Gidan Aro 22


22*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*Su Tabawa da ayarinta tuni suka fice Tabawa tana fad’in “Ku tashi muje zama bata ganmu ba an sace ango.. Wayyo Allah kud’ad’ena. Na shiga uku ni Tabawa waye zai biya bashin nan yanzu.. Wayyo Allah na shiga ukku. Gaskiya Sadiya farar k’afa gareki.. Ace aure biyu ana fasawa kaman bakin uwa.. Koda yake dama ‘yar bakin uwar ce ke.. Matsiyata masu bak’in k’addara..!” Haka Tabawa ta dinga ihu a lungun hannu aka tana tsine masu Sadiya,  Ita damuwarta ba b’acewar Alhaji Isyaku bane bashin su Sadiya ne da zai biya shine damuwarta..


A nan cikin gidansu Sadiya kaw kuka kawai Sadiyar take tana duban Sabeera dake ci gaba da jijjigata wacce itama kukan take, cikin kuka Sadiya ke furta “Sabeera ban sani ba.. Wllhi ban San komai ba, ki yarda dani ina zan d’auki Mahaifinki na kaisa..”


Cikin kuka Sabeeran ma ke girgiza kai tana ci gaba da jijjiga Sadiyar take fad’in “No you are a liar Sadiya.. You lied to me once.. What makes you think zan yarda dake wannan karon.. You are nothing but a gold digger, I was so stupid that I couldn’t see your true color tuntuni.. I no you never loved my father.. Sabida kud’insa ne kika amince da aurensa.. Kawai kud’insa kike so shiyasa kika sa aka sace shi Dan kar ki aure shi dan ki karb’i kud’ad’e masu yawa daga wajensa.. I feel like I don’t know you Sadiya. Tinda kikayi tarayya da D’antadda irin Sagir, zakiyi da ‘yan Garkuwa ma. You planned all this Sadiya.. Just admit.. Why can’t you admit it already..!” Ta k’arashe tana mai tura Sadiyar da k’arfin gaske.. Sadiya bata fad’a ko Ina ba Sai jikin Mu’azzam da shigowarsa kenan gidan.. Hannayesa duka biyu yasa ya tallafota.


Sadiya ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban mutumin data fad’o jikinsa wanda ba kowa bane face wannan D’ansandan wanda sukai karo kwanaki kuma shine mutumin dake bincike kan mutuwar Sagir.


Su duka biyun suka k’ura ma juna idanu.. Lokaci guda taji ya rik’o hannunta yana fad’in “Let’s go, you are no longer safe here.. Let’s go now..!” Ya k’arashe yana k’ok’arin janyo hannunta da k’arfin gaske.


Sadiya da tsananin tsoro ya gama cikata Ta soma k’ok’arin k’wace hannunta tana fad’in “Wait.. Ina zamuje..? Ina zaka kaini.. Just let me go.. Ka sakar min hannu.. Ka sakeni Ina zaka kaini..!” Ta finciki hannunta da k’arfin gaske tana huci take dubansa, lokaci guda take furta “Just because you are a Corp doesn’t mean  you can arrest me without any allegation. Mr Inspector..!” 


Mu’azzam dake tsananin huci yana dubanta, lokaci guda ya kuma takowa gabanta, wani irin duba yake mata wanda za’a iya kiransa da duban tsana “You wanna know who am I to you..?” Ya kuma matsowa kusanta sosai kafin yace “Well, I’ve every right over you.. Idan nace maku ni ne mutumin da ya biya bashin da kuka ciwo ma kanku fah..!”


K’irjinta ne yai wani irin bugawa tana dubansa da idanunta wanda har yanzu hawaye ne kwance cikinsu. Lokaci guda kuma taji wani irin k’arfin zuciya na zuwa mata bayan tulin iftil’ai na rayuwa data gani.. Hawaye ne a cikin idanunta amma murmushin takaici ta sakar masa tana duban cikin idanunsa ba tareda wani tsoro ko d’ar ba tace “A  cheap low life police officer like you.. Wanda bai dogara ga komai ba face cuku cuku da karb’an cin hanci da rashawa bashida wad’annan kud’ad’en da kake mafarkin ka biyasu a matsayin bashi na ni Sadiya.. Ka fahimta..?!!” Ta k’arashe tana sakin huci.


