Gurbin Ido 14

 


14


         Sanda aka gama musabaqar suna tsaye a jikin motar dr marwan(abbi) suna jiransa yayi kiransu,ya hadasu da mahaifin shaheeda da ita kanta shahidar suka gaisa,irin dadin da shaheeda taji ba qarami bane ganin cewa akwai sanayya tsakanin mahaifinta da

nashi,ko meye zai dan zo mata da sauqi,ba kamar ace babu komai tsakaninsu ba,kwata kwata bata nuna wannan farincikin a fili ba saboda kamun kai da kuma tsira da mutunci.


          Babu jimawa shaheeda ta ziyarci gidan dr marwan,nan da nan ta saba da mafi yawa na jama'ar gidan,tayi amfani da hikima da kuma hankalinta da wayo ta shiga jikin anni da amma mahaifiyar ja'afar sosai,a lokacin jaafar tuni sun koma hutunsu,bata damu ba tasan tana da target a kansa komai dadewa,baka isa kace son ja'afar take ba,don ko zancansa bata taba yi ba bare ka kawo hakan cikin ranka,saidai a hikimace ta gama karantar dabi'unsa daga hirarsa dake bakin 'yan uwansa,da kuma yawan ambatonsa da anni takeyi,ta gama gane abinda yakeso da wanda bayaso,ta haddacesu tsaf bisa kanta.


           Sanda suka dawo hutu sun samu shaheeda a gidan,don tuni ta maida gidan wajen zuwanta,sun kuma saba sosai ta zama kamar 'yar gida,da yawa suna cewa saboda gidansu duka maza ne shi yasa tafison gidan baba dr kamar yadda take kiransa,don nata 'yan uwan duka maza ne,ita daya ce mace.


          Eh tabbas,zamanta a gidan na mata dadi,saboda tana da abokan hira sosai ba kamar gidansu ba,saidai nata plan din ja'afar ne,boyayyen sirrinta da babu wanda ya sani,tayi qoqari matuqa wajen ganin ta janyo hankalinsa kanta cikin hikima da basira,ba tare da shi kansa ta bari ya fahimci komai ba,komai na ja'afar din dabanne,ita ke kula da wasu abubuwa nasa.


           Da farko bai farga ba,saboda sam hankalinsa bashi a wajen,mma daga bisani ya soma fahimtarta,ya kira qanwarsa nadiya,ita yake nema idan yana buqatar wani abu da anni ko su amma basu iya ba ko ba zasu iya ba,wadda tasu tafi zuwa daya saboda kamanceceniyar da kuma nutsuwarta,ya yanka mata warning akan ta cire shaheeda akan duka sabgarsa sai idan shine ya buqata.


         Farko nadiya ta kasa gayawa shaheeda,sai ita da kanta ta fahimta,ta kuma yiwa nadiya maganar,bata boye mata ba ta gaya mata,tun daga ranar shaheeda ta fita a sabgarsa gaba daya,duk wani abu da ya shafeshi ta fita a ciki,koda zaune take a wajen yazo zata tattara tabar wajen,hakanan abu idan ya dangaceshi komai yadda ta iya babu ita a ciki,abun yana cinta a rai,tana jin ciwo amma ta danne zuciyar tata,mutum ce mai yawan addu'a,maimakon damuwa ta rinjayeta,saita rinjayar da addu'a,takan hana idanunta barci ta tashi cikin dare ta gayawa Allah damuwarta.


           Sannu a hankali shima ya fara noticing canzawarta,sai ya fara jin damuwa a kanta cikin zuciyarsa,shi da kansa ya dinga mamakin kansa,damuwa for what?,akan wata mace?,sannu sannu Allah ya fara matsa zuciyarsa,sai ga ja'afar da kansa ya fara nema shaheeda tayi masa wasu abubuwan,kamar kalolin girke girken da take masa a baya,amma fur sai ta murje idonta taqiyi,duk da yadda zuciyarta kan buga,taji babu dadi amma haka take mazewa.


           Rana ta uku daya aika tace ace bata da lpy taqiyi zuciya tazo masa iya wuya,yana zaune a sannan yana duba saqonnin da yake samu daga companies na jiragen sama dakeson yin aiki tare dashi,zare laptop din yayi daga saman qafarsa ya ajjiyeta gefe ya miqe ya fice.


         A dakinsu nadeeya ya samesu zaune an kafa majalisar hira,tana ta dariya tana dariya harda riqe ciki,Har kowa yayi shuru bata ankara ba,sai da taga hankalin kowa ya karkata ga qofa,sun kuma saka nutsuwa a jikinsu sannan ta ankara,tayi hanzarin jawo dankwalinta ta rufe lallausar sumarta ta fulani,gabanta na wani irin faduwa saboda zallar kwarjinin da yayi mata,tana jin kamar zaman ma ba zata iya ba.


