Gidan Aro 7

 


*07

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Cikin tsananin tashin hankali Umma Ke jijjigata “Sadiya..! Sadiya.! Sadiya dan Allah Ki tashi, kar ki tafi ki barni.. Sadiya ki tashi dan Allah..”

Assad ya k’araso yana mata fifita da takardan dake hannunsa...


Kaman daga sama sai ji sukai an watsama Sadiya ruwa a saman fuskarta.. Suka d’ago idanu suna duban Mu’azzam dake tsaye saman kansu rik’eda bottle water. Dama tinda Sadiya ta sume ya nufi yanda suka aje motarsu ya d’auko ruwan gora a cikin motar..


Wani irin dogon numfashi Sadiya Ta saki tana mai k’ok’arin bud’e idanunta..

Daidai lokacin Mu’azzam ya d’an duk’a kad’an saitin fuskarta.. Aiko tana bud’e idanunta tai tozali dashi duk’e gabanta ya tsareta da wannan idanun nasa masu furgitarwa, fuskarsa sam babu alamun walwala..


Rungumeta Umma tai tana fad’in “Alhamdulillah.. Sadiya kar ki tafi ki barni kinji.. Ked’in nake so d’iyata.. A halin yanzu ban damu ki auri mai kud’i ko Talaka ba, idan dai zamu kasance tare...”

Wani irin kuka Sadiya ta fashe dashi had’ida fad’awa jikin Umma sanda ta tuna abinda D’ansandan nan yace Wai Sagir ya mutu gawarsa aka tsinta..


“The drama is over.. Tashi ki fad’a mana komai da kika sani akansa..” Mu’azzam ya fad’i yana mai mik’ewa tsaye had’ida zira hannayensa cikin aljihun wandonsa..


Umma ta taimakawa Sadiya suka mik’e a tare 

“Rankaidad’e wllhi bamu San mutumin nan ba kaman yanda na fad’a maka, yaudara rum yai ya gudu ya bar d’iyata tana jira.. Wllhi bamu San daga yanda yake ba..”


“Ta yaya zaku d’auki ‘yarku ku bada aurenta ga mutumin da baku sani ba..? Shin dama irin haka na faruwa..?” Assad yace yana mai tsare Umma da idanu..


Mu’azzam kam har wanann lokacin idanunsa na kan Sadiya, yanai mata wani irin duba.. Maganganun Alhaji Isyaku Baban Sabeera na Yawo a dodon kunnuwarsa cewa yarinyar Ballagaza ce mai bibiyan maza dan neman abin duniya..

Baima sauraron tambayoyin da Assad Kema mahaifiyar Sadiya dan Sadiyar kam har lokacin rawa kawai jikinta yake Ta kasa katsb’us sai kuka da take har lokacin. Tana cikin tsananin shock har wannan lokacin.


Cikin tambayoyin da Assad yayima Umma ya fahimci cewa su kansu basu san tak’amaimen wani abu gameda Sagir ba, son abun duniya ne da ya rufe masu idanu  ya sanyasu amincewa da Sagir har ta kaiga suna yunk’urin  aura masa d’iyarsu..


Ya d’an girgiza kai yana duban yanda Uwa da d’iyar suka rungume juna suna hawaye.. Yaji tausayinsu dan tausayi amma something was amiss a cikin labarin, something wasn’t clicking, the math wasn’t mathing.. shi bai tab’a jin yanda akayi aure haka ba.. 

“Hajiya baku San kowa nashi ba kuka amince zaku basa auren d’iyarku..?” Assad ya kuma fad’i yana dubanta..


D’an jim Umma tai dan bata fatan wani abu ya jefata cikin fitinan da Sagir yake ciki.. Uban bashin da Tabawa Ke binsu ma kad’ai ya ishesu.. Hakan yasa ta girgiza kai alamun a’a..


“Kina nufin bai turo magabata ba haka kurum kuka amince zaku d’auki d’iyarku ku basa..?” Assad ya kuma jefo mata tambayar..


Umma ta daburce ta shiga girgiza kai tana neman kalaman da zata had’o saman harshenta..


