Gurbin Ido 41


"Maimoon"

"Maimoon kuma?,maimunatu?" Anni ta fadi da yadda tafi ganewa a kirata


"Yeah eh" ya amsa mata a tausashe murya can qasa,don har ya qosa annin ta ajjiye waya,don yasan halinta yanzun zaa iya turkeshi da tambayoyin da wala'slla bashi da amsarsu


"Mene ya sameta?" Ta fadi cikin nuna damuwa


"I can't say" ya amsa mata a taqaice yana murza goshinsa da yatsun hannunsa


"Kaii,kayi ta kanka malam,idan zakamin fillanci ko hausa to kayi tun wuri bai qure maka ba"


"Ya salam" ya furta can qasan maqoshinsa yadda ba zata jishi ba sannan ya sake cewa


"Fever.....zazzabi da amai" ya sauya harshe don yasan yanzu zata kuma complain


"Ikon Allah,gata nan zuwa to" ta fada tana sauke wayar,wanda tuni ja'afar din ya rigata kashe wayar.


         "Kodai qaruwa muka samu ne haj anni?" Tabawa ta fada cikin zumudi,fuskarta dauke taf da murmushi,tana latse wayar ta tabe baki sannan ta miqawa tabawa tana cewa


"Banjin haka gaskiya,jikina bai bani ba,amma.....koma meye ki shirya ki wuce,inason ki sakamin ido akan duk abinda yake faruwa,inason na sanin koma meye,sun doshi shekara,ya kamata zuwa yanzu musan me ake ciki,akwai ci gaba koko babu shi"


"To in sha Allahu" tabawa ta fada tana yunqurawa ta wuce dakinta ta shirya,driver ya dauketa,kafin ta wuce sai data biya wajen amma ta gaya mata abinda ke faruwan,irin tunanin da ya darsu a ranta shine ya darsu a ran amman,farinciki sosai taji ya.mamayeta,tana qaunar ja'afar can qasan ranta,tana kuma qaunar duk wani abu daya danganceshi,tana boyewa ne saboda 'yan uwansa da kuma idanun mutane,tana da kara da alkunya irin wanda asalin bafulatanin mutum ke dashi.


          Sanda ta isa asibitin suna gaisawa ya fice a dakin,sai daya dan kalleta ta gefan idanu kafin fitar tashi,bacci take lakadan,sai ya taka a hankali yabar dakin,yana kiran waya yaji an kawo masa motar da yace a kawo masan.


              Sai da baba tabawa ta fidda mata hijabin jikin nata ta sake gyara mata kwanciya yadda zataji dadi kana ta zauna dab da ita kamar me gadinta,itama tana cikin masoya maimunatu,wadda Allah ya dora mata qaunar yarinyar har cikin ranta.


             Bayan la'asar kadan ya shiga gidan,main parlor din babu kowa,hakanan shuru yake sai na'urori daketa aikinsu,sama ya wuce kai tsaye,ya sanya key ya bude qofar dakin nasa kana ya tura yana furzar da iska daga bakinsa,da daya da daya yake duban dakin,yau dakin ya masa shirgi da yawa,baa kintse yake yadda yakeso ba,duk sai yaji ransa ya jagule,mutum ne shi da baya qaunar datti ko qanqani,don haka ya zare tie dinsa ya kuma soma fidda suit din jikinsa,ya zamana daga shi sai farar qal din singlet dinsa ta zallar auduga dake fidda wani sihirtaccen qamshi,a hankali ya fara picking duk abubuwan dake zube a qasa, yana kintsa dakin.


         Sam wannan ba rayuwarsa bace,dole ya koyeta,baya son kowa ya shigar masa daki,sai daya dauki good five thirty minutes sannan ya samu dakin ya masa yadda yakeso,bawai don ya gama qalqaleshi yadda ya kamata ba,yadda jikinsa yayi masa week yasa ya zame a gefan gadonsa ya kwanta,yana runtse idanunsa yana miqewa sambal,wanda tsahonsa gaba daya ya kusa cinye tsahon gadon,abinda zai tabbatar maka da baiwar tsahon da yake da ita kenan.


         Yadda shuru ya ratsa dakin haka yaji kwanyarsa ta dauki shurun,a hankali abinda ya faru dazun ya gifta cikin idanunsa,yadda ta tsorata sosai sanda hon dinsa yakai kunnuwanta,idanunta suka fidda wani kalar tsoro da ya sanyata durqushewa a wajen


"Astagfirullah" ya fada yana maida folding hannayensa a qirjinsa,yana jin ba dadi har cikin ransa,tausayinta ya ratsashi,a sannan baisan zazzabi ne a tare da ita ba,da bai matsa mata hon din ba.


