Gurbin Ido 44


 Ba wani qura sashen nata yayi sosai ba,saboda yanayin ginin gidan dama unguwar,amma duk da haka baba tabawa ta zage ta gyare mata sassan nata tas,ko ina ya dauki qamshi da qyalli,aikin da ada ita ke abunta duk sanda ta dawo hutu,abu nafarko data lura dashi,babu wani daki da maimunatun ta ware da sunan dakin maigidan,hakanan bataga wani abu ko guda daya daya danganceshi ba a sassan,koda agogo bare akai gasu hula,tsoronta daya kada dai ace fa yarinyar tana gefe suna rayuwarsu shida unaisa,kada suyi amfani da qanqantarta su cutar da ita,abinda bata sani ba duk kanwar ja ce,har gwara gwara maimunatun,yana tsayawa ya dubeta da idanunsa,yana mata kallon quruciya sometimes har yakanji abar tausayi ce a ransa (hmmmmm,ya manta duk qanqantar allura qarfe ce,mace babba da yarinya duk sunanta mace).


          Baaba tabawan batace dai da ita komai ba,taci gaba da sanya ido a fakaice,har zuwa sanda ta gama kintsa ko ina,sanna ta dora musu abincin dare saboda yammaci sosai yayi,sun kuma yi 'yan ciye ciyensu kafin ta gama aikin,babu kuma mejin yunwa a cikinsu,duk da maimunatun taso ta barta tadan dafa musu koda jallop ce kafin baban ta gama aikin amma ta hanata.


          Gab da magariban akayi knocking qofar falon,baba tabawa ta leqa,sai gata ta dawo tana gaya mata yaron gidanne da siyayyar kayan abinci,ta saba,kusan duk sanda ta dawo hutu zai aiko da cefane da kayan abinci a zuba mata a store,duk da ba rasa komai takeyi ba,hasalima kayan abincin kamar ba'a tabasu,saboda ita daya ce iya cikinta,ba kuma kasafai take wani girki ba,don idan tayi breakfast sai takai har rana bataji yunwa ba,bata sake dora girki sai na dare,ta riga data saba zama da yunwa,banda yanzun ma da cikinta yake komawa normal irin na mutane.


         Baba tabawa ce ta bude masa can qofar baya ta kitchen din,ya shiga ya zuba komai ya fitar da wanda zai fidda kamar yadda aka saba,sai daya tafi ta kulle wajen sannan ta dawo


"Niko nace,kuna gaisawa kuwa da abokiyar zamankin nan?" Kanta maimunatu ta daga daga qoqarin jona chargy da take a wayarta


"Ina shiga duk sanda na dawo a makaranta mu gaisa na gaya mata na dawo"


"Amma duk xaman da kikayi asibiti ban ganta ba" ta tambaya cikin mamaki,don ko yanzun ma taji motsinta,sun kuma hadu da masu aikinta a kitchen din gidan,saidai babu wanda yace mata kanzail a cikinsu.


          Shuru maimunatun tayi,don itama bata da amsar da zata ce,ta kuma fuskanci kusan ita kadai dince bata zo dubata ba,tasan kuma ta sani,koda mai gidan bai gaya mata ba sanda su laila sukazo daukar mata kayan sawa sun hadu,sun kuma gaya mata abinda ya kawosu,duk yadda taso kada taji babu dadi aka abun wannan karon sai dataji ranta ya sosu,ita din batasan ciwon kanta ba kenan da take shiga har sassanta duk randa ta dawo ta gaidata ta gaya mata ta dawo,badon komai ba sai don zaman lafiya dake da dadi,bawai rashin sanin ciwon kai bane,duk mutumin da zakayi ciwo ya kasa dubaka to lallai rashin qauna yakai iyaka,a take nan taji a cikin ranta itama tabar taka sassanta.


          A nan waje ta watsar da batun,kamar yadda baba tabawa bata sake daga batun ba,ta wuce bedroom dinta tayi wanka,ta shirya cikin dinkin doguwar rigar atamfa A shape,ta dora baby hijab dinta saman kanta bayan tayi sallar magariba,tasha magungunanta sannan ta fito falon,tana ji a ranta zuwa yanzu wayarta ta cika da chargy.


          Ta samu baba tabawa ta gama shirya musu abinci


"Na zuba sauran yana dumama don kada ya huce kafin yazo ci" baba tabawa tace da ita,sai ta amsa mata da to,ba tare data fuskanci ma'anar maganarta ba,tare suka zauna da ita sukaci abincin,suna ci suna hira,baba tabawa na bata labarai iri iri da suka shafi rayuwa,zamanta da kishiyoyinta da kuma mijinta,yadda mijin ke ji da ita saboda tafi duka sauran kula dashi,a fakaice take shigar mata da darasi.


