Gurbin Ido 7

 


07


Tun batayi nisa ba gaba daya qafafunta taji sun daddaure saboda tsakuyiyin da take takawa,wani gurin harda cabalbalin daya cakude da ruwa da qasa,tuni ta jima da sanin cewa ba qaramar rahama bane takalman a gareta,rashinsu a yan mintuna kadan yasa fa fara dandana kudarta,bata kuma san sanda zata sake mallakar wasu ba.


       A hankali motarsu daada ke kutsawa rubibbiyar hanyar mai yawan gargada,kamar yadda sukazo a yanzunma su hudune,saidai yanzun akwai qarin saddam da zai musu rakiya,a hanyarsu ta zuwa ziyara qauyen dake kusa da rugar ummarun.


         Cikin motar tattaunawa suke kan yadda gwamnati tayi banza da nuna halin ko in kula da jama'ar dake rayuwa a irin wadan nan muhallan,babu ruwa ba wuta babu hanya me kya bare azo ga maganar tsaro


"Subhanallah" salmanu driver ya fada yana taka burki sanda shanun suka fara keto burtalin xasu wuce,salmanu ya kalli agogon hannunsa yana cewa


"Aqalla sai sun kusa minti biyar ko takwas suna wucewa,shi yasa tun dazun nake sauri mu wuce kafin su iso"


"Wai daman kuna iya kula da dabbobi babu duka?" Laila ta fada cikin mamaki,idanunta nakan maimunatu dake koro shanun daga can baya


"Qalilan ne gaskiya,kiwo yana da wuya fa adda laila" maganar data ja hankalin daada,ta daga kanta zuwa ga sashen da maimunatu take.


        Ido ta zuba mata sosai cike da mamaki da kuma burgewa,gaskiya sadam ya fada ba kowane ke iyawa ba,kula da dabba koda guda daya ne abune mai matuqar wahala,sai mutum me haqurin gaske da kuma tausayi,bare wadan nan da sun haura talatin,banda akuyoyi,yarinya qarama irin wannan me qananun shekaru,ita daya babu mataimaki,zata iya cewa bata taba ganin wannan ba,koda akwai din sai jarumar mace mai kamar maza,wadda taga jiya ta kuma ga yau.


         Idanun maimunatu nakan motar sanda ya rage ita daya ce zata haura hanyar,idanunta cike fal da fargaba da tsoro,karo na biyu kenan da taga motar,amma sai take ga kamar abinda ya faru da ita shekarun baya zai sake faruwa da ita,sassanyar ajiyar zuciya ta saki sanda taga ta tsallaka,dai dai lokacin da anni ta sauke idanunta ga qafafuwan maimunatu,mamaki ya cikata ganin yadda take ratsa wajen da zallan qafarta ba takalmi.


        Ta buda baki xatayi magana ta jiyo sautin maimaunatun


"Wayyo Allah" tayi maganar a matuqar jigace tana duqawa zuwa qasa tana duban tafin qafafunta


"Tsaya salmanu.....dubamin me ya samu yarinyar can" anni ta tsaida salmanu dake shirin tada motar,wajen suka kalla su duka,laila tayi kamar zatayi magana amma sai ta fasa kada qilu ta jawo bau,seat belt din jikinsa ya zare ya bude murfin motar ya fita,bai wuce minti daya ba ya dawo


"Kaya ce ta shige mata qafa,ta huda wajen sosai,amma naga ta zareta ma"


"Garin yaya?" Wajen da take salmanun yakalla


"Qafarta ce ba takalmi,dana tambayeta yana ina sai tace ya tsinke ne"


"Ina silifa din nan da nace a sakaminsu a mota?,daukomin daya a ciki" ta fadawa laila,daukowa laila tayi ta miqowa annin


"Bawa salmanu yakai mata ta saka" hannu salmanun ya saka ya karba ya juya yakoma indatake,zuwa sannan ta miqe tsaye bayan ta yagi wani ganye dake gefanta ta manna a wajen.


          Daga kai tayi ta dubi salmanun sanda yake bata takalmin,sai taja baya kadan gami da girgiza kai alamun ba zata karba ba,abinda ya sanya salmanu dawowa inda anni ke zaune tana kallonsu


"Anni taqi karba fa,kamar bata yarda bane damu"


"Budeni" anni ta bashi umarni,sai ya zagayo ya bude mata qofar


"Anni,karkice zakiyi magana da ita,kaf fadin rugarmu babu wanda yake kulata" sadam ya fada,a mamakance anni ta kalleshi


"Saboda me?"

