Gidan Aro 30
*30*
©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Musaddiq ya girgiza kai kurum kafin ya fice daga parlorn gaba d’aya. Meema dake Ta faman sosa fuskarta yanda Musaddiq ya
mareta satan kallan Mu’azzam tai Ai kaw nan taga kaman jefo mata razannan kallon nan nasa babu shiri ta nemi hanyar ficewa daga parlorn itama. Gani take kaman daga kanta zai fara tinda ita ta kawo rahoton. Batama San ko kallon yanda take baiba balle yasan tana parlorn. Tsaban tsoro ne da imagination d’inta suka nuna mata hakan.Safeenah Sai kokawan k’wacewa daga rik’on da Aunty Shemau tai mata take “Daddy Mommy kuce ya fice bana son ganinsa.. I don’t want to see him.!”
“Ki rufe wa mutane baki ki natsu ki daina haukar nan..!” Daddy ya katseta da fad’in haka.
Lokaci guda Mu’azzam d’in ke k’ok’arin gaida Daddy kafin ya juyo yana duban Mommy “Mommy Ina kwana..”
Mommy baki sake take dubansa bayan d’aga masu hankali da yai har yanda guts d’in dubansu yace masu ina kwana.
“Da ban kwana ba ai bazaka ganni ba mugu kawai azzalumi macuci maci amana.. Kaji kunya Mu’azzam Bayan duk abinda naiwa mahaifiyarka a rayuwa, na d’auketa ‘yaruwa na kwashe shekaru ina mata jinya abinda zaka saka mun dashi kenan.. Ka rasa mai zakaiwa d’iyata sai ka dinga d’auko Karuwai kana kaiwa Gidan aurenta gidan da ko tarewa cikinsa batai ba.. Wllhi kaji kunya Mu’azzam.. Tirr.!”
“Mommy I don’t know what you’re talking about.. Ni ban kai wata Karuwa ko ina ba..” Ya fad’i cikin dakewar Murya.
Baki sake Su Mommy dasu Safeenah suke dubansa. Wai bai kai Karuwa ko ina ba.. Tsaban shi tacecce ne maimakon ya bada hak’uri ya amshi laifinsa denying ma yake hankalinsa kwance.
A hasale Mommy ta mik’e tana fad’in “Kai bari kaji na fad’a maka ba tsoronka fa ake ba.. Ka bar ganin kana dik abinda kaga dama ana d’auke ido..”
“Hajara ya isa haka..!” Daddy ya katseta cikin tsananin b’acin rai..
Da mamaki take duban Daddy kafin ta ci gaba da jinjina kai tana fad’in “Dama na sani bayansa zaka bi.. Ya cutar da d’iyarmu ya Zalinceta amma kana bin bayansa..!”
“Nace kimin shiru Hajara.. Ta yanda kika b’ullo bata nan za’a gyara al’amarin ba..!”
Safeenah dake kuka Ta bud’e murya tace “Daddy are you really taking his side..? Daddy karuwa fah Karuwa ya kai mun gida tun kafin na tare..!”
Wannan karon Mu’azzam ne ya mik’e a zuciye yana nuna Safeenah da yatsa “Don’t you ever call her Karuwa again..!”
Mommy ta soma salati tana tafe hannaye tana duban Daddy “Ka gani ko.. Ka gani da idonka.. Ya nuna mana shi tabattacene.. Goyon bayan Karuwa yake akan matarsa.”
Ya juyo ya dubi Mommy “Mommy ita ba Karuwa bace..”
“Idan ba Karuwa bace to mecece..?”
Kafin Mommy takai aya ya bata amsa da fad’in “She’s my wife..! Matata ce kaman yanda Safeenah take matata..!”
Yanzu kam gaba d’aya mutane parlorn in a shock suke dubansa kaman wanda aka danna masu pause aka hanasu motsi.
Daddy ya girgiza kai wannan karon “Mu’azzam matarka fah kace..?”
Ya jinjina kai a hankali yana mai sadda kai gaban Daddy.
Daddy yace “But.. But how’s is this possible... Wane irin matarka kuma..?”
Mu’azzam yace “Daddy I’ll explain everything..”
Mommy ta shiga tafe hannaye tana fad’in “La’ilaha’illahu na shiga uku ni Hajara..! Mu’azzam ta nan ka b’ullo kuma.. Na shiga uku wata irin mata Mu’azzam..!”
K’aran da Safeenah ta saki tana mai zubewa wajen yai daidai da soma kiran wayar Mu’azzam da akai.
Gaba d’aya su Daddy Mommy harma da Aunty Shemau sukai kan Safeenah suna jijjigata suna ambato sunanta.
Assad ne mai kiran nasa, ganin yak’i daina kira yasan dole abu ne mai mahimmanci..
Ya d’aga wayar yana sauraron Assad daga d’aya b’angaren
“Mu’azzam you need to come right away.. Ka baro duk abinda kake kazo.. Mun samu abinda zai fayyace mana wanene Sagir..!”
Ai Assad bai kai aya ba Mu’azzam yace “Alright.. I’m on my way there..!”
Ya dubi Daddy yace “Daddy I need to go now.. I’ll explain everything later..”
Shi kansa Daddy yau d’in bai iya amsa Mu’azzam ba sai zuba masa idanu da yai..
Safeenah wacce dama sumar k’arya tai jin zai fice bai ko bi takanta ba ta mik’e tana furta “Mommy Kun gani wajen Karuwar zai koma ya k’yaleni a nan bai damu ko mutuwa nai ba.. Daddy you need to stop him.. Wllhi wajenta zai koma..!”
Ko tsayuwa sauraronsu bai ba ya fice cikin sauri.
Safeenah ta saka hannayenta biyu aka tana k’walla wane irin birkitaccen k’ara.
Mommy taci gaba da bala’i tana fad’in wllhi sai Sun tafi Kotu da Mu’azzam.. Yau d’in nan ba sai gobe ba zasu rubuta masa sammaci.
Daddy ficewa yai a parlorn dan ya kasa controlling Safeenah da mahaifiyarta wanda gaba d’aya sun fice a giya sabida abunda Mu’azzam ya aikata masu.
Aunty Shemau kaw tsananin mamakin Mu’azzam ne ya mugun cikata. Ita batai tsammanin rashin mutuncin Mu’azzam ya kawo nan ba.. Wai matarsa ce ba Karuwa ba.. Ikon Allah Toh yaushe akai auren..? Yaushe ya aureta har ya kaita gidan Safeenah.. gidan da akai ma Safeenah jere.. Kuma ko kunyar cewa matarsa ce baiyi.. Ita yanzu kam ta fara razana da al’amaran Mu’azzam.. Harga Allah tsoro ya fara bata koda wasa batai tsammanin yakai wannan matakin a rashin mutunci ba.. Ko a labarai bata tab’a cin karo da D’an iskan miji irin Mu’azzam ba ka d’auki wata mata ka Kai gidan Amaryar ka da iyayenta suka zuba mata dukiya sukai mata jere ko tarewa matar batai ba. Lokaci guda tausayin Safeenah na rufeta, bata tab’a ganin Amaryar da aka ci mutuncinta irin Safeenah ba.. Ace aure ko tarewa Bakiyi ba. Bama kiga kalan gidanki ba har an auri wata mace an kaita ta rigaki sanin gidanki da mijinki da kayyakin ki.. Ikon Allah wannan kayan mamaki da yawa yake. Ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tana mai ci gaba da danna Safeenah dan Mommy kam tuni tabi bayan Daddy tana jaddada masa tafiya Kotu, dan cewa tai bataga Uban da zai hanata maka Mu’azzam a kotu ba sakamakon cin mutuncin da yai ma d’iyarta.
Safeenah ta mik’e ta d’au crutches d’inta Ta nufo waje.. Aunty Shemau ta biyo bayanta tana fad’in “Feenah ina zaki.. Bakida lafiya ki zauna a gida..”
