Gurbin Ido 27


 ********Sosai maimunatu takejin dadin zama gidan bappa sule,saboda tana samun kulawa qwarai da gaske,ga kuma 'yammatan 'ya'yansa da suke kusan sa'anni da ita,hanne da hauwa,sun fita wayo da kuma gogewa,don inda suke din ba za'a kirashi da karkara ba,maraya ce,jininsu ya hadu sosai saboda kirkinsu da yadda suke nuna mata qauna da janta a jiki,nan da nan shaquwa ta shiga tsakaninsu,abun na yiwa maimunatu dadi,ashe dangi dadi garesu,koda ace batasan dangin mahaifinta ba,amma a qalla samun wadan nan a kusa na dauke mata kewa da fargabar rasa dangin mahaifi da kaso hamsin cikin dari.


         A lokacin maimunatu ta sake tabbatarwa kanta lallai inna furera shigo shigo babu zurfi tayi musu,a duk sanda tazo gembu ashe nuna musu take komai lafiya lau,sannan maimunatu najin dadin can shi yasa taqi biyota nan ganin dangi,abunda yayi matuqar baiwa maimunatu mamaki,kasancewarta miskila ba kasafai takan buda baki tacewa inna furera zata bita b,saidai ita kanta takan karanci tsantsar yadda maimunatun ke son biyotan,don tasha gwaba mata baqar magana kan cewa duk ta gama nacin da qwallafa ran,wataqila ita da gembu sai idan taje yawon arba'in idan ta haihu gidan buderi,wani lokacin saidai ta sakaye taci kukanta,wani lokacin kuma har hanya take bin inna furera cike da fata da kuma burin zataji tausayinta ta tafi da ita,saidai ko sau daya bata taba sauyawa ba,daga bisani data qara wayo sai ta tattara ta qyale,ta sanyawa ranta dangana da haquri.


         A sannan maimunatu taga kara ta dangin mahaifiyarta da zumunci,kowa da abinda zai kawo bisa al'adar auren fulani,basu duba cewa DR yace abar komai zai mata ba,cikin qaramin lokaci aka tara mata kayan amfanin kitchen irin nasu kala kala,wanda ba lallai a sameshi a can ba.


**********Biki ya rage saura sati guda kacal,tun a lokacin hidima ta balle daga kowanne bangare,gidan dr da kuma gidan minister harda gidansu amarya ga jabir wato fatima,saidai hidimar da ake gidan minister zata baka mamaki,kai kace bikin yara shida za'ayi ba yarinya daya ba,tun a kwanaki bakwai din da sukayi saura gidan ya fara karbar baki.


*********Katafaren beauty parlor ne,wanda aka tanadeshi musamman saboda gyaran jiki,turara jiki,fidda duk wata dauda,tada komada da maida tsohuwa yarinya a zamanance,waje ne na wane da wane,waje ne na idan ka isa ka shiga.


           Daga cikin wajen fira ce ke tashi,da alama mata an hadu,kuma an samu abunda ake buqata,qawayen amarya samha ne,kowacce da abinda ake mata a wajen,wasu gyaran manicure and pedicure,wasu gyaran gashi,wasu kuma lalle ake zana musu,yayin da wasu kuma ake musu gyaran fuskarsu don su sake kyan gani a wajen bikin.


        Gefe guda amarya unaisa ce cikin wata irin riga data lullube jikinta da ita,sai kanta kawai ake gani,hayaqi dake cike da qamshi ne yake futowa daga wuyanta,magana suke qasa qasa ita da wata matashiya kamarta dake gefanta,wanda hayaniyar da sauran keyi yasa ba zaka iya jin me suke fada din sosai ba saika matsa kusa dasu


"Na samu information.....jibi zai dawo nigeria"


"Na rasa wanne irin so kike masa samiha,ta ya zaki auri mutumin dako zance bai taba zuwa wajenki ba bare ayi maganar so?" Murmushi ta saki tana girgiza kai


"Ba zaki gane ba husna,ja'afar na daban ne,irinsa ba'a jiran sai sunzo zance kafin su cancanta a auresu,na musamman ne shi,sabodashi naqi aure har sai da na samu cikar burina ta hanyar daddy,na nace duk da yayi aure,har Allah ya qaddara rabona ne,matarsa da yake matuqar so ta rasu,saboda shi naqi auren unais naqi auren ahmad naqi auren hanif ke da duk wanda kika sani" kai husna ta jinjina