         Tun asalinsa mutum ne mai tausayi da kuma son kyautatawa kowa,duk da zallar miskilancinsa ya boye hakan,mutane da dama suna masa kallon bahagon mutum mai zallar rashin son jama'a da mugun hali,musamman wadanda basu mu'amalanceshi na tsahon lokaci ba.


          Haka yayiya kokawa da kwanyarsa da kuma tarin tunane tunanen da take saqa masa,tsahon wasu mintuna kafin a sannu a hankali bacci yazo yayi awon gaba dashi.


          A hankali take takowa zuwa uwar dakin nasa,gabanta yana dukan uku uku,tana kuma warning daya yanka mata sati guda baya daya wuce,saidai zuciyarta ta kasa jurewa,bata samu komai daga gareshi ba sannan kuma ace ganinsa yana gagararta alhalin suna zaune a gida daya,amma idan batayi da gaske ba sai ta shafe sati bata sanyashi a idanunta ba.


          Da wata nutsuwa data aro ta murza handle din sannan ta tura qofar dakin,idanunta ya sauka a kanshi sanda yake baccinsa very calmly kamar babu wani abu da yake damunsa cikin duniya,idanunta a kansa ba tare data iya daukewa ba taci gaba da takawa,duk takun da zatayi zuwa inda yake bugun zuciyarta ne yake daduwa,yayin da fuskarsan nan dake dauke da wani sassanyan kyau da kuma kwarjini na musamman wanda bai gushe ba koda ckin bacci ne take sake kusantowa gareta.


         Dab dashi ta isa,sannan ta zauna gefan qafarsa a hankali idanunta na sauka kan sambala sambalan qafafunsa,kai kace baya taka qasa dash,fari qal sai lallausan gashin da ya yiwa yatsunsa ado,ya kuma kwanta luf a singalalin qafarsa,hannu takai kamar zata shafo sai kuma ta janye hannunta da sauri,ta maida dubanta ga fuskarsa,zaman da tayi yadan kare mata fuskar tasa,don haka sai ta sake miqewa tayi tsaye a kansa tana morewa kallonsa,kallon data tabbatar inda idanunsa biyu bata isa ta yishi ba,wani irin sonsa ke kwarara a ranta,takai hannuna hankali zata shafi kwantaccen sajen dake gefe da gefan fuskarsa


"Don't touch me" ya furta cikin kaushi cikin muryar mutumin dake bacci,sosai ta tsorata,ta janye hannunta da sauri tana fiddo idanu waje,dai dai lokacin da shima ya fara bude idanun nasa da kadan da kadan har ya zubesu fes kan fuskar unaisa.


        Kafeta yayi da idanu wani zallar bacin rai yana saukar masa,wannan shine karo na kusan biyar da take masa hakan,kamar bazai motsa ba sai daga bisani ya miqe daga kwanciyar a hankali,cikin zuciyarsa yana karanto addu'a,saman gadon ya zauna sosai bayan ya zubo da qafafunsa qasan gadon


"Me kikemin a daki?" Ya tambayeta kai tsaye,sosai tayi qoqarin sanyawa kanta dakiya,duk da yadda jiki da kuma muryarta suke dan shaking kadan


"Zuwa nayi na duba dawowarka,ga abinci can a gama" shuru yayi na second uku


"How many times nake gaya miki ba kowanne jagwalgwalon masu aiki da sunan abinci nake ci ba?,take note please,kada ki sake shigomin daki ba tare da izini na ba" ranta ya sosu kamar kullum,ta kuma kasa hadiyewa


"Amma dai kasan ni matarka ce ko?,sannan kuma ko yaya ne ina da hakki a kanka" qas yayi da kansa,murmushi nason kubce masa amma kuma ya hana kansa faruwar hakan,don baya son raini,daga bisani ya kuma daga kan nasa ya dubeta kai tsaye


"I know,i already know, that's why na baki zabi ai tuntuni,a mutunce zan baki takardarki ki qara wuta,i assure you zaki samu dai dai dake" wani qullutun baqinciki ne ya tokare mata wuya,wanda ta kasa riqeshi,sai ta saki kuka kawai ta juya gudu gudu sauri sauri tabar dakin,yayin da shi kuma ya bi bayanta da wani kallo da tsarabar tsaki,kana ya miqe a hankali yana sanya hannunsa cikin sumarsa yana maidata baya saboda yadda ta cakude,bawai bashi da feelings ba,ko kuma feelings dinsa ya mutu ba,aah.....yana nan a yadda yake,lafiyayyen namiji,wanda wannan dalilin ya sanya ko a baya ya riga jabir aure,amma dai for now bayajin komai akan kowacce diya mace,musamman unaisar da sai a yanzu yake gano fuskarta ranar da qaddara ta fara hadasu da ita a wani club sanda yake aviation school,zuwansa club na farko kenan a rayuwarsa,shima baisan can zasuje ba,daga wajen cin abinci suke shida abokinsa kuma abokin karatunsa muslim,yace yazo ya rakashi wajen wani abokinsa,as'ad zubair,dan gida wani babbban qusan gwamnati a nijeria,acan ya gansu tare da ita,wanda shikam kallo daya ya yiwa fuskarta ya dauke kai,abinda yasa ya kasa shaida fuskarta kenan da wurwuri sai daga baya,duk da ba shigar banza ko wani abu yaga tana sha ba amma abun ya tsaye masa a rai,don yana da tabbacin cikakkiyar mace mai cikakkiyar kunya ilimin addini da tarbiyya ba zaa sameta a wannan wajen ba.


