Idon Naira 19

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*

19

Duk wata alamar kulawa Ds ya nunawa zainab sbd Zainab din yanzu daban take da zainab din dah kwata kwata,


Ta wanke tafito fes da ita duk da gwagwarmayar datakeyi Amma tana cikin rufin asiri sosai.,


AMAL da Siddi suna cikin lafiyayyar kulawa da kaunar mahaifiyar tasu,


Ta tsaya musu a komai babu abinda suka nema yafi karfinsu,

Komai nasu iri daya take siya musu babu wani bambamci saidai babbancin kala sbd fatarsu ba daya ba, AMAL tafi siddi haske itakuma siddi tafita kaurin jiki..


Zuwa wannan lokacin kusan kowa ya manta da siddi ba zainab ce ta haifeta ba wainda ma basusan asalin waye mahaifiyar siddin ba sunfi yawa..


AMAL tana primary ita Kuma siddi tana nursery akai rikicin wata yarinya Qarama a anguwa da aka lalata abun babu Dadin ji da gani,


 Zainab taji hankalinta yayi matuqar tashi akan yayanta,


A duniya yanzu data bude Ido tasan kanta da yanci to mutuncin 'yayanta shine abinda kawai yake Bata tsoro da girgizata,

Bata kaunar ko sunan fyade taji sbd Su Amal dinta,

Sbd sune taji zama acikin gidan da anguwar yane neman ficewa a ranta sbd tako Ina anguwar 'yan duniya da mutanen banza ne aciki uwa uba gidan nasu dasuke ciki duk da dokar Lulu na Nan Bata Bari ta lalaceba saima qarfi jajircewa datayi ta qarawa dokar karfi sbd 'yaya matane da ita.Alhaji Bulama wani Dan kasuwa Kuma Dan siyasa shine ya nacewa buqatarta amma Sam taqi basa damar suyi lalata shiyasa yake sakar Mata kudi sosai Dan kawai ya samu sauya raayinta ta bashi Dama su huta..


A yanda ta Gama karance Shi tsaf ba sonta yakeyiba shaawarta yakeyi Mai tsanani itama Bata taba jin alamar zata so kowane namijin ba saidai shima tsabar nacinsa taqi yarda saiya bullo Mata da maganar aure...


Batayi mamaki ba hakama Bata Musawa aurenba Dan tana buqatan dauke 'yayanta daga gidan.Auren akayi ta tare Dan babban gidansa dake kusada anguwar tasu take ta bude sabuwar rayuwa,


Bude hannuwanta tayi ta ringa qwaqwalar kudi a gurin alhaji Bulaman ba sassauci sbd tagama sani da gano auren shaawa yayi Mata Kuma Yana Gama cire shaawarsa sallamarta zaiyi Dan Haka itama ta rufe idonta ta ringa amsar kudade a hannunsa kafin tabari yai yanda yakeso da ita din.


Mugun zama sukayi na tsawon wata hudu kafin ya sakota,


Tasan zaayi hakan tunda ta gane manufar aurensa Dan Haka Bata damuba ta tattaro yayanta suka dawo gida bayan tasa anyiwa gidan babban gyara tareda fadada shi yakoma tamkar sabo Dan Haka kudin gidan ta qaru ga kowa.Aurenta gidan Alhaji Bulama yasa idanuwanta suka sake budewa tas,


Tasake wankewa tas itama,


Daga ita har yayanta sun canja sunyi kyau da qarin lafiya abunsu,


Jikinta Mai kyau ne sbd batada qiba ko sakakken jiki Dan Haka saitayi fes fes abinta Kamar ba itace da yayan gabantab.


Ana cikin hakan babban tsautsayin Datafi tsoro a rayuwarta yaso afkawa siddinta Wato 'dan DS daya kusa lalata Mata ita,..


Maigadin gidan ne yaja siddin yakaiwa Suraj din sai gashi Allah yasa anga shigar siddin gidan akazo aka sanar Mata

Hankali tashe jiki na rawa ta Isa.Mummunan gani tayi alokacinda ta taradda siddinta tsaye gaban Suraj harya zare Mata wando....


Sumewa take neman Yi agurin saidai karfin da tafarfasar zuciyarta ya riqeta 

Jikinta na wani irin rawa ta qarasa da gudu ta fizgota daga gabansa Bata tsaya komaiba ta sauke Masa wasu irin mugayen marirrika guda biyar a jere kafin ta fidda wayarta ta dauki hotunansa..


Jikinta babu inda Baya rawa tace,


"Wannan shine karo na qarshe da wani daga zuriar DS ma zai Kuma kullon mace bare lalata,

Alqawarine wannan nayi muku da yardar Allah.


Juyawa tai da yarta zata fito ya biyota da sauri shima jikinsa na rawa yafara rokonta akan zai Bata ko nawane kada zancen ya fita 

Ko mahaifinsa bayason yaji sbd zai iya komai idan yaji ya aikata abinda zai taba Masa mutuncinsa da muqaminsa...