         Bata ji yace musu komai ba amma sai taga kowace ta fara miqewa tana fita a dakin,ganin sunata ficewa ba tare da tasan dalili ba sai itama ta miqe tayi joining dinsu.


        Nadeeya ce qarshe sai ita,nadiya na fita ya matsa yayi blocking qofar gaba daya da jikinsa yana kallonta da idanunsa da suke fasa mata zuciya,tayi baya kadan ta kuma sauke kanta qas,don ba zata iya jurewa kallonsa ba,ta fara lanqwasa yatsunta,tana son tace ya matsa mata itama ta fita amma kuma tasan cewa tayi kadan ta iya fadin hakan.


          "Baki da kunya ko?" Ya fada a taqaice kamar me ciwon baki,abinda yasa babu shiri ta daga kanta ta kalleshi,sai kuma ta sake saukarwa saboda idonsa yana kanta


"Ni sa'anki ne da zan dinga aikowa kiyimin abu kina rejecting,bakisan ba kowa nake sawa yayi mun abu ba?" Sosai maganar tasa tayi mata dadi,wani abu ya tsarga mata,gefe daya kuma rauni ya kama zuciyarta har ya sanya qwalla silalowa daga idanun nata tare da kalmar


"Kayi haquri" shuru na sakanni yayi kafin ya sauke hannayensa ya juya ya fara ficewa daga dakin,sai ta bishi da kallo har yabar wajen.


          Kwata kwata ji tayi bataji dadi ba,cikin ranta kuma tana tsoron kada fa ta barar da damarta,a sukwane tayi kitchen ta fara hada masa abinda ya buqata a daxun,tana tsaka da aikin su safina suka shigo


"Me yayi miki?,me ya faru?" Tambayar da suka dinga mata kenan


"Ba abinda yayimin" ta amsa musu hankalinta na ga girkinta


"To wannan abincin fa?,naga bamu jima da gama cin abinci ba" safina ta fada tana bude tukunyar


"Na yaa ja'afar ne" amsar daya sanyasu kallon kallo a junansu,suka fara kuma tsegumin anya kuwa?,bata bi ta kansu ba,itadai burinta ta gama ta kai masa.


           Sanda khadim yakai masa dawowa dashi akayi,yace bayaso,abinda yasa hankalinta ya tashi sosai,ta kuma boye ta dinga kuka,washegari ta hada kayanta tace zataje,duk da kwanakin da takeyi basu cika ba.


           Kwana biyu rak a tsakani ya karanci bata gidan,yayi kaman ya share amma sai yaji ya kasa,ya kira nadeeya ta tambayeta,bata boye masa ba ta gaya masa duk abinda ta sani,ya sallameta,sannan yayi shuru shi daya yana tunani,rashin cin abinda ta aiko masa ne ya kawo faruwar hakan?,washegari sai ya tsinci kansa da shiryawa ya tafi gidan daukota,babu ko rakiyar jabir.


           Suman zaune tayi sanda akace mata ja'afar ne na gidan baaba dr,bai shigo ba ya dai aiko da gaisuwa wajen ummanta,sannan yace a gaya mata ta fito su tafi,saqon da ya bata mamaki,haka ta shirya kayanta ta biyoshi.


         Cikin motar kamar bashi ba,har ta fara cire hope,saboda ko uffan bata hadasu ba,sai da suka kusa gida sannan ya magantu


"Idan kika sake wannan kuskurem sai na hukuntaki" ta fahimci da qaramar magana yake isar da saqo me yawa,maganarsa guda daya idan ka fassarata taka dauki.ma'anoni.masu yawa


"Kayi haquri" tace dashi,yaji dadi cikin ransa na yadda take da sauqin kai,saidai ko ka fuskarsa haka bai nuna ba.


        Wasa wasa sai shaheeda ta karbe komai nasa cikin gidan,nan da nan kowa ya fara daukan haske,duk da cewa shi gogan yana jin dadin hidimarta sosai saboda ya yadda da tsaftar ta da qwarewarta wajen girki,sannan yana jinta a ransa wanda yafi ta'allaqa hakan da sabo,amma babu wata maganar soyayya data taba gittawa tsakaninsu.


             Tsarin gidansu shaheeda daga candy mahaifinta bashi da ra'ayi barin diyarsa mace ta qara gaba,sai kuma gashi guda daya ce macen da Allah ya bashi,a lokacin shaheeda tayi candy,mahaifinta ya tasamma aurar da ita,dr marwan na samun labari ya nemawa ja'afar bisa shawarar anni,saboda qoqarin da taga shaheeda nayi a kansa,da kuma yadda ta karabceshi tsaf,tamkar ita ta haifeshi.


