Idon Naira 12

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*

12

Zainab Tunda ta zaunar da duwawunta kan gurin zama ta sunkuyar da kanta Bata sake motsiba bare iya magana.


Zuciyarta ta Dena harbawa da qarfi sbd rashin kuzarin jikinta dayayi sanyi matuqa da Hakan tayi shiru Tana jiran hukuncin Allah akansu.


Aqeel ma kallo daya yayi Mata ya fahimci tsananin sanyi da sarewar datayi Dan haka shima ya kasa magana suka barwa Allah komai.


Haj maryamah daketa faman kiransa a waya bai dagaba sbd wayar ya Barta a mota da Haka take Hankalinta ya tashi itama sbd taji fitar motarsa da daddaren.


Takira Haj Kaka Amma ance baya can gidan Dan Haka Kai tsaye insha Allah Yana gurin Zainab.


Wurgi tayi da wayarta kan gado tareda Dan rufe ido Tana dafe goshinta qaramin tsoki na fitowa bakinta.


A asibiti kuwa komai ya lalacewa su Zainab da likitoci sukaita fada akan rashin kawosa asibiti da wuri yaga likita.


Zainab dai Bata iya cewa komaiba saidai AQEEL dinne kawai yake iya Basu hakuri Yana sanar musu da shima bai sani rashin lafiyar tasaba.


Tun suna saka ran Jin wani bayani daga likitoci bayan tarin magani da allurai da drips dasuka rubuta aka siyo Babu abinda suka sanar musu sbd malam din dai su kansu Basu samu ya farfadoba Amma dai suna saka ran farfadowar tasa Koda tsakiyar dare ne.


Anan suka cinye Daren zaune kofar dakin emergency babu Mai iya doguwar magana acikinsu...


Qarfe biyar na asuba Allah ya karbi ran malam Umar sanda Bayan ya bude idanuwansa akan Zainab Aqeel dake gefen.,


Kallonta kawai yayi tsawon sakanni kamarma baisan meyake kalloba sbd kwata kwata baya hayyacinsa na lafiya,

Akan Aqeel yakuma juyar da kwayar idanuwansa shima ya kafesa da kallo daga Hakan ya iya bude Baki daqyar yana kokarin Jan shahada ahankali ahakan Ransa ya fita.


Innalillahi wainna IlayhirRajiun

Innalillahi wainna IlayhirRajiun"


Shi kadaine kalmar da Aqeel yake iya kamowa bakinsa da zuciyarsa..


Zainab kuwa ahankali ta Isa garesa tareda zuba Masa idanuwanta dasuka Gama galabaituwa.


Ahankali Allah yabata ikon iya bude Baki tace"


Ya rasu ne Aqeel????


Sunkuyar dakai Aqeel yayi Yana kasa riqe jarumtarsa hawaye na kufce Masa masu yawan gaske.


Ganin Hakan yasata itama sauke kan ahankali tareda matsawa ta zauna bakin gadon takai hannunta na rawa ta Dora akan na malam din,


Sam idanuwanta bushewa sukayi suna Mata wani radadin yaji Amma kukan yakasa zuwa tsabar tashin hankali da duhun daya rufe zuciyarta.


AQEEL kuwa kuka yakeyi na hawaye sosai sbd rasuwar shikam tazo Masa ne Kai tsaye daga sama sbd baisan uban nasa Kuma malaminsa baida lafiyaba duk kwanakin.


Rufe gawar akai suka fito daga dakin suka zauna Babu Mai iya magana acikinsu Dan kuwa dukkansu sunyi nisa a fita hayyaci.


Ta bangaren Haj maryamah ma kuwa Bata daina kiransaba tsawon Daren sbd bai taba kwana ba a waje duk rayuwarsa

Idan dai baya gida to Yana gidan Haj Kaka Amma yau din tazo da sabon Al'amari.


Kiransa take Tana sakewa Amma baya dauka sbd wayar na mota...


