Idon Naira 15

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*

15

Babu komai na abinci a gidan tunda ba kowa Dan haka sai data fita ta siyo bread da lemu tasha takwanta ita kadai a qaton gidan Kamar mayya.


Kusan ko anan dinma a tsorace take,

Tunda wancan lamarin ya faru da ita kowane dare a firgice take kwana rungume da MARYAMAH dinta.


Washe gari haka ta wuni zaune shiru Kamar hoto 

Sai yamma sosai saiga drivern gidan shafi'u yazo da kayan abinci masu yawa an zuba a store.


Koda aka kawo abincin harya kwana biyu Bata tababa sbd babu gas Kuma batason tabawa tunda ba cewa akaiba nata ne.


Kullum bread da lemu ko garinta take siyowa Tasha tayi renon yarta dare yayi su kwanta.


Sai datai sati biyu ahakan saiga haj maryamah din tadawo da masu aikinta har biyu, daya yarinya dayar Kuma dattijuwa.


Zuwansu yasa akayo refilling duka cylinders na gidan da gas aka kawo dole itace ta Dora girkin tunda sun iso a gajiye Kuma su din Basu taba zuwa Nan ba acan Abujan aka Samar Mata su dan haka a gidan Basu San koinaba da komai.


Dayake bata taba tsallake inda takeba taje bangaren Haj Maryamah sai ya zama bangaren nata yana buqatan gyara sosai.


Masu aikin nata ne sukai aikin gyara Mata koina a sashen nata suka wanke komai tareda gogewa suka kunna AC Ac dasu fridge da sauran kayan dayake aiki da wuta.


Abincin Haj Maryamah din data Gama ta Basu suka jera Mata a dining ita sai daga baya bayan ta tabbatarda tagama cin abinci da hutawa taje ta gaidata tana rungume da MARYAMAH dataqi bacci tanata rigima sbd aikin girkin dasukai sunsha zafi.


Kallon zainab Haj Maryamah din tayi dakyau kafin ta maida kallonta kan yarinyar daketa Kika duk ta ruda palon.


Kasa magana tayi sai kawai ta amsa gaisuwarta tareda sallamarta Dan kukan gabaki daya ya rudasu su dukan.


Zainab na fitowa daki ta nufa tayiwa MARYAMAH din wanka ta canja Mata kaya cikin kayanta dasuka fara Mata kadan sbd bayan kayanda Aqeel ya siya Mata batada wasu kayan gashi tanata girma.


Baya tayi Mata wanka bacci tayi sai kawai ta kwantar da ita ta fito taje ta gyare kitchen din data Gama aiki ta tattara komai tadawo daki itama tai wanka tayi sallah ta zauna tana kallon MARYAMAH dake bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin irin na yara.



Da daddare kasa nutsuwa da gyaran da shafa Mai aikinta tayi Mata Haj Maryamah tayi sbd akwai qura sosai Sam aikin baiyiba.


Fada sosai tayiwa shafa'atu din kafin qarshe tasa aka Kira zainab itace tayi Mata gyara Mai kyau dayasa hankalinta kwanciyar tasamu ta kwanta.


Washe gari zainab bata fitoba sbd batasan me zatayiba idan ta fito 

Babah ladi itace take aikin girkin gidan 

Shafa'atu Kuma tanata aikin shara da gyaran koina Dan haka saita Kama kanta a daki musamman dataga suna Mata kallon wulaqanci Dan daukarsu itama Mai aikince 

Gashi sunga an kushe gyaransu ansaka tayi sun dauka shiga tafisu samu agun hajiyar gidan basusan wulaqanta tafisuba.



Duk uban aikin dasuketa fama dashi kwana biyu babu Wanda Haj Maryamah ke yabawa sbd tsaurin raayinta da yai yawa,


Duk aikin dasuke Mata Dama acan Bata Jin dadinsa Kuma tana nunawa Koda yaushe Amma sbd su kadaine sai basa damuwa sunyi sabo da halinta shiyasa suka Dena damuwa,

Amma anan duk aikin dasukai bayayi saita saka zainab tayi Mata wani sai hakan yasa sukejin daci da zafin zainab din a ransu,


Musamman babah ladi data fito fili ta bayyanarda rashin kaunar zainab din dake ranta,

Ita shafa'atu tana Dan taqaitawa sbd MARYAMAH data shiga ranta Dan tana tsananin kaunar yara.


Girkin abincin gidan a hannun babah ladi yake Dan haka idan tagama kullum Dan kadan take bawa zainab

 haka zataci ko Bata koshiba zata Sha ruwa ta Kama kanta gashi tana shayarwa tana buqatan abinci sosoi gashi mukullin store a hannun babah din yake koyaushe da gayya take yawo dashi a jikinta duk inda zata.