            Kowa yayi tunanin za'a samu matsala sanda ja'afar yaji an nema masa auren shaheeda,sai gashi bai wani damu ba,hasalima kusancin dake tsakaninsu ne ya sake daduwa,hakanan itama ta sake qara qaimi wajen kula dashi,abinda yake matuqar yi masa dadi a rai,duk da dan uban miskilancinsa.


             Wata iriyar zazzafar soyayya yake mata silently,mutum ne shi da bai iya so ko qi ba,shi daya yasan girma da kimarta cikin ransa,ta kula da komai nasa,dai dai da lokacin sallah ta dauki wayarsa ta saita masa,hakanan duk sanda ta tashi sallar dare dai tasan yadda tayi ta tasheshi,ko.ta tura masa tex ko tayi masa flash call,duk sanda tayin kuwa sai ya gani,kasancewarsa mutum da baya bacci da wuri,ita ta koya masa sallar dare,ta kuma koya masa abubuwa da yawa wadanda daa basa cikin habit dinsa,ta samu gurabe sosai cikin rayuwarsa,wanda hakan ya qara soyayyarta da qaunarta cikin ransa ba tare da ya ankara ba.


           Sanda sukayi aure da shaheeda lokacin ya zaba kamfanin da zaiyi aiki,saidai ba anan nigeria yake ba,anni ta dinga fada,akanme zai zaba kamfani a wata qasar bayan yanzun yana da iyali,Allah sarki shaheeda ba haka taso ba,amma ita ta haqiqancw kan cewa babu komai,saboda fa fahimci burinsa kenan,yana matuqar qaunar piloting,tana bala'in girmama buqatarsa da burinsa saman nata,tayi kwance kwance ta dinga bawa anni haquri gami da kareshi.


         Suna kan hanyarsu ta komawa sashensu ya kama hannunta ya saka cikin nasa


"Me yasa kike bani kariya?,bayan kema nasan ba haka kikeso ba?"

Murmushi tayi sannan ta dora kanta a jikin kafadarsa


"Bani da wani zabi bayan naka,bani da wani abu da zanso sama da abinda kai kake sonshi,bazan taba son wani abu sama da wanda ka zaba ba,dukka zabina dama rayuwata ta narke cikin taka,taka ce" wani abu ne ya dunga tsarga masa,baisan wanne irin so shaheeda ke masa haka ba,kasa magana yayi,sai kawai yasa hannu ya dauketa cak yaci gaba da takawa da ita zuwa sashensu,abinda tafiso daga wajensa kenan fiye da komai,tayi luf a qirjinsa tana murmushi tare da shaqar daddadan qamshin da bata taba jin makamancinsa ako ina ba sai a wajensa.


           Mutum ne tsayayye dan gaske,wanda komai zaiyi baya daukarsa da wasa matuqar ya sa kansa,don haka sanda ya fara aikinsa ya bashi muhimmanci qwarai da gaske,abinda ya jawowa shaheeda samun qarancin kulawa,tana jin babu dadi amma ta danne,taci gaba da haquri dashi da kuma dukka abinda zai taso,a yawancin lokuta shi da kansa yasan tana buqatar kulawarsa,amma babu lokaci,hakan ya sanya shima yaqi dauketa daga cikin gidan nasu,saboda zamanta tare dasu anni xai rage mata kewa da zaman kadaici.


           A haka shaheeda ta samu cikin twins,a lokacin laulayinta tasamu zama dashi sosai saboda hutun qarshen shekara daya fara yi,ya kuma dan dade.


            Wata takwas da sati biyu ta haifa masa kyawawan 'yan biyu dukkaninsu mata,ikon Allah dayar shi tayo,dayar kuma babanta sakkk,ya kashe kudi bakin iyawarsa,ya kuma gatanta,ta samu gift masu yawa daga gareshi.


           Yaran yarane masu shiga rai kamar mahaifinsu,hatta da baban nasu wata iriyar soyayya yake musu ta musamman,a haka yara suka fara wayo,ya kuma koma bakin aikinsa.


          Sannu a hankali yara suka fara girma,sunata wayo abinsu,har zuwa sanda sukayi shekara biyu,ya dauki hutu yazo dai dai randa su nadeeya suka hada musu birthday,akayi komai dashi,ya kuma cikasu da gifts ya koma aikinsa.


           Kamar dai baya haka ya koma aikinsa ka'in da na'in,a wannan karon shaheeda kanyi qorafi lokaci xuwa lokaci


"Muna buqatarka,muna buqatar kulawarka,ba don ni ba ko don yaran nan" shi a kansa yasan da haka,don haka ya fara tsara musu yadda zasu xama kusa dashi ba tare da ya gaya mata ba,shi kansa yana kewarsu sosai.   *_MUTUWA rigar kowa_*       Tunda watan ya kama take masa complain din tana yawan jin ciwon kai,murmushi yakeyi yana tsokanarta,saboda yasan wani lokaci idan tana buqatarsa ko buqatar ganinsa da hakan take fakewa,har sai yabar dukka abinda yakeyi yazo ya gansu.