Da mugun mamaki Mu’azzam ke dubanta idanunsa na kuma kad’uwa,wani wulak’antaccen kallo yake mata daga sama zuwa k’asa yana tuna duk maganganun da ake fad’i na rashin kamun kai gameda da Ita ya kuma tuna maganan da yanzu Ta fad’i masa cewa cheap low life police Officer mai karb’an cin hanci da rashawa irinsa bai isa ya biya bashin da ake binta ba. A hankali yake kad’a kai idanunsa na kuma yin jazir “You’ll repeat this..! Zaki maimaita wannan idan sunana Mu’azzam Abubakar Gamji.. Zaki maimaita..!”


Daidai lokacin Umma ta K’araso tana k’ok’arin janye Sadiya, Ta d’ago ido tana aika wa Muazzma mugun kallo “Kaga Bawan Allah ka fice daga gidan nan dan kana a matsayin D’ansanda babu dokar data baka damar shigowa har cikin gidanmu kace zaka ci mana mutunci Dan muna talakawa. Fita nace..!” Umma ta k’arasa tana nuna masa hanya.


Idanunsa da suka kad’a sukai jazir yanaga Sadiya yana aika mata wani irin kallo kafin ya maidoda dubansa ga Umma, sai kuma ya sadda kansa k’asa kaman wanda ya tina wani abu duban cikin idanun Umma da yai.. Lokaci guda ya juya yasa kai ya fice daga gidan.. A daidai k’ofa ya had’u dasu Malam Liman suna sallama alamun zasu shige gidan.. Bai iya furta masu komai ba sai sa kai da yai ya wuce cikin sauri.. Malam Liman ya bisa da kallo yana jin zuciyarsa na masa wani irin rauni.. Anya baiyi gangancin bada auren Sadiya ma wannan D’ansandan ba.. Take yaji yana tuhumar kansa da aikata babban laifi.. Ji yai kaman bazai iya duban Sadiya da mahaifiyarta ya fad’a masu abinda ya aikata ba.. 


Mu’azzam kaw yana ficewa daga gidan ya nufi yanda Assad ke tsaye, Uncle Salman kam tuni ya cika ma rigarsa iska.


Mu’azzam na k’arasowa wajen yaga Assad ya k’ara waya a kunne yana fad’in “Yes Yusuf, we have a situation here.. I’ll send you our location..!” Ji yai an fuzge wayar kafin yakai aya.


Ya karkato yana duban Mu’azzam, da mamaki Assad ke duban Mu’azzam “Backup nake kira Mu’azzam ya kamata musan su waye suka d’auki mutumin nan..”


Ba tareda Mu’azzam ya basa amsa ba ya shiga janyo hannunsa yana fad’in “You ain’t calling anyone.. Just come with me..!”


Assad ya dubesa da mamaki har suka isa mota Mu’azzam d’in ya bud’e ya shige yayinda Assad d’inma ya bud’e d’aya b’angaren ya shige.. Shi yanzu harga Allah tsoro Mu’azzam ke basa bayan wannan birkitaccen auren da yai yanzu yanzu..

Assad zuba masa idanu kurum yai yanda yake kwasansu saman kwalta tamkar zasu bar gari.


**


Tabarma Umma ta shimfid’a wasu Malam Liman, ko daga yanayin da tagansa ciki ta fahimci akwai matsala mai girma, saidai ta jingina hakan da Sace Alhaji Isyaku da akace anyi.


Ta zauna daga d’aya b’angaren suka gaisa, bak’ar ledar viva aje gaban Malam Liman.


Saida ya d’anyi gyaran murya kafin ya soma fad’in “Watau Uwani ita rayuwar nan da kike gani komai rubutacce ne tun kafin a samemu, Idan Ubangiji ya k’addari faruwar abu Toh fah bawa bai isa yaja da hakan ba.. Sannan inaso ki sani mutum baya tsallake matarsa, muddin matarsa ce toh ko a ina take kuma ko menene sanadi sai yaje ya cinma matarsa a duk yanda take..”


