Gidan Aro 8
08*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽
Umma tana kallo Abba ya ida shirya yaransa Ashiru da Habib, tambayan duniya ta masa ya sanar da ita yanda zai kaisu yak’i kulata, ko kallon arziki ma bata ishesa ba balle ya
amsata.. Har saida suka gama shiryawasu tsaf kafin yace suje waje su jirasa. Yaran sukai kaman yanda mahaifinsu yace..Abba yai gyaran murya yana duban Umma “Uwani.”
Ta d’ago a raunane tana dubansa. Lokaci guda yaci gaba da furta “Bazan bar yarana suna ganin tashin hankalin da kuka janyo ma kanku Keda d’iyarki ba, a shekarun Ashiru da Habibu sunyi k’anana su dinga ganin ana sintiri cikin gidan nan ana Fad’a da mahaifiyarsu ana fad’in sai ta biya kud’ad’en data amsa, sannan bazan bar yarana sunaji ana cewa ‘yansanda na sallama da mahaifiyarsu ba.. Tsuntsun da yaja ruwa dama shi ruwa yake duka.. Kuma abinda ka shuka ko shakka babu shi zaka girba. Ashiru da Habib sun gama yini a gidan nan, idan Kinga mun dawo toh dare ne Yayi amma sam bazan barsu su yini a layin nan ana cewa ga abinda mahaifiyarsu da ‘yaruwarsu sukai ba.. Kunje can Keda d’iyarki ku warware abinda kuka sak’a..”
Umma cikin rawar murya take furta “Haba Abban Sadiya yanzu ficewa zakayi ka k’yalemu.. Idan ‘yansandan sukace zasu tafi damu fah..? Dan Allah ka tsaya ka zamo mana rumfa ka zamo mana Katanga.”
Da tsananin mamaki yake dubanta kafin ya murmusa yace “Wanda Allah ya zama gatansa shikeda cikakken Gata Uwani.. Amma yau naji dad’i da kika yarda duk talaucin miji da rashinsa akan iyalansa shi Katanga ne kuma rumfa ne..? Ashe yau kin amince ki tabbatar da hakan Uwani.. Na gode ma Allah da ya nuna mun wannan rana da kika furta hakan da bakinki kafin na bar duniya.. Ko kin mance abubuwan da kike fad’a mun a baya, cewa ni ban isa ba a gidan nan.. Idan inaso na zamto isasshe a gidana na maku abinda ranku ke so. Toh Alhamdulillah ban maku abinda ran naku ke so ba amma ku kunyi da kanku dan haka a wannan fanninma na kasa Uwani, saidai ku kuyi da kanku.. Ubangiji ya fiddaku..” Yana ida fad’in haka yasa kai zai fice..
Sadiya dake mak’ale bayan k’ofa tana sauraren tattaunawan iyayen nata wane irin kuka ne taji na taso mata, tai saurin fitowa daga mab’oyarta ta nufi Mahaifinta.. Durk’usawa tai ta kamo k’afarsa tana kuka tana fad’in “Abba dan Allah ka yafe mun.. Abba nayi imani hakkinka da rainikon da muka maka nida Umma shike bibiyanmu.. Dan Allah ka yafe mana Abba, kar kayi fushi damu ka yafe mana.. Wllhi na tuba Abba bazan sake ba..”
Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana mai rungume k’afar mahaifin nata...
K’uri yai mata kaman zai magana, sai kuma ya duk’a ya zame hannayenta daga rik’on da tai masa, lokaci guda yasa kai ya fice daga gidan..
Sady ta d’aura hannu aka tana kuka da duka zuciyarta tana fad’in ta shiga uku..
Ficewan Abba da kaman wasu mintoci wani yaro ya shigo ya sanar dasu ‘yansanda suna sallama a waje..
Sady ta kuma fashewa da sabon kuka tana fad’in “Shikenan Umma k’ila kud’ad’en da Sagir yayita bamu na shan jini ne.. K’ila ma kud’in kan mutane yayita bamu bamu sani ba Umma.. Na shiga uku ni Sadiya ina zan saka kaina..”
Umma ta girgiza kai tace “Aikin gama ya riga ya gama Sadiya, shige muje mu sami ‘yansandan dan ko bamu fita ba zasu shigo su samemu..”
A b’angaren Sadiya Ita bama fitan bane, ganin wannan D’ansandan ne bata sonyi wanda kallonsa kad’ai ba komai yake haifar mata ba face tsananin fad’uwan gaba.. Addu’a take Allah yasa kar tayi tozali dashi..
Aiko tayi sa’a domin kuwa yau d’in babu wancan D’ansanda Sai d’aya abokin aikin nasa da sukazo tare jiya saiko wata mace wacce itama tayi shiga cikin bak’ak’en kaya..