"Amma wanne qwarin gwiwa kk dashi na cewa zai soki?,da har zaki auri mijin matacciya wanda yake cikin halin SO BAYAN RAI?" Murmushi ta sake saki


"Karkiji komai,duk abinda kk so baka gajiya dashi,soyayyar da nake masa ita zata ja mana ragama,i will do all my best naga ya soni,kada ki manta,ni ba qaramar mace bace,na hada komai da kowanne namiji zaiyi sha'awa ya kuma burgeshi"


"But kin manta kina da kishiya kenan" murmushin dake nuna hankalinta a kwance yake ta saki


"Kusan hakan gaskiya,yarinya ce qarama wadda ta fito daga ruga,kinga yaushe zata tsoratani?,beside ma kuma itama hadi ne,rigima ce irin ta kakanni kawai,abun ma dariya yake ban idan na tuna,namiji irin ja'afar da wannan a matsayin mata idan banda rigimar tsofaffi?very classy guy,har na fara imagining yadda zai fatattaketa wlh a kurkusa duk sanda suka fara haduwa da ita" ta qarashe fada tana sakin dariya,don ta tabbata abinda zai biyo baya kenan,wannan shine yaqini bisa hasashenta.


          Ita kanta husna data hasaso ja'afar din,ta kuma san wayeshi da yadda yake,sai taji hasashen unaisan haka yake,'yar ruga?,ba shakka kam bazai iya zama da ita ba,kamar yadda tayi amanna ba zata iya goga kishi da kyakkyawa kuma me aji irin qawarta unaisa diyar minister ba.


_ba'asan maci tuwo ba sai miya ta qare,muje zuwa_


**********Ƙarfe hudu na rana agogon turkey,biyu na rana agogon nigeria jirgin Turkish airline ya sauka a filin sauka da tashin jirage na malam aminu kano,dauke da tarin passengers,ciki harda jabir usma khalid akko da ja'afar marwan khalid akko.


          Dukkansu sanye suke da wasu lafiyayyun Italian suit,kalolin da suka dace da gayu aji da kuma kyansu,duk wanda ya kallesu sai ya maida kansa ya dada kallonsu,zaratan fulanin samari guda biyu,wadanda ilimi hutu da kuma kudi ya ratsa kowannensu,jikoki kuma jinin khalidu akko.


          Zaman jiran jirgin da zai tashi zuwa gombe sukayi,wanda duka duka bai wuce awa guda ba suka daga zuwa gomben.


          Ta gefan idanu jabir yaketa karantar ja'afar tunda suka sauka a qasar,fuskarsa kadaran kadaham take,babu walwala hakanan ba wata fara'a bace saman fuskar tasa ba,hannunaa guda daya yana soke a aljihunsa,har zuwa sanda suke nufar motar da tazo daga gidan Dr marwan domin kaisu gida.


          Muslimu driver din abbi shine yazo daukansu,cikin wata baqar range Rover,ko ba'a gaya maka kasan cewa sabuwa ce,sai qyalli take da daukan idanu,jabir yayi tsammanin samun masu tarbarsu bayan muslimun da zai tuqa su,saidai babu kowa saishi din,sai ya alaqanta hakan da shakkar ja'afar da sukeyi,don ba kasafai ko a baya zasuyi tafiya tare a samu masu tarbarsu ba.


            Cikin matuqar girmamawa da jin dadin dawowarsu muslimu ya gaidasu,sannan ya sanya jakankunansu a mota,ya shiga ya tada motar suka dauki hanya.


            Tunda suka hau hanyar idanunsa na bisa titunansu,yana qiyasta watanni da ya share bashi qasarsa,watanni ne masu dan dama,dashi kansa baisan gudun da suke ba sai yanzu.


             Tazarar dake tsakanin gidan dr marwan akko da airport din ba mai yawa bace,dalilin da yasa basu dauki wani lokaci mai tsaho ba suka isa gidan.


          Bin ginin gidan nasu yake da kallo kamar wanda a yau yafara arba dashi,ba komai yake kallo ba sai sabon fenti da yaga anbi gidan dashi duk da girma da fadinsa,cikin qanqanin lokaci yaji zuciyarsa na masa qunci,da gaske shirin bikin suke kenan,sai ya dauke kansa daga inda yake kallo din,ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fito ya biyo bayan jabir.