Sai sannan Mu’azzam ya k’araso gaban Sadiya da kanta Ke kifi cikin jikin mahaifiyarta tana aikin kuka 


Cikin kuka Umma Ke fad’in “Rankaidad’e dan Allah kuyi hak’uri d’iyata Ta dawo cikin hayyacinta.. Dan Allah enough with the questions for now..”


Kafin yakaiga magana wayarsa Ta soma ruri, Chief Inspector Officer ne Ke kiransa daga ofishinsu can headquarters..


Ya matsa gefe yana amsa wayan.. Neman gaggawa da Chief Ke masu yasa ya k’araso yanda suke..


Ya d’an fuzar da fuci kafin ya dubi Umma yace “Ku tsammacemu ko wani lokaci daga yanzu..” Daga haka Assad yai yace suje...


Suna tafe Assad Ke fad’in “Maybe they’re telling the truth.. Maybe basusan komai akansa ba.. Kwad’ayin abin hannunsa ya rufe masu ido har sukayi tunanin basa auren d’iyarsu ba tareda sunyi bincike sunsan shid’in waye ba..”


“And you believe them.? Well idan ma haka d’in ne ita yarinyar dole tasan wani abu, dole tasan yanda ta had’u dashi.. I believe through wannan yarinyar zamu samu wani abu..”


Assad yai shiru yana nazari “You’re right.. Zatai linking  d’inmu to gaskiyar al’amarin..” 


**

Su Mu’azzam suna tafiya Umma ta janyo Sadiya suka shige gida harda saka ma gidan sakata..

Ita kanta Sadiyar sai sannan ta warware ta shiga rabe raben idanu tana fad’in “Umma yanzu ya zamuyi idan ‘yansandan nan suka sake dawowa.. Mai zamu ce masu..?”


Umma ta yarfe gumin dake kwance saman goshinta tace “Gwara mu barsu akan cewa bamu San komai ba kafin muje mu saka kanmu a UKU.. Allah kad’ai Yasan Sagir d’in nan wane irin gasunk’umin D’anta’addan ne..”


Umma ta nusa tace “Ni Anya bazamu bar garin nan ba, bazamuyi hijira ba kuwa.. Tashin hankalin tayi yawa, bamu gama da Tabawa ba yanzu ga wani ya kunno Kai..”


Sadiya tace “Umma mu tafi muje ina.. Bamuda wajen zuwa.. Kuma Tabawa bazata tab’a k’yalemu ba dik yanda muka je..Umma idan ma muka tafi bamusan wani irin fitina da tashin hankali zamu kuma fuskanta gaba garemu ba.. Sannan Umma ga Ashiru ga Habeeb yaya zamuyi dasu..? Sud’in fah yara ne Umma.. Tafiya dasu yana nufin jefa rayuwarsu cikin garari, and Umma bana fatan abinda zai b’ata rayuwan yaran nan.. Dik abinda nakeyi Umma inayi ne domin na inganta rayuwarsu.. Ina son mai  kud’i ne domin su sami rayuwa mai inganci su kuma girma cikin gata.. I don’t want my little brothers to experience what I have been through in the past...Umma bana son ‘yanuwana su sha wahala irin wahalan da ni nasha a baya a lokacin muna cikin tsnanin talauci Abba kuma yana cikin tsananin jinya..” Ta kasa ci gaba da magana sabida rawa da muryarta keyi..

Umma tai saurin k’arasawa ta rungume d’iyarta su duka biyun suna hawaye..


Cikin zuban hawaye take furta “Sadiya I don’t want you to suffer the same fate da mahaifiyarki na auren Talaka Shiyasa na dage sai kin auri mai kud’i.. Amma bayan abubuwan da suke faruwa yanzu, na yarda mutum baya wuce k’addararsa.. K’addararka tamkar inuwarka ce duk yanda kaje sai ta bika.. Ki yafe min ‘yata.. Ina ji kaman ni na saka rayuwarki cikin wannan gararin..”


Sady ta kuma rungume mahaifiyarta su duka biyun suna kuka mai ban tausayi..