Ko tsayuwa amsa Aunty Shemau batai ba.. Kiki da Meema hayaniyar ya fito dasu, Kai kana ganin gidan kawai Kasan babu lafiya. Meema kaw da ta lab’e taji komai mamaki ya kasa sakinta ita kanta yanzu al’amarin Ya Mu’azzam ya daina bata mamaki ya koma bata tsoro.. Wai matarsa ce ba Karuwa bace.. Ikon Allah kayan mamaki baya k’arewa a wannan ahali nasu.
Meema tai saurin rik’o Safeenah da tuni ta d’uko car keys d’inta tana fad’in “Adda Feenah what are you doing..? You can’t drive like this.. Dan Allah kiyi hak’uri abi komai a sannu.”
Cikin tsananin huci Safeenah ke fad’in “Let go of me Meema.. I’m not listening to you today.. Ki sake nace Meema..!” Ta k’arashe cikin tsananin daka tsawa hawaye na tsartsafo mata.
Babu shiri Meema Ta saketa ta shiga bin bayanta tana kiran sunanta. Kiki ma makarantar da bataje ba kenan ta soma bin bayan ‘yanuwan nata.. A haka har suka iso parking lot yanda motar Safeenah ke ajiye tana k’ok’arin bud’eta.. Meema taci gaba da rok’onta tana fad’in “Addah Feenah please you can’t drive like this.. Ki kalli condition d’in da kike ciki fah.. K’afarki babu lafiya how can you drive like this.. Ok bani key d’in I’ll drive you ko ina kike son zuwa..”
Ta k’arashe tana mik’o hannayenta biyu alamun Safeenah ta bata key d’in.
Huci kurum Safeenah take tana duban Meema. Lokaci guda ta dank’a mata key d’in tace “Take me to her..!”
Meema Ta juyo da dubi Kiki dake tsaye bayansu tana zaro idanu waje dan tsoro sabida tsananin tashin hankulan da suka tsinci kawunansu ciki a gidan.. Kai da ganin yanayi Safeenah Kasan zata iya aikata koma menene.
Kiki ta girgiza wa Meema Kai alamun kar ta kai Safeenah wajen matar da suka ganta tareda Ya Mu’azzam dan tsaf zata iya illatata komai ka iya lalacewa. Dama Kiki akwai tsoro.
Tsawa Safeenah ta dakawa Meema “I said take me to her Meema..!”
Lokaci guda Meema ta shiga jinjina kai kafin ta bud’e driver’s side Ta shige Safeenah ta shige mazaunin mai zaman banza..
Girgiza kai Kiki take tana furta “Oh no.. This is not good.. I must do something to stop them..!” A guje Ta koma cikin gidan tana k’walla kirawa Yayanta Musaddiq.
A main k’ofan fitowa daga gidan sukai kusan karo da Musaddiq yana mata fad’an shi sa’anta ne da zatake masa kiran tasha.
Kiki ta shiga girgiza kai tana fad’in “Ya Musaddiq Addah Feenah da Meema sun tafi gidan Ya Mu’azzam . Addah Feenah tace sai ta kashe matar da muka ganta tareda Ya Mu’azzam..! You need to stop them before Addah Feenah does something terrible..!”
“Damn it..!” Ya furta yana mai komawa cikin gidan.. Sauri sauri ya d’auko car keys d’insa ya fito zaibi bayansu.. Mommy ya gani tsaye gabansa tana sakin huci “Koma babu yanda zakaje.. Ka koma ka k’yalesu suje sucimin uwarta.. Idan kabi bayansu ka taresu ban yafe maka ba Musaddiq..!”
Musaddiq ya girgiza kai yace “Mommy idan sukaje suka kashe ‘yar mutane kamasu fah za’ayi, kulle yaranki za’ayi a prison.. Dan Allah ki bari na dakatar dasu kafin azo ana danasani gaba d’aya.. You don’t want your daughters to go to jail.. Do you..?”
“Kafin su tafi gidan yari sai shegen nan Mu’azzam ya tafi dan dik abinda ya faru shine sila shi ya jawo.. Dan haka na basu goyon baya d’ari bisa d’ari suje suci uwarta kafin shima mu tafi kotu ya amsa nasa..!”
“Mommy..!” Bai kai aya ba Ta katsesa da fad’in “ka sake kiran Sunana sai na tsine maka.. Shashasha kawai wanda baya kishin ‘yaruwarsa..!”
Kiki dake tsaye gefe kuka itakam ta fara dan tashin hankalin yayi yawa..
Cikin sauri ta sad’ad’a ta fice ba tareda Mommy ta ganta ba. Bazatso Addah Feenah ta kashe wannan matar a kaita gidan yari ba.. Zatabi bayansu tai k’ok’arin dakatar dasu koda bazata iya ba.
Mommy kaw tana nan tana jaddadawa Musaddiq cewa yana fita daga gidan sai ta kwashe masa albarka.
A parlor Aunty Shemau ta tadda Daddy asthma attack d’insa ya tashi sai numfashi yake da k’yar oxygen na neman gaza masa.. Ta saki kururwa tana doka kiran Mommy..
A tare Mommy da Musaddiq suka nufi cikin gidan a guje hankali tashe.
**
A can Headquarters kuwa Assad sai juya wayar da Sabeera Ta basa yake yana kuma dubawa. Ya d’an tsareta da idanu kafin yace “Zan so ki tsaya ki bada statement d’inki a gaban Mu’azzam..”
Sabeera ta girgiza kai tace “Rankaidad’e Kasan yanda yanayin wannan case d’in yake, yanzu haka ni da na kawo wayar nan ta yuwu rayuwata na cikin had’ari.. Da fari jefar da wayar nayi niyyan yi dan bana son wani abinda zai had’ani da case d’in nan duba da yanda Aminiyata keta faman shan wahala dik a sabida tarayyarta da Sagir. Da ace Nasan yanda zan sami Sadiya da bazanzo ofishinku ba, da kai tsaye wajenta zanje na kai mata wayar. I don’t want anything to associate me with this case.”
Assad ya murmusa kad’an kafin yace “I understand where you are coming from.. And believe me wannan abinda kikayi zai taimaka mana matuk’a wajen solving case d’in nan.. I must thank you.. Mun gode k’warai.. Ba k’awarki kawai kika taimaka ba harda entire NPF kika taimaka.. Idan aka kamo accomplices d’in Sagir an rage mugun iri cikin al’umma.. Thank you miss Beautiful..” Ya k’adashe yana sakar mata murmushi.
Murmushin itama tai kad’an tana mai sadda kanta k’asa. Cikin d’an daburcewa sabida irin kallon da yake jifanta dashi Ta mik’e tana fad’in “I.. I must leave now.. Goodbye..!” Ta k’arashe tana mai sa kai..”
Saurin bin bayanta yai yace “Wait.. Barin saka a kaiki..”
Tai saurin girgiza kai tace “No banso a ganni da wani d’ansanda balle naja ma kaina attention.. But thanks anyway.. I can manage..”
Assad ya jinjina kai yana dubanta “You take care..!” Ya fad’i sanda take ficewa. Ta jinjina kai a hankali kafin tai saurin ficewa daga wajen.
Yana nan tsaye Yusu ya k’araso ya samesa suna magana k’asa k’asa dan basu so wani ma yasan sun sami wayar Sagir a hannunsu har Sai Mu’azzam ya iso..
Aiko nan suka hangosa yana tafe ya kwab’e suit d’insa yai folding hannayen long sleeves d’insa wanda itace ‘yar cikin suit d’in nasa.. Da gani yanda yake tafiya Kasan ya shirya ma binciken.
Yana k’arasowa suka nufi building d’in suna tattauna batun.
Maleeka da k’arasowarta kenan nan ta hango Mu’azzam ya dawo aiki wani irin murmushi ne ya kufce mata ta k’araso gudu gudu tana d’ago masa hannu take fad’in “Sir....!”
A tare suka waigo suna duban Maleeka dake nufosu.. Team d’in nasu sun had’e gaba d’aya. Yusuf da Assad suka saki murmushi suna duban Maleeka wacce suka rasa walwalanta tin bayan dakatar da Mu’azzam da akai. Sai yau suke ganin murmushinta.
