Gurbin Ido 18


 18

 Karo na uku kenan da ta taba ganinsa cikin gidan tun zuwanta,ba zata iya cewa ga ainihin sunansa ba,don babu abinda ya taba hadata dashi da ya wuce gaisuwa,daga nan take barin waje,tana da dabi'ar barin guri a duk sanda taga iyalin gidan sun hadu waje guda,har sai idan sun buqaci tayi zamanta.


          Cikin tsarguwa ta janye idanunta daga cikin nasa tana sake gyara zamanta gami da jan skert dinta zuwa qasa sosai,duk da dama ya sauka din,shima nasa idanun ya dauke yana shigowa cikin gami da sassauta dariyarsa


"Ina yini" ta gaidashi idanunta nakan teddy din yarinyar data yar


"Lafiya lau.....anni na ciki ne?"


"Eh ta amsa masa a taqaice"


"Yimin kiranta idan ba damuwa" da to ta amsa masa tana yunqurin tashi tare da qoqarin ajjiye yarinyar,saidai fir taqi ta qanqame maimunatu da kyau,idanunta nakan hisham.


        Qaramar dariya ya sake yana kallonta


"Duk ki gama guje gujen naki tsaf kuma azo ayi allurar,wannan zazzabin jikin naki ta yaya za'a barki dashi" kafada ta noqe tana sake tale baki da alama zata sake sakin wani sabon kukan ne


"Miqomin ita ki kiramin annin" gam ta sake riqe maimunatu tana cukuikuye dan qaramin hijab din jikinta,har sai da maimunatun tadan jashi kadan saboda jikinta daya dame


"Qyaleta,bari na kira maka ita a hakan" ta fada tana saba ta a kafada,sannan ta fara takawa a hankali zuwa gefan anni.


         Da.kallo yadan bisu har suka bacewa ganinss,sai ya dauke idanunsa yana sakin boyayyar ajiyar zuciya,wannan shine karo na hudu daya ganta a gidan,baisan wacece ba,baisan kuma relation dinsu da ita ba,saidai akwai wani abu me fusgar hankali tattare da ita,bama kamar yanzun da sukayi kusa da juna ba kamar kwanakin da yake hangota daga nesa ba.


         Saman lallausar dardumar dake dakin ta samu anni,tanata danne danne a wayar da ala dole ta karbeta,saboda ciwo baki na jikokinta,bata daga kanta ba,tadai amsa mata sallamar cikin kulawa saboda hankalinta na ga wayar,har sai da maimunatun da zuwa yanzu ta maida yarinyar bayanta ta shigo dakin gaba daya


"Wa nake gani a bayanki kamar amna?" Leqowa yarinyar tayi da kanta don anni ta tabbatar


"Ja'ira,sai yau Allah yayi suka dawo mana dake kenan?" Anni tafada tana dariya,koda bata sake cewa komai ba maimunatu ta gane wacece,yarinyar da kullum rana ba zata fito ta fadi cikin gidan wani bai ambaceta ba,taji yadda akasha gwagwagwa da kakanninta na wajen uwa kafin su yarda su dawo da ita,saboda ita kadai ce jikarsu,jikarma kuma ta wajen diyarsu mace qwaya daya tal da suka mallaka,taji kuma ance mamanta ta rasu,take tausayi da qaunar yarinyar ya sake saukar mata fiye da dazu,qaramarta da ita tasan dacin maraicin uwa?,ko ita dake da girmanta yaya takeji a ranta bare wannan,hukuncin Allah ne,ba yadda baya tsarawa,haka bawa zai karba a duk yadda yazo masa.


        Kememe amna taqi sauka daga bayan maimunatu,duk yadda anni taso tazo gareta


"Yar nema,zamu hadu ne,wannan din kin santa ne?,daga zuwanki zaki dafewa diyar mutane?" Annin ta fada tana dungure mata kai,abinda yasa amnan ta sunne kai a bayan maimunatu ba tare data ce komai ba,maimunatu na jinsu tana tayasu da murmushi


"Yaa hisham ne yace nayi masa kiranki" ta fadi sunansa kamar yadda taji yaran gidan na fade


"Ya shigo mana,baisan dakin nawa bane da zai tattago ni ina fama da kaina?" Goye da amna ta fita a dakin don gaya masa saqon annin.