          Wannan karon sai yake basarwa,saboda so yake zuwa qarshen watan yayi musu suprise ya debosu suzo suyi hutu tare dashi.


           Sati kusan uku suna a haka,ranar wata alhamis..........


            A ranar akwai jirgin da zai tuqa,awa daya saura su tashi sai ga kiran shahidan,tana shaida masa gata a qasar,da fari ya dauka wasa take masa,don last week sunyi hirar taji duka schedules dinsa na satin,amma daya duba number ya tabbatar ta qasar ce sai ya yarda da hakan,mamaki ya cikashi,da alama ta gaji da kewarsa ne ta biyoshi kenan,waya ya dauka yayi musu booking masauki sannan ya kirata yace su biyo cave ta kawosu nan,a marairaice tace


"Yanxu ko sau daya?,ko sau daya ba zaka iya qarasowa na ganka ba kafin ka wuce?" Agogon dake daure a hannunsa ya kalla,lokaci ya qurace sosai,bashi da zabi illa ya bata haquri,cikin karyayyar murya ta amsa masa da


"Shikenan......ga amna" murmushi ne ya wadata a fuskarsa,ya karba wayar sukayi magana sosai da yarinyar,don bakinsu dukka ya bude,abinda ya jawo ma kenan wayar ta katse sanda 'yar uwarta amra ke shirin karba,yaso suyi magana da ita,don tunda suka fara waya da amnah take cewa ta bata daddy,zata bashi wani labari.


         A sannan lokacin fara aiki yayi,ya kalli wayar yanason kira a bashi yarinyar amma ba hali,sai ya yanke bari suje sukai passengers,lallai a ranar zai dawo in sha Allah,cikin ransa ya dinga jin excitement na haduwarsu,ashe samun nasu da bazaiyi ba kenan saidai ya taras da gawar matarsa da kuma gawar diyarsa guda daya amra.


            Lamarin yayi matuqar bugarsa da kuma gigitar dashi,don saura kadan ya zauce a sannan,bai taba kawo irin hakan a ransa ba,tun daga wannan lokacin komai ya tabarbare masa,ya tashi daga ja'afar akko ya koma wani mutum na daban,musamman lokacin da yaci karo da diary na shaheeda cikin kayanta,yadda take kewarsa da yawa da tarin qaunar da take masa, movement na yaransa a lokacin da baya kusa dasu.


         Sosai depression ya sameshi,ya tattara komai nasa ya ajjiye,ciki harda aikin nasa da yake matuqar so,yace shine sila na faruwar komai,dukka qoqari anyishi kan jaafar don ya koma dai dai,amma inaa abubuwan sai a hankali,sai da aka tsaya da addu'a da roqon Allah sannan aka fara samun sauqi,amma sam ya canza totally,hakanan duk sanda abun ya motsa masa birkicewa yake gaba daya.


          Sosai jabir ya taka rawar gani,saboda tsayawa da yayi akan jaafar din,da qyar aka sha kansa ya koma kan harkokinsa,amma piloting dai ya ajjiyeshi,ya zama wani mutum me zafin rai,miskilancinsa ya sake daduwa qwarai da gaske,babu abinda yake burgeshi a rayuwa,ya sake zama wani very careless akan sha'anin kowa,yafi ganewa kadaici,wanda kadaicin kuma illa ne tattare dashi,saboda shike tuna masa da shaheeda.


           Wata irin soyayya yakewa diyarsa guda daya data rage wato amnah,wani irin gata yake mata,soyayyar mahaifiyarta da 'yar uwarta duka sun dawo kanta,amma fir yaqi zaman nigeria duk da babban kamfaninsa anan yake kano gombe da lagos,dole don kada su matsa masa suka barshi,suke ci gaba da binsa da addu'a da kuma fatan Allah ya kawo qarshen komai.

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 16


     Da sallama tabawa ta tura dakin,ta ajjiye ledar  kayan hannunta fuskarta dauke da murmushi tana duban maimunatu


"Ki shiga kiyi wanka,ki canza kayan jikinki maimunatu ko?" Kai ta gyada mata,saidai ta maida dubanta ga jikinta,bata ga wani datti da zai sakata yin wanka ba,don yau din da safe Allah ya 'yantata,ta samu tayi wanka kafin su baro gida,kuma bataga wani aiki da tayi wanda ya bata mata jikinta ba,hasalima ta jima bata samu cikakken hutu da yanayi me kyau irin na yau ba


"Muje ko na nuna miki bayan gidan" abinda tabawa ta fada kenan bayan ta ajiiye wasu maya mayai saman madubi,sai kawai ta miqe tabi bayanta.


