Gurbin Ido 20


[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 20

        Sannu a hankali rayuwa ke juyawa,cikin wani yanayi me dadi ga maimunatu,dukkan wani ci gaba a hankali yake samunta,ta zama cikakkiyar diya ga Dr marwan,bai taba bari an banbantata cikin duka hidimar da zaiwa iyalinsa ba,bata da matsala da kowa

kasancewarta yarinya me haquri kawaici da kuma sanyin hali,zallar biyayya da kuma girmama kowa koda na qasanta ne,wannan ya siya mata soyayya sosai daga wajen iyalin gidan dr marwan,saidai a rayuwa ba kowane zai soka ba,hakanan bazaiyiwu ace kowa gudunka yake ba,cikin surukai da kuna sauran jikokin anni ba za'a rasa wadanda suke mata wani kallo na daban ba,duk da babu wanda yasan daga ina fa fito,ko kuma ita din wacece.


       Babu abinda yafi mata dadi irin ilimin da take samu,batasan cewa a baya rayuwar da take rayuwa ce dake cike da zallar duhu ba sai yanzu,batasan haka ilimi yake da dadi ba sai yanzu,duk cikin abinda anni tayi mata babu abinda take jin ya mata dadi fiye da kima irin karatun da take,qoqarinta kan karatun ya ninka adadin karatun da ake mata,wannan ya sanya ake qara mata karatun da yawa,yake kuma mugun gudu,hakanan ta fannin boko,shi kansa malamin yakanyi mamaki idan yaga wasu guraren da yawa ta iyasu kafin suxo wajen,dole hakan kuma ta kasance,don kuwa duk sanda ta koma gida bita take sosai,tare da duba duk wani karatun da ya shafi wanda aka qara matan,koda yaushe baka rabata da dan qaramin dakin karatu dake gidan,wanda dr ya qirqireshi saboda yaran,su din kuma ba wani damuwa sukayi dashi ba,ba kasafai suke shiga,zuwan maimunatu da yawan shigarta wajen sai wajen ya soma rayuwa,a kullum zata tsaftaceshi,ta kuma bata lokaci a can tana nazari,daga fannin bokon har na addini.


         Zuwa lokacin maimunatun ta goge sosai,a hakan ma don ba ita din ba me yawan buri ko son qyale qyale bace,sau tari idan zasu shopping ko wani abu makamancin haka bata binsu,suyita mata tsiya da kazar gida,saidai ta bisu da murmushi,ta gwammace ta zauna da amna suyita labarai,tatsuniya da sauransu,ko ta tsefe kanta ta gyara mata tayi mata kitso ko kalba,ita kanta yarinyar tunda maimunatu ta fara kula mata da kanta ta daina yarda a kaita saloon,har yanzu tana nan a bufulatanarta,bata bari ta jirkita komai nata ba baya ga suturar jiki da kuma tsaftarta data qaru.



************K'arfe uku na azahar anni ta sanyata ta shirya don rakata gidan uncle abbas qani ga dr marwan,zata duba diyarsa da bata da lafiya ita da yaron da amaryarsa ke goyo,magana tayi da maimunatu kan ta shirya tayi mata rakiya ita da tabawa,babu musu ta shirya din,karo na biyu kenan da zata fita tun zuwanta gidan,fitar farko ma hisham ne ya debesu ya kaisu wani eatery sukaci abinci saboda qarin girma da ya samu a asibitinsu,shima tun suna shirin take kallonsu,duk da sun mata tayi amma tace a'ah,zata zauna da anni,kada a barta ita kadai.


        Har sun fita suka dawo sukace yaa hisham din yace ta fito suje


"Kuje kawai ku dawo ina jiranku"


"A'ah,tashi ki shirya kuje" anni tace da ita,a dole ta sauya kaya ta bisu.


          Kusan daga tafiyar har dawowar a takure take,saboda yadda yace ta zauna gaban mota,suna tafe kuma yana janta da hira da 'yar tsokana,abinda ya aza mata nauyi sosai,yasa ta dinga jin kunya ta kuma gagara sakewa har suka dawo.


     Bala'in nauyin hisham din takeji,saboda yadda yake mu'amalantarta ya banbanta da yadda sauran mutan gidan suke mu'amala da ita,yana da kirki sosai,yawan barkwanci musamman idan a cikin gida yake cikin family dinsa.