Ta k’araso da sauri tana k’ok’arin saita kanta gaban Mu’azzam wanda ya tsime sosai yana dubanta “I.. I’m sorry Sir.. I just want to say welcome back.. Munyi kewarka sosai.. Welcome back Sir..!” Ta k’arashe tana rungume files d’in dake hannunta cikin k’irjinta.
Duk sukai tsaye suna duban Mu’azzam da ya tsareta da idanu wanda ba Maleeka dake Ta faman rarrabe idanu cikin tsoro tana addu’an Allah Sa ba wani laifin tai ba harta da su Assad saida suka d’anyi pause suna dubansa.
Murmushi ya sakar mata da gefen bakinsa kafin yace “Thank you..”
Daskarewa Maleeka tai tana jin Wai Mu’azzam ne ya ce da ita thank you har yana sakar mata wannan tsadadden murmushin nasa..
Bai kuma bi takanta ba yasa kai ya shige su Assad na biye dashi suna murmushin Daskarewar da Maleeka tai.. Lokaci guda Mu’azzam d’in ke fad’iwa su Assad “Let’s go.. To the tracking room and see what we can find inside..”
Yusuf da Assad suka jinjina masa kai suna tafe cikin sassarfa.
Saida har suka shige kafin Maleeka ta saki d’an k’aran murna tana cilla hannayenta sama “Yes yes.. He will fall for me eventually.. I’m sure of it.. Well done Maleeka kici gaba da hak’uri har ki saye zuciyarsa..” Daga haka saurin shigewa tai tabi bayansu.
**
Meema tana ida parking a k’ofar Gidan Safeenah ta k’arasa tana buga gate d’in da sandar crutch d’inta. Bugu take da iya k’arfin da Allah ya hore mata Meema na fad’in Addah Feenah take ita easy..!”
Bata ko saurari Meema ba tace “Ki d’auko min ultra pad d’in nan cikin mota nayi imani nata ne na gani wajensa ranan.. Ma ita ya saya zai kawo.. Wllhi I’ll make her eat it.. Sai na sakata Ta cinyesa.. Ki wuce nace ki d’auko mun Meema..!”
Cikin sauri Meema ta jinjina kai ta shige mota ta d’auko ledar ultra d’in.
Police man d’in dake gate ya bud’e yana duban Meema da Safeenah da mamaki.. Kafin yai magana Safeenah ta d’aga crutch d’inta ta shiga rabza masa aka kaman Allah ne ya aikota.. Dik k’ok’arin sa ganin ya hanasu shiga abu yaci tura dan Safeenah hauka tuburan take nunawa. Daidai lokacin Kiki ta k’araso ta ceci Police man d’in da k’yar wanda tuni jini ya soma zubowa daga goshinsa Sabida k’arafan da Safeenah ta dinga rabza masa.
A haka suka nufi gidan Safeenah na sakin huci tana duban fad’in gidan da kalan cin amanar da mijinta Mu’azzam yai mata.. Gidanta ne amma wata ‘yar iska ce ciki har yana kiranta da matarsa.
Suna isa ta shiga bugun k’ofar parlorn da iyaka k’arfinta.
Sadiya da har lokacin tak’ure take waje guda tana kukan rashin sanin ina ahalinta suke kaman daga sama taji ana bugun k’ofar.. A d’ari ta mik’e ta nufi k’ofar dan a zatonta Mu’azzam ne ya dawo mata da labari mai dad’i ta bud’e tana fad’in “Have you found them already..!” Cak ta tsaya ganin ba Mu’azzam bane wasu ‘yanmata ne guda biyu.. Take ta juya tana kallon hoton auren Safeenah da Mu’azzam, nan ta fahimci matarsa ce wannan.. D’ayar kuma taso ganeta ta rasa a ina ne.. Lokaci guda ta tuna Sune ‘yanmatan da suka tab’a had’uwa dasu a Police Headquarters har suka take mata k’afar Umma da tayar Mota.
Sud’inma dubanta suke suna son d’ago ina suka tab’a ganinta.. Meema ce ta soma d’ago hannu tana nunata alamun ta ganeta.
“Addah Feenah itace.. Itace wacce muka bugesu a k’ofar police headquarters last two weeks itada wata mata.. Ta saba binsa har wajen aiki..!”
Ai Meema bata kai aya ba Safeenah dake tsananin huci tana duban Sadiya ta yunk’ura takai mata wata jahilar mari.. Saidai Sadiya bata bari marin ya sauk’a a fuskarta ba Ta rik’e hannun Feenah tana sakin huci itama.. Tin kafin Feenah takai hannunta k’asa Sadiya Ta maida mata Martanin marinta tasss..! Lokaci guda take nunata da yatsa tana fad’in “Wannan shine sakamakon take mun k’afar mahaifiya da kikayi da Mota..!”
Kan uban can.! Safeenah tai tsaye tana dubanta dafe da k’uncinta. Meema ma kame baki tai tana duban Sadiya data kashe Safeenah da mari mai lafiya har cikin gidanta..
“Idan ban kasheki yau ba sunana ba Safeenah Marwan Gamji ba.. Sai nayi ajalinki shegiya Karuwa..!”
Tana ida fad’in haka ta shiga kokawan janyo Sadiya sabida k’afarta dake da ciwo yasa batai nasaran capketa ba takai mata duka da sandar hannunta Ta kauce.. Lokaci guda Safeenah ke fad’i da Meema “Tare mun shegiya Meema kar ki barta ta fice..!”
Daidai lokacin Kiki ta shigo Safeenah tace su toshe mata Sadiya..
Sarkin yawa yafi Sarkin k’arfi aiko Meema dake duk Ta fisu jiki dama tuni ta k’arasa ta had’e Sadiya jikin garu ta matseta sosai Safeenah na fad’iwa Kiki Ta taimakawa Meema.. Kiki ta k’araso ta saka ma Meema hannu suka danne Sadiya a k’asa. Safeenah na huci ta b’arke ledar ultra d’in ta shiga turawa bakin Sadiya tana fad’in “Sai kin cinye yau tas dan uwarki.. Shegiya Karuwa sauran kwalta mai bin mazan mutane.. Yau sai kinyi nadaman sanin mijina da kikai har kika yarda ya kawoki gidana ya ajiye..”
Sadiya tana kiciniyar k’watan kanta fa Safeenah na tura mata sanitary pad cikin bakinta.. Kiki Ta sunkuya saitin kunnen Sadiyar ta rad’a mata a hankali “Zan sakeki kiyi k’ok’ari ki tura Meema batada wani balance sai ki gudu..”
Safeenah ta kamo sumar Kiki tana fad’in “Mai kike fad’a mata munafuka..!”
Daidai lokacin Kiki ta saki Sadiya ta taimaka mata suka hankad’a Meema ta fad’i gefe tana sakin k’ara.. A guje Sadiya ta nufi upstairs ya maida k’ofa ta rufe..
Safeenah tayo kan Kiki zata jibga wayar Meema ya soma ringing dan dik tashin hankali da Meema zata shiga bata rabo da wayarta.. Kiki ce ta k’arasa ta d’auka dan Meema kam ta kasa tashi tana nan zube wajen tana ihun k’afarta.
Ganin Aunty Shemau ce mai kira ya sanya Kiki Saurin d’agawa..
Cikin rawar murya Kiki ke fad’in “How’s Daddy doing Aunty Shema..? Alright gamu nan zuwa..!”
Ta juyo tana duban ‘yanuwan nata sai kuma ta fashe da kuka tana fad’in “Daddy ne.. Daddy babu lafiya.. Aunty Shemau ce ta kira tace maza muje gida yanzun nan..”
Babu shiri Safeenah ta finciki wayar tai jifa dashi “Babu yanda zamuje sai na kashe shegiyar nan..!”
