Gurbin Ido 24


 24


        Kai tsaye jauro ya damqawa anni rubutaccen kwatance har zuwa gembu mahaifarsu maimunatu tushensu asalinsu,inda yake da tabbacin zasu samu qannen kakan maimunatu da sauran danginta na wajen uwa da zasu iya aurar da ita.


            Koda inna furera ta samu wannan labarin hankalinta yadan kwanta kadan,saboda tasan babu wadda zasu fara samu sai babarta inno,ta kuma san cewa duk kanwat jaa ce,inno ba zafa taba amincewa ba matuqar taga irin wannan ci gabanne zai samu jinin shatu.


              Saidai cikin rashin sa'a ga inna furera,sa'a gasu anni,sai suka samu qanin kakan maimunatu,wanda ya karbesu hannu bibbiyu,ya kuma laluba bangaren mahaifan shatu ya sanar musu da abinda ke faruwa,sukayi murna qwarai,suka kuma amshi su uncle umar wanda dr marwan ya wakilta nemo auren maimunatun,karba ta girma karamci da kyautatawa irin na fulani.


         Sun karba kudin auren maimunatu,sun kuma amince da satittikan da aka yanke na daurin auren maimunatu,an rabu cikin mutunci da mutuntaka,zuciyar dangin maimunatu fes,a yanzun duk wata shakka da suke da ita kan rayuwar da maimunatu ke ciki ta kau,hankulansu suka sake kwanciya.


           Sosai hankalin annin ya sake kwanciya,ta kuma sake nutsuwa,hukuncin kuma da suka yanke na wanzarwa da ja'afar komai ba tare da sun sake bi ta kansa ba taji bai dameta ba,tunda anyi me wuyar,sauran kuma zata sanar masa da kanta idan suka koma gida suka huta suka kuma nutsu.


           Sati daya kacal sukayi a adamawa suka tattaro sukayo gombe,anni cike da farinciki da murnar yadda aka basu maimunatun,kamar yadda honorable ya basu auren diyarsa shima,aka sanya rana kuma dai dai da wadda aka saka ta maimunatu,a yanzun abinda ke gaban anni shine shirin auren.


       Yammacin wata asabar,cikin daya daga cikin falukan annin wanda aka qawata da tattausan carpet,tana zaune ta miqe qafafunta sosai,daga gefanta surukarta ce,matar uncle usman,mahaifiya ga hafsat,shigowarta kenan gidanma gaba daya.


          Suna tsaka da gaisawa maimunatu ta shigo falon,sanye da brown din chiffon skert,sai rigarsa me dogon hannu,ta yane sassalkan gashinta da mayafin kayan light brown,fuskarta ta fito fayau tayi kyau sosai,duk da kasancewarta ba ma'abociyar son kwalliya ba,saika tsammaci ta fito ne daga yankin larabawa.


         Sai data isa gaban annin,ta ajjiye hadin fruit salad data yi,wanda duk cikin girke girken da take koya ne hannun tabawa tana murmushi ba tare data ce da annin komai ba


"Da kyau,sannu da qoqari muna" ta ambaceta da sunan da baba tabawa ke kiranta wasu lokutan,sai ta juya sashen da momy kamar yadda suke kiranta take ta soma gaidata.


            Sama sama ta amsa mata,maimunatun bata wani lura ba ta miqe abinta ta fice,duk da annin taga abinda ya farun,amma sai tayi kamar bata gani ba,ta jawo fruit salad dinta ta fara ci,dai dai lokacin da momy ta motsa kadan,ga duk wanda ya qare mata kallo yasan maganganu ne fal harshenta


"Su ja'afar kuma ashe ankai kudi,saiga daddynsu ya shigo da zancan"


"Eh,anyi haka" anni ta fada ba tare data dubeta ba


"Diyar commissioner ko?,samiha,sai kuma wata agwai,wannan yarinyar data shigo" cak anni ta dakata da shan fruit salad din da take,ta sanya hannu ta zare gilashin fuskarta da takanyo amfani dashi wasu lokuta


"Inaji yanzu kikaji na kirayi sunanta ko?,to ba agwai sunanta ba,kada na sake jin wannan sunan daga bakinki,maimunatu take"


"Ayi haquri,bada gangan na fada ba,sunanta ne ga kwantan"