Jikin Umma yakai matuk’a wajen yin sanyi. Ta jinjina masa kai a hankali tana mai furta “Haka ne Malam.”


Malam Liman yaci gaba da fad’in “Alhamdulillah naji dad’i da kika fahimci haka Uwani.. Sannan akwai magana mai girma da nake tafe inaso na sanar daku daga ke har Sadiya. Nasan Kunji cewa an d’auke Alhaji Isyaku yau a k’ofar gidansa bayan ya fito zai halarci wajen d’aurin aurensa da Sadiya.”


Umma ta jinjina kai a hankali tana jin k’irjinta na tsananta fad’uwa.


Malam Liman ya d’an kifa kansa kad’an yana ganin girman maganan da zai fad’a masu, ya d’an muskuta kad’an yana gyara zaman rawaninsa “Toh Uwani aure dai bai yuwu da Alhaji Isyaku ba..”


Umma ta dubesa da mamaki sai ta d’an murmusa tace “Allah sarki Malam ai Babu komai haka Allah ya nufa, dama kullum cikin kai masa kokenmu muke muna rok’onsa yama zab’in abinda yafi alkhairi ya kuma dubi lamarinmu.. Na tabbata idan bai k’addari wannan aure ba k’udirarsa da Buwayarsa su suka dakatar da aukuwan wannan aure, inada tabbacin hakan shine abinda ya zab’arwa d’iyata.. Mun kuma gode da jarabawar da yake aiko mana daki daki.. Fatana Allah ya nufa muci wad’annan jarabawa.. Malam kar ka damu nasan kayi iyaka k’ok’arinka wajen ganin an sauk’e mana wannan nauyi na bashi dake bisa kanmu, Ubangiji ya saka maka da alkhairi duniya da lahira.. Idan Allah ya nufa zai turo mana wani hanyar da zamu samu mu biya wannan bashi dake kanmu..”


Malam Liman ya d’an share k’wallan da ya zubo masa, lokaci guda yake furta “Sadiya d’iya ce a wajena Uwani, ki daina min godiya ni babu abinda nayi mata.. Sannan idan babu damuwa inaso ta fito itama domin abinda zan fad’a maku yanzu ya shafi rayuwarta kacaukam. Sannan zai iya canza rayuwarta gaba d’aya..”


Wannan karon bugun zuciyar Umma ya k’aru. Ta dubi Habeeb dake zaune daga can gefe yana ‘yan wasansa abinka da yaro tace “Habeeb shiga ka kira Addarku..”


Habeeb ya jinjina kai kafin ya mik’e ya shige ciki kiran Sadiya.


Jiki a matuk’ar sanyaye Sadiya Ta fito, ga zuciyarta data tsananta yankewa tinda Habeeb yace su Malam Liman da Umma ke kiranta.


Sadiya ta fito sanye da hijabinta ta duk’a daga can gefe kusan Umma ta gaida Malam Liman.

Malam Liman ya amsa zuciyarsa cikeda tausayin yarinyar, bazai gushe ba yana mata add’uan samun Farin ciki mai d’orewa cikin gidan aurenta. Yana fata wannan aure nata da ya had’a da Mu’azzam ya zamto alkhairi gareta da mahaifiyarta harma da ‘yanuwanta.


Malam Liman ya dubeta yana jin rauni sosai had’ida tuhumar kansa “Halimatu.!” Ya ambato asalin sunanta wanda babu mai kiranta da wannan sunan sai mahaifinta.


“Na’am.. Baba..!” Taji bajinta na furta haka ba tareda tasan dalili ba, saidai tafi danganta hakan da cewa ya kira sunanta ne da sigan da mahaifinta ke kiranta shiyasa ta kirasa da Baba itama.


Malam Liman yaji dad’in ambatonsa da Baba da tai, a hankali ya soma furta “Inaso ki sani, da ace inada halin da zan sauk’e wannan bashi da basai kin kaiga sadaukar da Farin cikin ki ba kin auri wanda baki so.. Halimatu kin d’aukeni a matsayin mahaifi..?”