Duk yanda takai ga danne zuciyarta saida ranta yakai maqura a baci tareda shiga tsoro da tashin hankalin idan ba wani abun ya samu Dan nataba,


Tanason Kiran Zainab taji idan gurinta yazo Amma zuciyarta taqi barinta Kiran dan Haka a tsakiyar Daren gaf da asuba takira umma ta sanar da ita sbd ita takira Zainab din.


Adaidai lokacinda ake fitowa sallar asuba alokacin Kiran umma yashigo wayar Zainab dake zaune kofar dakin da gawar mijinta yake, AQEEL kuwa yashiga masallacin asibitin sallah baidawoba.


Idanuwanta sunyi wani irin nauyi sosai,Babu abinda yake cikinsa sai radadin bushewa na kukan da suka gaza,


Daqyar ta iya gane sunan Mai Kiran ta daga ahankali takai kunnenta tareda Yar shaqaqqiyar sallama sbd makoshinta daya bushe tun tsakar dare har zuwa lokacinda mijinta ya karba Kiran ubangiji.


Umman na Jin Zainab ta dauki wayar Bata tsaya Jin komaiba Kai tsaye tace"


AQEEL na gurinki???


Daqyar Zainab taja numfashi tace,


"Eh....


Bayan Hakan umma Bata tsaya Jin komaiba ta rufe Zainab din da fada sosai akan bazata iya Bari maryamah ta Sabu da 'danta ba harsai ya tafi Babu sabo da shakuwa tsakaninsu,


Meyasa bazata zama sanadi na alkhairi ba saina fitina,,???

Kuma ita Maryamah data haifi 'dan batai qyashin bar Mata shi Yana yaroba sai itace zataji qyashin barin maryamah da 'dan su samu nasu lokacin suma......


Dan batasan zafi da ciwon ciki da haihuwar 'da bane shiyasa take saka son Kai a lamarin uwar data haifi 'da...


Zainab zuciyarta takusa bugawa ta tarwatse tun lokacinda rai ya fita ajikin malam sai alokacin tasamu kuka Mai karfi yazo Mata Dama nemansa takeyi Amma zuciyarta ta mushe qyam sbd girman tashin hankalin data Shiga sai gashi masifar su umman tasa kukan yasamu zuwa.


Umma cikin waya dataji kukan sai ta tsaya da mamaki Tana cewa,


"Lallai Zainab kin samu sake,

Ina fara Miki fadan shine Zaki fashemun da wannan kukan kamar wadda na kashewa miji

Wato ke bakyason fada yanzu......


Wurgi Zainab tayi da wayar da qarfi Tana sake fashewa da kuka sosai Mai bayyanarda tsananin qunci da radadin dake cikin zuciya da jininta ga wani ciwon Mara Mai qarfi daya soketa a take sbd tsananin tashin hankalin baqin ciki da qunci wani akan wani..


Irin kukan datakeyi yasa AQEEL daya kusa isowa gurinta ya qaraso da sauri hankalinsa na sake tashi sbd bai taba ganin Mamin tayi irin wannan kukanba.


Yana isowa gurinta taji nauyin zuciyarta ya qaru sbd itadai Allah ne ya saka Mata kaunarsa fiyeda komai Amma koyaushe baqin jininta da kukan da ake sakata akansa ne....


Wane tashin hankali yafi na rashin mijinta Wanda shi kadai ne gatanta,


Rufin asirinta,


Uban cikinta, tarasashi ayau Amma ko ayau din laifinta ake gani tareda gorin haihuwa da maganganu masu qunar Rai da qarin radadi akan Wanda tasamu kanta aciki yau.


Neman rikicewa Aqeel keyi da yanayinta Amma ta dakatar dashi ta hanyar dakatar da kukan nata aka Basu gawar a motar asibiti suka nufi gida.


Koda suka iso gida kusan duka dattijan anguwa wasu daga jama'arsa da dalibansa manya da yara kusan duk sun fara halarta Dan Jin labarin rasuwar tasa.