          Tun a harabar gidan tarin ma'aikata dake aiki a qarqashin gidan suka fara musu maraba,kusan da jabir ya barsu,dama shike da wannan juriyar,ya sanya kansa zuwa cikin gidan,a yau din da yake a cikin gidan,sai yaji wani irin kewa da zumudi mai yawan gaske nason ganin mahaifiyarsa ita da gudan jininsa amna,baisan yayi kewarsu kamar hauka ba sai yanzu da yake a kusa dasu.


          Da tattausar muryarsa mai zurfin nan yayi sallama cikin falon nasa,haj aishatu dake nutse saman kujerun alfarma da aka yiwa falon nata qawanya dasu ta daga kanta daga duban farar takardar dake dauke da rubutu a hannunta tana amsa sallamar tasa,idanunsu suka gauraya da juna,ta saki boyayyar ajiyar zuciya mai nauyi


"Alhmadlh ya rabb" ta fada can qasan zuciyarta,sai ta dubi matar da suke tare


"Ki shiga ciki kice ina samra?,ta baki waje kici abinci,zan kiraki mintuna kadan" miqewa tayi tana godiya,sannan tabi hanyar da zata sadata da farfajiyar sassan haj aishatun da take kamae qaramin tsakar gida mai siffar garden da aka wadata da wasu fararen duwatsu na wuta.


         Ci gaba yayi da takowa cikin falon,yayin da amma wannan karon tayi qoqarin ajjiye kunyar dake tsakaninsu


"Maraba lale,ashe kuna gab da isowa?" Wani dan qaramin miskilin murmushi ya subuce masa,ya qaraso gabanta ya zube ya soma gaisheta,tana amsa masa itama cikin kulawa tare da karantar yanayinsa.


             Baiyi wata qiba ba sam,saidai jikinsa a murje yake kadan,sai kuma fatarsa data sakw fresh da kuma haske,alamin weather din qasar data karbeshi,akwai maganganu masu tarin yawa dake ran amma,saidai a yanzun kamar yayi wuri tace komai,don haka ta barwa lokaci na gaba idan suka gama warwarewa daga gajiyar tafiya.


           Yadda ja'afar ya zube mata haka jabir,don marabarsa da ja'afar din daukan cikinsa ne na tsahon wata tara ne kawai batayi ba.


        Kusan shi ya fara fita yabar jabiru da amma,wanda dama koda a baya abun kusan haka yake,hirarsu da amman bata qarewa,zaka sauka jabir ya haifa ba ja'afar ba.


        Yana fitowa sukayi kacibus da ammi,kana kallonta kasan an fara shiga hidima,daga boys quarters na gidan take,taje ta duba yadda aka gyara gami da tsara wajen saboda saukar baqi 'yan biki.


         "Oyoyo,saukar yaushe?,ina ta ciki ban jiku ba?" Murmushin gefan baki yayi,ya gaidata itama a girmame kamar yadda suka saba


"Me zakuci?,don gidan gaba daya a hargitse yake,banjin zaku samu kalar abincin da kuke so"


"Ki turo mana hisham kawai ammi" muryar jabir dake tahowa daga baya ta bata amsa,don yasan halim ja'afar din sarai,tsaf zai iya cewa


"We are okay" bayan shi magana ta gaskiya yunwa yakeji


"Banajin zaku samu hisham cikin gidan nan jabir,gidan yau kusan babu kowa sai baqi,yana can hidimar saukar nasu baqin"


"Ba damuwa zan kirashi" jabir ya fada suka soma gaisawa sannan shima yabi bayan ja'afar wanda ya wuce sassan anni,ammi tayi gaba tana tunanin abinda zata sa a samar musu me dan sauqi da zasu iya ci.


           Sanda ya sanya kai falon har yayi kamar zai koma saboda muryoyin baqi da yaji sai kuma yaci gaba da cusa kai,sai daya shiga din sannan ya fuskanci su waye a falon,anty maama ce,sai ummi badi'a matar uncle abbas.


         Qaramin tsaki yaja qasan ransa,su kadai amma sun cika falon da hayaniya kamar mutum dubu,dukkansu maraba suke masa banda anni da taja bakinta ta tsuke,ya qaraso ya zauna saman hannun kujera yana amsa marabarsu,kafin dukansu su biyun su miqe anty maama tana cewa


"Anni bari muje,nan da awa biyu idan bamu dawo ba don Allah hayatu ko muslimu suje su debomin yaran nan"


"Zan gaya musu,amma kada kuje ku zauna kuma"


"Muna samo abinda mukeso zamu dawo"


"Allah ya tsare" suka amsa suna ficewa,sai falon ya rage saura shi da annin.