Shi wannan Officer d’in kam nada kirki ba kaman abokin aikinsa da sukazo jiya ba, haka Sadiya tace cikin zuciyarta dan ko yanzu ma a natse yake masu tambayoyi shida abokiyar aikin tasa..
Tambayar k’arshe ne da yayi masu yasa Sadiya da Umma duban juna..
Assad yana hankalce dasu, d’an gyaran murya yai kafin yace “Zaki iya gane mutumin da ya turo a matsayin Uncle d’in nasa..?”
Umma Ta girgiza kai tace “Gaskiya nikam bazan ganesa ba, dan sau d’aya na gansa kuma da Mahaifin ita Sadiyar sukai magana..”
Maleeka ta d’an matso kad’an tace “Bazaki iya suffanta mana yanda kamanninsa yake ba..? Kiyi dogon tinani da nazari..”
Girgiza kai Umma ta kumayi alamun a’a.. Sadiya dake gefe ta bud’e baki tace “Officer idan kuka sami wannan mutumin zaku k’yalemu..?”
Assad ya dubeta kad’an yace “Kinga mutumin ne..?”
Jinjina masa kai tai kad’an tana furta “ Eh na gansa kuma zan iya ganesa.. A tsakar gidan nan sukai magana da Abba ni kuma ina lab’e kitchen ina hangensu.. Zan iya gane kamanninsa...”
Jinjina kai Assad yai yana mai zira hannayensa cikin aljihu “Da kyau, yanzu zaki bimu can ofishinmu dake headquarters, akwai masu ilimin zana kamanni cikin bayanan da aka masu wanda su aikinsu kenan.. Zamuje ofishinmu tareda ke zaki masu bayanin kamannin wannan mutumin su kuma zasuyi sketching d’insa..”
Sadiya jin ance zaa tafi da ita police station ya sanyata zaro idanu waje tana duban mahaifiyarta “Umma Wai tafiya dani zasuyi..?”
Maleeka da kanta ke kife tana rubutu cikin wata ‘yar k’amar littafi mai yanayi da jotter d’agowa tai Ta dubi Sadiya tace “Kar ki d’aga hankalinki ba tsareki za’ayi a can ba, wasu tambayoyi kawai zaki amsa mana sai kiyi bayanin wannan mutumin..”
Assad ya murmusa kad’an ganin yanda tsoro ya cika Sadiyar yace “Ki daina tsoronmu.. Police are your friends kinji koh.. Had’in kanki kawai muke buk’ata domin mu cire gurb’atattu cikin al’umma..”
A hankali Sadiya Ta jinjina kai har lokacin tsoro bai bar saman fuskarta ba..
Umma Ta matso da sauri tace “Rankaidad’e dan Allah zan iya raka d’iyata.. Dan Allah ku taimakeni ku barni na tafi tareda d’iyata..”
Shiru Assad yai yana dubanta kafin ya jinina Kai a hankali yana mai nuna masu yanda motar take pake..
Gaba d’aya suka d’unguma suka tafi police headquarters..
Zuciyar Sadiya sai tsinkewa take, ta d’aga idanu tana duban dogon ginin.. Oh yau kuma Ita Sadiya ce a ofishin ‘yansanda, abinda takeji take kuma ganina finafinai sai gashi yau yana faruwa da ita.. Tabbas a rayuwa kar kayi ma k’addaran wani dariya domin bakasan da mai gobe zata Zo maka ba.. Tana ganin yanda mutane ke shige da fice. Assad na gaba yana masu jagora yayinda Maleeka ke take masu baya.. Sady dai sai rabe raben idanu take tana kallon kanta a wajen da bata tab’a tsammanin zatazo ba..
Suna tafe ta hangosa yana tsaye k’ofan wani Office kansa kife yana duba wani file.. D’ago kan da zai suka had’a idanu.. Take taga annurin fuskarsa ya kuma d’aukewa, Ta lura mutumin kaman haushinta yakeji, Ta kula baik’i ya sami wani dalilin da zaisa ya jefata kurkuku ba.. Take ta shiga b’oyewa bayan Maleeka tana k’ok’arin b’oye fuskarta tana lek’ensa.. Tana ganin Assad ya isa garesa yana nuna masa wani k’aramin d’aki mai kaman office.. A tare suka shige Assad d’in nayima Maleeka alama da hannu kan su k’araso..
Office ne madaidaici mai d’aukeda table guda biyu, d’aya table d’in wani mutum ne zaune da computer gabansa wanda take tinanin shima d’ansandan ne.. Sai d’aya table d’in kuma wani mutum ne zaune da takardu gabansa da k’aramar cup wanda pens ne da dangin abin rubutu ciki.