Meema ta mik’e da k’yar tana fad’in “Toh wllhi saidai kiyi ke kad’ai Addah Feenah.. What if Daddy ya mutu muna tsaye a nan.. Kiki shige muje I want to see Daddy..!” Ta k’arashe tana kamo Kikin cikin d’ingishi.
Safeenah ta d’aga ido tana duban upstairs d’in “This is far from over..! Zan dawo dan Ubanki.. Kuma sai na kashe ki..!” Daga haka ta janyo crutches d’inta ta nufo bayansu.. Saidai suna fitowa sukaga d’akin karnukan a bud’e. Aiko nan karnukan suka soma haushi.. A d’ari suka arce suka nufo gate a guje suna ihu.. Harta Safeenah watsar da Crutches d’inta tai ta fito a guje.. har suna bangaje police d’in dake gate.. Dik gudun nan basu san k’ofar d’akin karnukan bane kawai a bud’e amma suna d’aure da chain d’insu.
Police d’in ya tattaro sandunan Safeenah ya mik’a masu cikin Mota yace a sauk’a lafiya.. Aka barsa da kumburarren goshi yanda Safeenah ta jibgesa da sanda.
**
CID
Bayan wayar tai chaji suka soma binkicen k’wak’waf cikin wayar. Suka soma Retrieving dik wani sak’o ko kira da aka fitar daga kan wayar. Lamba d’aya suka samu cikin wayar da kuma kan SIM card din, sannan wannan lambar ita kad’ai aka tab’a contacting da SIM card d’in.. Sannan sak’o d’aya ce aka tura da wayar kuma ma lamba d’aya tak aka tura sak’on.. Sak’on Address ne aka tura da wayar. Location d’in da aka sami gawar Ikram da Sagir.
Mu’azzam idanunsa sukai jazir yana karanta sak’on. Lokaci guda Assad ke fad’in “Let’s see idan zamu iya tracking lambar da aka aika ma sak’on..!”
Bai Kai aya ba Mu’azzam da gumi ke tsartsafo masa yace ya basa wayar. Babu musu Assad ya mik’a masa duk suka zuba masa idanu.
K’ura ma lambar da aka turama sak’on ido yai yana duban digits d’in yana karantsrsu one by one.. He’s familiar with number, for sure yasan wannan lambar... D’aukan lambar yai cikin wayarsa ya soma dialing yana jin bugun zuciyarsa na ninkuwa.
Sunan da ya fito masa b’oro b’oro saman screen d’insa shine ya sanyasa tsayawa Cak yana duban fuskar wayar tasa, lokaci guda yana jin duniyar na juya masa.
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*31*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ji yai k’afafunsa suna barazanar kasa d’aukarsa, lokaci guda zuciyarsa na barazanar tarwatsewa.
Assad Yusuf harma da Maleeka mik’ewa sukai suna dubansa cikin tsananin kad’uwa da tashin hankali. Zasu iya cewa yanayin da suka gansa ciki basu tab’a ganinsa cikin irin yanayin a baya ba.
Assad ya matso yana jijjiga Mu’azzam wanda ya koma tamkar mutum mutumi “Mu’azzam.. Mu’azzam lafiya.. What’s wrong Mu’azzam..?!”
Mu’azzam bai iya amsa Sa ba sai zuba masa rinannun idanunsa da yai yana dubansa har lokacin takara bashi a duniyar haka yake jinsa.
Wayar hannunsa Assad ya amsa nan yaga sunan Safeenah ya bayyana saman wayar. Yusuf da Maleeka suka dubi juna bayan sunga sunan da fuskar wayar Mu’azzam ya nuna.
Lokaci guda Yusuf yai alamawa Maleeka da idanu cewa su fice. Babu musu Maleeka tabi umarnin Yusuf suka fice daga d’akin.
Gijif haka Mu’azzam ya zauna saman kujera idanunsa na k’ok’arin kawo ruwa . Cikin wane irin murya mai gauraye da tashin hankali had’ida rud’ani yake furta “It’s Safeenah’s phone number Assad..! That text message...was sent to her.!”
Ya d’ago yana duban Assad wanda tsananin shock shima ya nuna a fuskarsa, lokaci guda Mu’azzam yaci gaba da fad’in “But Assad how’s this possible..? I mean.. Safeenah is my blood.. And Ikram... Ikram was like a sister to her...!” Ya mik’e yana girgiza kai yana duban Assad d’in yake damk’e wayar Sagir cikin hannunsa, lokaci guda yake jijjiga wayar yana fad’in “Assad lambar matata.. Matata Assad, sak’on ma ita aka tura.. She couldn’t have killed my sister right..?!” Yanda yake maganar zaka fahimci yana cikin tsananin rud’ani ne da tashin hankali.
Kamo kafad’unsa Assad yai ya zaunarsa saman kujera yana k’ok’arin calming nasa “Please try to calm down Mu’azzam.”
D’ago idanu yai yana duban Assad d’in wanda gaba d’aya shima ya zama lost and confused.
Kauda Kai gefe kad’an Mu’azzam yai yana tinanin abubuwan da suka faru tun bayan rasa Ikram, lokaci guda yana dunk’ule hannayesa yana murzasu.
Assad ya d’an shafi kansa kad’an yana duban Mu’azzam d’in cikeda tausayawa. Fuzar da fuci yai kafin ya isa jikin window cikin rashin sanin abinda zai fad’iwa abokin nasa.. Tabbas Mu’azzam yana cikin yanayi mai matuk’ar wahala. Ace kana bincike kwatsam sai ka samu Matarka itace prime suspect na binciken da kake.. Kuma k’anwarka ce aka kashe sannan matarka ‘yaruwarka ta zamto Prime suspect.. Tabbas al’amarin akwai matuk’ar tashin hankali.
K’ok’arin saita kanta Assad yai kafin ya nufo Mu’azzam d’in wanda har lokaci ke zaune ya k’ura ma waje guda rinannun idanunsa.
Lokaci guda Mu’azzam d’in ke furta “All this while.. The killer’s right in front of me. Makashiyar tana nan a gabana.. Ina can inata neman makashin ba tareda sanin tana nan tare dani ba.. Claiming to be my wife.. wacce tafi kowa kusanci a gareni bayan mahaifiyata..”
Ya d’ago idonsa wanda siririn hawaye ke gangarowa daga ciki yana duban Assad. Lokaci guda yaci gaba da furta “She killed my sister Assad, and then she acts innocent.. Like she was also grieving for Ikram’s death.. She made me look like a complete idiot. Ina can inata bincike kaman wani wawa.. Tanata toshe duk wani hanyar da zanbi na samu gaskiya.. Assad she insulted my profession, you know.!”
Saurin dafasa Assad yai yana fad’in “Try to calm down first.. please Mu’azzam..”
Mik’ewa Mu’azzam yai yana fad’in “You’re not the one who’s being fooled by the woman you call her wife..! You are not the one who lost a sister in the most painful way.. So don’t.. even.. ask me to Calm down..!” Yai maganar jijiyar goshinsa na kuma fitowa sosai gumi na kuma tsartsafo masa.
Kafin Assad yace wani abu Mu’azzam ya nufi k’ofa. Assad yai saurin take masa baya yana ambaton sunansa amma inaa ko sauraronsa baiba.
Karo suka kusan yi da Chief Jaja wanda ya nufo Office d’in.
Mu’azzam ya tsaya Cak yana duban Chief da idanunsa da suka gama kad’uwa.
Chief yana murmushi yake shafa hab’arsa lokaci guda yana duban Mu’azzam d’in “Inspector Gamji, I hope you learned your lesson.. You should know there’s no right way to do wrong things.. Next time sai a kiyaye..!” Ya k’arashe yana bubbuga kafad’an Mu’azzam d’in guda.
Maleeka dake tsaye gefe itada Yusuf sai aika ma Chief mugun kallo take musamman da taga yanayin Mu’azzam d’in.
Mu’azzam baice da Chief komai ba har ya gama maganganunsa sai dubansa da rinannun idanunsa da yake.