"Ban sani ba nima,amma tsoron mata magana akeyi" shuru anni tayi na wasu sakanni sannan ta zura qafafunta waje ba tare data sake bi ta batun saddam ba


       Har maimunatun tayi taku daya biyu taji muryar anni


"Yarinya" cak ta tsaya,a tsorace ta waiwayo idanunta akan anni,tsoro ya sake kamata,don sam annin batayi zubin mutanensu ba.


"Yallijam" maimunatu ta fada a hankali ganin idanun annin har yanzu yana kanta


"Jam" anni ta maida mata tana kallonta tare da karantar yanayinta


"ya kike tafiya haka ba takalmi?" Qafarta ta kalla sannan ta kalla annin


"Sun tsinke ne daada" yadda ta kirata da girmamawa sai yasa anni ta saki murmushi


"Salmanu bata wadan nan ta saka,da hatsari wajen taka gurin nan haka" da fari kai maimunatu ta sake girgizawa kamar yadda ta yiwa salmanu,don batasan me zatacewa inna ba idan ta ganta da takalmin


"Na gode daada,zan qarasa a haka" haka kawai taji ta burgeta,akwai alamun tarbiyya da kamun kai me yawa tattare da ita


"Karki damu ki saka,idan ma kina tsoron fada ne a gida kice baquwa ce daga gidan bappa labaran ta baki" daga kai tayi sosai tana duban anni,idan ta canka dai dai fa kenam gidansu himu take nufi,ita a wa sa zata ambaci sunan gidan tace wani abu daga hannunsu ya fito zuwa gareta,a sanyaye ta karba takalman ta sakawa qafarta.


        Cif da cif kuwa kamar an aunata,wasu irin slipper ne na danqo amma me garai garai dake nuna hoton flowers daga dukka jikin takalmin kaman tangaran,kallon qafar tata tayi ta sake kalla,sai ta daga kai a hankali tace


"Na gode sosai daada" duk kuwa da tana da yaqinin wannan takalmin idanunsa idanun inna ba rabonta bane,murmushi anni tayi


"Ba komai" sai ta juya maimunatun tana qara hanzari don ta taddo dabbobinta da sukayi gaba,tana kuma kiransu da wani irin salo da yasa anni ta bita da kallo.


        "Anni....anni kenan,qaqale qaqalen mutane,tayiya jajibo jama'a ana zaune qalau" laila tayi 'ya qaramar mita ciki ciki,abinda yaja hankalin anni dake maida qafafunta cikin motar salmanu yana shirin rufe mata


"Me kike cewa ke kuma?"


"Bance komai ba"


"Oho miki,idan ma zagina kikayi kin zagi marwanu da Aishatu" idanu laila ta lumshe tana dafe goshinta,kafin tace wani abu wayarta dake kan cinyarta ta dauki sautin kida me dadi,saita daga wayar tana dubawa


"Ga marwanun nan" lailan ta fada tana hade rai tare da miqawa anni wayar


"Kin fada dai dai ai,sunan ubanki kenan" ta amsata tana warce wayar daketa harbawa da sunan super dad,ta shafa ta kara a kunnenta.


        "Sai da salma ta gargadeni kan tafiyar nan,ashe ni zan karba gashin" bata daddara ba dai ta sake yin qorafin murya can cikin maqoshi,saidai babu yadda za'ayi anni taji,saboda tayi nisa a waya da shalelen dan nata.


           Sai da tayi duk wani abu daya zame mata al'ada idan ta dawo da dabbobin daga kiwo sannan ta kira sunan innar,saidai babu ita ba motsinta,dole ta fara takawa zuwa cikin gidan,qirjinta yanata dukan uku uku,don batasan me zai biyo baya game da takalmin qafarta ba.


         Daga qofar dakin innar ta tsaya


"Miwarti ɗilaulake inna(na dawo daga kiwo inna)" shuru taji,hakan yasa ta sake maimaitawa


"Dalla malama matsa ki bamu waje,kinxo kinata yiwa mutane hayaniya aka" muryar gaje ta fito daga cikin dakin,da alama itace kwance a dakin,wanda dama kusan aikinta kenan ko da yaushe,taci ta sha ta kwanta.