         Sosai take jin dadin labaran,tunda take tsahon watanni sai yau ne takejin gidan a matsayin gida,sai yau ta taba jin dadin zaman gidan,sun jima sosai suna hira,harta soma jin bacci yana fusgarta,don haka ta miqe ta bada faralin sallar isha'i,ta dubi baba idanuwanta na lumshewa


"Inajin akwai maganin dake sanya barci cikin magungunan da nasha"


"Bacci ko?" Kai ta gyada mata


"Eh wallahi,zan je na kwanta"


"To Allah ya tashemu lafiya" da kallo tabi maimunatu sanda take shigewa dakinta,tana jinjina kai tare da sake tabbatarwa kanta akwai matsala,bata ga ya shigo ba,bata ga taje nemansa ba,koda kuwa ba kwananta bane,tana kuma da tabbacin zuwa yanzu ai yana gida,don ba mai yawon dare bane shi tun asali,amna zatabi komai a sannu,koda yau da gobe ba kwananta bane,dole jibi ya zamanto kwananta,jinjina kai tayi tana ci gaba da kallonta,saidai kuma gefe guda na zuciyarta tana ayyana mata yadda zata tafi da komai.


           ******washegari ta kunna wayarta,ta kuma dauko number afra fatima da ayman ta sanya,tayi saving number kowa,sannan ta fara kiransu daya bayan daya,duk wadda ta kira sai ta yi mamaki,cike da murna da farincikin samun number aminiyar tasu,afrah ce a qarshe,don tasan dole sufi dadewa da juna akan kowa.


       Da tsiya afra ta fara yi mata

"Kin yiwa kanki fada kenan?" Dariya maimunatu tayi


"Na gaji da kewarku ne" hira sosai suka sha da afrah din,har sai da katinta da hisham ya taba lodawa layin ya qare,afran ta biyota


"Ina fata kin fara shawo mana kai captain" dan shuru tayi tana son tuna waye captain,sai kuma tadan saki fuska


"Manta da wannan batun"


"Seriously you are doing wrong fa maimunatu,kina nufin a haka zaki yita zama,meye ma'anar auren kenan?"


"Karfa ki damu,ni dashi duka bamu damu ba"


"Amma kin sauke amanar anni da amma kamar yadda suka baki?" Tambayar da ta sanya maimunatun yin shuru kenan,har sai da afrah tace


"Qarshen term na ss 2 nima za'a karbi kudin aure na da farid,lalurar abba tasa uncle kamal yace a daga,amma abban da kansa yace a karba,babu wata damuwa,sannan hajja ma tace itama tafi nutsuwa nayi auren,naci gaba da karatun a dakina,tunda shima farid din yana da ra'ayin karatun"


"Allah sarki,Allah ya bashi lafiya kafin lokacin bikin,Allah yasa za'ayi damu,qawata kice na fara shiri tun yanzu" hararar gefanta afrah tayi,kamar maimunatun tana kusa da ita


"Nifa mun kusa raba gaari dake,muddin ba zaki tsaya kiyi abinda ya kamata ba" murmushi maimunatun tayi


"Nifa baki fahimta ba,wai ta yaya kukeso na mu'amalanci mutumin da babu soyayyata ko digo a ransa sai ta marigayiyar matarsa,sannan kuma nima din babu qaunarsa ko qanqani a rai na,hasalima ni wani kallo na daban nake masa,ko inuwa daya idan muka hada Allah Allah nake yabar wajen ko kuma ni nabar wajen,infact ma kallon mugu nake masa,tunda na ganshi yana smoking,bansan ta inda zan fara sonshi ko sakashi ya soni ba" wata qaramar dariya afrah ta saki


"Ban yarda dake ba,ban kuma yarda da dukka hujjojinki ba,kece number one a cikin mu hudu da kika fi kowa son kallon k-dramas na soyayya,har turkish drama kin koya kallo....."


"Kin tunamin ma,akwai wani da naga talla,zanje na kalla" taka katse afran tana miqewa daga kwanciyar da tayi


"Ahaf,kyaji dashi,kici gaba da zama,zaki mamaki idan kk ga wata tayi muku wuf dashi" dariya maimunatun ta saki,idan hakan ta faru batajin tana da asara,saidai unaisa,don ta fuskanci tana da damuwa sosai a kanshi.


         Agogo ta kalla sanda suka gama waya,sai taga lokaci yaja,abinda ya sanyata miqewa kawai ta shiga wanka,so take ta shirya ta fita su gaisa da baba tabawa.


          Dai dai lokacin da yake shigowa sassan nasu,cikin shirin office kamar kullum,slim fit three pieces suits ne a jikinsa Dim gray color dake da ratsin butter color,kwantacciyar fatarsa dake nuna zallar hutu da gayu tayi kyau cikin shigar,jikinsa ba abinda yake sai fidda sassanyan qamshin turaren prive rose George armani dan qasan turkey,kwantacciyar sumarsa sai fidda qyalli take kamar qura baya tabata,komai nashi me kyau tsari da kuma tsafta ne.


       A nutse baba tabawa dake gyara abinci saman dining hannunta kuma maqale da carbi tana ja ta waiwayo tana amsa sallamarsa


"Barka da fitowa" ta fada tana sakin murmushi,taji dadin ganinsa sosai,don ya soma wanke zato da zargin dake ranta,kadan ya motsa fuskarsa,abinda ke alamta yanayin nasa murmushi ko fara'ar kenan


"Barka da asuba"


"Barka kadai manya,mun tashi lafiya?"


