Idon Naira 10

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*

10

Daga umma har haj Maryamah da Aqeel din Kansa Babu Wanda bai girgixa matuqaba da matakinda Zainab din ta daukaba a Karo na farko a rayuwart datai ikon kanta.


Kasa gasgatawa umma da haj Maryamah sukai farko

sbd Babu Wanda acikinsu yayi tunanin zata iya bude baki ma tayi wata maganar Bayan ban hakuri dazataitayi.


Umma cikeda mamakinta tace,


" Zainab kin fahimci abinda ake nufi ne da zakiyi gaban kanki da ikon kanki?


Magana fa ake akan Aqeel da duka tarbiyarkice da kikai masa anan yake nunawa Babu Wanda ya Isa dashi sai ke

Haka kika nuna Masa ko Zainab?

Babu me mahimmanci agurinsa sai ke da kikai wahala dashi 

Mu duk bama sonsa,

Uwarsa data haifesa ma bata Sansa saike Tunda kece kika haifesa

Gashi yanzu ana magana Zaki zaqe kice aurenki kika zaba zakiyi Bayan kin lalata alaqar uwa da 'danta Zaki tattara ki tafi ko????


Ni ban Isa ba akanki da bazaki tsaya kiji raayinaba a zancen auren idan na yarda idan ban yardaba kin zaba aurenki da kanki..


Daga qarshe dai gashinan duk Rikon amanar danai Miki kin nunamin ba nice na haifekiba.


Maganganun umma ba zuciyar Zainab kawai suke duka harda gangar jikinta datayi sanyi Tana daukar rawa da zafi sbd acikin bacin Rai da mamakin butulcin da ita ake ganin tayi ummar ke maganar,


Haj maryamah kuwa idanuwanta jajir suke sbd kukan datai na bacin Rai da Dana sanin barwa Zainab danta da Yana qarami.


Aqeel kuwa Kansa a qasa yake yanajin ciwo da radadin kalaman da ake fadawa Mamin Amma Kuma tarbiyarsa ba irin wadda zai iya musu ko sai'insa da manyansa bane,


Yasani komai zai fada bazasu bar Mamin da fada da maganganu marasa dadi ba 

Yayi yayi sun kasa fahimtarsa saima laifi dayake qarawa Mamin idan Yana tsaya Mata Dan haka yayi shiru zuciyarsa data Mamin dake tsayayar hawaye da girmamata suna dukan zucuyarsu.


Zainab Bata iya ko motsawaba Bayan hawayenta dake gangarowa kan fuskarta,

A yanda zuciyarta da gangar jikinta sukai sanyi ta tabbatarda ta gaji,


Rauninta yayi yawa,


Batason fitina,


Batason koyaushe ta zama sanadin fadan Antynta da 'danta,


Har abada bazata taba son Aqeel dinta ya samu raunin karatun da su Haj maryamah din ke cewan shine ci gabansa,


Wannan sadaukarwar ta amincewa da auren ta zabi subarta har abada sbd Aqeel din tayita sbd matuqar Basu aminta da aurenba tasan kome zaayi bazai tafiba Dan shi din Dan kaifi daya ne,


Suma Kuma tasan bazasu taba amincewa da auren nataba sbd Babu Wanda zai iya yiwa Haj maryamah din bauta yanda takeso har abada kamarta....


Dan haka wannan hukuncin data zabarwa kanta shine mafita da maslahar ahalin gidan gabaki daya da hankalinsu ya tashi akan fashij tafiya karatun Aqeel din.


Sbd su Kansa dangin mahaifinsa a yanda suka dauki zafi da akace itace take zigasa Hakan 

Sun bada tabbacin matuqar Aqeel bai tafi karatun ba zata bar gidan.


Tayi kukan da koyaushe aka tashi yiwa rayuwarta barazana sai ayi Mata barazanar Kora...


Duk yanda umma zata dage da nuna fushi da bacin Rai akan Zainab bazatai aurenba 

Zainab tsayawa tayi akan ta zaba auren sbd shine maslaha.


Aqeel Tunda ta amince da auren hankalinsa ya kwanta Dan haka ko zama sosai ya rage Yi a gidan motarsa yake ja ya fice zuwa gidan kakarsa sai dare yake dawowa.


Haj maryamah da umma kuwa kyara sosai da fada Mai tsanani Koda yaushe suke rufe Zainab din dashi akan bazaayi aurenba Amma dai batacewa komai.


Har malam Sanda umma Haj maryamah sukai magana dashi akan ya janye Amma Kai tsaye ya sanar musu Tunda Zainab ta zabi aurensa bazai janyeba zai aureta insha Allah.