        A sanyaye ta juya don barin wajen,dai dai sanda innar ta fito daga makewaye dauke da buta,sam bata lura da yanayin da fuskarta ke ciki ba


"Miwar......." Ragowar kalmar ta tsaya mata a maqoshi,sakamakon wani zazzafan mari daya sauka a kuncinta hagu da dama,a take ta gigice,ta dafe dukka kuncin nata da tafukan hannayenta tana kallon inna,wadda ta taka gefan wani qaramin rumbu dake daura da ita,take tashin hankali ya bayyana muraran saman fuskar maimunatu,tunda taga ta doshi wajen tasan me zata dauko.


        Tsumammiyar bulala ce,wadda ta debi shekaru ana azabtar da ita da bulalar,yadda ta tsani mutuwar ta haka tabtsani bulala,wannan ne dalilin da yasanya take dukka iya bakin qoqarinta taga bata aikata wani laifi da bulalar zata taba lafiyarta ba,zata iya cewa tabon da bulalar ta bar mata a gadon bayanta ba zaya lissafu ba.


         Kusan daukewa numfashinta yayi sanda innar ta ware dukka qarfinta ta zuba mata ita,kafin daga bisani qarfin dukan ya sanyata ta sulale ta duqe a wajen,tun tana iya roqarta tare da bata haquri har bakinta ya mutu,duk da batasan me ta aikatawa innar ba,sai data gamsu don kanta da yawan dukan data yi mata sannan ta tsaya tana maida numfashi


"Gaje....gaje zo nan" ta qwalawa gaje dake daki abinta kira,gajen da duk yawan dukan da akewa maimunatun,duk magiyar da takewa innar bai sanyata ta koda leqo ba,hatta da sassan dake maqotaka dasu dukka kowacce ta leqo tana tsaye tana kallo,wasunsu suna qus qus a junansu tare da tir da dabi'a da halayen inna,wasu kuma suna fadin 


"Allah ne kadai yasan me tayi mata,kila ko yau ta dana halin uwarta ne" saidai babu ko mutum daya a cikinsu da ya isa ya tukari innar da sunan ceton maimunatu,kowanne irin hukunci ko horo kuwa zatayi mata.


        A gadarance gajen ta fito daga dakin,tsaf da ita cikin kwalliyar kayan saqi,wanda kusan ko da yaushe cikin canza mata su innar take,idanun gajen sun kumbura sunyi jazur,abinda.ya bayyana har saman fuskarta,da alama kuka tasha ta qoshi.


        Tsaye tayi saman kan maimunatu tana hura hanci tare da harare harare


"Daga kanki ki kalleta.....tayi kama da sa'arki?" Inna ta fada cikin hargagi,koda ciwon mutuwa maimunatun takeji a jikinta ya zame mata dole ta kalli gaje kamar yadda inna ta buqata,idan kuwa ta saba hakan wani sabon tashin hankalin ne,da qyar ta daga kanta ta dubi gaje,suna hada idanu gajen ta sanya qafa ta haureta cike da baqinciki da kuma jin haushin maimunatun,tasa hannu ta dafe wajen saboda radadi da zafin da ya ziyarceta


"Shegiya munafuka,ni zaki ha'inta,ashe yaron dana ganki dashi rannan ibrahimu ne?,to idan bakisan waye ibrahimu ba bari na gaya miki,shi din alqawarin gaje ne,bashi da matar aure sai gaje kiji na gaya miki,kusantar inda yake kuma shine babban kuskure da zaki aikatawa rayuwarki,wallahi wallahi kinjin na rantse miki,kome kike taqama dashi baki isa ki shiga tsakanin tsohon alqawari ba.....kukan da kika saka gaje yau sai kinyi mafiyinsa,ki bata haquri!" Inna ta fada tana kai mata harbi da qafa,ta sameta kuwa a gwiwarta wadda ta bugu sosai,tana dafe da wajen,cikin tsananin azaba tana dafe da gwiwarta ta fara baiwa gaje haquri,wadda keta qunci,tana jin babu abinda maimunatu zatayi mata ta huce haushin kula mata Ibrahim da tayi,tsahon wanne lokaci sukayi suna tare da ibrahim din?,tunda hatta da mutanen gari sun san da haka,baya ga haka kuma ace har sai da daadarsa tazo da kanta don yiwa tufkar hanci sannan sukasan da batun,lallai maimunatun ta cika cikakkiyar makira kuma macijin sari ka noqe kamar yadda innarta tasha fada mata.