"Ato,gwara kiyi ta kanki" ta amsata tana maida gilashinta,maganar data tsayawa haj munubiya Momy a rai,wanne irin so annin ke gwadawa yarinyar ne?,duk yadda su shaffa'u ke gaya mata bata yarda ba sai yanzu da dukka alamu suka nuna,tanaso tayi shuru hakanan amma kuma maganganun bakinta basu qare ba,don haka fa sake motsawa


"Amma yanzu anni,fisabilillahi ba za'a duba halin da yarinyar nan hafsat ke ciki ba?,gida bai qoshi ba za'a kaiwa dawa?" Sake dubanta tayi wannan karon kallon tsakiyar idanu,tafi kowa sanin wacece munubiya,kaf surukanta babu wadda take fama da ita kamarta


"Shi sagirun da yazo da zancan,bai gaya miki anihin abinda nace dashi bane?" Kai ta gyada tana jinjina taurin kai irin na annin


"Ya gaya min"


"To du Allah du annabi munubiya,banason maida hannun agogo baya kinji ko" sai ta gyada kai kawai,zuciyarta fal takaici,taso ace diyarta ta samu ja'afar,ba tun yanzu ba,tun aurensa na fari,a sannan hafsat din bata wani nuna da yawa ba,take gani shine silar data gaza jan hankalinsa har ya auri shaheeda,a yanzun kuma da take ganin komai yakai anni tayi ruwa tayi tsaki ta hana wannan damar.


            Miqewa tayi tana rataya jakarta,annin ta dubeta


"Zan wuce anni,Alla ya sanya alheri"


"Ameen,ki gaida gida,a gaida yaran" har tayi gaba ta sake cewa da ita


"Yauwa,ji mana" tsaiwa haj munubiya tayi


"Ki turon khalid,na gaza samunsa a waya,kice ina nemansa" dole hakanan ta amsa mata da to,sannan ta taka ta fice.


            A hanya ita kadai kamar ta taune zuciyarta saboda baqinciki,haka ta fitoma daga gidan babu wanda ta yiwa sallama,duk irin bautar da khalid din kewa annin har yau bata jin tana masa rabin son da takewa ja'afar,a bakinsu shaffa'u takejin kamar ya soma son yarinyar amma annin ta hanashi ta bawa ja'afar,duk da bata taba jin qaunar yarinyar ba amma taji zafin hakan,hakanan ta hana hafsat ja'afar ta bawa wasu baare daban,wannan babu abinda yake nunawa illa zallar qin da take mata,qwafa taja gami da dogon tsaki,zata gamu da khalid dinne.


          "Allah ya sawwaqe,ya yaye miki munubiya" anni ta fada tana jan wayarta


"Shima zan gamu dashi,shegiyar kafiya da riqon abu a rai,wannan wanne irin SO BAYAN RAI ne?,tana nan tana yaqi a kansa bai sani ba,tana ta baqin jini wajen jama'a.


           Tana ta bulayin nemansa khadim ya shigo


"Kiramin jafaru da wayarka"


"Allah yasa ya daga,na canza sabon layi" ya fada yana laluben wayar a aljihunsa,sannan ya zauna daga gefan annin yana tambayarta me zaya samu cikin dakin nata


"Ban sani ba,zaka kamomin shi ko sai ka cinye kurwata tukunna" ta fada tana harararsa,don tace khadim din ya cuka kwadayin tsiya,yana qunshe dariyarsa ya dannan kiran ja'afar din,saidai har tayi ta tsinke bai daga ba,sai da ya maimaita kiran ana uku ya dace ya daga,kai tsaye ya miqawa anni wayar ya koma corner falon yayi zamansa yana daukar wayar annin.


         Dan madaidaicin waje ne dake bayan gine ginen gidajen nasu,wanda ke shimfide da korran ciyayi,kujerun qarfe ne masu kyau guda uku da table dinsu a tsakiya,saman table din akwai glass cup daya cika da lemo yana kurba time to time,tsaye yake ya baiwa table din baya,hannuwansa riqe da wasu fararen takardu kusan guda shida,wanda ya bada hankali sosai a kansu,da alama akwai muhimmin abu da yake dubawa a ciki,sanye yake cikin shirt da trouser masu taushi duka na kamfanin Louis Vuitton,iskar wajen ta gauraya da daddadan turaren jikinsa tana bada wani yanayi me dadi,wasu slippers ne masu kyau na fata sanye a qafarsa,hannayensa goye a bayansa,lokaci lokaci yakan cire hannun ya shafi tausasan labbansa.