          Komai na cikin bandakin ta nuna mata tare da yi mata bayani,maimunatu na biye tabawan har ta gama nuna mata komai sannan tace


"Idan kin gama kin fito ki dannan nan ina daga falo,zan shigo na gyara miki kanki" kai kawai ta gyadamata,har ta fice tana tsaye tana bin toilet din da kallo.


         Yadda ta nuna mata komai haka tayi amfani dashi,sai gashi ta dauki lokaci me tsaho tana wanke jikinta lungu da saqo,irin wankan da daadanta ta koya mata ta dinga yi a sanda take da gatanta.


           Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana shaqar qamshin sabulun da tayi wanka dashi,ga wata iska tana ratsata tako ina,bata buda ledar da tabawa ta shigo da ita ba,sai ta zauna qasan tiles din tana qanqame da jikinta waje daya,saboda har wani sanyi sanyi takeji,ta kuma danna inda tace matan,a haka ta share wasu mintuna tana zaune.


       Gajiya da zaman jira tabawa tayi,gashi anata kiraye kirayen sallar magariba,don haka ta dawo dakin,ta samu maimunatu zaune


"Ya kike zaune haka?baki kirani ba baki kuma saka kayan naki ba?" Qas tayi da kanta,tabawa ta karanci akwai baqunta sosai da kuma takura kai ga maimunatu,wataqila rayuwarta ta baya ce tayi tasiri sosai a kanta.


         Kayan ta fidda mata harda half vest tace ta koma bandakin ta sanya tazo suyi gyaran kan.


           Ta jima tana jujjuya kayan a hannunta,tamfar ba zata iya sanyasu ba,sai kuma ta tuna jiranta akeyi,abinda yasa ta budasu ta saka sannan ta daure kanta da dankwalin tayo waje,daf da zata fita ta hangi kanta ta wani dogon madubi da akayi cikin bandakin,harta gota ta dawo tana duba kanta.


            Farat daya ta fara canzawa daga maimunatun bafulatanar riga,babu mudukajenta(kayan saqi) babu wuffije,babu komai na fulani tattare da ita sai duwatsun hannunta da na kunnenta,hakanan fatarta haskenta ya qaru koda ba'a gaya mata ba idanuwanta sun gaya mata hakan,sai ta soma takawa a hankali tana saqe saqe masu yawa cikin ranta.


"Babu ma wani datti me yawa akan naki ai" tabawa ta fada sanda maimunatu ta bude mata yalwatacciyar sumar kanta,tabbas babu datti,amma kuma tana da buqatar qyara,ita da kanta idan ta samu sarari take guzurin toka duk sanda taji kan nata ya dameta,ta tsaya daga bakin rafinsu sanda shanunta ke shan ruwa ta badeshi da toka ta wankeshi,saidai tana shan wahala qwarai,saboda wata irin suma Allah ya bata ga tsaho ga cika,babu mataimaki,a baya daadarta ke gyare mata shi fes,ta xauna duk tsahonsa ta bata lokaci ta zuba mata kitson fulani a bishi da wasu irin duwatsu nasu masu kyan gaske,duk randa zatayi mata irin wannan aikin wuni guda suke kashewa kafin a gama,amma fa duk wanda ya kalla kan sai ya kalla ya sake kalla ya kuma tanka,daadarta kadai ke iya mata wannan aikin,ita kanta duk randa ta wareshi ta wanke saidai ta cukuikuyeshi cikin dankwali ta maidashi yadda yake taci gaba da rayuwa dashi a haka,babu cikakkiyar taza bare ta samu kitson arziqi.


          Tabawa batayi tsammanin aikin zai daukesu lokaci mai tsaho ba,sai gashi kafin ta gama wanke mata shi ta busar a hand Drayer sun dauki kusan awa biyu,har anni ta aiko laila.


           Tsaye laila tayi tana fiddo idanu sanda ta shigo dakin


"La la laaaaa......maimunatu,dama haka kike da suma?,ma sha Allah,kice mu fulani kawai muka rako duniya,ga inda ainihin fulanin suke" murmushi kawai maimunatun tayi,kasancewarta bame yawan son magana ba,zama laila tayi tace tare zasu tafi,tana ta qarewa maimunatun kallo,cikin zuciyarta tana tadinta,yadda cikin awanni kadan kamanninta da kyawunta sun fara fita tun ba'aje ko ina ba.         Duka su ukun da sallama suka shiga falon anni,a lokacin ta nutsu tana amsa wayar jabir,sun fahimci waya take mai muhimmanci harda maimunatu dake baquwar gidan,sai suka samu waje kowa ya zauna,laila ce ta qarasa gaban tv ta dauka remote kafin takai ga zama ta canza channel sannan ta dawo itama ta sama waje ta zauna kamar su.