Lokaci guda Chief ya gyara tsayuwarsa had’ida gyaran murya “Any update regarding your case, Inspector Gamji..?” Ya tambaya yana tsare Mu’azzam d’in da idanu wanda ko motsi mai kyau ya kasa Sai dad’a damk’e wayar Sagir dake cikin hannunsa yake.
Chief ya gyara tsayuwarsa yana karantar Mu’azzam d’in.. Lokaci guda Maleeka da Yusuf suka k’araso yayinda Assad ma gaba d’aya za’a iya cewa ya shiga missed call. Yama rasa mai zai yi sai duban Chief yake yana kuma duban Mu’azzam.
Chief ya dubi Assad ya kuma duban sauran team members d’in Wato Yusuf da Maleeka. Nan yaga gaba d’ayansu kaman an cire masu laka.
“Detectives..!” Chief ya fad’i yana dubansu d’aya bayan d’aya kafin ya tsaida idanunsa kan Assad.
“Shattima.!” Ya kira surname d’in Assad.
Assad ya sara masa “Sir.!”
Chief yaci gaba da fad’in “Any progress..?”
Duban Mu’azzam Assad yai cikin rasa mai zai fad’i.
Yanzu kam ran Chief ya soma kad’uwa wajen b’aci. Cikin tsananin zafin nama yake furta “Why are you all mute.?”
Ya girgiza kai yana ci gaba da furta “It seems we assigned this case to bunch of incompetent Detectives.. Am I right.?” Ya k’arashe cikin daka tsawa. Yayinda suka duk’ar da kawunansu k’asa idan ka cire Mu’azzam wanda har lokacin duban Chief yake bai daina murza hannunsa ba.
“Give me updates now. Detectives.!” Ya k’arashe cikin tsananin daka tsawa.
Zuciyar Chief fari k’al ganin basu ce komai ba, yanzu ya tabbata dole a gaji ai closing case d’in kaman dai yanda suka tsara. Ya wani gyara tsayuwa yasha mur sosai kafin ya soma jinjina kai cikin tsananin b’acin rai yana duban Mu’azzam d’in “I am going to warn you for that last time Inspector Gamji..! Bring all your team together to collaborate more effectively on this case.. Unless kana so ai maka retire before your retirement period.!”
Lokaci guda Mu’azzam ya d’ago wayar daketa faman dunk’ulewa cikin hannunsa yana nunawa saitin fuskar Chief.
“Meye wannan..?” Chief ya tambaya.
“It’s Sagir’s cell phone.. Sir.!” Mu’azzam ya basa amsa kai tsaye.
Dukda cewa zuciyar Chief ya yanke, ya kuma razana da ganin wayar Sagir d’in amma Sai ya wayance yace “Good.. At last something good came out of your investigation.! Good Inspector Gamji.. You’re one of our best agents. Nasan bazaka bamu kunya ba.. Let’s see what you found inside..” Ya k’arashe yana mai kad’a kafin ya nufi office yana fad’in su biyosa.. Babu musu suka bi bayan Chief.
Zuciyar Chief sai yankewa take. Ya kula Mu’azzam bazai tab’a dakatawa ba har Sai ya tono komai. Ya tsani Mu’azzam.. Sannan zai komai in his power ya tabbata Mu’azzam ya bar aikin D’ansanda for good.
**
Su Safeenah suna komawa guda suka tadda Daddy zaune harabar gidan saman kujeru na shak’atawa. Sai kallon kallo suke ma juna ganin Daddy ras kaman ba shine Aunty Shemau ta kira ta sanar dasu Baida lafiya sosai ba. Dan har kaman kuka sukaji tanayi cikin wayar.
Gaba d’aya suka fito suka nufi mahaifinsu wanda Mommy ke zaune gefensa ta cika tayi fam sai girgiza take.
A guje Meema da Kiki suka k’arasa suka rungumesa “Daddy wai bakada lafiya..? Daddy munji tsoro sosai.?”
Murmushi ya sakar masu ya shafi fuskokinsu kafin yace “I’m fine now.. Ku kwantar da hankalinku Kunji koh...”
Kiki ta kuma rungumarsa tana fad’in “Daddy banso mu rasaka.. I can’t even bear the thought of it..”
Ya shafi kanta kad’an yana murmushi kafin yace “Ku shige ciki zamuyi magana da Addarku..”
Babu musu suka shige dan Mommy kam basu ma ga fuskar mata magana ba tsaban tafarfasa da take.
Safeenah dake tsaye daga baya tana hawaye suna shigewa ta k’araso ta zube kanta saman cinyar Daddy dake zaune kan kujera. Kuka take sosai tana fad’in “Daddy it is true..! Daddy Mu’azzam mace yakai cikin gidana.. Daddy zan mutu.. Mutuwa zanyi Daddy.. I can’t take this anymore..!”
Bai hanata kukan har saida tai mai isanta kafin ya dubi Mommy yace “Can I have a moment with my daughter, Please.”
Mommy Ta dubesa da mamaki kafin Ta soma magana cikin huci “Wllhi wllhi kaji na rantse maka da Allah sai na maka Mu’azzam a kotu.. Ko ka shawo kan Safeenah ka danneta wllhi sai nayi k’aran Mu’azzam kan abinda yayima Safeenah. Har ofishin nasu zan tafi na kai masa sammaci wllhi.. Babu ruwana da cewa shi D’ansanda ne.. Idan shi bakin bindiga ne k’arewar tsaro wllhi Sai na maka k’ararsa ehe..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye.
Daddy ya d’ago yana dubanta “Kin gama.?”
Bata basa amsa ba sai ci gaba da jijjiga da take.
“Idan kin gama leave us alone with my Daughter.. Please..”
Mugun kallo ta watsa masu daga shi har Safeenar kafin Ta wuce fuu kaman zata tashi sama.
Aunty Shemau dake tsaye saman Balcony d’in Mommy akan idonta komai ya faru. Tana ganin Mommy ta nufo cikin gidan ta nufo k’asa itama.
Daddy ya d’ago Safeenah ya zaunarta saman kujerar gefensa yanda Mommy ta tashi. Har lokacin Safeenah bata daina jan zuciya ba alamun taci kuka.
Daddy yai gyaran murya a hankali kafin ya soma fad’in “I know you’re hurt.. And you’ve the right be angry.. Dole kiji zafi dan jin zafi.. Amma abinda nake so ki sani shine tashin hankali bai tab’a kawo solution wa matsala ba, saidai ma ya k’ara b’ata komai.”
Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Safeenah my Daughter, don’t allow your anger to consume you.. Kiyi hak’uri mubi komai a sannu.. Give your husband a chance to explain himself.. Bamusan dalilinsa na yin auren ba.. And yace zaiyi bayani, I’m sure Mu’azzam yanada bayanin da zaiyi.. You and I both know Mu’azzam is a good person.. He might have his faults as a human being, but he’s not a bad person.. Ba ina fad’in haka dan nafi sonsa ne ko nafi sonki ba.. No, I’m not taking sides here.. I love you both.. Kai gaba d’ayanku yarana ina k’aunarku kuma bazanso naga abinda zai cutar da d’ayanku ba.. Kiyi hak’uri Safeenah.. Da zafi na sani. Amma ki daure ki saurari mijinki kiji dalilinsa.. Allah ya miki albarka tashi ki shige..”
Da tsananin mamaki Safeenah ke duban Daddy, lokaci guda take girgiza kai still hawaye na zubo mata.
“Seriously Daddy.. This is all you can say..?!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka kafin taci gaba da fad’in “I can’t believe you are asking me to give him a chance to explain.. “ Ta girgiza kai kafin taci gaba da fad’in “Daddy what explanation kuma. Bayan abinda na gani da idanuna Daddy you still ask me to wait for his explanation..?”
Taci gaba da hawaye tana girgiza kai “Daddy Mu’azzam fooled me.. He fooled us all. All this while wata ya aje gidana shiyasa yak’i amincewa na tare.. And yet you’re asking me to give him a chance to explain how he cheated on me with that prostitute he called wife..!”