         Waya yake dannawa,amma jin takunta yasa ya tsaya ta daga kansa yana dubanta,ta shaida masa abinda anni tace,har ya miqe kira ya shigo wayar tasa,sai yace


"Ina zuwa" yana duban fuskar wayar ya fice daga falon,dai dai lokacin da daya daga cikin ma'aikatan gidan me suna sha'awa ta shigo falon tana shaidawa maimunatu malaminta yazo


"To ina zuwa" ta amsa tana komawa wajen anni ta gaya mata abinda hisham din yace,taso aje mata amna amma yarinyar taqi,haka ta juya zuwa kitchen don kaita wajen tabawa,wadda dama ita ke rainonta amma sam wajen tabawan ma taqi zaman


"Haba uwar gijiyata,wannan zazzabin na jikinki da kin haqura kin zauna,bakya fita gurin shukokin can ba iska ta sake kadaki" fir taqi,saboda tana tsoron kada hisham din ya biyota nan yayi mata allurar da ya ambata din,haka maimunatu ta fita da ita inda ake mata karatun tana goye da ita,hannunta kuma riqe da litattafanta.


          Tana cikin jikinta suna karatun,tana bala'in qaunar karatun nata,saboda.malamin ba qaramin qwarewa yayi ba da kuma sanin makamar koyarwa,cikin watanni uku kacal ta fara gogewa fiye da tsammaninta,duk da dama dai ta samu foundation me dan kyau ba laifi daga makarantar primary din da tayi a gembu.         Gab da magariba suka gama karatun kamar kullum,tana goye da amna da barci ke dibanta suka shiga cikin gidan,ta taras dasu laila duk sun dawo,sun sha qunshi da gyaran kai tubarkalla,kowacce cikinsu tana da suma dai dai gwargwado irin na fulani.


        Duk yadda suke daukin amna tazo gurinsu taqi kowa,kowa da kalar wayon da zaiyi mata amma ta qiya,murmushi maimunatu ta sake,har fararen haqoranta suna fitowa


"Saiku haqura,yau dai kam ni ta zaba" sunata yiwa yarinyar tsiya ta wuce da ita dakinta ta kwantar da ita saman gadonta,zuwa lokacin bacci yayi awon gaba da ita.


     Washegari amnan tana barci maimunatu ta wuce islamiyya,sanda ta farka bata ganta ba ta saka rigima,rarrashin duniya kowa yayi mata amma ta qiya,hatta da anni da amman da suke dasawa yau taqi,saboda sun bari hisham kafin ya fita aiki ya nata allura,basu samu lafiya ba sai da maimunatu ta dawo,da gudu ta taryeta kuwa tun daga bakin qofa,maimunatu ta dagata tana taba jikinta,ta samu zazzabin ya sauka,baki ta tura gaba cikin murya irin ta yaran da suka samu gata


"Ba uncle hisham bane yayimin allura"


"Ya salam,sannu kinji,kiyi haquri" maimunatu ta fada tana shafa bayanta,saita kwanta luf a jikinta tana bata labarai har suka qarasa cikin gidan.


         Cikin kwanakin wata irin shaquwa ce sosai ta shiga tsakanin amna da maimunatu,ta maisheta tamkar uwarta,duk gidan a yanzu babu wanda take dafewa kamarta,kowa yasan hakan cikin gidan,gaba daya ma ta dawo da kwananta dakin maimunatu,hakan yayiwa maimunatu dadi sosai,saboda tafi sakewa da amnan akan kowa cikin gidan,zasuyi zamansu a daki suyita hira da amnan kai ka dauka da wata babba take magana,sosai amnan ke jin maganarta,da gaske yarinyar qaunarta take,amna yarinya ce me wayo da surutu,haka zata zauna ta yita baiwa maimunatu labarin mommynta da twin sister dinta da ta rasu,takan ce