Sadiya ta dubesa sai kuma ta dubi mahaifiyarta, a hankali ta jinjina masa kai.. Malam Liman ya share hawayen da suka gangaro masa “Bansan ya zaku d’auki al’amarin ba.. Amma inaso ku Sani ina mai neman yafiyarku.. Musamman ke Sadiya.. Ki yafe mun kan had’a aurenki da nayi ba tareda saninki ba bayan kin d’auki matsayi mai girma kin bani.. Ki yafe ni d’iyata banyi haka dan wulak’anci ko cin zarafi ba saidai nayi haka ne gudun kar dama na k’arshe ya kufce mana.. Sannan inaso ku Sani ni d’an adam ne ajizi wanda yake kuskure.. Kar ku dubeni a matsayin malami ko limami.. Ku dubeni a matsayin D’anadam kuma Bawan Allah mai kuskure..”


Izuwa lokacin hawayen Sadiya ya k’aru.. Girgiza Kai take tana fad’in “Baba Liman dik abinda ka yanke akaina zanyi na’am dashi kuma zaka sameni Ina mai maka biyayya kaman yanda zanyiwa mahaifina.. Zanji dad’i matuk’a ace na samu damar yi maka biyayya irin wacce banyiwa mahaifina ba a lokacin da yake raye.. Hak’ik’a zanji dad’in hakan.. Duk hukuncin da ka yanke kayi daidai nasan bazakayi abinda zai cutar dani ba..”


Malam Liman da abokin tafiyarsa suka share hawayen da ya gangaro masu, da k’yar Malam Liman ya saita kansa kafin yace “Halimatu a yau sanda mukayi zaton Alhaji Isyaku ya janye aurenki ne gudun kar ya biya bashi na bada aurenki ga wani..”


Umma da Sadiya suka dubi juna cikin tsananin sanyin jiki..


Malam Liman ya mik’a wa Umma dubu d’ari sadakin Sadiya dasu Mu’azzam suka biya “Wannan shine kud’in auren Sadiya..” 


Sadiya Ta kuma duban Umma cikeda kad’uwa. Cikin rawar murya Umma tace “Malam ko zamu iya sanin wanene mijin nata.?”


Malam Liman ya d’an gyara zamana kafin yace “Mu’azzam Abubakar Gamji. Shine sunan mijinki Halimatu.”


“Mu’azzam Abubakar Gamji.!” Sadiya ta nanata a hankali zuciyarta naci gaba da tsinkewa.. Take ta tina tattaunawarsu da Mu’azzam da ko minti talatin baiba kalamansa na k’arshe take tunawa _Idan Sunana Mu’azzam Abubakar Gamji ne zaki maimaita abinda kika fad’i_


A hankali Ta furta “The Corp!”

Sai kuma ta mik’e tana jin wani irin kuka na zuwa mata.. Babu shiri ta shige d’aki a guje tana mai k’unshe bakinta da kuka gadan gadan ke shirin fitowa.


Umma ta dubi su Malam Liman tace “Malam kuyi hak’uri zan shiga na kula da Sadiya.”


Malam yace “Babu komai.. Ga kud’in Tabawa nan sun biya idan yaso sai a had’u tareda ku da shaidu a biya Tabawa kud’inta.. Babu sauran maganan bashi..”


Jinjina masa kai kurum Umma tai kafin sukai sallama ta shige wajen d’iyarta da sumewa ne kawai batayi ba sabida firgici.Malam Liman suna ficewa ya dubi abokin tafiyarsa suka tafe hannu.


Abokin Tafiyarsa yace “Kai Malam Wato dai harta ku malamai kuna d’an tab’a wuru wuru..”


Malam Liman yace “Kai Munkaila rayuwar nan tayi wuya fah, ai muma Malamai sai mun d’an had’a da cida addini bacin haka bazamu kai labari ba. Kai badon zan sami nawa kason ciki ba maizaisa na dage nayita wa’azi ina rok’on a biya masu bashin da suka ciwo, bashinma da ashararancinsu na buki kawai sukai dashi.. Ai tsuntsun da ya jawo ruwa shi ruwa yake bugu Munkaila, ni ko tausayi basu bani ba kuma nima kasuwancina nai dasu..Yanzu kaga kud’ad’en nan Tabawa tamin alk’awari akwai Kaso na ciki shiyasa dole na aurar da yarinyar nan ma koma wanene.. Yo zanyima d’iyata irin wannan auren ne..? Mutane suzo bagatatan babu bincike babu komai a d’auki d’an mutum sukutum a basu.. Kai ina ka tab’a jin anyi irin wannan aure idan ba don zan sami kaso na ciki ba.”