Babu Bata lokaci aka hau gyara gawar Dan janaizarsa,


Aqeel duk da matashi ne da shekarunsa Basu Gama zama na manya sosai ba dashi akai komai sbd shine tamkar Dan malam din Dan Haka kusan kowama shi yakewa gaisuwar rasuwar.


Ahaka akai janaizar Malam Umar Sanda mijin Zainab aka kaisa gidansa na gaskia.


Dangin mahaifin Aqeel din wasu da yawansu sun halarci janaizar sbd Malam din dakuma Aqeel dayayi rashin wani uban a Karo na biyu.


Gashi rasuwar ta dakesa sosai shima kamar yanda tayiwa Zainab mugun duka.


Acan cikin gida kuwa Zainab Tunda suka dawo makotanta ne a tareda ita suna tayata zaman,.


Bayansu batada dangi batada kowa da zaizo Mata.


Haj maryamah sai bayan da aka kaisa makwancinsa aka dawo Aqeel ya iya samun damar kiranta ya sanar Mata abinda yafaru.


Addua tayiwa malam din tareda nema Masa rahamar Allah daga Hakan sukai sallama.


Umma Haj maryamah dince takirata ta sanar da ita sai alokacin ta fahimci abinda yasa Zainab ta kashe Mata waya dazu Dan kuwa harta dauka zafi da Hakan matuqa.


Itama adduar samun rahama tayiwa malam Sanda din sukai sallama.


Kiran wayar Zainab din sukayi su dukan Dan Yi Mata taaziya Amma Bata shiga sbd Tunda tayi wurgi da ita  a asibiti batasake bi kan neman wayarba Hankalinta baya kan wayar kwata kwata.


Da daddare gidan yakoma daga ita sai Aqeel Wanda daqyar ya iya sata taci abinci da maganin zazzabi sbd zazzabi Mai qarfin gaske ta wuni dashi dan har wani hucin zafi jikinta keyi na zazzabi...


A gidan ya kwana palon malam sbd bazai iya barinta takwana gidanba ita kadai sbd yanayinta.


Cikin tsakiyar dare ciwon Mara Mai qarfi dataketa daurewa tun safe ya taso Mata gadan gadan..


Tsoro da tashin hankalin rasa cikinta yasata kasa neman Aqeel ta zauna Tana hawaye da hada uban zufan azaba.


Cikinta wata bakwai ne tasan bai Isa haihuwaba Amma ayanda takejin wannan azabar da wuya idan ba barin cikin zatayiba.


Acan bangaren Aqeel Tunda ya shige yaketa sallolin darensa daya saba

Yana idarwa yayi adduoinsa ya zauna Yana Shiga tunanin daketa addabar ransa tun Bayan janaizar Baba malam  wato jibi ne tafiyarsa UK

Yaya zaiyi da Maminsa kenan yanzu??


Ga juna biyu ajikinta Dan Haka a yanzu dinne tafi buqatarsa itada babyn Dan kuwa sunzama amanarsa yanzu,

Sun zama ahalinsa da zai tsaya musu ya zama gatansu Dan kuwa Amanar Hakan ce malam yabar Masa alokacinda ya kafesa da ido gabanin rasuwar tasa.


Yanzu tayaya zai iya tafiya yabarsu anan tsawon shekaru?

Waye zai kula Masa dasu kafin yadawo din??


Bazaiso qaninsa ko qanwarsa su taso ba acikin gata da kulawarsaba.......


Nishin Maminsa Mai qara yasashi juyawa ya kalli kofar palon Yana Dan miqewa tsaye ahankali yanufi kofar Dan tabbatarda abinda yakeji.


Wani wahalallen nishin takuma saki cikin azaba 


Ba shiri ya fito Yana Kiran sunanta cikin kulawa da damuwa daga bakin kofar dakinta yace"


Mami bakida lafiya ne?

Meyake faruwa??


Daqyar ta iya Kiran sunansa Tana cewa yashigo.


Da saurinsa ya shigo Yana kallonta zaune ta hada gumi da hawaye sosai

Kusan ma azabar taci qarfinta da Haka ba wani tsaiko Tunda baisan mezaiyiba ya kamata suka fito 

Allah yasa motarsa na taredashi bai aka gida ba sbd Nan din ba gurin ajiye motar Dole sai kofar gida.