         Karamin tsaki yaja sanda wayarsa ta sake qara,karo na kusan uku kenan,sauke takardun yayi daga fuskarsa a hankali,kyakkyawar fuskarsa dake fidda wani irin kwarjini da kuma calmness irin nashi ta bayyana,taku biyu yayi baya ya isa gab da table din inda wayar tasa take,har yanzun wani busar sarewa take me dadin sauraro.


         Sai daya kalla screen din some few seconds sannan ya shafa wayar ya karata a kunne


"Assalamu alaikum" ya fadi with husky voice,daga can bangaren anni ta amsa,saiya dan sauke numfashi kadan jin anni ce,ya maqale wayar a kafadarsa yana gyara takardun bayan ya soma da gaisheta


"Lafiya alhmdlh,manya,me yasa kake mancewa da gida?"


"Taya zan mance daku anni?,akwai abubuwa ne da har yanzu bayi settling dinsu ba" haushi ya cikata,koda yaushe maganarsa kenan,to itakam koma meye dai ai ta kawo qarshen abun,don haka cikin kaushi tace dashi


"Kullum maganar dai kenan,tamkar kaine kafi kowa sabga a duniya,to koma dai meye wannan matsalarka ne,mukam ba zamu zauna mu zuba idanu rayuwarka taci gaba da tangal tangal a haka ba,bayan ko talatarka bakaci ba balle laraba,ban sani ba ko dan uwanka ya labarta maka" ta sauke maganar tana jiran amsarsa,dai dai sanda ya gama gyaran takardun ya duqa yana niyyar ajjiyesu saman table din


"Me kenan?"


"Kai kudin aurenka wa 'yammata biyu,nan da sati hudu kuma in sha Allahu kowacce zata shigo gidanka a matsayin matarka,saboda haka ka maida hankalinka,ka tattaro kayo gida,koma meye daga baya zaka qarasashi"


"What a funny story anni" ya fada cike da tantama yanayin fuskarsa na sauyawa zuwa ga yanayi na son yin murmushi,saisai murmushin bai fita ba,saboda yadda yaji labarin yafi masa kama da tatsuniya


"Anni,zancan aure fa kike da mata har biyu" ya fada sounding like dariya zata kubce masa,yanayin da anni tagama karantoshi tsaf,saita hade muryarta itama


"Kafi kowa sanin wacece maryama farouq akko ko?"


Yes,yasan anni fiye da kowa a gidan dama family dinsu,tuna hakan ya sanya duk wani shakku dake ransa wankewa,uwa uba yadda ta kirayi sunanta in full ya sake tabbatar masa she's serious


"Seriously?" Yayi tambayar da wani irin tune,tambayar da baisan dawa yake ba,da anni yake koda kansa?


"Inadai gaya maka,sati hudu kacal suka rage"


"Ya salam ya Allah,anni why?, Me yasa?,mu nawa ke zaune a gidan,amma why me?" Ya fada yana jin wani irin zafi na taso masa har saman fuskarsa


"Bakai kadai ba,wannan karon duk wanda yakai munzali sai ya bar gidan nan ya tafi nasa,abun ya isa hakanan"


"Okay okay fine.....zan dawo zanyi packing komai nawa zan bar gidan,but..... please anni,kada kiyi punishing nawa ta wannan hanyar,bazan iya zama da kowacce mace ba anni please" ya fada cikin kwantar da murya,tare da fatan zai shawo kan annin.


         Baki ta tabe daga can,dama tasan za'a rina,tasan halin ja'afar sarai,tasan komai zai iya faruwa,kuma dama bata tarki abun ba sai data shirya masa


"Kaga babu fa wannan zancan,an riga an gama magana da magabantansu,ba zaka maidamu qananan yara ba,kuma ba gidan mukeso ka bari ba,zaman aure mukeso kayi" zaman aure kamar wani mace?, Ya qiyasta hakan cikin ransa


"Anni,ki fahimceni mana,ta yaya za'a auramin mata har biyu bayan babu fahimtar juna a tsakanina da kowaccensu bare azo maganar soyayya wadda already nayi banning dinta"


"Zaku fahimci kawunanku a dakunanku ai" ya zuwa yanzu ranshi ya sake baci fiye da dazun


"Anni!" Ya kirayeta da murya mai kaushi kadan,wanda shi kansa baisan yayi hakan ba

"it will not be possible,ta yaya hakan zai yiwu?"