         "Shikenan......amma ka zama cikin shirin kai jabiru,ba lallai sai ka sanar masa ba,ka rabu dashi kawai kaci gaba da sabgarka.....toh....Allah ya bamu alkhairi" shine maganar qarshe da annin tayi tana sauke wayar daga kunnenta tare da bin wayar da kallo,kana ta dauke idanunta tana maidowa kansu.


          "Sannu tabawa,kun gama kenan?" Ta fadi tana murmushin jin dadin yadda taga maimunatun fuskarta ta sake fitowa fayau,sannan kuma tayi tarwai


"Eh hajiya anni,aikinma bamai yawa bane"


"Kedai sannunki da qoqari" anni ta fada tana sake kallon maimunatu


"Me zakici maimunatu?" Kanta a qasa ta girgiza kai,don har yanzu cikinta a cushe yake,tana jin daga nan har gobe da hantsi zata iya zama babu komai a cikin nata


"Bana jin yunwa anni"


"Badai a gidan nan ba,ke lailaa,shiga madafi,ki cewa lami ta zubo tuwon nan da aishatu ta kawo,cin mutum biyu ta kawo mana" ambatar sunan da anni tayi sai taji ya tsarga mata har cikin ranta,a duk sanda aka kirayi me irin sunan,babu abinda yake tuna mata face mahaifiyarta.           Sanda laila ta kawo tuwon zama tayi zataci,amma anni tace batasan wannan zance ba,ta koma can wajen uwarta taci


"Wallahi anni ke kadai ta yiwa tuwon nan duk gidan nan,ko abbi babu shi a ciki"


"A nan kuka fi kauri,wajen bada gudunmawar ci,da wani cikinku nace yayimin babu me katabus" ita dai laila bata damu ba,ta saka hannu a kwanon maimunatu ta fara cin abincinta tana sakowa maimunatu hira,abinda yasa anni fa sake qyale lailan kenan,saboda hakan da tayi tasan zai bawa maimunatu damar sakewa.


         Ta kuwa dan sake din,tana tsakurar abincin,iyakarta da hirar laila uhmm ko um um,sai kuma murmushi wani lokacin,duka anni tana ankare da ita,tausayin maimunatu take ji sosai cikin ranta,gefe guda kuma tana sake shiga ranta,komai nata mai sanyi ne,cike kuma da nutsuwa a cikinsa.


            A hankali a hankali 'yan mata matan gidan suka fara shigowa da daya da daya kamar yadda suke yawancin darare,suna shigowa anni su kuma dade wajenta,don ma fadanta yakan sanya wani lokaci suqi zama,amma idan suka sameta akan laushinta har kwana sukanyi.


          Duk wadda ta shigo sai tabi maimunatu da kallo,wasu suce


"Ma sha Allah,anni baquwa mukayi?,ina kika samu balarabiya?" 


"Yar uwarku ce" amsar da take basu kenan taci gaba da harkar gabanta,cikin girmamawa maimunatun take gaida duk wanda ga shigo,har suka dan cika a falon,sunata hirarrakinsu tana jinsu,koda sun sakota saidai tayi musu murmushi kawai,abinda ta lura dashi,su din mutane ne masu mutunci da girmama dan adam,hakanan suna da sauqin kai,duk da adan taqin zaman nasu ta fuskanci wani yafi wani sauqin kai a cikinsu,dama haka halittarmu take,kowa da dabi'a da kuma yanayin da Allah yayi masa.


          Ranan kusan a nan duka suka sukaci abincin dare,maimunatu nata kallon banbancin rayuwa da kuma gaskiyar karin maganar nan ta bahaushe da yake cewa 'Allah daya gari bam bam' kowa yakanje ya diba zabinsa ne da abinda yakeson ci,ya kuma buda ma'ajiyar abunsha ya dauka kalar lemo da ruwan da yakeso,wasunsu kuma su sanya ma'aikatan gidan su kawo musu,babu kyara babu tsangwama,akwai alamun hadin kai da zaman lafiya bakin gwargwado tsakaninsu.