“Safeenahhh!!” Daddy ya daka mata tsawa yana mai d’auketa da mari mai ji da lafiya wanda ya haifar mata da gani giftawan walk’ila harda taurari.
Ta d’ago a gigice tana duban Daddy dake tsaye kanta rik’eda k’uncinta.
Yaci gaba da nunata da yatsa “Ban haifi ‘yarda zatafi k’arfina ba. Idanma mahaifiyarki ce mai zugaki.. kije.. Go ahead, ku shigar da Mu’azzam Kotu.. Ni kuma na rantse sai na tsaya masa tinda duk kayan jeren naki da kud’ina aka saya.. Shashasha kawai maras hankali..! Get out of my sight now..! B’ace min da gani.. Stupid kawai..!”
Da d’ingishi Safeenah ta wuce rik’eda k’uncinta ko takan crutches d’inta batabi ba.. Tana tafe tana kuka tana k’wallawa Mommy kira.
**
Mota guda suka d’auka ta ‘yan sanda irin yanda ake idan za’ayi arresting mai laifi, bayan Maleeka harda wata ‘yar sanda mace mai sanye da uniform d’in police.
Lokaci guda Mu’azzam ya nufi nasa motar yana jin zuciyarsa na masa wane irin k’una.
Assad ya biyosa dan bazai barsa yai driving a yanayin da yake ciki ba.
Wayar Mu’azzam d’in ne Ta soma ringing, nan ya duba yaga Mommy ce mai kira.
Ya d’aga without saying a word.
Daga d’aya b’angaren Mommy ke fad’i cikin tsananin huci “Ka gama gudunka Mu’azzam wllhi wllhi kaji na rantse maka sai ka biya abinda ka aikata ma Safeenah.. Bazan dubi zumunci ba Mu’azzam ba kuma zan dubi alak’a Ta jini dake tsakaninku da Safeenah ba balle na duba matsayinka na kasancewa miji a wajenta.. Sai na maka ka a kotu saidai duk abinda za’a fad’I a fad’I.. Ka riga da ka ruguza ahalin da Kakarku tai k’ok’arin ginawa tsawon shekaru. Wllhi you will pay dearly for what you did to my daughter.. I don’t give a damn about your police uniform..!” Tana ida fad’in haka ta katse kiran ba tareda ta tsaya ta saurara daga nasa b’angaren ba.
Tana katse kiran ya cire wayar daga kunnensa yana jinjina kai idanunsa na duban waje guda. A hankali yake furta “You’re right Mommy.. Ahalin ya tarwatse.! Kuma zamu tafi Kotu kaman dai yanda kikace.!”
Suna shigewa Maleeka Ta silale Ta ciro wayarta Ta soma dialing layin Barr Amir.
Bugu d’aya a na biyu Amir ya d’aga kaman wanda yake jira.
Cikin sauri Maleeka ta soma fad’in “I’ve always known matar Mu’azzam tanada saka hannu a mutuwar k’anwarsa, tarayyar da nakeda Chief Jaja ba’a banza ba, Domin na mallaki Mu’azzam zanyi komai ni Maleeka. zance na ya tabbata gaskiya... Yanzu zaka yarda da batuna Barr.”
Barr Ameer ya mik’e kad’an daga kishingid’en da yake “Tell me, mai kika samo mana daga wajen saurayin naki..? Ina nufin Chief Jaja.!”
Ta d’an murmusa kafin tace “Ka shirya za’a tafi ayi arresting Safeenah Gamji. If you want to defend her in court, this is the perfect time for you to make a move..After all, I’ve done my part da na kiraka na sanar dakai. The NPF are on there way to arrest her so Sai ka zama cikin shiri idan har baka so Safeenah ta kufce maka.. I want her out of Mu’azzam’s life completely, ka fahimta.. Idan ta nawa ne bank’i ta tafi jail ba ta k’arashi rayuwarta a can.. Amma idan kana sonta dama ya sameka, sai ka tsaya mata ka kareta a Kotu dan na tabbata bayan abinda Mu’azzam yai discovering yau d’in bazai ci gaba da zama da ita matsayin mata ba.” Tana ida fad’in haka ta katse kiran tai saurin k’arasawa ta shige motar ‘yansandan.
Barr Ameer yai wata k’asaitacciyar murmushi yana furta “Now it’s your time to shine Ameer..! Good Job Officer Maleeka.. I knew it from the very start. You and I would make a perfect team, nasan zaki min amfani.. Good job Officer.”
Ya wani murmusa yana karkad’a k’afa guda kafin yaci gaba da fad’in “Yanzu za’a fara buga wasan tsakanin Lawyer da kuma Inspector.. I told you Safeenah, you are mine.. Ni Ameer ni ne mijinki nan gidan duniya.. Now it is time for me to play a perfect Attorney role..!” Yana ida fad’in haka ya bushe da muguwar dariya kafin ya mik’e yana sab’a suit d’insa.
**
Daddy na nan zaune waje aka soma bud’e gate, motar ‘yansanda da ya hango na danno kai cikin gidansa shi ya bala’in d’aga masa hankali. Badai Safeenah taje ta aiwatar da wani mugun abin ga matar Mu’azzam ba. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum Daddy ke iya nanatawa cikin zuciyarsa. Bai ida tinanin ba ya hango Motar Mu’azzam biyeda na ‘yansandan.
Daddy ya mik’e yana tambayar kansa meke faruwa.
‘Yansandan suna ida parking Mu’azzam ma yai parking a gefe. Saidai basuyi yunk’urin aiwatar da komai ba dan umarnin Mu’azzam d’in suke jira.
Mu’azzam yana fitowa daga mota ya hangi Daddy tsaye yana dubansa cikin rashin gane meke faruwa.
Take Mu’azzam yaji zuciyarsa ya masa wane irin rauni. Idanunsa suka soma k’ok’arin kawo ruwa. Ji yai k’afafunsa na barazanar gaza d’aukarsa.. Dik k’arfin hali irin nasa saida yaji zuciyarsa Ta gaza juran abinda ke faruwa. He looks shattered.
A hankali yake takowa yanda Daddy ke tsaye. Yana k’arasowa ya kifa kansa ba tareda ya iya ci gaba da duban Daddy ba. Shi kansa Daddy ya Sani ba k’aramin abu bane zai jefa Mu’azzam cikin irin yanayin da ya gansa ciki.
A hankali Daddy ya soma furta “Mu’azzam. Son, are you alright..? What’s the matter.. Talk to me Mu’azzam, meke faruwa..?!”
Daga nan yanda yake tsaye kansa na kife sai sautin fitar kukansa Daddy yaji jikinsa na vibrating kaman dai wanda aka jona masa electric shock.
Saurin kamosa Daddy yai cikin tsananin kad’uwa da tashin hankali “Mu’azzam.. Son.. Talk to me.. Mai ya faru Mu’azzam.. Dan Allah ka mun magana..!”
D’agowa Mu’azzam yai yana duban Daddy sai kuma ya rungumesa yana kuka sosai, kukan dake tare cikin k’irjinsa wanda bai iya fitarwa ba.
Jikin Daddy ya gama sanyi Mu’azzam d’in na rungume cikin k’irjinsa.
Abinda kawai Daddy ya kawo shine kodai Nuratu ce ta rasu.. Kar dai Sun kuma rasa ahali.
Daddy ya kasa jurewa, kafad’un Mu’azzam ya damk’e sosai ya shiga jijjigasa kad’an “Mu’azzam tell me.. Tell me it’s not your Mom.. Talk to me Mu’azzam.. Please talk now..!”
Mu’azzam ya d’ago gajiyayyun idanunsa yana duban Daddy, tausayinsu gaba d’aya ya rufesa. Cikin rawar murya yake furta “It’s Safeenah..! I’m sorry Daddy.!”
Ya sunkuyar da kansa ba tareda ya iya ci gaba da magana ba.
Cak Daddy ya tsaya ya daina jijjiga Mu’azzam d’in.. Ya dai San yanzu Safeenah ta bar gabansa ta shige gida.. Toh mai kuma ya faru.