"Ahap gashinan kuwa?" Da gaske take ba zata fahimceshi ba,saidai ma idan bai wasa ba ta sake tunzurashi,don haka sai kawai ya yanke wayar da sauri,sannan cikin wani irin zafin nama yaja kujera guda daya gabansa ya zauna a kai bayan ya jefa wayar saman table din,baya ko tsoron ta fashe.


        Dukka hannayensa ya cusa cikin gashinsa yana yamutsawa tare da fadin


"No...no,it can't.....it can't.....am not ready.....am not ready to face it this challenge" ya fada cikin zafi,sai kuma ya sake miqewa,yana buqatar yayi magana da wani,sai ya janyo wayar yana furzar da zazzafar iska daga bakinsa ya soma laluben number ammansa,gab da zata shiga ya sauya shawara ya kashe,sai ya maida kiran kan jabir


"Where are you?" Ya tambayesa kai tsaye,tsabar bacin rai yama manta inda yace masa zaije,tunda jabir din yaji muryarsa yasan cewa akwai matsala,cikin ransa yake fatan Allah yasa ba depression mode dinsa ne ya motsa ba


"Am on my way,is there a problem?"


"Zaka dauki mintuna nawa?"


"Few" ya amsa masa a taqaice


"Okay,am waiting for you, please don't stay long" bai jira amsarsa ba ya katse wayar ya sake jefata inda ya dauko,dukka hannayensa ya zura cikin aljihun wandonsa,yahau kai kawo tsakanin wannan bangaren zuwa wancan,wanne irin hukuncine wannan da zasuyi masa?,wannan auren aiko mace a wannan zamanin ba za'ayi mata shi ba,wadanne irin mata ne su kansu da suka dauki kasadar aurensa ba tare da sun gana dashi ba?,kawai sun amince da auren mutumin da bashi ya nema yardarsu ba?,anni tana tunanin akwai macen da zata cike masa GURBIN shaheeda ne?,babu?,sam babu,yanajin cewa daga kanta an gama haifar diya mace a duniyarsa,wadan nan matan data debo GURBIN IDO ne kawai,fanko ne,ba zasu taba zamtowa IDO ba wato shaheedansa,yayi imani da hakan har cikin zuciyarsa.


        Kafin jabir yakai ga isowa ya duba agogo sau babu adadi,a gaban idanunsa cave ta saukeshi,ya fito dauke da niqi niqin siyayya a manyan ledoji,sai a sannan yayi noticing wani abu,kwana biyun jabir fita yake siyayya kusan koda yaushe,kamar wanda ke shirin komawa gida.


             Sai daya shiga gida ya aje kayan sannan ya sake fitowa,kafadarsa ya dafa daga baya


"Meye haka ne man?" Waiwayowa yayi ya dubi jabir,idanunsa a sannan har sun kada sun sauya kala saboda zallar bacin rai,wanda ta nan ake iya gane qurewar bacin ransa


"Yanzu kamar ni?,kamar ni anni zatayi forcing dina akan aure?" Tuntuni ya shanshano komai,don yasan da komai din,ya samu labari,saidai baiyi gangancin shaidawa ja'afar din ba,ya zuba idanu yaga ya caftar zata kaya.


        Dubansa sosai jabir yayi


"That's right...." Sosai maganar ta baiwa ja'afar mamaki,ta kuma sake qular dashi


"Like how? what are you trying to say jabir?" Ajiyar zuciya ya sauke,shima ya maida hannayensa aljihunsa


"Ja'afar,ka gaza nutsuwa ka karbi qaddarar rayuwarka kayi moving forward yadda ya dace....."


"Yanzu qoqarin me nake?" Ya fada da zafinsa


"Yes,naga canji,kanata qoqarin maida harkokinka yadda ya dace,amma bata iya wannan fannin kawai ya kamata ka maida kai ba wajen gyarawa,ya kamata ka sake building a new family da zasu debe maka kewa,su sake maidaka cikakken mutum,abinda kai ka gaza yi anni ta tayaka ginashi,so bai kamata ka zargeta ko kaji haushi ba,a shawarce ka tsaya ka nutsu,ka yiwa abun kallo na fahimta,don't upset please"


"Okay na gane,kaima kana goyon bayan abinda tayimin kenan?, wait.....waima wa yace musu a yanzun ina sa buqatar wata mace cikin rayuwata?,dolen sai na rayu da wata,a barni nayi rayuwata a haka mana,me na ragu dashi" jabir zai sake cewa wani abu ja'afar din yaja tsaki ya daukin wayarsa a fusace ya wuce cikin gida da sassarfarsa.


No comments

Powered by Blogger.