane akwaisu ba adadi,


So take yayan nata su tsayu a karatunsu su tsayawa kansu kafin Auren ya biyo baya duk da hakan batajin zata aurar da yayanta inda baa gane yaren NERA,


Yayanta insha Allah tana musu fatar rayuwar arziki da yayansu ma,


Zuriarta gabaki daya ayanzu Bata fatar tayi talauci Dan Haka takeda buri da fata akan yayanta tareda gatan Allah bless a cika Mata wannan burin.


Daga AMAL har siddi sun San basuda uba,

Idanma sunadashi to Basu taba tambaya ba sbd umman Bata bada fuska ba hakama sun bar kowane irin sirri momynsu ta boye Akan asalinsu da Bata taba fadaba,,,,


Uwarsu da yayan uwar tasu sun tsaya musu a komai Dan Haka basuda wata damuwar Dan ance basuda uba to bai damesuba sbd suna taka duk rayuwar dasuke so Wanda masu uban ma basa takawa..Lulu IDON NERA ahakan Zainab IDON NERA ta takura Masa yayi aurenda baiyi niyaba sbd wata Yar tsohon daya daga cikin Mazanta ta maqale tana son lulun....


Mahaifinta Mai kudin gaske ne Kuma itace kadai yarsa dayakeda Amma ta nace lulun takeso duk da ya kusan haihuwarta.....


Su Kuma duk inda yaren NERA yake suna ganewa Dan Haka IDON NERA ta amincewa auren Wanda aka zubarda dukiya aka Kuma kafa tarihin daya qara daukaka sunan familyn IDON NERA...


Shogowar Fareedah jarma familyn nasu yasa suka zama kamar family daya da mahaifin nata tsohon senator Dan Haka sai suka sake bajewa musamman itama Fareedah kamar su din take wayayyar kanta ce kanta a sake yake sosai..


Dukkaninsu a qatoton baban gidansu dake ikeja GRA suke zaune Dan sun saba basa rabuwa,


Zuwan Fareedah cikinsu itama ahankali aqidarsu da halinsu na tsananin kaunar juna ya shigeta sai itama ta sake zama cikakkiyar IDON NERA family....*******AMAL IDON NERA halayenta sun banbanta Dana Yar uwarta siddi IDON NERA,


AMAL Bata dauko halayen mahaifiyarta ko Mahaifinta ba sbd ita matashiyar budurwace mara daukan Reni ko kadan shiyasa Bata hulda da mutane sosai,

Bata shiga sabgar da Bata shafetaba sbd Bata daukan renin kowa,

Tanada wani irin kyau da kyan jiki Mai daukan hankali sbd hasken fatarta da hutu da Jin dadi tareda zaunawar NERA suka nuna akoina tareda ita...


Ita mace ce Mai ado da gayu duk da Bata kwalliya Amma komai nata a tsari da burgewa tareda wayewa yake tafiya irin asalin yayan gata masu abun duniya...


AMAL IDON NERA batada raayi ko shaawar soyayya ko aure da wuri sbd Boko da wayewar dasukai tashigeta sosai hakama Bata shakkar fadawa duk Wanda ya takata magana,


Akwai manyan mutane masu kudi dasuke budewa Haj Zainab bakin aljihun NERA sbd shaawar auren yayanta musamman AMAL da itace Allah yasa batada raayin auren yanzu Kuma auren ma da wainda suka kusan haihuwarta,


A raayinta Bata taba shaawar auren Mai Mata ko Wanda ya kusan haihuwarta kokuma yahaifeta,

A taqaice idan zatayi tanada raayin sabon jini ne irinta ko tsaranta ma wannan shine raayinta da kowa yasanta dashi.....


Dukkanin halayenta na rashin daukan Reni da fadar magana ba tsoro kusan halayen Lulu ne ta dauko kamar shi din jininta ne da gaske....******siddi IDON NERA kuwa ta kasance complete opposite din AMAL sbd ita tayo gadon mahaifiyarsu ne na raayin auren masu kudin duniya idan sun Kai nawa,

Bata taba shaawar auren saurayi ko Wanda bai Isa haihuwarta ba,


Itama kyakkyawa ce sosai gashi tafi AMAL din cika sosai sbd yanayin jiki datafi AMAL,


Tata wayewar da gayun na kwalliya da qyale qyale ne

Hakama ita batayi fadan AMAL ba tana hulda da mutane yayan manya wainda suke daidai matsayinsu musamman dayake tafi AMAL din yawo duk da AMAL dinma ba bayana gurin yawo da zuba rayuwa.....


