Idon Naira 14


 _*Arewabooks@Mamuhgee*_

14

Yana barin asibitin ta zainab ta sauke wani kasalallen numfashi tareda sauke kanta qasa sbd idanuwanta dake kadawa jajir..


Fatan samun nasara da albarkar ubangiji tayi Masa a duk dinta yake sbd Allah ne kawai yasan ranar dawowarsa yasamesu ko wane yanayi Kuma sai yanda Allah yasa.


Zamewa tayi ahankali ta kwanta kan gadon datake tana rufe idanuwanta duk tasan ba baccin zatayiba.



Aqeel kuwa Yana Isa gida breakfast yayi batareda Bata lokaciba yagama aka fiddo da luggages dinsa suka fito hannunsa cikin na mahaifiyarsa dakejin kamar ta goyasa Dan dadi da farin ciki,

Ta matsu taga ya wuce kafin zainab ta bugo tace 'yarta ta mutu yafasa tafiyar Kuma.


Dashi da uncle dinsa alh Yusuf suka wuce 

Har airport haj maryamah din ta rakasa sukabi jirgin Abuja Wanda a Daren ranar jirginsa zai tashi shima daga Abujan.


Tana dawowa wata irin lafiyayyar hamdala tayi tada tabbatarda jirginsu ya daga 

At last dai tasamu 'danta yatafi

Yayi nesa da zainab

Yanzu tasamu damar da zata ringa ziyartarsa shaquwa da kaunar dayakewa zainab duk zai maido kanta ya ragewa zainab din.


Wuni sukai a gidan cikin nutsuwa da farin ciki daga ita har umma.


Saida yamma tafito a shirye Dan zuwa asibiti ganin likitanta dazai sake duba dp din nata.


Tareda umma suka tafi asibitin 

Suna baya driver na jansu cikin daya daga cikin lafiyayyun motacin gidan.


Umma ma ciwon baya da qafafun datake fama dashi aka dubata akai suka fito zasu nufi mota umman tace suje haj maryamah ta dubo zainab tunda tana asibitin itama.


Da mamaki haj maryamah takalli umman sbd sanin asibitin ta kudine sosai Dan basuda ko irin dogayen dakunan ward haka

Duka dakunansu daddaya ne Amenity rooms dai Kai tsaye.


Cikin basarwa umman tace"


Atoh, ai danki ne ya kawota

Allah ne kawai yasan uban kudin daya kashe daga haihuwarta zuwa yanzu,

Ko kudin haihuwar ba qananu bane gana jinyar 'yar Kuma acan wani dakin daban..,ai wlh maryamah kinyi sake sosai,.


Ace 'danki da Kika Haifa Yana hada kainarki data wata

Duk laifinki ne Dan kece Kika barwa zainab 'dan gashinan yanzu bake kadaiba munata fama dashi 

Ga shegiyar kafiyar tsiya agunsa 

Shi ala dole yasan Allah baya qarya baya magana biyu.


Numfashi haj maryamah ta sauke tana kasa cewa komai sbd tarasa abin fada.


Dakin da zainab din take suka nufa tunda umma tasan dakin dasukazo tareda aqeel kafin wucewar tasa.


Koda sukaje tana kwance idanuwanta a rufe tana tunanin mijinta da 'yarta datazo ta zauna tsakiyar ranta,


Sam Bata qarar da hakan da yake zaunuwa Aran mahaifiyarsa ba sai yanzu data sake qararwa duk da har lokacin kaunar aqeel mai girma tana cikeda ran nata sai takejinsu su biyun sun cike mata zuciya tako Ina.



A tsawon shekarun datayi tana wankin wasu daga cikin kayan haj maryamah da gyaran dakinta tareda wankin toilet dinsa to tariga ta haddace qamshinta ras acikin hancinta Dan haka suna shogowa dakin tun kafin ta bude ido hancinta ya tabbatar mata da 'yar uwartace ta shigo.


Ahankali ta bude idanuwanta dasukai jajir a kumbure ta kallesu tareda sauke Kai tana sake gaida umma kafin ta gaida haj maryamah din.


Dukkaninsu kusan atare suka amsa gaisuwar sai haj maryamah data gyara tsayuwarta tana kallonta tayi mata gaisuwar rasuwar Mijinta kafin daga baya ta tambaya baby.


Amsawa zainab tayi tareda cewa ta gode Allah yabada ladan gaisuwar malam din.


Shiru sukai dukkaninsu saidai umma ce tafara maganar zainab din idan ansallameta taje gidanta tafara tattara kayanta tasan yanda zatayi dasu tukuna saita wuce can gidan haj maryamah din.


Gyada kai tayi kawai batareda ta iya bude Baki tai maganaba Dan batajin zata iya.


Basu wani jimaba suka tafi bayan haj maryamah din ta Ciro 10k daga handbag dinta ta ajiye mata a gefe

 na dubiyane ko sadaka ne tabata oho.