Suka kuma k’yak’yata dariya a tare Munkaila  na fad’in “Nima kuma zan sami nawa ba..” 


Malam Liman yace “Bani son zari Munkaila ka jira na dafe nawa tukuna..”


Munkaila yana murmushi yake jinjina kai kafin suka wuce.

**


Wani uncompleted building sukazo, Assad sai dubansa yake cikeda tsananin mamaki dan shi har wannan lokacin ya gaza yarda da abinda abokin nasa ya aikata.


“What are we doing here..?” Assad ya fad’i yana duban Mu’azzam d’in.


Mu’azzam bai kaiga basa amsa ba saiga su Yusuf team mate d’insu da kuma wani abokin aikinsu a CID mai suna Jabir sun fito daga building d’in.


A tare Yusuf da Jabir suka k’araso suna sara ma Mu’azzam da Assad..


Baki sake Assad ke dubansu, ya kuma dubi Mu’azzam kafin ya sake duban Yusuf yace “Wai ba yanzu na kiraka nake sanar dakai abinda ke faruwa ba..”


Murmusawa kurum Yusuf yai yana mai mik’a masu hannu alamun musabaha. Jabir ma ya k’araso suna gaisawa.


Mu’azzam ya dubi Yusuf da hannunsa ke d’aure alamun an kuskuresa da bindiga yace “Wait.. What really happened.. Why are you wounded..?” Yai tambayar cikeda kulawa yana duban Jabir d’in.


Jabir ya d’an murmusa yana duba hannun nasa dake d’aure da bandage yace “This.? It’s nothing Sir, just a scratch.”


Mu’azzam ya girgiza kai yana duban Yusuf da Jabir d’in.. Lokaci guda ya kuma duban Yusuf yace “What really happened Yusuf..?”


Yusuf ya soma basa labarin abinda ya faru “Bayan ka turamu Mu d’auke Alhaji Isyaku, koda muka isa k’ofar gidansa munga wasu mutane Sun shiga motarsa.. Muka bi bayansu Toh Sai suka tsere mana, a nan ne abductors d’in suka kuskuri Jabir da Bindiga..”


Da tsananin mamaki Mu’azzam ke dubansu kafin yace “Kuna nufin wasu sun rigamu, wasu suna targeting Alhaji Iskyaku.?”


Yusuf ya jinjina kai yace “K’warai kuwa wasu sun rigamu.. And I’m suspecting zasu iya zama yaran Danger..”


Mu’azzam yace “Kun kub’utar da Alhaji Isyakun..?” 


Suka jinjina masa kai a tare Jabir na fad’in “Yana cikin building d’in nan, saidai bamu fara interrogating nasa ba muna jiran isowarka.”


Mu’azzam ya jinjina masu kai kafin yace “Muje ciki..”


Saurin rik’osa Assad yai, ya dubi su Yusuf yace “Officers ku k’arasa ciki muna zuwa..”


Suka jinjina kai kafin suka shige ciki.


Aka bar Assad da Mu’azzam tsaye a wajen..


Huci kurum Assad yake yana duban Mu’azzam wanda shima fuskar tasa tamau take.


Assad ya fuzar da fuci kafin ya d’ago yana duban Mu’azzam cikin tsananin b’acin rai “What the hell have you done Mu’azzam.. What has gotten into you.. Bayan auren yarinyar can  da kai ashe kai ka d’auke Alhaji Isyaku.. Maiyasa na kasa gano hakan ma..? Mu’azzam anya lafiya kake.. Maiyasa zaka auri yarinyar nan idan ba sonta kake ba.. Kafi kowa sanin cewa marriage is a serious commitment.”


Katsesa Mu’azzam yai cikin tsananin b’acin rai “You know perfectly well that I didn’t marry that girl  because I wanted to be with her.. Abu d’aya ne yasa na aureta because she’s the key to finding my real sister’s murderer.!”