**


Da tsananin mamaki Mu’azzam ke duban Chief Inspector, ya kasa yarda da abinda yake ci.. D’an girgiza kai yai kafin yace “Chief you need to believe me mutumin nan ba Iyakacin gaskiya yake fad’i ba.. Sir, I’m positive shid’in yasan Sagir sosai.. And yes munje location d’in da ya bamu and we found something.. Mun sami yarinyar da Sagir was about to marry.. Sir idan ka amince mun we are so close to finding the truth.”


Girgiza kai Chief Inspector yai yana mai duban Mu’azzam d’in idanu a kannare yace “I can understand you’re desperate to get to the bottom of this case.. And According to your team report Officer Gamji, mutumin nan ya sanar dakai Iyakacin hiran da yaji daga tattaunawar shi Sagir d’in yake da budurwarsa.. And kaima ka fad’a da kanka kaje wannan location d’in ka tabbatar da hakan, harma ka samu yarinyar.. So tell me, wani hujja kakeda shi da zaisa kaci gaba da ajiye shi a nan..?”


Huci kurum Mu’azzam yake yana duban Chief Inspector wanda yayi imani biyansa akayi ya kare mai laifi..


A hankali yake takowa gaban Chief kafin yace “Sir, I know my job.. I know exactly what I’m doing.. I only need a little more time to prove to you that..”


Katsesa Chief yai da fad’in “All the decisions are taking by me Inspector Gamji..! Now I’m ordering you to process his release immediately...!”

Cikin tsananin daka tsawa Yai maganar..


Mu’azzam dake ci gaba da sakin huci ji yake kaman ya shak’o wuyan che of inspector ya matsesa Sai ya fad’a masa uban wa yake karewa.. Assad ya kula da hakan, a hankali ya soma k’ok’arin janyo Mu’azzam yana fad’i cikin rad’a “Control yourself, don’t do anything foolish..”


K’ok’arin saita kansa Mu’azzam yai kafin ya jinjina kai yace “Yes, Sir.. Permission to leave, Sir.”


Chief ya jinjina kai yace “Good.. Dismiss now..”


Sara masa Mu’azzam d’in yai kafin yasa kai ya fice daga office d’in zuciyarsa na masa wani irin zafi...Shi kad’ai Sai wani irin tsuma yake.. Yana isowa ofishinsu buga benci yai yana sakin huci.. Maleeka ne da wasu abokan aikinsu guda biyu.. Suna ganinsa a haka duk suka mimmik’e.


Cikin tsananin huci yake furta “Out.. Everyone out..!” Babu shiri duk suka fice daga ofishin suna duban yananyin da yake ciki mai ban tsoro..


Assad ya turo k’ofar ya shigo kafin ya maida ya rufe yana mai fuzar da huci a hankali, lokaci guda yake furtawa cikin tsananin b’acin rai “What do you think you’re doing Mu’azzam.. What exactly is wrong with you.. You almost got yourself into trouble back there.. Ko kasan a gaban wa kake.. Chief ne fah Mu’azzam.. Ba case d’in nan kawai ba, harta aikinka zaka iya rasuwa Mu’azzam.. C’mon get a grip.!” Cikin b’acin rai Assad Ke maganar


“Shut up..! Just shut up Assad..!” Yai maganar yana mai d’ago kansa dake kife kafin ya k’araso gaban Assad d’in su duka biyun suna sakin huci...


Mu’azzam yaci gaba da fad’in “To hell with everything.. I don’t give a damn about his so called position.. I’ve always known mutumin nan is a corrupt police officer.. Nasan akwai wanda yake karewa.. Sanin kanka ne Assad sabida mutumin nan da gurb’atcciyar zuciyarsa wanda cin hanci da rashawa suka masa katutu munsha losing cases da Dama.. Criminals sun sha tsallake laifukansu. Da irin wannan mutumin a police force baza’a tab’a cin galaba ba.. Sune ‘yansandan da suke b’ata mana suna kuma suke walak’anta aikinmu takai matakin da Uniform d’in mu baida wani daraja a idon mutane.. But I promise you.. Ka rubuta wannan ka ajiye Assad, idan b’era na Yawo mage tana Yawo wata rana zasu had’e.. Sai na kawo k’arshen cin hancinsa da rashawarsa.. Kuma sai na kamo wannan mutumin da yake karewa..”