         "A'ah,lafiya?,me yake faruwa?" Muryar jauro ta ratsa kunnensu,abinda ya sanyasu waiwayowa gaba dayansu,duk da cewa innar bata so dawowarsa yanzu ba amma sai ta dake


"Meye hakane?,me ya faru?" Ya sake tambaya yana kallon gaje kafin ya maida dubansa ga maimunatu dake zube a qasa,hakan ya baiwa gaje damar sulalewa zuwa dakonsu,tasan halin jauro tabbas yau cikin gidan ba za'a qarke lafiya ba


"Gata nan ka tambayeta maciyar amana" inna ta fada tana huci.


         Gabanta ya duqa yana kiran sunanta,ta daga kanta wande ta sokeshi tsakanin qafafuwanta tana duban ardo din,yanayin yadda yaga maimunatun ya tabbatar masa lallai ta daku,hatta da bakinta a kumbure yake,gefan fuskarta yayi kwanciyar jini da shacin bulala


"Wanne irin rashin imani ne wannan furera?" Jauro ya fada a mugun fusace yana miqewa tsaye


"Ita ya kamata ka yiwa wannan fadan bani ba,qanwar bayan gaje har ta iya hilatar maza tana binsu?,saboda rashin kintsi ta rasa wa zata bi sai ibrahimu?"


"Shine kikayi mata irin wannan dukan?,inda kuma kin nakastata fa?"


"Shikenan da kowa ya huta da ganin shegiyar fuskar dake daukan hankalin maza" cacar baki ce taso barkewa a tsakaninsu,ran jauro yayi mutuqar baci


"Waike wacce iriyar macace furera?,maimunatun zaki yiwa irin wannan dukan?,kowanne irin laifi ma tayi miki?,don kinga ina dauke kai ina barinki saboda kina nuna min kunfi kusa ko?"


"To dama meye naka a ciki?" Kai ya gyada cikin bacin rai,iskar data fara kadawa wadda ke tafe da dan yayyafi yasa jauro ya maida hankalinsa ga maimunatu 


"Tashi ki shiga dakinku,Allah zai saka miki,a kusa ko a nesa,baya yafe zalunci" kasa miqewa tayi,ya tabbatar ba zata iya tashi ba,cikin muryar fushi ya qwalawa gaje kira.


          A tsorace ta qaraso tana raba ido hadi da matse hawaye,tsawa ya daka mata


"A'ah ya haka?,ka bita a sannu,rai aka bata mata fisabilillahi sannan ka bita da irin wanna tsawar?" Kallon banza ya watsa mata,yana ganin zallar son rai da son kai irin na innar


"Munafuka,kamata ki kaita daki" ya fadi yana zabga mata harara,da sauri ta zabura ta matso ta kama maimunatun,irin riqon tsaurin da tayi mata na mugunta yasa maimunatun cewa


"Wash hannuna"


"Sassauta mata riqon kafin nayo kanki na maimaita miki irin dukan da uwarki tayi mata"


"Dalili dame?,ke bi masharranciya a sannu ku rabu lafiya kada ta shafa miki jarfa ba gaira ba dalili" inna ta fada saboda tasan tsaf jauro zai aikata daga yadda ranshi yayi mummunan baci.


        Sakin maimunatu tayi sanda suka isa dakin,abinda ya sanyata ta buge gefan kanta,qauuuuu taji wani abu na yawo cikin kwanyarta,ya dafe wajen tana kiran sunan Allah,gaje na tsaye a kanta tana zuba mata harara


"Shegiya mayya,wallahi kikayi gangancin sake rabar ibrahim sai mun kasheki a gidan nan nida inna mun binneki,kuma mun kashe banza,tunda babu wanda zai tuhumemu" daga haka ga tsallaketa kamar zata takata,ta haure kan katifarta.


         Ta jima tana jinta a wata duniya ta daban,kowacce gaba ta jikinta ta zame mata kamar wani gyambo,da qyar take iya motsawa.


         Kiran sunanta da jauro yayi ya sanyata bude idanunta da qyar


"Tashi zan shigo" ya fada yana tsaye daga bakin qofar dakin,duk da yayyafin dake sauka har yanzu,jikinta taja ta miqe ta zauna sosai tana jingina da bango,ya dage labulen bayan ya shigo ya maqale shi sannan ya tsugunna daga gefe yana turo mata kwanon abincinsa


"Dauki kici maza diyam" sunan da ya kirata dashi yayi matuqar karya mata zuciya,ya tuna mata da tata daadarta,itace wadda ke kiranta da sunan,suna mafi soyuwa a gareta,fararen manyan idanunta suka cika da qwalla,tasa hannu a kasalance ta jawo kwanon gabanta ta fara ci.