Ya girgiza kai cikin rashin gane ina kalaman Mu’azzam suka dosa.
“What happened to Safeenah..? I mean tana cikin gida, right.?”
Mu’azzam ya d’ago ya dubi Daddy cikeda tausayawa “Unfortunately Daddy.. We.. We are here to arrest Safeenah. Bincikenmu ya gangaro zuwa kanta Daddy..!”
Dummm!! Haka k’irjin Daddy ya buga. Mu’azzam yai saurin kama Daddy ya zaunar dashi.
Daddy yaci gaba da girgiza kai yana fad’in “Tell me mai Ta aikatawa matarka.. Ta mata wani illan koh..?”
Girgiza kai Mu’azzam yai yana duk’e gaban Daddy. Hannayen Daddyn rik’e cikin nasa yake fad’in “Bata aikata mata ba.. Amma ta aikata ma Ikram Daddy.!”
“Ikram kuma..?!” Daddy ya tambaya cikin tsananin kad’uwa.
Mu’azzam ya jinjina kai a hankali.
“But.. But.. Mai kake nufi Mu’azzam.. Ikram ta rigayemu gidan gaskiya.. A ina Safeenah zata ganta.. What.. what is all this Mu’azzam.?!”
Mu’azzam ya kuma damk’e hannayen Daddy cikin nasa kafin yace “Safeenah is now our prime suspect game da case d’in mutuwar Ikram Daddy.!”
Wannan karon cire hannayensa Daddy yai daga cikin na Mu’azzam yana girgiza kai yake duban Mu’azzam d’in “No Mu’azzam.. You must have got this wrong.. Safeenah.. Safeenah would never do something terrible irin wannan.. Mu’azzam ka mun magana yanda zan fahimceka.. Ikram da Safeenah duka yarana ne.. Bazai yuwu hakan ta kasance ba.. Safeenah nada kurakurenta a rayuwa amma bazata tab’a zama makashiya ba.. Right Mu’azzam.. She’s your wife. You should know better, bazata iya kashe Ikram ba.. Mu’azzam wannan wasa ne ba gaskiya ba.!”
Mu’azzam ya shafi fuskarsa da duka tafukan hannayensa kafin ya girgiza kai yace “Daddy I wish ba gaskiya bane nima.. But... Gaskiyan kenan..!”
Daddy yaci gaba da girgiza kai hawaye mai zafi yana gangaro masa.. Daidai lokacin da Mu’azzam ya kifa kansa k’asa.
Muryar Daddy ya sinkayo yana fad’in “Ku shiga ku tafi da ita a binciketa..
Go Mu’azzam.. Go ahead.. Jeka kayi aikinka..!”
Mu’azzam ya d’ago yana duban Daddy.. Kafin ya kuma furta wani kalma Daddy yace “Bazan hanaka ka bincike Safeenah ba.. Sannan idan har an kamata da laifi nayi maka alk’awarin zata biya abinda Ta aikata.. Go ahead now.. Ku shiga ku tafi da ita.!” Yana ida fad’in haka ya kauda kansa gefe yana k’ok’arin maida k’wallan da suka taru idanunsa.
Lokaci guda Mu’azzam ya juya ya dubi su Assad yai masa alama da kai.
Jiki a matuk’ar sanyaye Assad ya jinjina kansa kafin ya dubi su Maleeka da d’aya ‘yar sanda macen mai sanye da uniform yace su shiga su fito da Safeenah.
Maleeka ta jinjina kai kafin ta dubi sergente d’in tace suje.
Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, yau Wai Safeenah aka Zo arresting ana tuhumar Ta da zargin kisa. Wane irin tashin hankula ne suka tsinci kawunansu ciki wanda za’a iya cewa yazo masu bagatatan babu zato balle tsammani. Aunty Shemau kam Ta kasa daina mamakin abubuwan tashin hankula dake kan faruwa tun bayan zuwanta. Babu wani abin arziki da faru tinda tazo.
Mommy masu shirin maka Mu’azzam a kotu sai gashi su ake shirin makawa.
Safeenah ta ci gaba da b’oyewa bayan Mommy tana fad’in “Mommy wllhi ba gaskiya bane.. Wllhi ban kashe Ta ba.. Mommy I can’t go to jail.. Na shiga uku.. Daddy please help me.. Na rantse da Allah bansan komai ba.. Wllhi Allah I’m innocent..!”
Maleeka tayo kanta tana fad’in “Idan munje Headquarters zaki k’arasa bayananki.”
Safeenah ta rapza mata crutch akai tana fad’in “K’arya kike k’aramar Karuwa kinyi kad’an kiyi arresting d’ina.. Bak’ar munafuka Kema kina cikin Karuwan nasa..”
Sergeant Teena ta k’araso tana fad’in “Madam you’ll be charged for attacking the police officer.. Ki shige muje..”
Mommy ta shiga tsakani ta tare d’iyarta tana fad’in “K’arya ne..! Wllhi babu ubanda ya isa yai arresting ‘yata.. My daughter is not a killer.. Ku fice mana a gida ko muyi suing naku for trace passing..!”
Maleeka ta mik’o mata takarda a linke tana fad’in “Hajiya, we have the warrant of your Daughter’s arrest.”
Mommy ta fuzge takardan ta yaga tai kaca kaca dashi tana fad’in sunci ubansu dasu da warrant d’in.
Daidai lokacin Mu’azzam ya shigo, idanunsa kan Safeenah dake b’oye bayan Mommy tana kuka.
Mommy taci gaba da k’are Safeenah tana fad’in “Mu’azzam ta nan ka b’ullo dan ka guje ma laifinka.. What kind of a monster are you.. You’re not taking my daughter.. Kai ko kunya bakaji ba ka tattaro ‘yansanda ka kawo mana gida.. Haven’t you thought of our family’s reputation.. Haven’t you thought of what people might say.. Zakayi arresting matarka kuma ‘yaruwarka kana tuhumarta da kisan k’anwarka.. So kake sunan ahalinmu ya lalace ko mai.. So kake mu tafi kotu muna shari’a ana nuna mu da yatsa.”
Da rinannun idanunsa yake duban Mommy wannan karon kafin ya girgiza kai yace “Mommy, Safeenah should’ve thought about that before committing the crime..! And yes kafin nace za’a tafi Kotu kin riga kowa cewa zamu tafi Kotu muyi shari’a. Idan ban mance ba yanzu kika gama fad’a mun a waya, ashe idan mun tafi Kotu da sunan ahalin nan ba komai bane wajenki. Abinda kike so ne.. Kuma ina mai tabbatarki zamu tafi Kotu, kuma za’ayi sharia..!” Yana ida fad’in haka ya kamo hannayensa Safeenah yana zira mata handcuffs. Lokaci guda yake furta “You have the right to remain silent. Everything you say can be used against you in the court of law. Kinada damar da zaki d’aukarma kanki lauya.. Idan kuma baki dashi the Authority will assign one for you.!” Ya ida maganar sanda ya gama rufe hannayenta.
Shaye da tsananin mamaki Safeenah ke dubansa. Bakinta na tsananin rawa take girgiza kai tana furta “I.. I didn’t do it.. Na rantse da Allah ban aikata ba Mu’azzam.. You need to believe me.. How can you arrest your wife..? Mu’azzam ni ce Safeenah.. Kaga abinda ka min.. Haba my Halal, Please don’t do this.. Wllhi I’m innocent. Maiyasa zan kashe Ikram..? What could be my motive.!”
“Ki ajiye bayananki har sai munje ofishinmu.!” Ya fad’i cikin kad’uwa kafin ya dubi Maleeka yace “Take her.!”
Wane irin k’ara Safeenah ta saki wanda saida ya firgita kowa dake cikin gidan. Su Kiki da dake d’aki basusan wainar da ake toyawa ba ihun Safeenah ne ya fiddo dasu gaba d’aya.