           Tabawa anni data jima da tashi a falon ta aiko kan maimunatu ta tafi ta kwanta,kusan dama ta gaji da zaman,don bata saba hira da mutane ba,duk sai zaman ya gundureta,amma ta rasa ta yadda zata tashi ta wuce dakin,don haka tabawa na idar da saqon ta miqe


"Balenjam" ta fada da tattausar muryarta,sai kuma ta danyi sak ganin yadda suka zubo mata idanu


"Sai da safenku" ta fada da harshen hausa,laila ce ta saki murmushi


"Allah ya tashemu lafiya fillo" murmushin tayi itama sannan ta juya zuwa ciki,tana mamakin yadda suna fulani amma basu damu da yin yaren a tsakaninsu ba,don tunda tazo da hausa taji suna hira har yanzun data tashi,wala'alla shi yasa suka bita da kallo sanda ta yaara musu.


         "Gaskiya yarinyar nan kyakkyawa ce,tana da hankali da alama" salma data miqe dauke da.plate din data gama shan farfesun kayan ciki ta fada,dubanta laila tayi


"Sosai,tana da nutsuwa sosai,tana burgeni"


"Ni kaina haka" fa'iza ta amsa musu,daga haka laila bata ce musu komai ba,don tasan cewa ba wanda yasan komai kan zuwan maimunatu gidan,bai kuma kamata ita din ta fara cewa komai ba.


           Sanda ta shiga dakin idanunta sun fara mata nauyi saboda bacci,qullin kayanta data hana tabawa dauka daxu ta janyo ta tasa kanta dasu,bayan tayi kwanciyarta qasan tiles ba tare da tayi gigin hawa gadon ba,babu jimawa wani nannauyan bacci mai dadi yayi awon gaba da ita.


*********Kyakkyawar macace wadda shekarunta na haihuwa suka kusa arba'in da bakwai,kana mata kallon farko zakasan cewa sanda take da qananun shekaru ba qaramin kasa maza dr marwan yayi a kanta ba,tana da siffa me kyau ko a yanzun ma,fara ce sosai kamar yadda akasan asalin farin bafullace,hakanan bata da tsaho can can,kamar yadda ba zaka kirata gajeriya ba,saidai alamun tsafta da qamshi da suka samu wajen zama a tattare da ita sun nuna kansu muraran.


       Cikin nutsuwa kamewa da kuma sanin kimar kai take shigowa bangaren surukar tata,sanye cikin atamfa england me ruwan ganye,dinkin riga da plain zani,bayanta masu aikin gidan ne wadanda ke qarqashin bangarenta masu kula da bangaren kitchen dauke da trays,sai kuma salma dake riqe da wani warmer me kyau guda daya a hannunta,a shirye take tsaf da alama wani wajen zata wuce,tana daga gefan mahaifiyarta(Aishatu amma) suna magana ita da salma din.


         Dakatawa masu aikin sukayi har zuwa sanda amma da salma sukayi sallama cikin qawataccen falon annin,wanda sam baiyi kama da falon tsohuwa ba,dai dai lokacin da DR marwan ke zaune gaban mahaifiyar tasa yana gaisheta,shima sanye da wata dakakkiyar shadda fara qal,kamar kusan ko yaushe kansa nannade da tattausan farin rawani na zallar auduga,da alama shima din fita zaiyi.


          Jinin sarauta ce ita amma sam ba zaka dauka haka ba,saboda sauqin kai da take dashi da kuma sanyin hali,Gefan anni amma ta qarasa tana zama a qasa kamar yadda ta samu me gidanta,wannan din wata dabi'a ce tasu ita da dr marwan tun suna da jajayen sahunsu,dabi'ar data maida aishatu tauraruwa a zuciyar anni cikin kafatanin surukanta,ya sanya kuma wasu daga cikinsu suke kishin hakan,duk kuwa da cewa anni tana matuqar qoqarin boye hakan,saidai ko daga yadda ja'afar keda matsayi a wajen annin kadai ya isa ya fallasa maka wace aishatu a zuciyarta.


            Sai data fara gaida anni sannan ta waiwaya ga me gidanta shima ta gaidashi,duk da cewa sun gaisa a ciki kafin ya fito,ya amsa mata cikin kulawa kamar ko yaushe,salma ta matsa kadan ta gaida dr sannan ta maida dubanta ga anni,murya qasa qasa tace 


"Ranki ya dade hajjaju anni" wani kallo ta jefi salman dashi,tasan duk me salman take wa


"Allah ya baki haquri anni ina kwana"


"Lafiya sumul natashi 'yar nema,duk take takeki kar nake kallonki,gwara kiyi ta kanki 'yar nan" wuri wuri salma tayi,da alama tonin silili anni keson yi mata a gaban wadanda take gudun yin maganar a gabansu,bata gama tunanin ba kuwa maganar annin tayi mata saukar aradu


"Wai marwanu.....ita wannan kazar mayun har yanzu bata isa ayi maganar aurenta bane?" Ji salma tayi kamar qasa ta tsage ta shige,maganar da tayin tana nuna kuma yasa dr maida idanunsa kan salma


"Me ya faru anni?" Gyara zamanta tayi


"Yo ni na gaji da hada kafada dasu idan ku baku gaji ba,ina buqatar ganin wasu 'yan dagwai dagwai din,ko ka aurar dasu ko ka auro,zuri'a nake da buqatar gani me tarin yawa......yawwa......duk gidan nan billhillazi babu yaron da bai isa aure ba,ramatu ce kawai za'a iya dagawa qafa,amma ace babu me aure?,baga mazan ba baga matan ba?,to idan baqinjini garesu zan buga gangar bada sadakarsu mazansu da matansu" kafin ta diga aya salma ta kwashi takalmanta a hannu tayi waje,don taga alama yau annin me manya manya take barota.