Umma bata shigo office d’inba saiko Sadiyar. Addu’a take Allah Sa kar wannan mutumin ya shigo.. Aiko bata ida addu’an ba Ta gansa ya shigo yana amsa waya.. Assad yai mata nuni da wani kujera yace ta zauna.. Babu musu ta k’arasa ta zauna.
Mutumin dake gaban computer shike tattara bayanan da Sadiya keyi cikin computer d’in yayinda d’aya Mutumin dake zaune gaban table d ya shiga shirya takardunsa alamun yana jira ta suffanta masu kamannin Kawun Sagir..
Assad yai mata umarni data fara bayani..
Yanda take masu bayanin a tsorace yasa mutumin bai fahimci komai ba, tana kuma d’agowa idan ta dubi Mu’azzam sai ta kuma daburcewa ta rasa bayanin da take..
Assad ya lura da hakan, ya d’ago yana duban Mu’azzam ya kuma dubi Sadiya dake satan kallonsa.
D’an sosa kunnensa kad’an Assad yai kafin ya dubeta yace “Are you alright..?”
Girgiza masa kai tai alamun a’a..
“What’s the matter then.?” Ya tambaya yana dubanta.
Satan kallon Mu’azzam da ta kumayi yasa Assad murmusawa kad’an kafin ya k’arasa yanda Mu’azzam yake ya d’an janyo Mu’azzam d’in da har lokacin waya yake yana tsaye jikin window.. Cikin dabara Assad ya fiddashi daga cikin office kafin suka samu full attention d’in Sadiya..
Ai kuwa suna fidda Mu’azzam daga office d’in suka samu full attention d’in Sadiya, tai masu bayanin kamannin Kawun Sagir tiryan tiryan..
Mai zana hoto ya zano kamannin data fad’i.. A daidai lokacin Mu’azzam da ya ida wayan da yake ya turo k’ofa ya shigo.. Bai wata wata ba ya isa table d’in yana duba zanen wanda ba fuskan kowa bane ya bayyana face Danger..
Wani irin huci kurum Mu’azzam yake yana dunk’ule hannunsa, lokaci guda ya bugi table d’in yana furta “I knew it.!” Lokaci guda ya fuzgi takardan ya fice daga office d’in cikin tsananin b’acin rai sai sakin huci yake kaman zai kifa k’asa...
Cikin sauri Assad yabi bayansa dan yasan komai ka iya faruwa tsakanin Mu’azzam da Chief Inspector.
Hankali tashe Assad ke k’ok’arin taresa ko kula Assad baiba har saida ya daki k’ofan Office d’in Chief..
Chief na cikin waya yana kwance cikin kujerarsa mai juyawa sai ganin Mu’azzam yai akansa yana sakin huci kaman wani mayuwancin zaki..
Babu shiri Chief ya katse wayar da yake yana duban Mu’azzam da tsananin mamaki
“How dare you barge into my office.. Who do you think you are..!” Cikin tsananin b’acin rai Chief yake maganar yana duban Mu’azzam dake tsaye gabansa idanunsa babu alamun tsoro..
Lokaci guda Mu’azzam ya d’ago Sketch d’in yana nunama Chief “Do you still have any reason to depend this criminal..?!”
Ko ba’a fad’a maka ba tsoro ya bayyana a fuskar Chief Inspector amma Sai ya dake yace “Kai k’aramin maras kunya. Kasan da wanda kake magana.. Naga irinka dubu kuma na gama dasu..”
Baikai aya ba Mu’azzam ya katsesa da fad’in “Bakaga irina ba kuma kafin kaga irina sai na tabbatar na gama dakai..”
Wannan karon murmushi Chief yai yace “Mind your language boy.. Bakada hujjan cewa na kare mai laifi domin kuwa dani da kai bamu San wanene Danger bamusan he’s connected to crime d’in nan ba sai yanzu...” Ya murmusa kad’an kafin yace “Har yanzu kaid’in yaro ne a gidan nan.. Har yanzu bakasan yanda Al’amara ke gudana a gida irin wannan ba.. You’re lucky, you’re from well known and respective family, I should’ve thrown you out cikin k’ask’anci . Now, get out of my office befor you lose everything .. Including your career as a police officer..!” Ya k’arashe muguwar murmushin saman fuskarsa..
Daidai lokacin Assad ya shigo a rud’e yana neman afuwan Chief on behalf of friend’s behavior..
Mu’azzam kaw har lokacin huci kurum yake yana duban Chief Inspector da idanunsa da tuni sun gama rinewa..