"Ummu(mamam shaheeda)amma/anni sunce sunje maka,zasu dawo,zasu siyomin tsaraba me yawa ko?" Sai maimunatu ta gyada mata kai cike da tausayinta


"Amma me yasa ni mommy bata tafi dani ba?,kuma ta tafi da amra ta barni?" Ire iren maganganun dake karya zuciyar maimunatu kenan akan yarinyar,yake qara mata sonta da kuma tausayinta,sau tari takan faki idanun yarinyar ta share hawayenta,saboda ita da yarinyar dukkaninsu suna cikin jarabawar maraici,har gwara amna,tana da gata gaba da baya,saboda tsabar gata ma kowa so yake a bashi ita ya riqeta,ita kuma fa?.


          Idan ta gama wannan kuma sai ta koma zancan mahaifinta,wanda maimunatu batasan wayeshi ba,saidai da alama yarinyar tana kewar mahaifin nata kewa me tarin yawa,a zuciyarta take jin tunda yana raye bai kamata ya nisanci yarinyar haka ba,tana da buqatarsa a kusa da ita,duk randa ko ta samu yin waya dashi,ranar gaba daya labaranta nasa ne,maimunatun takan bata lokacinta ta biye mata suyita yi,abinda ya qara sabonsu da shaquwarsu kenan da ita.


        Yammaci ne sosai,wanda yake dauke da lullumi sosai da zakayi tsammani damina ce zata fara,saidai maimakon daminar ana dakon zuwan zafi ne kafin gabatowarta.


        A irin wannan lokacin gidan yakan kasance shuru,rana ce da babu makaranta both islamiyya da boko,yawanci a wannan lokacin 'yammatan gidan sunfi kwanciya suyi barci idan basu da abinda zasuyi,idan kuma suna dashi kowa yakan kama aikin gabansa,zuwa dare kuma su hadu zaman hira,ma'aikata kuwa na kitchen na sassan biyu,sassan dr marwan ko na hajiya anni.


         Maimunatu ce ta dage dan qaramin falon da anni kan zauna ta huta lokaci zuwa lokaci,hannunta dauke da zobo data dafawa annin tsurarsa,babu suger bare kayan hadi sai citta da kanunfari kawai,tun zuwanta gidan takan dafawa anni shi akai akai,saboda qarin jimi da kuma gyara zuciya da sauran cututtukan hawan jini,sosai anni takejin dadinsa,don tana ganin amfaninsa a jikinta.


         Tashi xaune anni tayi tana amsa sallamar cikin sakin fuska,idanunta nakan maimunatu,a duk sanda ta kalleta tana jin dadin sauyin da ake samu tattare da ita,zuciyarta kuma a kullum tana gaya mata kamar lokaci yayi da zata bayyanawa maimunatu qudurinta.


         "Sannu da hutawa anni"


"Yauwa maimunatu,ke zaa yiwa sannu" murmushi tayi ta zauna ta fara zuba mata zobon,annin ta karba tana godiya ta fara kurba,jifa jifa suna hira.


"Maimunatu......qarasa jikin soket ki ciromin wayar can da Allah" amsawa tayi ta ciro kamar yadda ta umarceta


"Yauwa laluba ki kamomin ja'afar" maida dubanta tayi ga numbers din dake kan wayar,ta fara laluba sunayen,har takai ga sunan da annin ta nema


"Gashi anni"


"Yauwa kiramin shi" ta fada tana ci gaba da kurbar zobon,zuciyarta na ayyana mata tunani kala daban daban.


           A nutse la latsa icon na kira,kiran kuwa ya tafi kai tsaye,take daga qasan sunan number wayar qasar waje ya bayyana,kuma sunan TURKEY ya fito daga gaban number kadan


         *TURKEY*


     *TURKEY CAPITAL*

      _ANKARA yanimahalle_

_Green forest mahalle_       Cikin babban ginin me dauke da apartments apartments,hawa na biyu,madaidaicin falo ne da ba zaka kirashi tangamene ba,kamar yadda ya wuce ya amsa sunan qarami,me dauke rantsatsun kujeru irin na asalin qasar turkey din,lafiyayyen carpet da curtains ash color light and dark dukka na qirar qasar,sai rantsatsiyar wallpaper kalar kayan dake falon,qananun sideel table da babbansu daga tsakiya,dining space da aka maqalawa fridge dukkansu kalolin kayan falon ne.