Ayanda yasan komai da komai na rayuwar Zainab tun haihuwa har girma zuwa yanzu bayajin zai iya kasa aurenta Koda kuwa zasuyi Mata Baki ne sbd maraicinta tallafi yake nema sosai...

Sun kashe rayuwar yarinya qarama tun daga quruciya harta girma ta wuce layin ya Mata sbd son Rai Dana zuciya da Wasa da haqqin maraya.


Haj maryamah tasan wanene malam Sanda,

Sam ba malamin Wasa bane,

Baya wani daukar zancen kowane idan har yaga akwai son Rai aciki,


Tasani Tunda yace zai aura Zainab din bazai taba fasawaba matuqar ba Zainab din ce tace batasoba ta fasa.


Dan haka sai suka sake maida pressure din kan Zainab musamman umma wadda a fili take bayyanarda Dana sanin Rikon Zainab din dasukai har girmanta..


Ayanzu da Haj maryamah zatafi buqatarta shine ta nace da wannan auren na malaminda komaima baida sai Dan rufin asiri..


Idan Aqeel ya tafi Abuja taso komawa gurin mijinta tareda Zainab basai ta nema wasu masu aikinba sbd qyanqyaminta tafison Zainab din dai ta zama permanent Mai aikinta,


yanzu gashi ta yarda da wannan auren da Babu abinda zata samu agurin malam Sanda din Tunda dai ya manyanta har tsufa ma yafara.


Qarin takaici da kunya tasan kusan Aqeel dinne zai dauki dawainiyarsu.


Zainab dai zuciyarta tagama raunana da komaima na rayuwa Dan haka koyaushe sukai Mata fadan da zasuyi mata kuka takeyi ta hakura Bata iya cewa komai Dan ko bakinta Bata iya budewa tai magana sbd raunanar datai sosai da rayuwar.


Su Kuma wannan yanayin data shiga shine yake qara zurfafa bacin ransu sbd takasa fadar zata fasa auren ko bazata fasaba gashi a yanda Aqeel yasake fada saura kwana biyu auren..


Dan ma rigimar da akai tasa an daga auren ne da yanzu tayi sati kusan uku da auren.


Aqeel da Kansa yabada kudi a gurin qanwar Dadynsa tayowa Zainab dunkunan sabbin sitirar alfarma da Zainab din Bata taba sakawaba 

Dan kuwa masu kudine ba laifi kayan..


Hatta takarma da hijabs harma da veils biyu da tirarika da Yan cosmetics duk an siya Mata kusan dai akwati uku aka cika matada duk kayan buqata shidai yabada kudin.


Malam Sanda ma ya Aiko Mata da atampa guda uku da hijabs manya guda biyu har qasa da takarmi daya sai tirare daya.


Umma dataga bazata iya kallar wannan lamarinba fushi tayi ta tafiyarta Koda Zainab din zata shiga damuwa ta fasa Amma harta Isa Babu wani labari.


Da Zainab din takira Dan yimata barka da Isa lafiya Tana dauka taji ba maganar fasa auren bace ko sauraron ya haryar datake Mata Bata gamaba ta kashe wayarta ta ajiye tana rasa yazataiwa Zainab din afasa wannan auren Dan baida wata doguwar alfanu gareta,

Me zatayi da tsoho tanada sauran kuruciyarta.


Haj maryamah ko fuskar Zainab din Bata buqatar gani Tunda dai tazama cikakkiyar butulu Dan haka karshema tattarawa tayi itama tayi tafiyarta Abuja bataredama Zainab din tasaniba Dan haka Koda aka daura auren ranar juma'a Zainab batada kowa sai Aqeel Wanda shine ya tsaya Mata aka daura auren.


Matar datake Mata kitso itace tashigo ta wanke Mata kan tayi Mata sabon kitso Mai kyau da lallen hausa.


Dama ita ba qazama bace Dan Babu inda wani dogon gyara yake atareda ita Kuma Allah yasa dattijo ne Kuma malami zata aura Bata buqatar wani qyale qyale Dan batadama Mai Mata qyale qyalen..


Lallen da kitson ma Dan matar ta dage akan zatai matane shiyasa

Amma badan hakanba ko Mai matasu batashi.


Alokacinda aka daura aurenta Ita Zainab Adamu batada waliyyi dazai tsaya Mata ya bada aurenta sai 'danta Aqeel Wanda aka Haifa agabanta..


Shine ya karbi sadakin aurenta daga malaminsa ya bada aurenta jamaa suka sheda aurenta da Malam Umar Sanda Wanda dagashi har ita Babu Mai dangi Amma shi Mai jamaa ne Dan haka aka Dan samu mutane sosai gurin taron daurin auren Wanda ko IV baa buga ba andaiyi sanarwa a masallacin anguwar.