       Tsaf ta shirya cikin doguwar rigar atamfa,sabuwa ce,cikin dinkunan da anni tasa akayi mata,ta yane kanta da madaidaicin mayafi,dankwalin yana riqe a hannuta saboda rashin sabo da daurashi


"Ma sha Allah"anni ta samu kanta da furtawa,saboda wani irin kyau da maimunatun tayi mata,tana ji a ranta ko a yanzu ja'afar ya dawo bai isa ya kushe maimunatu ba,don ta goge qwarai,ta tabbata ko a rugarsu yanzun sai sunyi mamaki idan suka ganta.


       Daga ita sai annin sai amna suka tafi,drivern gidan shike tuqa su,jifa jifa suna hira da anni,hankalinta kuma na sama hanya,tana sake ganin ainihin garin na gombe,tafiyar duka duka bata wuce minti talatin ba suka isa unguwar,unguwa ce itama me kyau dake dauke da gidan masu wadata.


           Maimunatu na dauke da amna suka fara takawa zuwa cikin gidan,jikokin annin uku suna biye da ita suna ta tsokanarta,saidai taqi kulasu,da alama a qule take dasu,saida sukazo qofar falon daya daga cikinsu tace


"Anni,bari na cire miki takalman"ta fada tana dariya gami da duqawa


"Ke arcan,kiyi ta kanki,ni ba take nake ba,gwandamar banza,wallahi ina tafe cikin gidan nan,duk saina bada sadakarku" ihu yammatan suka saki,namijin na musu dariya harda dafe ciki


"Eh,ba zaku saka min 'ya'ya a gaba kuna cinye tattalin arziqinsu ba,kowa ya kama gabansa mazanku da matanku" tasa kai cikin falon abinta tana sakin sallama,yayin data barsu suna ihu da dariya na tsiyar data lafta musu.


        Karbar girma amaryar uncle abbas tayi musu,ta dinga nan nan da annin,da alama yar gaban goshinta ce,saida suka gama shafe wasu mintuna sannan dayar ta shigo,haj munubiya,uwar gidan uncle abbas.


          Da kallo anni ta bita kafin ta dauke kai tana amsa sallamarta,ta samu waje cikin jin izza ta soma gaida anni,saidai cikin girmamawa ne,sanin cewa annin bata daukar raini sam,daga nan ta zauna ana taba hira da ita lokaci lokaci.


         Karo na kusan biyar idanunta suka sake kaiwa kan maimunatu dake wasa da hannayen amna


"Anni a ina aka samo mana bafulatana haka?" Waiwaya tayi ta dubi maimunatu sannan ta dawo da dubanta ga munubiya


"Surukarku ce"


"Matar wa kenan?" Dan qaramin murmushi annin ta sake


"Ina fatima.....ke fadima" ta qwalawa daya daga cikin 'yammatan gidan kira ,dubanta tayi sanda ta qaraso


"Dauketa ki kaita dakinku,daga nan ki duban idan hafsatun ta farka"


"To anni" ta amsa da girmamawa,da alamu dukka cikin yaran ta fisu nutsuwa da hankali,waiwayawa tayi fuskarta dauke da murmushi ta cewa maimunatu ta taso.


        Tana gaba tana biye da ita,har zuwa sanda suka isa isa qofar wani daki,ta tura ta saka kai da sallama a bakinta maimunatun na biye da ita.


        Wata matashiya ce zaune saman gadon,ta jingina bayanta da fuskar gadon,sanye da wata doguwar riga cotton me yankakken hannu,kanta hula ce baqa da ta dan jata baya kadan,fuskarta babu alamun annuri,da alama itace mara lafiyan da annin taxo dubawa.


         "Ya hafsa,anni tazo dubaki,tace na duba naga idan kin tashi" fuska ta yatsine,murya kuma can qasa tace


"Banga amfanin zuwa duba nin data yi ba,tunda ba zata iya maganta min komai ba" maganganun da maimunatu ta jisu wasu iri a kunnuwanta,har sai daa dan saci kallonta,wadda take qoqarin sake shigewa cikin bargo ta kuma kwanciya abinta


           "Ayyah yaa hafsa,wai me yasa kike irin wadan nan maganganun ne?"


"Kinfi kowa sanin dalilin,ja'afar ne,ja'afar shine dalili" dubanta fatima tayi,sannan ta matso gefanta kadan ta zauna


"Me yasa ba zaki haqura da yaa ja'afar ba yaa hafsa?" Idanu ta zubawa fatiman,tana kuma qanqanceshi,tsahon wasu sakanni sannan ta amsa mata da


"Ashe baki da hankali fatima,hala bakisan meye ainihin haqiqanin ma'anar so ba ko?,ta yaya zan bar ja'afar?,kinsan yadda nake sonshi kuwa?,wait.....waye ma ya gaya miki ja'afar irin mutanen da ake iya haqura da soyayyarsu ne?" Kai fatima ta rausayar


"Amma dai yaa hafsa,bake kadai cikin family kike da irin wannan qudurin ba,kuna da yawa,ke surayya hannah da walida,ga madina dama sauran wadanda basu bayyana ba,kunfi kowa sanin waye yaa ja'afar tun sanda yake lafiyarshi lau ma bare yanxu da kura tayi hauka,ke kinsan wayeshi,duk cikinku bana jin akwai wadda zata iya dashi idan aka barku,wannan dakatarwar da anni tayi muku ma kamar taimakonku tayi,ta kuma tsare muku mutunci da martabarku"


"Ta barmu din yafimin,yafimin wannan kisan mummuqen......"