          Daga gefan fridge din lafiyayyen matashin saurayi ne jingine da fridge din,hannunsa riqe da cup daya cika da tataccen ruwan kayan marmari kala daban daban da aka markada aka kuma tacesu a mazubi guda,dogo ne me murjajjen jiki,yana sanye da shirt mai dogon hannu da kuma trouser,yayi crossing qafafunsa hannunsa daya soke a aljihun wandon nasa,daya hannun kuma yana riqe da cup din da yake kaiwa bakin nasa lokaci bayan lokaci.


         Kana kallonsa zakasan yayi nisa a tunani da kuma nazarin inda idanuwansa suke kallo,gaba kadan dashi inda aka tsara rukunin kujerun dake falon.


         Mutum biyu dake zaune cikin falon,daya farar fata ne,bature sosai,mr denis evoy dan asalin qasar Belarus,yayin da dayan ya kasance baqar fata ne,wanda ya mallaki wata sassalkar fata me kyan gani da kuma burgewa ko cikin jinsin masu baqar fatar da ake kira da chocolate color,CAPTAIN JA'AFAR MARWAN KHALID AKKO qwararren kuma sanannen matuqin jirgin sama wanda ya ajjiye aikinsa,ya kuma yi switching kansa ya zuwa babban dan kasuwa,mamallakin kamfanoni dake samar da manyan gine gine na manyan ma'aikatu jami'o'i da manyan kamfanoni tituna dama gidaje,manyan gine gine masu ban sha'awa da qayatarwa.


         Kyakkyawa ajin farko,irin kyan nan da a hankali yake bayyana kansa,wankan tarwada ne,a very husky man built like a football player,dukka qirar jikinsa na nuna alamun qarfi dake bayyana cikar mazantaka,yana da tsaho da kuma kauri dai dai misali wanda ya taimaka wajen sake boye ainihin tsahonsa,wasu irin shanyayyun idanu masu matuqar daukan hankali da kuma tafiya da imanin diya mace ko wacece ita,lafiyayyen qasumba ne dashi wansa bata rabo da saisaye da kuma gyara,gyaran da yake dacewa da kyawawan labbansa hancinsa me tsaho da tudu da kuma cikakkiyar girarsa,akwai wata suma ta musamman saman kansa mai sulbi da kuma sheqi ta asalin bafullace,wadda batayi yawa ba hakanan ba kadan bace.


        Iya lafiyayyar fatarsa da kuma zara zaran yatsun qafarsa da na hannu kadai idan ka kalla zakasan cewa a huce yake cikin cikakkiyar wadata da kuma hutu,sau tari qannensa na sha'awar yanayin qafarsa dake luwai luwai kamar ta mace,saboda yadda ta samu hutu da kuma gyara,tako ina ja'afar ya cika cikakken namiji,wanda ya samu kusan cikar komai na rayuwa......saidai abu biyu daya rageshi,na farko mutum ne shi miskili na gasken gaske,irin miskilancin dake baiwa mutane da dama mamaki,ake kuma tunanin lokaci zaizo da zai sauya,saidai har zuwa lokacin da aka tsammaci zai sauya din yazo bai sauya ba,lokacin kuma ya sake zuwa ya hade masa da baqar qaddarar rasa matarsa da kuma diyarsa mafi soyuwa a wajensa,abinda ya sake canzashi kenan,ya kuma sake cillashi duniyar miskilanci.


          Sosai yayi relaxing bayansa da jikin kujerar da yake zaune,very calmly yake kallon Mr Denis,sai kayi tsammanin duk duniya bashi da wata matsala a rayuwarsa dake barazana ga farinciki da kuma ci gabansa.


No comments

Powered by Blogger.