Aqeel ne yasake ajiye Mata sadakinta gabanta tareda sanar da ita an daura auren.


Addua da fatar samun nasara da rayuwar farin ciki da kwanciyar hankali yayi Mata.


Wasu hawayen radadi da dacin zuciyane suka gangaro Mata Dan kuwa ayau ta sake tabbatarda batada kowa sai kanta,


Ayau Aqeel ya tabbatar Mata da Bayan shi batada kowa sai rayuwa dazata samu gaba a gidan wannan auren wanda take fatar ya zamar Mata alkhairi sbd yanda su umma da Haj maryamah suka juya Mata baya tareda ficewa daga rayuwarta suka juya mata baya a lokacinda yakamata ace sune suka tsaya mata.


Ayau data shiga sabuwar rayuwa Mai girma 'danta ne kawai tareda ita..


Batai kukaba saida Aqeel din yayi Mata wasu maganganu masu Kama da nasiha.. kenan shine zaiyi mata nasihar aurenta..danta?

Wanda aka Haifa gabanta?


Wani kukan mara sauti takuma saki zuciyarta na sake nauyi..


Babu Wanda yasan menene qaddarar dake jiransa agabansa,

Babu Wanda yasa menene sanadinsa na alkhairi ko sabaninsa,


Ashe Aqeel shine sanadinta na matsawa da Isa ga wani matakin na rayuwa Bata saniba,..


Tana godiya ga Allah da Bata taba cutatar dashiba ko so daya,


Da zuciya daya take tsananin kaunarsa kamar jininta,


Tana fatar yanda ya zama Sila Kuma sanadin shigarta wannan rayuwar ta aure

Allah yasa wannan auren ya zama Sila Kuma sanadin nasa farin cikin da Lada Mai girma tareda girban alkhairin Hakan a gaba.


Sabuwar Mai aikin gidan Zainab tabarwa komai Tunda Haj maryamah din Bata gari Kuma tayita Kiran wayoyinsu daga ita har umma Amma Babu Mai daga kiranta,


Har gwara umma Tana dauka wani lokacin Amma Bata amsa Mata cikin dadi saidai fada.


Aqeel da Kansa ya dauketa a motarsa duk da Babu wani nisa da anguwar yakaita qaramin gidanta da Malam din ya Kama haha Mai Palo daya daki daya sai bandaki da babban palon karatu Wanda mutanensa zasu ringa daukar karatu sbd yanzu kam bazaije gidan kowaba bada karatun saidai azo Tunda Daman rashin iyali ga malami kamarsa yasa bayason ana zuwa gunsa din daukar karatu saidai yaje can yabada.


Barema tun rasuwar Mai dakinsa Yana qarqashin kulawar Alh Asad Dan haka tuni a anguwar yake zaune qaramin boys quarters din da aka Gina Masa ta wajen gidan 

Yanzu Kuma gurin bazai zaunu da iyaliba Dan Babu sakewa sosai.


Yanzu anan din hayace ya Kama sbd Zainab tasamu kanta a sabon guri ko zatayi saurin sakewa tayi rayuwa kamar kowa cikin walwalarta da kwanciyar hankali.


Koda suka Zo Malam sanda din Yana palon karatunsa da wasu baqin Anguwar dasukazo su gaisa sbd sun Dan San juna.


Aqeel din bai shigaba Yana ajiyeta yajuya ya tafi sbd baisan mezai shiga yayiba Dan ko kawowar wani irin nauyin lamarin yakeji to Amma Tunda baida Wanda zai Mata Dole shine zaiyiwa Mamin tasa.


*****Zainab tasamu kyakkyawar tarba da kulawa irin dattijon dayasan Kansa daga mijinta Malam Sanda,


Da farko taso tsorata da lamarin Amma Kuma ganin Babu gudu ba ja da baya Tunda sukai Kuma daga shidai ba qaramin mutum bane hakama itama ba qanqanuwar yarinya bace Dan haka ta cire komai aranta ta Bari Kai tsaye ya maidata sahun Mata batareda wahalarwaba.


Shi Kansa malam Sanda sosai tasake shiga ransa ya Yaba da nutsuwarta Dan kuwa komai nata na nutsuwa ne,


A macenta cikakkiya ya sameta duk da ta jima gida hakama ga aikin wahala Amma still dai mutuncinta na Nan koba kamar na budurwa danya sharaf ba.

##MAMUH#

#NEW BEGINNING

#DR SHAYKH AQEEL ASAD

#AMAL SANDA IDON NERA##LOVE#MARRIAGE#ROMANCE#


*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.