Tashin hankali bisa tashin hankali. A fujajan Mommy tabi bayansu Safeenah tana fad’in Mu’azzam bai isa yakai mata ‘ya ofishin ‘yansanda ba. Dik abinda ake bama tai zaton Daddy na gidan ba. Ta zaci ya fice.. Ta dubi Meema hanaki tashe tace “Call your Dad right now..!” Ta kuma duban Aunty Shemau da tuni ta d’auko mata mayafi tana rufa mata. “Muje Shemau..!” Ta fad’i suna ficewa cikin sauri.
Wani irin wawan birki Mommy tai ganin Wai da sanin Daddy Mu’azzam yazo d’aukan Safeenah. Kuka Mommy Ta fashe dashi sanda Safeenah ke sanar da Daddy cewa batada laifi cikin kuka.
Daddy ya girgiza kai yace “‘Yansanda zasuyi aikinsu.. And if you are proven guilty.. Ki mance kinada mahaifi Marwan Gamji. I do not have a daughter for a criminal.!” Yana ida fad’in haka ya juya cikin gida yana matsan k’walla.
Mommy Ta bisa da kallo baki sake. Lokaci guda ta isa tana janyo Daddy “She’s your daughter.. You should believe her.. Kasan Safeenah bazata tab’a aikata abinda ake zargin Ta ba.. Wllhi our daughter is not a killer.. She can be anything.. But not a murderer.. You can’t neglect your daughter.. She needs you now.. Kai tunanin sunan ahalinmu.. Wannan zai b’ata maka sunanka da sunan ahalinmu ne.. Mu’azzam ba d’an halak bane tinda har ya shigo da ‘yansanda cikin gidan nan akai arresting Safeenah.”
Sai lokacin Daddy ya juyo ya katseta da fad’in “Ina jin kin mance cewa kafin Mu’azzam ya tsaya akan case d’in nan ni ne mutum na farko da yai failing case d’in mutuwar Ikram ma ‘Yansanda.. Kin mance cewa ni ne nan nai k’udirin za’a bincike mutuwar nata dukda cewa ga sakamon da ya bayyana cewa mutumin da ya kasheta ya riga ya kashe kansa.”
Mommy cikin kuka Ta katsesa da fad’in “Amma ai duk mun amince mutumin da ya kashe Ikram ya kashe kansa.. Mu’azzam neman wanda zai d’aura ma Alhaki kawai yake..” Ta k’arashe cikin kuka.
Daddy ya jinjina kai yace “Ki k’yale ‘Yansanda suyi aikinsu Hajara.” Daga haka Sa kai yai ya shige.
Mommy ta soma kururuwa ta nufi mota tana fad’in driver yazo ya tuk’asu itada Aunty Shemau, dole subi bayan ‘yansandan idan Daddy bazaije ba.
Meema da Kiki kaw kuka suka dingayi suna ganin Bak’on al’amaren dake faruwa cikin ahalin nasu. Wai Ya Mu’azzam yai arresting Addah Feenah kuma wai da kisan Ikram ake tuhumarta. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.
Cikin sauri Meema ta shiga neman layin Musaddiq dan Ta sanar dashi abindake faruwa dashike baya gida.
**
Mu’azzam ya k’ura mata idanu sanda aka barsu su biyu a interrogation room saiko d’an mindow mai kaman glass wanda abokan aikinsa zasu iya hangosu daga nan.
Idanunsa jazir yake duban Safeenah sanda ya nuna mata lambar wayarta da time da date da komai da komai na lokacin da aka tura mata sak’on.
Safeenah taci gaba da girgiza kai tana furta “Na rantse da Allah bansan komai ba Mu’azzam..”
Tsawa ya daka mata yana mai buga table d’in da ya raba tsakaninsu “Don’t you dare lie to my face.! You received this text message a ranan d’aurin aurenmu.. Admit it Safeenah.!” Yai maganar idanunsa tar akanta wayar Sagir rik’e cikin hannunsa yana mata nuni da sak’on.
Safeenah taci gaba da girgiza kai tana hawaye ba tareda tace komai ba.
Mu’azzam yaci gaba da furta “You were not yourself that day Idan ban mance ba. You were acting very strange.. I even asked you meke damunki, but what did you say..? Ce min kikai nervousness ne na barin gida sabida zakiyi aure.. Washe garin wannan ranan aka tsinci gawar Ikram... Haka ne..?!”
Ta kuma girgiza kai tana hawaye “Na rantse da Allah ban San komai ba..”
Wani Farin takarda Mu’azzam ya ajiye gabanta nan saman table d’in wannan karon cikin rawar murya yake magana “This is the autopsy result of Ikram’s death Safeenah..!” Muryarsa yaci gaba da rawa yana furta “Take a look Safeenah.. Ki duba autopsy result d’in.. Binciken da likita ta gudanar akan gawan Ikram.. She was raped Safeenah..!” Izuwa lokacin hawaye ne ke gangaro masa haka ma Safeenar wacce take girgiza kai tana duban takardan.
Mu’azzam yaci gaba da furta “My sister was raped and then shot.. An mata fyad’e sannan aka harbeta da bindiga.. An kasheta a wulak’ance. Wulak’ancin da ko dabba baza’a masa ba.. Idan kinada zuciya cikin k’irjinki Safeenah zaki sanar dani gaskiyan al’amarin.. Zaki sanar dani gaskiyar da kika sani..!” Ya k’arashe gumi na gangarowa daga cikin sumarsa zuwa goshinsa.
Safeenah taci gaba da girgiza kai tana hawaye “Wllhi ni bansan komai ba Mu’azzam.. Ka yarda dani.!”
Buga table d’in ya kuma da k’arfin gaske wanda saida ya storata Safeenah “Isn’t it enough that you’ve been fooling me for almost a month now.. You insulted my intelligence and my profession as a police officer.. Safeenah let’s not make this difficult anymore.. Ki sanar dani mai kika sani..”
Safeenah ta d’ago tana dubansa cikin huci wannan karon “Banfa mance abinda ka min ba Mu’azzam.. Dan Mommy tace zata maka ka a Kotu shine bari ka b’ullo ta nan.. Bazaka tsere ma laifinka ba.. Ka cuceni ka kai min mace cikin gidana.. Kana kwanciya da ita a saman gado na kai ko kunya bakaji ba.. Tell me mata nawa ka kai min gida ka kwanta dasu saman gadona.”
“Feenahh..!!” Ya daka mata tsawa yana mai d’ago hannunsa kaman zai mareta. Sai kuma ya sauk’e hannun nasa a hankali..
Safeenah taci gaba da kuka tana fad’in “Kai mugu ne Mu’azzam.. Azzalumi ne kai.. Ka cuceni Ka cuceni.!” Tai maganar tana k’ok’arin turasa tana kuka sosai tana bige bige.
Mu’azzam ya shiga k’ok’arin kame hannayenta dole Maleeka ta shigo tana taimaka masa da rik’e Safeenah dake Ta faman buge buge kaman sabuwar kamun hauka.
Ficewa yai daga interrogation d’in to get some fresh air, saida Safeenah ta daina bige bigen da take kafin ya dawo cikin tsananin tsimewa. Tai zaune saman kujeran tana sakin huci.
“Shall we continue.”ya fad’i yana dubanta.
Kauda Kai gefe tai kafin tace “Ina son magana da lawyer na. Ko shima banida dama.?”
Yai mata K’uri yana dubanta “Daddy yace lauyansa bazai tsaya miki ba. Kinada wanda kike so a kira miki in mind.”
Ta d’ago da mamaki tana dubansa jin abinda ya fad’i. Kafin Safeenah takai ga magana sukaji an turo k’ofa an shigo.
“I need to speak to my client. Mr Inspector.” Abinda ya fad’i kenan daga nan yanda yake tsaye cikin bak’ar suit d’insa.
Daga Safeenah har Mu’azzam juyawa sukai suna duban Ameer dake tsaye kansu.
Mu’azzam ya mik’e shaye da mamaki yana duban Brr Ameer dan tsaf ya ganesa tsohon saurayin Safeenah ne.
Leave a Comment