        "Ayi haquri anni" abinda dr yake fada kenan,don yasan da biyu take wannan fadan,tana tunanin kamar shike qin bada auren yaran nasa,bayan kuma yaran da kansu suke sha'awar karatu shi yasa ya qyale kowacce da zabinsa,uwa uba ma duka duka salma  hafsat da laila ne a makarantun gaba da secondary,samma hafsa nadiya fa'iza da khadija sune 'yan candyn bana,zahra'u na ss one,sai rahama dake j.s,mazan kuwa dukkansu ba wanda ya gama jami'a banda ja'afar da haisam,sai Mahmoud dake ajin qarshe 


"Yanzu fisabillahi....salma zaman me take?,shi karatun da take cewa akayi bashi yuwuwa ta qarasashi cikin dakinta?"


"Ta fiddo wanda takeso anni,ai baza'a qi aurar da ita ba"


"To ta fitar kuma shi take ta raragefan gaya maka kai da uwar tata" qas amma tayi da kanta,wal'alla ta gayawa anni sunyi zancan da ita kenan


"To ba damuwa anni,zanyi magana da umar(qaninsa kenan me bi masa),saita turashi can yaje ya gaidasu"


"To ba laifi" annin ta fada tana sassautan fadan,dai dai sanda salma tayi dake labe daga waje tayi tsallen dadi,anni tasu,anni ta wajensu,ayi tsiya ayi dadi,ga tsiya ga aiki,lallai yau dole ta yiwa annin wani tagomashi,saita juya cikin jin dadi zuwa ma'ajiyar motocin gidan,inda driver yake jiranta,ranta fari qal.


          Daga can falo kuwa duban dr anni ta sakeyi


"Shi kuma jabiru da ja'afar fa?,da aka barsu suke zaune a wata uwa duniya,ga wancan qaton tuzurun haisam?" Miqewa amma tayi saboda kara da yakana irin tata,tana ganin ya kamata ta basu waje suyi maganrsu sosai


"Ina kuma zuwa?" Anni ta fada tana binta da kallo


"Zan duba meye baku dashi a kitchen"


"Idan kin shiga,kiyi waya can gidansu marigayiya,ya kamata a dawo da amna,jimawar da tayi a can wannan karon tayi yawa"


"To anni" ta amsa mata cikin girmamawa tayi ciki,dawo da dubanta tayi ga dr marwan tana tattara hankalinta sosai a kansa sanda ya fara mata bayani


"Maganar da nakeso muyi kenan.....a jiya da kika sameni da baqi kamar yadda na gaya miki ministern ilimi ne na qasa ya kawomin ziyara,bayan mun gama tattaunawa kan batutuwa irin namu,sai kuma ya jefomin maganar diyarsa unaisa,ya yimin tayin aurenta da ja'afar kamar sanda ya taba yimin a baya ban karba ba,lokacin ja'afar din yana aviation school,magana kuma tayi nisa tsakaninsa da marigayiya,to a yanzun inajin nauyi na sake qin karba din,kada yaga kamar banason hada zuri'a ne dashi ko kuma wani abu makamancin haka,na amsa masa ne duba da cewa gaba dayanmu dama muna laluben masa abokiyar zaman da zata iya zama dashi bisa juriya da kuma haquri kan sauyin hali da dabi'arsa,na kuma tabbatar kema idan kikaji hakan zaki farinciki,tunda burinmu kenan gaba daya"

 

          Shuru anni tayi tana duban dr marwan,bawai don yayi kuskure ko kuma maganganunsa ba'a kan hanya suke ba,a'a......saidai tana tunanin wace unaisa?,akwai yiwuwar samun dacewar zama tsakaninta da ja'afar din?,uwa uba kuma ga batun maimunatu da take tafe dashi,sai takega kamar akwai matsala.


_To masu karatu,muje zuwa,shin al'amarin zai yiwu?,duk da bamusan wacece unaisa ba,abbi baisan wace maimunatu ba,kamar yadda wanda aketa abun a kansa baisan wainar da ake toyawa bama_


No comments

Powered by Blogger.