Daga haka bai kuma cewa komai ba ya bud’e k’ofar yai ficewarsa, yanda yake tafiyar kad’ai zai tabbatar maka ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci..


Daga bakin cell d’in Danger ya tsaya suna aika ma juna kallo.. Danger sai sakin murmushi yake yana shafa hab’arsa.. Lokaci guda yake furta “Mr Inspector.. It looks like nida Kai bazamu d’auki dogon lokaci a nan muna sha coffee ba..”

Ya d’anyi fasali yana mai girgiza kai had’ida tab’e baki kad’an kafin yace “Too bad you don’t smoke da mun had’e a mashaya.. So get off my neck already..!”


Baikai aya ba Mu’azzam dake tsananin huci ya zira hannunsa guda ta cikin k’arfen cell d’in ya fincikosa yana fad’in “This is not yet over.. I’ll make sure you rot in jail, you criminal..”


Cikin sauri Assad ya shiga janyesa, sai sakin huci yake.. Lokaci guda sergeant guda ya k’araso ya bud’e cell d’in Danger.. Aka fito dashi aka nufi bakin kanta dashi yanda Su agogonsa da wasu kayansa suke.. Sai sakin murmushi yake yana kashe ma Mu’azzam idanu..


Mu’azzam bai iya zama cikin wajen ba sai ficewa da yai cikin sassarfa.. Kafin Assad ya cimmasa har yayi key wa motarsa..


Yana isa gida baibi takan kowa ba ya nufi part d’insu shida Musaddiq dake cikin gidan.. 

Safeenah dake zaune balcony d’in d’akinta tana ganin shigowar motarsa ta mik’e.. Dama dawowarsa take jira, taci gayunta cikin navy blue Dubai material mai d’aukan idanu..  d’inkin fitted gown akai mata da ya mugun mata kyau ya zauna jikinta sosai.. Dikda bata faye fad’in kwankwaso ba amma ya mata kyau dan ko babu komai Safeenah tanada kyaun fuska da hasken fata.. D’aki ta komo ta isa gaba dressing mirror tana kuma k’yalk’yale fuskarta da kwalliya.. Ta sakar ma kanta murmushi ganin yanda tai kyau kafin Ta nufi b’angaren Mu’azzam...


Shi kaw yana fad’awa d’aki bathroom ya shige ya sakar ma kansa shower.. D’umin ruwan na ratsasa yana tuno abubuwan da suka faru dashi a ranan.. Na farko buge juna da sukai shida wannan ‘yar tashan yarinyar da jifa masa ultra da tai a fuskarsa... Sai kuma Chief Inspector da yasa aka saki Danger.. Lokaci guda ya bud’e idanunsa ya saka hannayensa biyu ya maida sumarsa da ruwa ya jik’a zuwa bayan kansa.. Fuzar da fuci yai yana mai kuma lumshe idanunsa.. Bai Sa a ransa  zai losing hope ba.. Binciken mutuwar Ikram yanzu ya fara koda hakan na nufin zai rasa komai nasa ne including his job as a police officer...


Safeenah da tin shigowarta d’akin Ta fahimci wanka yake dan tana iya jin zuban ruwa daga cikin bathroom d’in hakan yasa Ta zauna saman gado tana mai mik’e k’afafunta alamun tana jiran fitowarsa.. A nan saman gadon ta hangi suit d’insa da ya cire.. 


Murmushi ta d’anyi kafin ta mik’e tana furta “Maza Feenah tashi Ki fara gudanar da duty d’inki as a wife..” Tai maganar tana sakin murmushi kafin ta isa ta d’ago suit d’in nasa..

Jin kaman da abu gefen rigar ya sanyata kuma shafawa tana jin kaman soso.. Nan dai ta zira hannunta ta ciro abun..