       Wasa wasa sai gashi ta kusa tashi da abincin duk yawansa,ta riga ta saba ba kullum take samun abinci ba,idan ma ta samun to sau daya ne a rana,tana ci yana mata nasiha tare da kwantar mata da hankali,gaje na kwance tamkar mai barci,ranta ya baci sosai,shi babanta wai baya kishinta?,me yasa yafi nuna kulawarsa ga maimunatu fiye da ita diyar cikinsa?.


"Miyatti bappa" maimunatun ta fada a tausashe kanta a qasa cikin nuna jin dadin kulawar da ya bata


"Ba komai,kema diyata ce kamar yadda gaje take" kai ta jinjina,tana kin sauqi cikin ranta,ko babu komai yau din ba zata kwana da yunwar dake da take matuqar wahal da ita ba a duk dare.


         Har jauro ya juya ya fita maimunatu tana binsa da kallo,sai daya sauke labulen ya qarasa ficewa sannan ta sauke nannauyar aiiyar zuciya tana janye idanunta daga wajen,dai dai lokacin da gajee tayi caraf ta miqe zaune


"Munafuka algunguma,kamar a idanun inna akayi wallahi,Allah ya kaimu safiya" tsoro ne ya cika zuciyar maimunatu,saboda tasan tunda gajen ta fada sai ta aiwatar,idanunta fal da qwalla ta shiga roqon gajeen tayi haquri,maimakon ta amsa mata sai ta lullube kanta da mayafi tayi kwanciyarta gami da juyawa maimunatun baya.


         Sai da dukka yawun bakinta ya dauke kan roqon gajee tayi haquri,daga qarshe dole ta haqura da roqon,ta rufe idanunta,hawayen da suka taru suka gangaro mata.


        Wani wahalallen barci tayi mara dadi,saboda ko ina na jikinta ciwo yake mata,ko da tayi sallar asuba ma zaune tayi a wajen,saboda ciwon da jikin yake mata,inda ace shimfida ce mai laushi irin ta gaje wala'alla ta iya rabawa takwanta,amma shinfida irin tata da bata da maraba da tattauran dutse babu ta inda zata iya kwanciya taji dadi.


          "Maimunatu!!!,ke maimunatu!!"kiran mafarautan da ya ratsa tsakiyar baccinta ya sanyata farkawa firgigit,inna ce tsaye a kanta,hannunta riqe da robar da yawancin lokuta suke tatsar nono a cikinta,duban maimunatun take kamar zata afka mata


"Yahudillo dirgul.....(zoki tafi kiwo)......"

"A ina?" Maganar jauro ta katse hargagin da inna ta fara yi mata,ratsowa yayi sanye da riga 'yar shara da malfare a kansa,hannunsa riqe da baqar leda,bisa dukkan alamu fita zaiyi


"Daga yau.....har zuwa ranar da maimunatu zata warke babu ita babu zuwa kiwo,wallahi wallahi wallahi sau nawa kenan?"


"Tati(uku)" innar ta amsa masa tana riqe da qugunta tana kallonsa


"Idan naga akasin hakan zakisan waye ainihin jauro wanda ada can baki sanshi ba,wannan shine hukuncinki na irin dukan da kikayi mata"


"Wai dakata,wai me kake nufi ne?,ko kana yimin baqinciki ne da dukiyar dabbobin da Allah ya bani ne?,wanda dama an jima ana fada,ganin muna zaune shekara da shekaru tare yasa ban gasgata ba,amma ayanzu na fara ganin alamu ganin idona kuwa" dubanta yayi


"Ki bari sai zuwa sanda kika tara taki dukiyar ta halastacciyar hanya saiki gayamin haka" sosai maganar daya fada tayi mata ciwo,tana ganin jauro shi daya ne mutumin da yasan sirrinta yake kuma shirin xamar mata tarnaqi a rayuwa,wannan amsar da ya bata ta hautsinata,ta dinga jifansa da kalamai,wanda kalmarta ta qarshe ita ta sanya ya tsaya cak yana dubanta


"Ban sani ba ko son maimunatu ma dai kake yi a taqaice,idan sonta kake ai gwara ka fito ka gayamin,saika hadamu mu duka ka aure"


"Idan ke mahaukaciya ce ni da hankalina" sai ya qara gaba kawai ya fice yabar mata gidan,ya tabbata idan ya tsaya yaci gaba da biye mata zasu raba abun fada ne gaban 'ya'yansu,wannan ba komai bane a wajen furera.


No comments

Powered by Blogger.