Maigadin na ganin hakan yasan wasa ya 'baci Dan Haka ya miqe da sauri zai nufota 

A haukace tadauki sandarsa ta gora ta ringa dukansa ta koina tana musu ihu tana Kiran jamaa 


Kafin kace me gidan yacika da mutane 

Ta rufe Ido tanata ihu da neman daukin sun lalata Mata yarinya...


Dayake DS ya Jima da barin gidan 'dan nasa ne kawai aciki Yana aikata Barnarsa kala kala da Yan Mata da shaye shaye

Shikuma DS din da matarsa da sauran yaransa Mata da wancan Dan nasa daya da Lulu ya illata sun koma babban makeken gidansa dayafi wannan din so da Dama,


Kuma Daman sbd ya ringa lura dame basa barazana wato Lulu yasa ya zauna a anguwar 

To yanzu daya Gama da matsalar lulun saiya tashi daga anguwar Dama ba mutuncinsa bane zama anan din.Wani irin mummunan duka zainab tayiwa maigadin dashi Kansa Suraj Wanda yasa Dole akai Kiran hukuma tazo ta kwashesu 

Itama tayi hakan ne Dan case din ya zama babba.


Ana zuwa gurin hukuma babu Bata lokaci yan anguwa suka bada shaidar abinda zainab ta fada 

Aka Kai yarinyar asibiti aka duba bai Kai ga yimata fyaden ba Amma dai hukunci yahau kansu dagashi har maigadi gashi dukansu suna asibitin sbd Shi maigadi har haqorinsa hudu ya rasa dan harda Yan anguwar aka taru aka rufar musu da shegen duka Mai muni.


Zance yanata yaduwa a duniya da social media take hankalin DS ya tashi yayi duk yanda zaiyi Amma zancen yariga ya yadu mutane idanma baayi adalciba zainab a shirye take da Kai zancen sama inda komai zai sake lalace masa..


Matar DS ta samu zainab har gidanta ta fada Mata maganganu masu daci da tozarci,


Takirata da karuwa,

Mai 'yaya shegu Dan Haka kome akai musu ai ba fyade bane tunda sanaar uwarsu ce,

Ta kirata da Mara asali Kuma zuriar Yan daudu...


Tayi kukan data manta Yaya akeyin kukan ma sai aranar, saidai Kuma aikine ya tashi Dan kuwa qudurinta akansu ma sauyawa yayi,


Ds yayita nemanta a sirrance akan tajanye case din taqi sai shima ya bullo Mata da maganar aure Dan yayi amfani da damar su janye case din sbd yazama babba lamarin.


Kamar yanda ko yanzu tasan cewan auren manufa ne zaiyi da ita itama saita sakawa ranta hukuntasu da manufar tasa.


Amincewa aurensa tayi sai gashi cikin  qanqanin lokaci akayi auren 

Aka Kuma yada cewan sbd karamcinsa ya aure matarda 'dansa ya lalatawa 'ya shine abinda zaiyi ya kare mutuncin yarinyar da aka so lalatawar.


Hakan yasa mutuncinsa ya ringa qaruwa a idon mutane sai hakan ya ringa Masa Dadi musamman da zainab din ta fito ta nunawa duniya irin kulawa da kaunar dayake Mata itada 'yayanta...


Aikuwa hakan datake nunawa yasa DS sake mutuwa akanta da yayanta,


Matarsa Haj sadiya hankalinta mummunan tashi yayi ganin DS gabaki daya ya koma wani iri agun zainab,

Ga Suraj din har lokacin Yana gidan yari zainab taqi ma yarda DS ya tasa zancen,

Cikin salon daukar hankali ta nuna Masa abar Suraj din acan sai bayan zabe sai a fiddosa gudun yadawo ya lalata Masa komai tunda yanajin haushin an aureta din.


Aikuwa hakan akayi ds yabar maganar Suraj din akan sai angama zabe....


Sabuwar rayuwa zainab ta bude a gidan uban siddi batareda kowa yasan siddin DS ne ubantaba,


Kudi da Jin dadin rayuwa suke ja tako Ina hakama duk wani tattalin arzikinsa tanata janyewa tana tanadarwa 'yarta siddi Dan kuwa tayi alqawarin duk sai sunbiya abinda sukaiwa Lulu da marigayya siddi.


Koda aurenta da Ds yayi watanni Tara tagama tarwatsa gidansa Dan kuwa hatta matarsa Saida sukayi rabuwar kotu inda tun anan mutunsa yafara zubewa mutane,


Dan kuwa Haj sadiya cikin bacin Rai tonan asiri tai Masa Wanda zainab tayi amfani da hakan aka tada case din Lulu.


Tada case din Lulu yasa hankalin ds tashi haka zainab tasa ya ringa sakin kudi koina yanaso a sake rufe case din Amma baisaniba hakan yasake badashi da kuwa duka kudaden dayake badawa a banza suke tafiya....


Qanqanin lokaci rayuwarsa da iyalinsa tagama wargajewa 

Akai zaben Kuma bai ci aikuwa qaramar hauka ta taso Masa gadan gadan.....