"Don Allah ina bandaki?" Maimunatu ta katse musayar maganganun da suke a tsakaninsu,sai a sannan fatima ta waiwayo


"Yi haquri don Allah,na barki a tsaye,gashi can" ta fada tana mata nuni da wata qofa dake kulle,takawa tayi a hankali ta nufi bandakin,saidai zuciyarta cike fal da mamakin maganganun hafsah,har yanzu dama akwai irin wannan soyayyar?,waye ne shi wanda takewa irin wannan soyayyar?,wannan tunanin ya tuna mata da himunta da kuma buderi,ko a wanne yanayi kowannensu yake ciki?,ta tabbatar himu yana can yana dakonta,yana kuma nege da shauqin ganinta,wanda kusan ita dinma tana jin hakan a ranta a kansa.


         Fitsari tayi sannan ta daura alwala,ta fito daga bandakin tana gyara rolling din mayafinta


"Ba zaki gane ba fatima....na jima inason yaa ja'afar,ba zaki gane me nakeji ba a kansa" kalaman hafsa da suka sake shiga kunnuwanta kenan,ta dan kauda kanta tana jin kunya da mamakin yadda budurwar keta haqilo akan namiji,ta tayar da sallah abinta.


         Kafin ta idar sun gama maganar,wanda fatima ce ta sakar mata ganin ba zata fahimci abinda takeson nuna mata ba,a nan suka zauna suna taba hira ita da fatima,wanda dukka kusan akan islamiyya ce,da alama itama mayyar islamiyyar ce kamar yadda maimunatu take,kusan bata taba ganin fatima a gidansu ba,saboda yawanci tana islamiyya,ko a makarantar boko bangaren islamic take,abinda ya bawa maimunatu sha'awa sosai,har taji itama islamic take sha'awar yi inda zata samu dama,saidai ba zata iya buda baki ta yiwa anni ko dr maganar ba.


            Daya daga cikin yaran gidan ne ya leqo bayan sallar magariba,yace maimunatun tazo inji anni taci abinci zasu wuce gida,da hanzarinta ta tashi,abinda yasa fatima zolayarta


"Dama kin gaji da gidan namu,da alama so kike dama a tafi" murmushi maimunatun ta sakar mata ba tare da tace komai ba


"Allah yasa ki iya zuwa mana ma da bikin anty amira ki kwana"


"Allah ya kaimu" ta amsa mata tana murmushi,sai fatiman ta taka mata zuwa falon da annin ke zaune.


        Tun kafin ta qaraso muryar mai kauri da zurfi take ratso inda suke,matashi ne mai cikar haiba da kamala zaune sosai gaban annin suna magan,da alama akwai sabo sosai a tsakaninsu,farin bafullatani sak,wanda yake diban kama ta sosai da haj munira.


          "Dole cikin satin nan kije,ko fatima saita rakaki,tunda kina jin dadin maganin bai kamata a fara fashi ba,zan kirashi na gaya masa sati daya zakuyi" ya qarashe maganar yana daga kansa,dai dai sanda idanuwansa suka sauka kan fuskar maimunatu dake takowa a hankali jere da fatima.


            Tamkar haduwar mayen qarfe da maganadisu haka yaji wani abu mai qarfi ya fusgeshi,duk yadda yaso ya dauke idanunsa daga kanta hakan ya gagara,harta qaraso ta soma gaidashi a darare tana lafewa daga gefan anni.


            Da mamaki fatima ke satar kallon yaa khalid din,shi da baya yiwa mace kallo uku amma yau gashi ya kafe idanunsa akan maimunatu?,sai daya fuskanci fatiman na kallonsa sannan yajanye idanun nasa ya kuma bata rai yana komawa ga batunsu shida annin,saidai lokaci lokaci yana satar kallon ta.


             Iya tafiya ta tafi dashi,duk da bata qarasa kalar macen da yakeson aure ba,amma fa hada komai da komai,special care kawai zata samu ta wasu bangarori ta yiwa mata fintikau.