Cak Ta tsaya tana juya ledar cikin hannunta.. Daidai lokacin Mu’azzam ya fito daga bathroom d’aure da towel saman kunkuminsa, hannunsa rik’e da k’arami yana tsane sumarsa..


Kallo d’aya yai mata yaci gaba da abinda yake, tana tsaye tana kallonsa ba tareda ta janye idanunta ba.. Zai iya cewa zama a turai yasa Safeenah take wasu abubuwan kaman dai k’arancin kunya, amma yasha mamaki da har Ta gansa a haka bai Ko d’ad’areta ba saima ci gaba da dubansa da take.. Ganin ko tarewa basuyi ba..

Ya d’an kuma satan kallonta still bai daina abinda yake ba, sai sannan yaga abinda ke rik’e hannunta...


Baice da Ita komai ba saima k’ok’arin nufan closet da yake..


Cikin sauri ta take masa baya har lokacin tana rik’e da pad d’in...


“Mu’azzam what is this doing in your pocket..?”


Ya d’an dubeta kad’an ba tareda yace komai ba yaci gaba da abinda yake...


Zata kuma magana ya soma takowa gabanta, ganin yanda ya had’e rai yana nufota ya sanya gabanta wani irin fad’uwa ta shiga matsawa baya baya cikeda tsoro... Saida ta isa jikin gini kafin ta daina matsawa har lokacin pad d’in na rik’e hannunta..


Rank’wafo da kansa da yai kaman zai sumbaceta yasa Safeenah saurin rintse idanunta tana jin sanyin ruwan dake jikinsa had’ida hucin numfashinsa..


Saitin kunnenta yake fad’i tamkar mai rad’a “I hate it when someone messes with my stuff..” Daga haka zare ultra d’in yai cikin hannunta ba tareda ya kuma cewa komai ba..


“But I’m not someone.. I’m your wife.. And dan  na tambayi ina ka samo ai banyi laifi ba..”


“Safeenah Zo ki fice min a d’aki..” Ya fad’i yana nuna mata k’ofa.


Idanunta suka kawo ruwa, zuciyarta ta shiga mata zogi, meke shirin faruwa da aurenta tin baaje ko Ina ba.. Auren data d’au alwashin protecting d’insa no matter the costs..


“But you know this is not fair..” Ta fad’i cikin rawar murya irinta mai kuka..


“Get out please...” Ya kuma fad’i yana nuna mata hanya..


Jinjina kai tai kafin ta tako gabansa tana goge siraran hawayen dake gangarowa saman fuskarta “Wannan shine dalilin da yasa kak’i mu tare har yanzu.. Do you have another woman in your life..?”


Da tsananin mamaki yake dubanta, shine Safeenah take kallo tana fad’a masa magana haka, mai ta d’aukesa mai Ta maidashi.. Idan baiyi k’ok’arin rik’e kansa ba yanda ransa yake b’acen nan zai iya mata komai l..


K’ofa ya kuma nuna mata “Leave now..!”


Zata k’ara bud’e baki kenan taji ya fizgota da k’arfin gaske ya nufi k’ofa da Ita.. Har waje ya fitar da Ita kafin ya maida k’ofan ya rufe..


Safeenah taji wani irin kuka na zuwa mata, durk’usawa tai wajen tana cazgan kuka.. Allah ya gani bazata iya sharing mijinta da wata shegiya a waje ba... Da wannan tinanin ta tashi ta nufi side d’insu..


A k’ofar parlor Ta had’u da Meema zata fito waje..


Meema ta dubi Safeenah da har lokacin da ragowar hawaye a fuskarta..


“Addah Feenah lafiya.. Ya na ganki haka.. Keda kika koremu d’azu kikace kwalliya kike wa Ya Mu’azzam mu fice mu baki waje.. Ya kuma naga Fuskar Ki haka..?”


Harara ta raka Meema dashi “Mind your  own business..” Ta fad’i tana mai shigew..


Meema ta tab’e baki kad’an kafin tabi bayanta tana fad’in “Aaaa badai Meeman ba, I don’t mind my own business.. Duk abinda babu ruwana a gidan nan shi nake shiga.. I love to meddle with other people’s lives..” Tana ida fad’in haka ta nufi bayan Safeenah..


