Gidan Aro 2


 *02*

Tagumi Ta rapka tana duban yaran yanda suke kukan basu k’oshi ba.

“Oh ni Uwani naga takaina, yanzu ta Ina zan samo kud’ad’en nan..”


“Umma bamu k’oshi ba..” K’aramin yaron ya fad’i yana mutsuke ragowar hawayen dake idanunsa..


Janyo yaran tayi jikinta tana lallashi tana fad’in suyi hak’uri yanzu zata girka masu ragowar waken data tsince.. 


“Umma nidai ba zanci wake ba, ni abinci mai dad’i da Aunty Sadiya take kawo mana zanci.. Kuma ai Umma kince idan tayi aure Gidanta zamu koma dukanmu.. Kince gidan Babba ne kuma zai d’auke mu gaba d’aya.. Abba kawai zamu bari a nan gidan..” Ya k’arashe daidai sanda wani magidancin mutumi ya fito daga wata d’aki dake can gefe, goge bakinsa yake da karar aswaki ya isa ya d’auki buta ya d’ebi ruwa a famfo dake filin tsakar gidan ba tareda yaceda matar komai ba.. Ta bisa da idanu tana jira taga ko zai mata magana amma shiru baice komai ba, kodashike tasan za’a rina haka.. Bazai ce komi d’in ba dan tinda aka soma hidiman bikin baya saka kansa ciki dan Dama ba’a saka shi ba dukda duwa cewa Sadiya d’iyarsa ce ta cikinsa amma baida ta cewa a gidan sai abinda Sadiya da mahaifiyarta Uwani sukace akeyi.. Uwani irin matan nan ne masu bala’in son abin duniya wanda kwad’ayi ya rufe masu idanu basa gane daidai daga abinda yake ba daidai ba koda kuwa gaskiyar Ta bayyana masu k’arara.. 

Tun aurensa da Uwani haka nan take, da yana dashi da baidashi sai ta tursasa masa ya kawo mata, koda suka haifi yara ma Uwani bata fasa halinta na kwad’ayi da tsaban son abin duniya had’ida hangen na sama da ita ba.. D’iyarsu Ta fari itace Sadiya Sai Ashiru da Habib d’an autansu.. Sadiya kyakkyawa ce ta gani a fad’a dan tun tana k’arama ake mata lak’abi da Sady pretty a layinsu.. Tinda ta soma zama budurwa Uwani mahafiyarta da suke kira da Umma ta maida ita hanyar samun kud’inta.. Tuni Umma ta hure ma Sadiya kunne cewa ta dinga karb’o masu kud’i hannun samaruka, hakan yasa Sadiya bata raina samari hardai zata samu ta tatsesa ta rariki rabonta.. Kowa a unguwar yayi shaida ma Sady pretty da Ummarta indai akan tara samari barkatai ne da amsan abin hannunsu.. Babu yanda Malam Ibrahim mahaifin Sadiya da suke kirada Abba baiyi ba wajen ganin ya karkatar da Uwani da kuma mummunan d’abi’ar data d’aura d’iyarsu amma abu yaci tura.. Tsaf Uwani take tsefe masa ruwan bala’i tace bazata zauna tanaji tana gani d’iyarta ta k’are a auren matsiyaci ba kaman yanda ita ta k’are.. A haka har Sadiya ta sami gurbin karatu a Jami’ar babban birnin Tarayya.. Idanun Sadiya sun kuma bud’ewa yanda Ta soma gogayya da manyan ‘yanmata masu ji da kansu da kuma yaran masu hannu da shuni.. Tuni Sadiya Ta kumaji Lallai batada miji sai mai Kud’i ko d’an mai kud’i musamman ganin yanda daga shigarta samaruka sukai mata chaa sabida kyaun halitta da Allah yayi mata.. Idan tayi wanka ta shiga makaranta sai ka rantse d’iyar wani hamshak’i ne, daga nan duk wasu situru da abubuwan more rayuwa da take amfani dasu maza Ke bata su.. Daidai da registration da kud’in samari tayi.. Hoto kuwa idan zatayi posting a social media saidai ta tafi can layin bayansu gidan su wata k’awarta Sabeera a nan take hoto dashike mahaifin Sabeera yanada d’an rufin asiri dan babban d’an canji ne cikin Abuja amma gidansa na nan Suleja.. Gida mai d’an karan kyau ya cancad’a.. Kullum Sady pretty tana gidansu Sabeera dan dama tare suka sami gurbin karatu a nan Jami’ar Abuja, course d’aya suke tare suke tafiya tare suke dawowa, a motar gidansu Sabeera ake kaisu a d’auko su wasu sunyi zaton ma ‘yan gida d’aya ne wasu kuma sukanyi zaton Sady ce d’iyar mai Kud’i Sabeera ce ‘yar k’wak’warta.. Bugu da k’ari Sabeera irin ‘yanmatan nan ne da abun hannun iyayensu bai rufe masu ido ba, Sam abun duniya bai d’ad’areta ba kaman k’awarta Sady pretty.. Sady sam bata bari k’awaye suzo gidansu saidai Su had’e a gidansu Sabeera.. A haka Sabeera Ta zamto Aminiyar Sady, sau tari Sabeera takanyi nasiha ma Sady kan irin rayuwar data d’aukar ma kanta amma ko a jikinta takan ce lokacinta gwara taci duniyarta da tsinke.. Bazata bari kyaun da Allah yayi mata ya zamto a wofi ba tinda basu da kud’i zata iya amfani da kyaun da Allah ya bata ta sama masu rayuwa mai inganci itada iyayenta.. 