Dare ne sosai Amma baiji shakkar komaiba ya nufi asibiti da ita 

Duk hankalinsa yagama tashi,


Tsoro yakeji yanzu na mutuwa,

Yana tsananin son Maminsa bazaizo mutuwa ta rabasu ba yanzu,

Idan itama ta tafi tabarsa a duniyarsa baida kowa kenan Dan kuwa Maminsa itace yakejinta a jininsa tamkar itace jininta yake yawo ajikinsa.


Kai tsaye labour room akai da ita sbd da Alama haihuwace tazo Mata gadan gadan Babu shiri lokaci baiyiba.


Kasa zama yayi Tunda aka Shiga da ita gashi yakira wayar ummansa yafi so ashirin Bata dagawa duk da yasan darene Amma yasan batada nauyin bacci Kuma takan tashi itama sallar dare wani lokacin Dan Haka zaiyi wuya a nemeta baa sametaba da dare.


Magani da duka abubuwan da ake buqata aka rubuta Masa yaje pharmacy din dake cikin asibitin ya siyosu Komai ishashe Mai yawa.


Kaya akace yaje yakawo sbd haihuwace zatayi.


Da mamaki da tsoro yace,


"Mamin ce zata haihu yanzu?


Dama lokacin yayi ne?


Bayani sukai Masa na cewan preterm labor ce maana haihuwa a wata bakwai din zata sbd matsalolin da cikin yasamu gashi bai kaiba.


Da sauri ya juya ya nufi gurin motarsa saikuma ya tsaya sbd yasan Babu inda zai samu shago a lokacin.


Dawowa yayi Yana jiran afito sallar asuba dasuke kokarin Shiga shima yai alwala ya Shiga masallacin.


Ana idarwa sama sama yayi adhkar ya fito ya ja mota ya nufi gidan tsohon driver din Dadynsa da yanzu shagone dashi na siyarda Kaya.


Aminu na masallaci Aqeel yazo nemansa Dole ya dauko mukalullan shagonsa suka nufi shagon ya bude ya basa kayanda yake buqata

Shima Dole transfer yayi Masa Dan Babu cash a jikinsa,

Allah Kuma sai yasa shagon nasa baa sakuwa yakeba da Babu Wanda zai bude musu kasuwar alokacin.


Koda ya dawo asibiti da siyayyar kayan baby masu yawa sosai har Allah yasa Zainab din ta haihu lafiya ta samu baby girl wato 'ya mace saidai babyn batada qwari ko kadan Dan Haka Yana kawo kayan aka Danyi Mata Shiri aka sakata cikin babys incubator da ake aje jarirai irinta. 


Da farko tsoro yaji Jin babyn na cikin kwalba Amma Kuma sun Masa iya bayaninda zai gane yakuma ganar da mamarsa kamar yanda suke tunani.


Bacci Mamin tasamu bayan magani da allurai tareda tea Mai zafi datasha Dan Haka sai alokacin yasamu ya tafi gida guraren 9 na safe kenan.


Gidansu ya nufa direct sashen mahaifiyarsa ya nufa ya taddata zaune akan dining Tana breakfast a shirye cikin shigar dake nuni da fita zatayi.


Qarasowa yayi jiki a mace yana gaidata ya zauna kan dining din ya zuba ruwan zafi Yana hada tea.


Kallonsa tayi lokacinda yake Shan tea din ahankali cikin sanyi da nutsuwa tinaninsa nakan Maminsa.


Zatayi magana ya dago ya kalleta cikin nutsuwa yace"


Umma Mami ta haihu da asuba yau Amma babyn is not okay Tana incubator..


Kallonsa tayi cikeda mamakin Dama Zainab cikin da aka fada gaskia ne harya tsufa da haihuwa yanzu haka..

##MAMUH#*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯

Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯

Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*πŸ”₯

No comments

Powered by Blogger.