Chief ya dubi Assad d’in yace “Take him out.. Fitar dashi daga nan..!”
“Don’t touch me.. Don’t you dare touch me..!” Mu’azzam yai kashedi ma Assad kafin ya dubi Chief yace “Wata rana zamu had’u..! Alk’awari ne..!” Daga haka juyawa yai ya fice zuciyarsa na masa tsananin k’una..
Assad zai magana Mu’azzam ya d’aga masa hannu alamun dakatarwa “Not now Assad.!”
Fuzar da fuci kurum Assad yai kafin yabi bayan Mu’azzam d’in...
Su duka hud’in suna tsartsaye sunyi carko carko.. Suna kuma duban hoton Danger da ya bayyana cikin sketch d’in..
Assad ya nusa yace “What do we do now.. Danger must be in a hide tinda yasan dole za’a nemesa... Bazai tab’a zama nan kusa ba.. Allah Sa ma bai gudu ya bar gari ba..”
Yusuf yace “Ba Lallai Danger yasan ana nemansa ba, so ba lallai ace tsakanin jiya zuwa yau ya gudu ba..”
Muryar Mu’azzam suka sinkayo yana fad’in “We will track him down before yayi making move.. I know by now informer d’insa ya sanar dashi muna nemansa..!”
Gaba d’aya suka jinjina kai..
“Zamu fita yanzun nan zamuje unguwarsu Danger, but zamu fita ne a shirye dan nasan wannan area d’in territory d’insa ne komai ka iya faruwa..”
Suka jinjina kai suna amsawa.. Tuni ko Wannen su ya soma shirya weapon d’insa..
Maleeka ta d’an saci kallonsu yayinda suke ci gaba da tattaunawar yanda zasu tunk’ari al’amarin.. A hankali ta silale ta fice daga Ofishin gaba d’aya sai sauri take waya manne kunnenta tana faman waige waige..
A haka take gangarowa har ta d’anyi k’asa kad’an daga Building d’in nasu still tana ‘yan waige waige tana amsa waya..
Safeenah da k’arasowar motarsu wajen kenan Ta hangi Maleeka tsaye waya mak’ale kunnenta...
Wani irin wawan birki ta taka saida Meema dake zaune kujerar mai zaman banza ta saki ihu.
Hakan yayi daidai da k’aran da Umman Sadiya Ta saki wacce tayar Mota guda tabi mata kan k’afarta dan dama tin fitowarsu suke tsaye wajen suna neman abin hawa.. Umma ta sunkuya tana kame k’afarta dake mata zogi Sadiya na mata sannu..
D’agowa Sadiya tai tana jiran tagafitowar maras mutuncin matuk’in motar nan da yabi mata kan k’afar mahaifiya..
Wasu ‘yanmata ne ‘yangayun gaske guda biyu ta gansu Sun fito.. D’ayar fad’i take “Meema ki bud’e backseat ki d’auko.. Kiyi sauri mu k’arasa muci uwarta wllhi itace.. Bazan tab’a mance munin fuskarta ba..!”
Safeenah Batakai aya ba taji an rik’ota, ta juyo da mamaki tana duban wacce ta rik’eta.. Saida gabanta yayi wani irin fad’uwa da ganin kyakkyawar yarinyar data rik’ota tana sakin huci..
“Baiwar Allah baki gani ne kika bige min mahaifiya..?”
Sadiya tace tana duban Safeenar..
Wani irin wualak’antaccen kallo Safeenah da Meema suka raka Su Sadiya dashi kafin Meema tace “An bige ku d’in, ku makafi ne zaku tsaya bakin kwalta.. Ko kuma kurame ne ku da bazakuji sautin mota na zuwa ba..!”
Safeenah Ta finciki hannunta tana fad’in “Ke kika tsaya biyesu Meema, Ai shi Talaka dik yanda yaga mai kud’I hassada dashi yake.. K’iris yake jira ya hau d’aura masa laifi.. Muje kafin wancan shegiyar Ta tsere mana..”
Suka nufi d’aya length d’in cikin sauri yanda Maleeka take..
Sady tai kaman zatabi bayansu Umma ta rik’ota tana fad’in “K’yalesu Sadiya muji da rikicin dake kanmu bana fata mu kuma shiga wani fitinan..”
Sady tace “Amma Umma baki ganin abinda suka mana.”
Umma ta katseta da fad’in “K’yalesu Sadiya, ni mu samu mu bar wajen nan ma..” Ta k’arashe tana mai jan k’afar nata da k’yar Sadiya na mata sannu..
Maleeka tana tsaye taji an fincikota an fuzge wayar hannunta anyi jifa dashi had’ida kwasheta da wane irin mari mai walk’iya...
Leave a Comment