Cikin b’acin rai Assad ya katsesa da fad’in “Kan wannan dalilin ne zakai making huge decision na aurenta..”


“Yes Assad..!!! If that’s what it takes me to do.. Then I’d marry her just to find my real sister’s murderer.. Ka fahimta..!” Ya k’arashe idanunsa na firfitowa waje tsananin b’acin rai.


Assad ya fuzar da huci yace “Don’t you think you’re ruining the girl’s life aurenta da kai ba tareda kana sonta ba Sai dan ka cimma burinka na binciken da kake..”


“Her damn life has already been ruined tin lokacin da ta zab’i kasancewa da wannan d’aniskan criminal d’in..! And just to remind you, dama ‘yar tasha ce rayuwarta lalatacce ne tuntuni..!”


Assad ya shafi kansa yana mai fuzar da huci kafin yace “Toh shi kuma Alhaji Isyaku daka d’aukosa ka ajiye sa nan fah..? Ta yaya zaka aikata abu makamancin wannan Mu’azzam, karfa ka mance you’re still on your suspension, sanin kanka ne mutumin nan can file a case against you d’aukosa da kai ka ajiyesa a nan, sannan baka tinanin Yusuf da Jabir zaka iya jefasu cikin matsala.. And.. waima da ka aje mutumin nan mai zai maka.. kanaji sunce anyi abducting d’insa sukai bata kashi da ‘yanta’addan suka k’wacesa.. Idan na fahimta Alhaji Isyaku baida masaniya akan abinda ke faruwa he’s only caught in the middle of all this a matsayinsa na wanda zai auri yarinyar.. Ya kamata ka saki mutumin nan ya tafi Mu’azzam kafin ka janyo ma kanka wani matsalar bayan wanda kake ciki.”


Mu’azzam dake dubansa da rinannun idanunsa yace “I thought I told you, idan banzanyi k’ark’ashin umarnin NPF ba I’d do it my way.. And this is my way of doing things Assad.. Kafi kowa sanin hakan.!”


Assad ya d’an shafi kansa kafin ya d’ago cikin tsananin b’abin rai yace “Baka tinanin mutumin nan Danger ke targeting d’insa.. He’s innocent Mu’azzam you can’t keep him here.. You’ll be charged with kidnapping..”


Assad Bai Kai aya ba Mu’azzam dake tsananin huci ya katse sa da fad’in “Assad, If I keep doubting everybody then my real sister’s killer  will never be found.!”


“Then what..! So is it okay to abduct an innocent person if it means finding the killer..?” Assad yace cikin tsananin b’acin rai.

Ya d’an sassauta murya yana duban Mu’azzam d’in “I know how frustrated you can be to wait for justice to come through.. We can’t take laws to our hands Mu’azzam.. You’re a police officer, you should know better..!”


Da tsananin mamaki wannan karon Mu’azzam ke dubansa, ya bigi bonnet d’in Mota kafin yace “What the hell has happened to you.? Because you used to be so determined on solving this case.. Tell me Assad.. Are you backing off now..?!” Ya k’arashe cikin tsananin zafin zuciya gumi na karyowa daga sumarsa zuwa goshinsa.


Girgiza kai kurum Assad yai dan ya gama yarda Mu’azzam yayi nisa.. Zai dik abinda zai domin ya gano waye ya kashe masa ‘yaruwa.


A hankali Assad ke furta “Just don’t do anything that you’ll later regret Mu’azzam.. Please..! Let’s do everything the right way.. Hanyar da doka ta aminta dashi..”


Da gefen idanu Mu’azzam ke dubansa kafin yace “I’ll interrogate that man.. Zaka shigo ne ko zaka tafi..?”


Assad ya girgiza kai kad’an yana mai fuzar da huci kafin yabi bayan Mu’azzam d’in, suka shige cikin ginin yanda Alhaji Iskyaku ke zaune saman kujera Jabir da Yusuf na tsartsaye b’angarorinsa guda biyu..Mu’azzam na shigowa ya janyo kujera da k’afarsa ya saita Ta gaban Alhaji Isyaku kafin ya zauna suna duban juna.


No comments

Powered by Blogger.