Bayan tafiyarsu tashi tayi ta nufi toilet din dakin tasake Dan kamo ruwa ta fito Takoma ta zauna tana zubawa 10k din da itace alkhairin farko dazatace Yar uwarta tayi mata na kudi dai.


Da daddare Saida aka Kuma zuwa aka  matsa nononta still har lokacin ba komai dayake Acikin siyayyar da aka rubutawa Aqeel ya siyo harda Madara Kuma kaman yasani ya siyo musu da yawa.



Washe gari da yamma tayi tunanin Kiran aqeel din sbd tasan Kila ya Isa a time din,

Tunaninta tsayawa yayi data tuno da batada waya yanzu tun rasuwar malam ta rasa wayar da rikicinta dasu umma.


Wani nannauyan numfashi ta sauke sbd shima Aqeel ya manta da batada wayar saiya nemeta yajita babu.


Sanyi jikinta Yakuma Yi sai kawai ta cire ran jinsa sai Randa Allah yabada iko.



****Cikin kwanaki hudu ita kam ta warke sumul batada ciwo ko damuwar komai a jikinta Dan haka hankalinta gabaki daya nakan 'yarta MARYAMAH da itama tana Dan samun kuzari da kulawa sosai Dan kuwa Aqeel babu abinda bai tanadarba ya biya kafin ya wuce din.


Baa kawo mata abinci daga gida Dan haka itace take siyan abincinta taci anan duk da nata jegon dakuma damuwar rashin miji duk yasa cikinta a bushe yake batason cin abincin,

Wanda ma take nace tana siya tanaci sbd tanason tasamu Nononta ya taru MARYAMAH tasamu nono.


Wasu daga cikin maqotanta sunzo har asibitin sun dubata da yarta duk da baa bada babyn 

Kuma dazasuzo kusan duka sun kawo mata abici wasu kudi harda kunun haihuwa mai kyau suka kawo mata Tasha kuma taji dadinsa sbd ya taimaka mata gurin samun nonon Dan ajiyewa tai tana shansa kwana biyu kafin yaqare dayake dakin akwai fridge harma da heater ta ruwan zafi.


Samun ruwan Nononta yasa babynta tafara samun kuzari da lafiya sosai Dan haka takesan nono sosai gashi Daman ba laifi babyn tanada Dan girma kadan ba irin sosai takeda rashin girman Nan ba ko kadan.


Acan gidan haj maryamah kuwa umma sati daya tayi ta komawarta bayan tasake zuwa asibitin so daya kafin ta wuce.


Aqeel kuwa ya Isa lfy yanata kokarin fara karatunsa Amma yakasa samun Maminsa 

Yayiwa ummansa magana ta sanar dashi baa sallamosuba tukuna dole ya hakura harsu dawo gidan yasamu ko ummansa zata hadasa da mamin tasa a waya.


Haj maryamah kuwa tini ta tattara ta wuce Abuja itama kafin tawuce tazo asibitin ta sake dubata so daya taqara Bata wasu 10k din ta wucewarta bataredama zainab din tasan gari zata Bari ba.



Ahankali ahankali Saida zainab ta share kusan sati uku a asibitin kafin aka sallameta ta nufi gidanta da 'yarta.


Gidan yayi datti sosai dayake lokacin iska ne Dan haka dole ta goya Maryamah tafara aikin gyaran gidan.


Saidata gyare koina ta share ta wanke kafin ta fito ta samu yaro ya siyo gawayi ta Dora ruwan zafi tayi wanka tayiwa maryamah da aka koyo mata yanda zatayi mata daga asibitin.


Ruwan zafin Tasha da Lipton ta kwanta suka Dan samu bacci tana tashi maqotanta Wanda Basu samu zuwa asibitinba suka shigo sunatayi mata barka da qarin gaisuwar malam.


Da daddare Dole ta dafa shinkafa dayake akwai sauran abinci dasuke dashi.


Da manja taci shinkafar tasake Shan ruwan Lipton tagama sauran ayyukanta ta kwanta.


Washe gari ma haka ta wuni ita kadai a gidanta daga ita sai 'yarta dare yayi suka kwanta abinsu.


Haka ta runguma rayuwarta data 'yarta data zama sanyin idaniyarta Kuma sanyin zuciyarta,

A yanzu duniyarta 'yarta itace babban abinda yake gabanta,

Batada buri ko buqatan daya wuce inganta rayuwar yarta data warware abinta tayi mulmul sbd nono mai kyau da sauran madarar datake Bata wadda har lokacin sunada sauran kusan gwanwani biyu da Basu fasaba.