            "Nidai bansan me kakeson maidani ba khalid,wannan jewar fa ta isheni,nidai a barni,ciwo ai ba mutuwa ba,idan lokaci kuma yayi dole na tafi" anni tayi statement din qarshe tana miqewa tsaye da zummar tafiya,bayan maimunatu taqi cin abincin da aka kawo mata,sam ba zata iya ba,tana jinta ne duk a daure saboda kallon data fuskanci saurayin yana ritsata dashi,wai shin kam haka samarin family dinsu suke ko kuwa su din su biyun daga garesu ne?.


       Shi ya musu tattaki har zuwa bakin motar da sunan yiwa anni rakiya,fiye da rabin hankalinsa yana kan maimunatun,duk da yana yine yana basarwa har motarsu ta daga.


           Yayi tunanin da sun yafi shikenan,saidai kuma kasa nutsuwa zuciyarsa tayi,har sai da yakai kansa gida dr marwan,ya kuma sakeyin ido biyu da.maimunatu,tun daga sannan abun ya zame masa kamar wani jarrabi,duk bayan kwana biyu daga office yake zartowa nan din,baya barin gidan sai bayan sallar isha'i.


*********Karfe shida suka dawo daga islamiyya,tana sanye da babban hijabinta da ya saukar mata har qasan qafafunta,kalar blue black,abinda yasa yayi matuqar haskata tare da yi mata kyau,tana rungume da qur'aninta a qirji,laila na gefanta tana amsa waya.


          Suna sallama a falon sukayi idanu biyu dashi,qirjinta yayi mugun faduwa,taja da baya kamar zata koma sai kuma ta kasa,ganin ya ganta sarai,cikin zuciyarta bata son haduwarta dashi,saboda kallon da yake tsareta dashi da kuma sanyata cikin lamuransa da yawa,har fiye dasu laila da suke jininsa.


            A hankali ta biyo bayan laila kamar me tsoron wani abu zai iya kamata,tana jin laila na masa sannu da zuwa sai itama tabi sahunta,ta kuma sulale da niyyar wucewa dakinta,saidai ya tsayar da ita da tambayoyi kan karatunta,abinda ya bawa laila damar wucewa ta barsu su daya a wajen.


           Sallamar hisham daga bakin qofa ya ja hankalinsu duka,suka hada idanu da dukka su biyun,take fara'ar dake saman fuskarsa ta bace bat,ya fara shigowa falon cikin rashin walwala yana faman shan qamshi.


         Kowa a cikinsu cikakken matashi ne mai jin kansa,wanda ya hada komai da komai,musabaha sukayi da juna kowa yana dauke wuta,ba kamar yadda suka saba ba,har zuwa sannan kan maimunatu yana qasa,ta yiwa hisham sannu da zuwa,maimakon ya amsa,sai ya koma da baya ya zauna cikin daya daga cikin kujerun falon yana cewa


"Je kitchen ki kawomin ruwa" a hankali ta tashi tana jin wani nauyi na raguwa daga cikin zuciyarta,zamanta a wajen tana jinta ne kamar cikin wani matsatstsen keji ne da babu sakewa.


           Shuru ne ya biyo baya a falon,hisham na danne danne a wayarsa,khalid kuma yana kallon news,kowanne da tunanin da yake a ransa game da dan uwansa,ba tun yau ba duka sun tsargu da juna,sun kuma fahimci mawuyaci ne idan basiu tarayya akan wani abu guda ba.


           Ruwan ta kawo masa hade da cup,ya dauki gorar ruwan yana cewa


"Ba daga islamiyya kike ba?" Kai ta gyada masa


"Bita ce ta kamaceki ba ki zauna kina surutun banza ba...wuce daki ki ajjiye qur'anin hannunki" cikin jin kai da isa khalid ya gyara zamansa sosai yana kuma dubansa kai tsaye


"Dakata mana hisham?,wanne irin nonsense ne zaka same mu tare sannan kace ta wuce ciki?.... please kada ka shiga hurumin da ba naka ba" wani kallo hisham ya watsawa khalid sannan ya saki murmushi


"Nonsense?......hmmmm,dani da kai za'a samu wanda ya dace a gayawa hakan,wuce maimunatu tun raina bai fara baci ba"


"Ba zata wuce ba!" Khalid ya fada a tsawace,dai dai sanda anni ke qarasowa falon,ta bisu da kallo cikin mamakin yanayin data taras dasu.


_To fa masu karatu,khalid dinne ko hisham?,ko kuma ja'afar?,waye zaiyi wining?,muje zuwa yanzu aka fara wasan_


No comments

Powered by Blogger.