Duk wasu kayan more rayuwa da Sady zata kawo gidan Abba baya amfani dasu bai kuma fasa masu nasiha ba musamman ga Uwani mahaifiyar Sadiya.. Ita kam Sadiya ya mata nasihar ya mata fad’an har duka yasha mata amma babu abinda ya canza dan Tuni mahaifiyarta ta hure mata kunne.. K’arshe Umma ce masa tai idan dai bazai bar mata d’iya ta sakata ta wala ba toh wllhi zata kwashe yaran ta tafi taredasu kuma bazai sake ganinsu ba Eritrea zasu koma da shike dama Mahaifiyar Sady ‘yar asalin k’asar Eritrea ce, haka nan take  kyakkyawa kaman mutanen k’asar Eritrea masu kusanci da Ethiopia dan a wajenta Sady ta samo tsantsan kyaun halitta da Allah yayi mata, saidai Ita Sady har ta d’ara mahaifiyar tata.


Sosai Malam Ibrahim ya  samu matsala da Umma akan Barin Sadiya da tai sakaka tana Yawo dan har Dattijan unguwa sun gaji sun soma masa magana, yayi dik yanda zaiyi ya hana hakan abu yaci tura..K’arshe dai shine yace saidai Sady ta fiddo da miji a mata aure kafin ta k’arasa shekararta ta farko a jami’a.. Ana haka ta had’u da wani saurayi mai suna Sagir a Yanargizo.. Nan da nan Sagir ya samu gurbi mai girma a zuciyar Sady dan sosai yake mata b’arin kud’i kuma yace da aure yake nemanta.. Sady ta gama sakankacewa ta yarda ta amince Sagir masoyinta ne Tuni tace masa ya turo ayi maganar aurensu dan Dama Abbanta ya saka mata takunkumi.. Nan Sagir yake sanar da ita cewa iyayensa US suke  basa zama a Nigeria.. Shima abinda ya kawosa zuwa yayi dan ya nemi mata ‘yar k’asar Nigeria ya aura ya d’auketa su koma can US suci gaba da zama.. Haba nan fah Sady da Umma suka kuma susucewa akan Sagir.. Ya turo masu wani mutumi guda d’aya a matsayin Uncle d’insa akai maganar aure.. Sagir yace kar suji komai shi zaiyi komai na aure, nan suka kuma jin dad’i.. Nan da nan zance ya d’auka Sady zata auri d’an gidan k’usa bama cikin Abuja suke zama ba cen k’asar Amurka suke da zama shida iyayensa neman macen aure ya dawo dashi gida Nigeria, iyayensa zasu Zo da zaran ya samu mata an soma shagulgulan biki..


Hakan yasa Uwani cin alwashin yin Bikin kece raini ga Sadiyarta, Ta shiga ciwo bashi dan tayi Bikin kece raini, Bikin yaran masu hannu da shuni Bikin nunuwa a shafukan sada zumunta na yanar gizo.. 

Ana biki kwatsam aka nemi ango aka rasa har rana mai kaman Ta yau basu san abinda ya faru da ango ba.. Ga wayar salulansa ta dena shiga.. Tun Sady na damuwa har dai Umma tace ta daina damuwa k’ila America ya koma dan ya taho da iyayensa tinda an soma shagulgulan biki.. Sabeera ma cewa tayi k’ila US d’in ya tafi kuma ba lallai wayarsa Ta shiga ba.. Hankalin Sady sosai ya tashi, taci kuka tana fad’in Maiyasa bazai kirata ba da zaran ya saka layinsa na k’asar Amurka, Sabeera tace k’ila surprise yake son mata.. Abu kaman wasa babu Sagir babu dalilinsa har zuwa ranan d’aurin aure da aka rasa ango aka rasa mai karb’awa ango aure.. Toh daga nan ne fah Umma da Sadiya suka fara shakku da yinin wane irin mutumi suka jajib’o...