"Alhmdlh,jiya na gaji sosai,kuma na dawo late,ban leqo ba" murmushi tayi


"Ai babu komai,ta warware ma" agogon daure a tsintsiyar hannunsa wanda yake mix da zallar ruwan gwal ya kalla


"Zan wuce office,akwai wani abu da kuke buqata?" Kai ta girgiza


"Babu komai,amma ga abinci ko zaka ci" wajen ya kalla,ya sani baba tabawa is the best cook a duk gidansu,tana cikin list din mutanen da yake iya zama hankali kwance yaci abincinsu,amma yanzun sai yakejin bazai iya zaman ba,baima saba cin abinci cikin gidan ba, infact ma bai taba ba


"Ina sauri ne,zan makara"


"Amma akwai kunun gyada irin wanda kakeso,ka daure ko cup daya kasha" ta fada tana hada masa da sauri,bayan ta saka madara da suger madaidaita,don tasan bai cika sonsu ba


"Na gode" ya fada yana karba,har cikin ransa yaji dadin hakan,yayin da baba tabawan ke karantarsa a fakaice,babu wadda ke girki a cikinsu ta bashi kenan?,abinda ya fara zuwa kanta kenan,lallai akwai aiki jazur a gidan,akwai kuma gyara.


         "Tana ciki,ina tsammanin ta tashi,zan shiga ciki na watsa ruwa" tayi masa tayin shiga wajen maimunatun a fakaice,tanason haifar da kyakkyawar alaqa a tsakaninsu,tanason tayi wani aiki da anni zataji dadinsa,sannan kuma ba zata manta dashi ba. Bashi da wani sauran zabi face soma takawa a hankali zuwa dakin,tunda har ta fahimci bashi da nufin shiga,bayaso ta zargi wani abu a ranta game dashi,ya kuma tabbatar kome yayin kamar yayishi ne gaban idanun anni,tunda da ita da anni duka abu daya ne,hannunsa guda daya cikin aljihun wandon suit dinsa,daya hannun kuma cup din kunun ne yana sipping a hankali,ya masa dadi qwarai,ya kuma yi masa yadda yakeso.


         Daure da babban towel ta fito daga bandakin,ta dora qarami saman kanta da yadan jiqe ya kuma bawa sumarta daman kwanciya a bayanta da gefan fuskarta,yau din sakayau take jinta,da alama lafiya tana sake samuwa a gareta,kai tsaye ta isa gaban mirror taja dressing chair ta zauna tana kallon fuskarta data yi wani irin haske ta kuma yi fresh har ita da kanta abun yana bata mamaki,kamar zaka taba ta jini ya fito,ta canza totally,irin canjin da ita da kanta yake bata mamaki.


        Towel din saman kan nata ta cire ta fara goge fuskarta dashi tana maida sumartata dake son shige mata idanu baya,bayan ta miqa hannunta ta jona hand drayer amma bata kai ga kunnata ba,tana goge gashin nata tana dan rera karatun qur'ani,haddarta ta qarshe da bata baiwa ya shaik nasu ba,saboda zazzabin da ta dinga fama dashi kafin tafiyarsu hutu,ta miqe tsaye tana ture kujerar baya,ta kunna hand drayer din ta soma busar da kanta in a low heat.


         Dai dai sanda ya murda qofar dakin ya kuma turo cikin cikakkiyar nutsuwa,tashin farko qamshin hair mist dinta dana hair oil da take amfani dashi wanda ya cika dakin saboda zafin hand drayer din dake kadoshi,ya kuma cakude da qamshin turarenta daya kama dakin suka buso saman fuskarsa.


           Wata ajiyar zuciya ce ta qwace masa ba tare daya shirya hakan ba,bai kuma san dalilin faruwar hakan ba,ajiyar zuciyar data wuce da idanunsa suka lumshe na wasu gajerun sakanni sannan ya budesu tarwai,basu sauka ko ina ba sai santala santalan qafafunta da suma fito ta qasan towel din da take daure dashi,wanda ya tsaya mata iyaka gwiwarta,soma yawo yayi da idanunsa zuwa samanta,faffadan qugunta ya fito sosai ta cikin towel din,kallo daya zaka masa kasan daya daga cikin baiwar da Allah yayi mata ne,ci gaba yayi da kallonta zuwa sama,bayanta dake dauke da farar fata me sulbi da qyalli ya bayyana muraran,da wasu daga cikin gashin kanta da suka kwanta luf a kansa.


         Cikin nauyin zuciya da kuma mutuwar jiki ya daga qafafunsa yaci gaba da shigowa dakin ba tare da maimunatu tasan an shigo ba,don zuwa sannan ta tattaro sumar tata zuwa fuskarta tana tajewa bayan ta kashe hand drayer din,tana kuma ci gaba da rera karatunta da qaramar muryarta mai zaqi da sanyi,karon farko ya sake sakin boyayyar ajiyar zuciya,qira'arta sak irin ta shaheeda,qira'ar malami guda suke bi,sai ya maida qofar ya rufe ya sake matsowa ciki sosai sannan yayi sallama idanunsa bisa kanta.


No comments

Powered by Blogger.