Bai qarasa Aron haukaba sai ranarda zainab tayi winning case din Lulu akansa sai gashi Lulu ya fito.....


Qarar qarshe data kusan buga zuciyar DS itace qarar yayiwa siddi fyade hartasamu cikin yarta ta rasu gurin haihuwa.....


Binciken asibiti da kotu ta bayar ya tabbatarda siddi yarsa ce Dan Haka aka yanke Masa hukuncin bin dansa gidan yari shima.


Dukiya Mai tarin yawa tasamu daga da aurensa Dan Haka fitowar Lulu ta sauya musu rayuwa gabaki daya...


Lulu yai kukan ganinta tare dana mutuwar siddi,


Daga Shi har ita zaman anguwar data garin fita kansu yayi gabaki daya sbd a rayuwa bayan Rashi da baqin ciki Basu San komaiba....


Amma a yanzu dasuke da 'yaya gabansu bazasu sake barin quncin kowa ya illata rayuwarsu data 'yayansuba.


Qaton gidan DS dayake kusa dasu tuni ya mallaka Mata Shi da Ana zaman Dadi kafin ta fara tarwatsashi Dan Haka gidan Mahaifinta ya dawo Mata.


Da gidan da gidan Lulu suka hade tareda maidasa wani irin babban gida da shaguna a waje suka zuba yan haya....


Mutuwar aurenta da Ds babu abinda yaja Mata sa suna da farin jinin manya Dan Haka cikin qanqanin lokacin takuma wani auren sadai shima baifi watanni huduba suka rabu Wanda Shi yamafi ds din arzki Wanda ta aura daga bayan..


Yawan aurace auracenta yasa Ake Mata kirari da IDON NERA,


sunan yafara binta ne tun anan kafin suka tattara sukabar garin sanadiyar wani Mai kudin data aura ya kaita Lagos...


Zuwansu Lagos da wata shida shima auren ya lalace daganan sai Bata dawoba Lulu ya sameta acan suka bude babin wata baudaddiyar rayuwar zaman Kai da budewar ido....


Kamar yanda akace zaman gidan yari qarin course,,,to hakan ne ga Lulu sbd yanzu daya fitone yake asalin hamshaqin tantirin Kansa bare sun dawo Lagos sun sake zama fitsararru..


Gidan kansu ne dasu na masaukin duk wata Yar barikin data rasa gurin zama to suna tallafa Mata sbd sabo da zama da karuwai da sukai tun acan dasuma gararin dasukai anan karuwan ne suka karbesu da mutunci sai basa iya ganinsu Acikin garari....


Da farko Suma Lagos din sunsha tsananin wuya da garari kafin suka gane kanta suka fara gwagwarmaya da Fadi tashi Dan duk arzikinsu da zainab ta Tara Saida ya qare musu a yawon Haya da wahalhalu a garin kafin da Lulu yaga ta kwabe masu suna neman wulaqanta kudin cin abinci ma na neman gagarsu ya tsunduma harkar dillanci Mata da alhazai shine fa suka fara daidaita...


A wani babba gidan karuwai suke zaune wanda ya hada mutane sama da 40,


A gidan kowa karuwanci sukeyi shine sanaarsu,

Ita Kuma zainab auren masu kudi shine nata,

Suna nan suna karuwancin Basu Tara komaiba ita Kuma a aure biyu ta Tara wani irin arziki suka tattara suka koma sabon gidansu itada Lulu dasu Amal sai sabuwar Mai aikin datayi....


Sunan IDON NERA yayi sunane a aure auren manyan data ringa Yi a garin Wanda yaja Mata attention din mutane sbd zuwa lokacin manyan gaske take aura,


Asalinta da kowa ya sani shine karuwanci Wanda har lokacin Bata taba jin shaawa ko tunanin tsayawa ko so daya tace ita ba karuwar bace,

Duk Wanda yaji ya fahimta ita karuwa ce to aje hakan Dan kuwa tai Nisan da saidai a fada a iya inda kake badai a fili ba.


Business sukeyi sosai Wanda shima ya karbu Kuma sunanta yasake habbaka sunan kasuwancin nasu,


Ta goge,

Ta sauya,

Takoma kamar ba uwar Yan Matan dasuka fara girma ba a gabanta,


Ta rufe idonta batajin komai Bata gane kowane yare saina NERA,


Shi kansa lulu baka ganesa Dan kuwa yakoma hamshaqin Dan daudunsa mai hulda da manya 

Dan kuwa shine asalin wanda yake kutsawa ya shiga ya fita ya samo Masu rumbun nerar da zainab ke aurewa.


Babbar kaunar dake tsakaninsu da karuwai baya sauyaba tana Nan dan haka gida garesu na musamman dasuke bawa karuwanda basuda mafita gurin zama wasu Kuma sune suke zama gatansu 

Ire iren wainda karuwancin bai Gama shigarsuba kenan...

##MAMUH#

#HOTLOVE/AMAL IDON NERA

#AQEEL ASAD
*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯

Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯

Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*πŸ”₯

No comments

Powered by Blogger.