Aduk lokacinda tayi sallah iyayenta da Malam da Aqeel sune farko a adduarta da 'yarta kafin kanta,


Ayanxu wata rayuwa take gudanarwa ta kadaici da rashin kowa,


Batada wani farin ciki ko jin dadi

'yarta kawai take kalla taji qwarin gwiwa da farin cikin rayuwa,


Ba laifi tana hulfar arziki da maqotanta duk da babu Wanda ya taba zuwa yabata taimako ko tallafi daga cikin mutanen malam harna Aqeel Dan haka taci gaba da lallaba abubuwan datake dasu Shi abincinta tuni ya qare dole kayayyakin gidan ta tattara ta Saida tabar katifar kwanciyarsu kawai da kayan kitchen.


'yar sanaar Saida gawayi da kayan Miya tafara Amma mutane sun maida komai bashi take suke kwashe komai data kawo Amma bashi 

Qarshe Kuma wasu da yawa basa biya haka zataita yawon bin bashin kudin Amma basa bayarwa koyaushe da qaryar da zasu fada.



Babu inda sanaar taje komai ya karye aka rasa kudin gabaki daya Takoma tana kame kame.


Watanta uku da dawowa hayarsu ta qare masu gidan suka Bata notice dole tafara tunanin barin gidan.


Batada gurin zuwa,

Batasan Ina zata da jinjirar 'ya ba gashi bazaso 'yarta tayi tashin garari ba.


Har notice yacika batada gurin zuwa,


Ana hakan ne Daren wata asabar wani mummunan tsautsayi ya sameta na shogowar qato gidanta 

Allah bai basa ikon yimata komaiba saidai fuskarta ta kumbura da irin Marin daya ringa zabga mata sbd taqi yarda yayi Mata komai

Qarshe haka ya gudu bai samu damar lalata mutuncintaba haka itama Bata samu taga fuskarsaba.


Tunda take hankalinta bai taba tashi da tsoroba irin hakan Dan haka gari na wayewa takai maganar gurin Mai anguwa Amma qarshe dai haka mutuncinta ya zube babu wani takamaimai sheda ko tabbacin abinda ta fada din sbd kusan duka anguwar ansan juna

Basuda samari duka dattijai ne da tsofi 

To tayaya take tunanin zasu yarda kowa da mutuncinsa zai shiga yayi irin hakan.


Qarshe hakuri aka Bata akan saidai daga wata anguwar aka shigo aka Mata hakan.


Wannan lamarin ya sake firgita tsayuwarta ta rasa inda zata saka kanta da 'yarta,

Tsoron gidan da anguwar ma takeji kwata kwata Dan kuwa duka rayuwarta ko yanda ake fyade Bata saniba sai yanzu da hakan yaso faruwa da ita,


Ba kanta takejiba

MARYAMAH dinta takeji tunda fyaden yanzu har yara qanana Ana yiwa,


Wannan tunanin ya toshe dukkanin wata basirarta da tunanin,...


Tunaninta kan rayuwarta na baya yakoma,

Da wani abun yasamu 'yarta gwara taje tayita bauta har tsufa acan din.


Batada zabi, batada dabara, batada mafita tunda ko abin kanta batada dolenta ta juya ta fuskantar bayanta.


Littafan addini da Alqur'anan malam masallacin anguwarsu ta bada aka aje Dan masu karatu hakama siturunsa badawa tayi akaiwa dattijan anguwar kyauta 

Sauran kayan tarkacenta na kitchen saidawa tayi wasu Kuma ta bada sbd duk ba wasu kayan kirki bane.



Koda ta iso babban tsohuwar kurkukunta wato gidan haj maryamah Adam Asad babu kowa gidan sai masu gadin gidan biyu.


Dukkaninsu sun santa Dan haka babu Wanda ya hanata shiga saidai Basu bari ta qarasa cikiba dan koina a rufe yake Saida aka Kira Haj maryamah din tace abarta tashiga tukuna suka bata mukullan gidan.


Kai tsaye bayan ta bude koina inda tasan kanta a dah can takuma Kai kanta goye da 'yarta.


Babu inda baiyi wata irin quraba da datti a gidan,


Kallon kanta tayi taji hawayen baqin ciki na gangaro mata Dan kuwa tasan rayuwar data Bari ce tadawo

Amma Kuma zata iya kowace irin wahalace akan MARYAMAH dinta tasamu rayuwa a natsatsen guri da rayuwa Mai kyau.


Babban aikinta na farko data fara komawa shine aikin shara..


Goya MARYAMAH tayi ta rufeta sbd qura tafara aikin shara da gyaran koina.


Har harabar gidan sai data share ta gyare koina tas tadawo ta gyara Mata dakin ta wanke toilet tukuna ta sauke Maryamah sukayi wanka tazo tayi sallah ta kwanta daqyar tana rintse idanuwanta sbd ciwon baya Dana kwankwaso mai qarfi daya taso Mata.

##MAMUH#

#MARYAMAH AMAL IDON NERA

#MARRIAGE/HOTLOVE

#ZAINAB IDON NERA




*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.