           "Barka da warhaka" ya fada cikin rusunawa

"Barkan ka" ta bashi amsa a taqaice tana bata fuska,saidai a yau din baiji bata fuskarta ya dameshi ba kamar yadda suke da ita a baya,yana jin a wannan bigiren shi yafi cancanta ya bata fuska akan kowa


"Ina wuni?"

"Daban wuni ba zaka ganni?,ai da zamanka kayi a sassanka,ni yafi cancanta nazo na gaisheka ai,tunda yanzu ka zama uban kowa,sai abinda kakeso ka tsara zamu dinga bi,tunda kaika haifi kanka" kyawawan idanunsa ya lumshe kana ya budesu,ita tsohuwar batasan abinda yakeji bane?,batasan irin qunci da ciwon data haddasa masa ba haka siddan yana zaman zamansa yana lallaba rayuwarsa?


          Muryoyin sallamarsu ta katse anni daga ruwan tijarar data debo ta shirya sauke masa su tas yau a kansa,duka 'yammatan gidan ne suka shigo,wansa dawowarsu kenan daga gyaran gashi.


        Da hayaniya suka shigo saboda yadda sabgogin bikin suka fara musu dadi,amma suna hada idanu kowacce sai tayi turus,ta kuma saita bakinta,kudin goro ya yiwa gaisuwarsu ya amsa su gaba daya,babu wadda tayi gigin zama dukka suka juya suna barin sashen,daidai lokacin da amna wadda aka yiwa kanta gyara na musamman take rugowa cikin falon riqe da leda a hannunta cike da kayan qwalam tana qwalawa anni kira gami da cewa tazo suci.


         Cak ta tsaya sanda tayi idanu hudu da mahaifin nata,sai kuma ta watsar da ledar hannun nata,ta take da gudu tayo wajensa tana kiran 


"Dadddyyyyy...." Qasa ya sauko ya tanqwashe qafafunsa,ya kuma bude mata hannayensa gaba daya,yana jin wata irin qauna da qarfin jini dake tsakanin uba da diyarsa yana fusgarsa,ta kuwa iso ta fada jikinsa,ya sanya hannayensa gaba daya ya rungumeta cikin jikinsa yana sauke ajiyar zuciyaSosai ta qanqameshi itama kamar zata koma jikinsa


"Daddy" ta sake kira tana sauke ajiyar zuciya bayan shuru da tayi na wasu sakanni,dukka gaba dayansu shida annin sai tausayinta ya lullubesu,ya dagata sosai ya sake tallafarta yana dubanta


"Amnee" ya kirata da sunan da shaheeda kadai take kiranta da shi


"Daddy....kaima shine ka tafi ka barni?,mommy ta tafi,amra ta tafi,kaima haka?" Kai ya girgiza yana shafa sumarta da tasha gyara tana ta qyalli


"Am sorry my little angel......daddy yana neman afuwa,bazai sake tafiya ya barki ba" fuskarta ta washe sosai,da alama taji dadin maganarsa,sai kuma ta sake cune fuska


"Adda maimoon ma ta tafi,har yanzu bata dawo ba,daddy zaka je ka dauko min ita?" Anni ya kalla da alama yana da buqatar qarin bayanin sanin wacece ita,kamar kuma ya jijji sunan a bakin annin da ammansa,ganin anni bata bashi wani hint da zai gane wacece ba sai ya gyada kai kawai


"Zan dauko miki ita lil princess" qanqameshi tayi tana murna


"I love you daddy"


"Love you more amne na" sai ta shige jikinsa tana sauke ajiyar zuciya dake nuni da samun cikakkiyar nutsuwa.


        Karamin tsaki anni ta sake


"Kalli.....wannan daukar hakkin har ina?,Allah ya kyauta wannan banzar zuciyar taka data kasa daukan kalar tata qaddarar" bai tankawa annin ba,don yasan jiqaqqiya ce tsakaninsa da annin,kuma ba zata qyaleshi ba tabbas sai ta maida masa kai tsaye ko kuma a fakaice.


        Koda ya tashi tafiya qin yarda amna tayi ta sauka daga jikinsa,tana maqale dashi,da ita yatafi sassansa,ya samu.jabir har ya fito a wanka,yanata fama da wayoyin al'umma.


No comments

Powered by Blogger.