Kafin Safeenah Ta rufe k’ofa Meema ta shige..


“Addah Feenah Wai meke faruwa ne.. Sai fah kin fad’a mun.. You know bazan k’yaleki ba har sai naji komai..”


Feenah ta isa saman gado ta zauna tana jin hawaye na kuma zuwa mata, cikin muryar kuka take furta “I thought babu ruwansa da mata.. I thought baida lokacinsu.. But then I was wrong..” Kuka ya hanata ci gaba da magana..


Meema ta tab’e baki kad’an tace “Dama ke Addah Safeenah wani namiji ne mai lafiya zaice babu ruwansa da mace.. Wllhi k’arya ce kawai.. Ai haka aka haliccesu da son mata.. Ke yanzu jinki Ya Mu’azzam zaik’i amincewa da tariyarki ne idan baida me d’ebe masa kewa.. Ahap.. Allah yasa ma ba a Gidanki yake cin amanarki ba dai..”


Cikin kuka Safeenah ta katse Meema da fad’in “Enough Meema.. Ya isheki haka.. I know my husband is not like that..”


Tab’e baki Meema tai kafin tace “Aw really..? Shisa naga kinzo nan kina kuka ai.. Addah Safeenah you need to face reality.. Your Husband is a cheater.. Abinda ya kamaceki shine ki tashi tsaye, and fight for what’s rightfully yours kafin kiyi latti.. That’s if you really love him..!” Ta k’arashe tana ware idanunta fuskar Safeenar..


Shiru Safeenah tai kaman mai nazari sai kuma tace “What do i do now Meema..?”


Meema Ta tab’e baki kad’an tace “Baki sanar dani abinda ya faru ba ta yaya zan samo miki solution..”


Safeenah ta karanto mata tiryan tiryan abinda ta gani wajen Mu’azzam da yanda suka kwashe..


“Tabb amma wllhi Adda Feenah gayen nan ya raina miki hankali.. D’an anjima ma ce miki zai is a piece of evidence na wani binciken da yake.. Wllhi mata yake bi idan ba haka ba babu abinda zai had’asa da ultra.. Kinsan me..?”


Safeenah Ta girgiza kai alamun a’a..


Meema ta jinjina kai tace “Kin bincika wacece budurwar tasa ni kuma na miki alk’awarin shirya miki wulak’ancin da zaki mata wanda ko kallon yanda mijinki yake bazata k’ara ba koda kuwa Colleague d’insa ce a wajen aiki..”


Safeenah tai saurin d’agowa tana duban Meema, lokaci guda ta shiga jinjina kai tana fad’in “Itace.. Junior colleague d’insu ce a police Academy bani mancewa dik tare sukayi da best friend d’insa Assad.. And yanzu kuma tare suke aiki a CID.. Ta jima tana son Mu’azzam..”


Meema ta dara kad’an tace “Ahap wllhi itace take neman rabaki da mijinki..”


Safeenah tace “Toh amma ai shi baya sonta, kuma ita d’in ba ajin Mu’azzam bace..”


Gajeren tsuka Meema tai tace “Wllhi idan kikayi magana Sai naga kaman Bakida experience na rayuwa.. Shi namiji ina ruwansa indai zai samu abinda yake nema.. Wllhi Ko kaffara bazanyi ba itace tinda kullum suna tare wajen aiki..”


Safeenah ta jinjina kai tana huci “Wllhi sai na mata mugun wulak’anci.. Sai nasa ta soma jin kunyar kanta a ofishin nasu.. Sai naci mutuncinta a bainar jama’a..!” Ta k’arashe tana sakin huci..


Meema ta murmusa tace “Good. Now you’re talking like my real sister.. Ni ko a sch ban tab’a losing battle ba.”


Safeenah tace “Mai zan mata Meema ta fita daga rayuwar mijina..?”


Meema ta matso kad’an tace “Kawo kunnenki kiji..


No comments

Powered by Blogger.