Siddi tun suna jamia 200level ta nacewa aure zatayi sbd wani gawurtaccen tsohon Ambassador daya nema aurenta agun Haj Zainab. 


Kudi yake sakarwa familyn kamar baisan zafinsuba 

Kudi Kuma ba qanana ba...


Kai tsaye Siddi ta nacewa momynsu akan aurensa Dole aka samu daqyar takai 300 level akai auren Wanda shima akaci uwar NERA ta watsar da karatun tabi Mijinta sukai Cyprus.


Auren siddi yasa AMAL komawa kamar ita kadaice Yar IDON NERA tunda Takoma ita kadaice 'ya a familyn sai Anty Fareedah da Allah yayi Uncle lulunsu zai haihu.


AMAL lokacinta take bugu dakya yanda ya Kamata sbd irin motocin datake Hawa da sitirar datake duka masu tsada,


Komai nata na musamman ne a rayuwarta,

A tsari take komai nata,


Suna tayi sosai kamar yanda mahaifiyarta tayi,...


Suna ne da ake fassarashi da sunyisa ne sbd suna tareda manya,

Su din yayan uwar karuwai ne,

Su din IDON NERA ne babu abinda suke ganewa fiyeda NERA,


Duk dukiyar da suka Tara Bata isarsu kullum qari suke nema,


Auren mahaifiyarsu baya qirguwa kamar yanda na Yar uwarta Siddi yafara qirguwa Dan kuwa ta rabu da Mijinta ta sake auren wani Wanda yaci ubansa a maiqo...


Dukkaninsu duk wainnan maganganun da ake binsu dasu Bai taba damunsuba sbd sundan daukakarsu ce da sunan dasukai a duniya yazo da hakan...


Shiyasa suke zuba rayuwarsu yanda suke so su taka yanda sukeso babu Wanda ya Isa ya tanka musu...Zainab da Lulu sunyi rayuwar garari da qunci a garin Lagos kafin zuwansu nan dasuke yanzu,


Sunyi kwanan bola,

Sunyi na gangayen gida,

Sunyi na shaguna,

Sunyi na qarqashin gada,

Sunyi yawo a garin Lagos da Yaya goye a bayansu,

Shi AMAL ita siddi,


Har kamensu antaba Yi Amma baa taimakesuba,

Sunyi kuka atare, sunyi a bacci, sunyi a farke,


Arzikinsu ba a lokaci daya suka yisaba,


Shekaru suka debo masu nauyi da wahala da qunci masu yawa kafin sukayisa Dan Haka basuda daukan Renin dazaisa a iya tozartasu a dare daye ko rana daya komai nasu da yardar Allah sunyi gaba ranakun kuka da damuwa tini suka shude musu

Kuma gashi komai ya wuce yanzu Dan Haka babu wani malami dazai kirasu yayi musu waazi Kai tsaye su fahimcesa....sbd malaman ne yanzu suketa kutsen rayuwarta suna kokarin dawo da ita hanya dan girmamar da bariki tayi ta yayan musulmai hausawa a qarqashinta lamarin yanata ciwa manya malaman addinin dake can tuwo a kwarya...


Anyi kamen,

Anyi nasihar,.anyi baraza Amma babu sauki ko nasara sbd hukumar dake tareda manya,

Manyan Kuma tare suke da Haj Zainab din Dan Haka suketa kokarin ganin ta inda zasu bullowa lamarin Dan Haj Zainab IDON NERA din Koda suke malamai Bata gane yaren nasu tunda basuda nerar dazata bude kanta ta fahimcesu.


Ta bangaren Mata da karuwai da ake magana kuwa bayan maganar Haj Zainab din su kansu basa gane komai..

Duk da kusan karuwai da Matan set set ne wasu duk ta aurar dasu ga manyan mutane sunacan suna rayuwar aurensu hankali kwance cikin aminci shiyasa dai kota Ina tanada connection dinta yanda takeso...

Wannan shine Asalin wacece Haj Zainab IDON NERA da ahalinta datake so da kauna fiyeda komai data mallaka wato,

'yarta jininta AMAL IDON NERA da 'yarta 'daya SIDDI IDON NERA

Sai 'dan uwanta Rabin jikinta LULU IDON NERA da matarsa Fareedah jarma IDON NERA da sabon farin cikin gidan da aka haifo Fahat IDON NERA.

##MAMUH#

#AMAL IDON NERA

#LOVE/MARRIAGE/ROMANCE
*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯

Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯

Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*πŸ”₯

No comments

Powered by Blogger.