         Ruwa mai dumi sosai ya sakarwa kansa,bayan ya gama yayi brush ya feshe bakinsa da turaren mouth mint mai qamshin strawberry,ya dauki babban towel yana tsane jikinsa daya jiqe da lema sosai saboda yawaj gargasar da yake da ita saman lafiyayyar fatarsa.


            Cikin wasu lafiyayyun kaftan ya shirya kansa farare qal,duk motsin da zaiyi jikinsa na fidda wani irin qamshi mai taushi,ba kasafai ya fiya sanya hula ba,don haka ya riqeta a hannu bayan ya laluba key din motar da yake son fita da ita,ya kalli agogo yana duba lokaci,sai ya sanya wayoyinsa a aljihu bayan yayi kiran daya daga cikin drivers dinsa yaji yana kusa don qyuyar tuqi yakeji,har yanzu kasalar bata sakeshi ba,yayo waje cikin takunsan nan dake dauke da wani salo na dabam da zaka tsammaci tsabar jin kai ne ko izza.


         Sai da suka tsaya sukayi sallar magariba da isha'i a hanya sannan suka qarasa a asibitin,a sannan har yayi waya an musu take away na abinci awa daya kafin ya isa,qarfe takwas da wasu motsi,driver yayi parking motar tasu,ya balle murfin motar ya ficw cikin nutsuwa,iskar asibitin tana kadashi,tana kuma tuna masa wasu abubuwa sa suka shude cikin rayuwarsa.


       Babu yawan jama'a sosai a asibitin,hakan ya bashi damar isa qofar dakin kai tsaye,tun bai shiga ba ya tabbatar akwai mutane a ciki,sai ya tura qofan a nutse da sallama.


             su hudu ne 'yammatan gidan nasu,sai baba tabawa ta biyar dinsu,sallamarsa ta sanya su duka yin dif,yayin da wuta ta daukewa maimunatu dake zaune ta jingine bayanta da filo tana sauraren hirar tasu,sanye take da doguwar rigar atamfa wadda ta zauna mata sosai a madaidaicin jikinta,ta kuma fidda mata shape dinta saboda yadda breast curve din aka yishi cif da cif,ya kuma zauna mata sosai,dogon hannu aka yiwa dinkin saidai an yayyanka shi ya koma kamar spaghetti sleeve,tayi tayi sanda ta sanya kayan a bata baby hijab dinta data saba sakawa amma fa'iza tace a'ah,su da su waye a dakin da sai ta sanya hijab,baba tabawa ma tace


"Ki barshi kawai maimunatu,kada kije ya dameki ma ya gotar miki da canola din" kasancewar sun cire mata ruwan da ake qara matan don ta huta.


            A ladabce suka gaidashi bayan baba tabawa ta miqe ta bashi kujerar da take kai ta matsar da ita gaban gadon maimunatu,maimunatun da tunda ya shigo tayi qas da kanta,ko sau daya bata dago ba,idanunta nakan Canola din hannunta.


         Takalmanta baba tabawa ta jawo tana sanyawa,dai dai sanda anni ke fitowa daga bandaki


"Yaushe ka shigo?" Da hannu ya nuna mata yanzu yanzu


"Zamu wuce,dama shirin tafiya muke"


"Akwai driver?" Ya tambaya a taqaice da muryarsan nan me cike da ginshira


"A'ah a'ah,salma ta tuqomu,gani nayi tafiyar babu yawa" cikin salma ya duri ruwa,ita anni me yasa ba'a sirri da ita?,kawai tace masa eh driver dinne,na meye saita bashi labari?.


          Qarasa dibibicewa tayi sanda ya watsa mata wani kallo na gargadin kinyi na farko kinyi na qarshe,baa baau mota su tuqa a gidan,saidai idan kinyi aure mijinki ya baki,suk inda zasu driver ke kaisu


            Da daya da daya suka fice a dakin suna yima maimunatu sallama tare da cewa zai gobe,murya can qasa take amsa musu,gabanta na wani irin faduwa,tana jin kamar tabi bayansu sanda suka fita,dakin ya rage daga ita saishi daya sanya waya a gaba yana dannawa


No comments

Powered by Blogger.