Idan har tasamu taci abinci isashe yanda ya Kamata to itace tayiwa Haj Maryamah girki aranar dan bako yaushe haj maryamah din ke Jin Dadin abincin babah ba.


Shi gyaran bangarenta Kuma tuni yadawo kan zainab din da batason na shafa'atu Kuma tanada qarancin yarda shiyasa zainab kawai ke Mata gyaran daki taji hankalinta akwance da dukiyarta.


Bayan gyaran sashen Haj Maryamah harda abincinta yadawo kanta sai gashi kusan duka aikin gidan kadan ne basa kanta ga MARYAMAH da rigima sosai harma da qyuya Dan haka duk aikin dazatayi tana bayanta ko hannunta.



Ahakan suka fara Jan lokaci sosai suna wani irin mugun zama a gidan tsakaninta dasu babah..


'yarta MARYAMAH tayi wayo sosai harta iya zama da rarrafe Amma batasan kowaba bayan mahaifiyarta,


Bata sabu dasu babah ba Dan basa janta ajiki bare hajiyar gidan da iyakacinta da ita idone.


Aqeel kuwa yayi rokon,

Yayi neman ummansa ta hadasa da mamin tasa Amma kullum uzuri take basa

Har waya yace asiya abata Amma duk dai hakan bai samuba Amma tunda dai ta sanar dashi suna lafiya hakanma yasa hankalinsa ya kwanta.



Babbar matsalar da aka fara samu a gidan shine tsanar da ake nunawa 'yarta wadda ko sunanta basa Kira sbd sunan hajiyar gidan ne da hakan qarfi da yaji suke Kiran yarta da KE, kokuma 'YAR ZAINAB..wannan kalmar itace abinda yake sosa ran Zainba aduk lokacinda suka Kira MARYAMAH dinta da hakan,


Tana danne wannan lamarin ne matsala ta bullo tsakaninta da Haj Maryamah akan MARYAMAH din datake zuwa da ita gyaran bangarenta Dan yarinyar nata barna sosai.


Tun lamarin na dannuwa a ranta har abin yafara yimata yawa Dan kuwa kusan kowa a gidan kyarar Mata 'ya sukeyi.


Daga ita har yarta kamar wasu almajirai suke a gidan Dan kuwa kayansu na sakawa tuni suka mutu wasuma duk basa shigar MARYAMAH din Amma ahakn take saka Mata su tunda basuda wasu.



MARYAMAH sai datai kusan shekara biyu Ta yayeta sbd yarinyar itama yanayin rayuwar dasuke ciki yafara tabata,

Sam yanzu batada walwala ko sakewa yarinyar,

Duk da qarancinta tasan batada sakewa komai tayi na barna dukanta su babah da shafa'atu sukeyi tun zainab na kauda Kai har tayi magana sai abin ya zama fitina 

Dama babah mutuniyar banza ce gidan abinci a Tasha takeda Jin gida masu kudine zaa Kai yar aikin abinci ta rufe shagonta tazo ta karbi aikin shiyasa take tsula tsiyarta son ranta tunda Haj Maryamah din Bata wani zama ba ruwanta da Yan aiki gashi yanzu itace shugaban masu aikin gidan Dan haka take zuba tsiyarta son ranta.


Zainab rayuwa a gidan tafara yimata tsanani,

Komai ya juye a rayuwar gidan ba kamar da ba,

Idan zata sashen Haj Maryamah ta dena zuwa da MARYAMAH 'dinta sbd gudun fitinar dazata biyo baya idan tayi Mata wata barnar datafi fasa Mata laptop datayi ta aikinta.


Acan dinma idan tabarta kafin Takoma sai ta tadda bacin ran wani abun 

Duk tabi ta fige da masifar gidan da yanzu komai ya lalace mata,


MARYAMAH sbd tsangwama da kyarar datakesha yasa gabaki daya ta rasa walwala da kuzari tareda sakewa irinta yara,

Idan har ba ajikin uwarta takeba Bata wani dogon motsi a gidan.


Wannan yasa itama zainab din ta tasa kuzarinta gabaki daya suka koma kamar Yan gudun hijirar gidan kullum suna daki kamar masu abin kunya.


Ana haka kwatsam Allah yayiwa mijin Haj Maryamah yace ta tattara tadawo Abuja gabaki daya.


Da farko shafa'atu aka fara sallama sbd idan Takoma Abuja Bata buqatar ya aiki da yawa sbd hutawa takeson Yi batason hayaniyarsu Dan can gidan baiyi girman wannan ba da bazakaji motsin masu aikinbama.


Ganin an sallami shafa'atu yasa hankalin babah tashi Dan ta fahimci zaiyi wuya a kori zainab duk da gata da 'ya da Bata barin tayi aiki dakyau.



Babban tashin hankalin farko data fara fuskanta akan tafiyar tasu Abuja shine Haj Maryamah data Kira umma akan zata Aika Mata da MARYAMAH Qarama acan Cameroon bazasu da ita Abujan ba.


Bugawar da zuciyar zainab tayi yasata dafa bango tana Dan bude idanuwanta dake Mata dishi dishi.


A gabanta umma da aka Kira Kai tsaye itama tace bazata iya riqon MARYAMAH dinba sbd tsufa yazo Mata Kuma dasuka riqe uwarta tun tana jinjira me ta saka musu dashi Banda butulci Dan haka ita ma wanna halin uwarta zatayi itakam bazata iyaba.


Haj Maryamah ma Kai tsaye ta nuna zainab bazataje da MARYAMAH dinba idan har umma bazata karbetaba to gwara zainab din ta nema dangin mahaifinta ta miqa musu ita.



Tunda zainab take Bata taba Jin daci da radadin zuciyaba akansu sai wannan karon,


'yarta ake ture turen inda zaa Kai kowa nacewa baya son saikace wani mugun abun,

Me tayi musu da tsanar dasuke Mata zata shafa 'yarta hakan wadda batasan komaiba.


Tafiyar na matsowa umma ta Dage akan bazata karbi maryamah dinba,


Kukan da zainab tayi Saida takai idanuwanta ma basa gani sosai,

Tayaya zata iya bada qanqanuwar marainiyar 'yarta har Cameroon itama taje ta taso Acikin qangi da wahala.


Kukan Rashi iyaye Dana Mijinta tayi tareda na Aqeel Wanda tuni ta cire Rai daga Kansa itada yarta.


Hada dukkanin tsumman kayanta tayi guri daya Dan tasan rigimarda zaayi idan tafada raayinta na bazata taba rabuwa da 'yartaba,

Idan har Haj Maryamah zataje Abuja da ita to zataje da yarta,


Tasan hakan zai kawo rigima tunda ansaba takuma san ran kowa zai baci Amma bazata iya barin arabata da yartaba.



Rigimar kuwa akayi sosai tareda bacin rayika alokacinda ta sanarda Haj Maryamah bazata tafi bada MARYAMAH dintaba.


Umma ranta kusan yafi na Haj Maryamah din baci sbd mamaki da takaicin zainab take tafara jero Mata gorin irin rokon da Aqeel yayi musu akan su amsheta ta zauna gurinsa shine yanzu an zabar Mata rayuwar sauki da Jin Dadi zatace bazata rabu da yartaba,

Ashe 'da yanada dadi shine ita ta raba haj Maryamah da nata Dan kullum cikin fada yake da mahaifiyarsa akanta.


Haj Maryamah kuwa tsabar takaicin da baqin ciki Kai tsaye ta Bata zabin Idan bazataba Saida yarta to tayi zamanta Amma tasan Wana gidan an saidashi gabaki daya har masu gadi tafiyarsu zasuyi.


Irin cin zarafi da tozarcinda umma tayi Mata dakuma maganganun Haj Maryamah din yasa ta sake hada kayanta guri daya.


Haj Maryamah ganin Bata bar gidanba yasa tayi tunanin ta aminta da tafiyar MARYAMAH din Cameroon Dan haka tasa babah ta shirya Dan itace zatakai MARYAMAH din har Cameroon.


Sai ranar tafiyar tun kafin asuba babah ta shirya sbd sammako zasuyi a tafiyar.


Ayau zainab ta fito tayi magana Kai tsaye cewan bazata bada 'yartaba,


Tsananin fushin da haj Maryamah da umma suka dauka yasa akai hayaniya mai girman gaske da har tasa Haj Maryamah sakarwa zainab Marin daya bawa kowa tsoro.


Kasa hawaye zainab tayi sbd zuciyarta datakai qololuwar 'daci da qunci,

Ayau ta tabbatarda har abada bazasu taba kaunartaba sbd qiyayyar dasuke Mata a jininsu take...


Maganganun Haj Maryamah suka rufe ganinta saidai batajin zata iya barin ko gari ya waye tunda umma tabata umarnin barin gidan daga ita har yarta dasuke neman aibatawa sbd rufewar zuciya.


Daurin kayanta ta dauka ta fito daga gidan tana Jin zuciyarta na tiririn zafi da azaba.

##MAMUH#

#SISTERS#

#MARYAMAH AMAL IDON NERA

#DR AQEEL ASAD

#LOVE/HOTLOVE




*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.