Umma Ta nusa tana duban Abba da har ya ida alwalansa yana d’auraye slippers d’insa da sauran ruwan butar har lokacin karan goge bakinsa na cikin bakinsa..


“Abban Sadiya yanzu bazakace komai ba.. Kana jin yanda ake shigo gidan nan sahu sahu ana d’aga min hankali sai na fidda kud’ad’en dana ciwo bashi..”


Sai sann ya d’ago ya dubeta “Toh ki biyasu kud’insu mana sai su daina miki sintiri a gida..” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa.


Ta k’walalo idanu waje “Ina zan iya kashin  tulin kud’ad’en nan Abban Sadiya..?”


“Aw dama Kinsan Bakida hanyar samu Kika ciwosu.. Kan wane dalili.? Dan ki birge mutane..? Ai sai ki jira mak’aryacin da ya yaudareku d’in yazo ya biya miki bashin dan nikam Kinsan Ko kud’in haya na shekara da nake biya idan an had’a bazasu isa ba..”


Umma ta dafe fuskarta da hannu tana salallami tana furta “Oh ni Uwani na shiga uku, Sadiya kin d’ebo mana ruwan dafa kanmu..”


Tana jiyo muryar mijinta na kiran Ashiru da Habib suzo su shige masallaci...


Umma ta nufi d’aki yanda Sadiya Ke kwance tana aikin abu guda..


“Ki tashi ki daina wannan koke koken mu soma tunanin yanda zamu samo mafita.” Umma Ta fad’i tana mai zama gefen katifar da Sadiya Ke duk’unk’une tana zuban hawaye, sautin kukan ma ya daina fita.. Idanunta sunyi luhu luhu haka nan ma fuskarta tayi jajazir, tsinin hancinta shima yayi ja har kaman ya k’ara tsawo.. Kallo guda zakai ma Sadiya ka fahimci cewa tana cikin tsananin tashin hankali wanda tinda tazo duniya bata tab’a shiga irinsa ba.


“Umma.. Sagir..” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka, sai kuma ta kasa ci gaba da magana sakamakon kukan da ya dad’a taso mata 


Nan ta kifa kanta tana mai isarta yayinda Umman tai tagumi Ta zuba mata Ta mujiya..


**



Suna tafe saman kwalta Assad naci gaba da jefo masa tambayoyi wanda akasari ba samun amsarsu yake ba shidai kawai damuwarsa su isa wannan location d’in da Danger ya basa..


Wayar Mu’azzam d’in Ta soma ringing.. Yai saurin ciro wayar a aljihu yana duban mai kiran nasa, a d’an kasalce ya k’arawa a kunnensa dan yasan mai kiran nasa matsala zai kunno masa.. Shiru yai ga dukkan alamu yana sauraren d’aya b’angaren ne..


 A hankali ya lumshe idanunsa yace “Tell me your location..?” Alright alright I’ll be on my way.. Don’t call a cab just wait for me there..” D’if ya kashe wayar yana mai fuzar da fuci..


“Pull the car over Assad.” 


Assad da kacaukam hankalinsa kega kwalta d’an kaikaitowa yai yana dubansa “Wait what..?”


“Stop the car, zan sauk’a a nan.. I need to go back..”


“You mean to the station..?” Assad ya kuma tambaya yana k’ok’arin parking motar gefen kwalta..


Yana k’ok’arin ficewa daga motar yake fad’in “No..MUSADDIQ ne... Daga yanda yake mun magana nasan ba cikin hayyacinsa yake ba..”


“Musaddiq kuma..? Na kwana biyu  banji kana tare tare da gagaransa ba.. What really happened..?”


D’an tab’e baki Mu’azzam yai kafin yace “How would I know.. Abunda na sani kawai shine ya kasa karb’an k’addarar cewa Ikram ta tafi kuma bazata tab’a dawowa ba.. I’m afraid rashin Ikram ka iya jefa Musaddiq halinda ya riga ya bari a baya..” Ya k’arashe damuwa saman fuskarsa..


Cikeda tausayawa Assad yake duban abokin nasa, yasan d’awainiya ne da dama zasu kuma hawa kan Mu’azzam d’in...


Daidai lokacinda cab ya tsaya.. Mu’azzam ya shige yana fad’in “Kaje kayi sauri ka isa location d’in zamuyi waya..”


Baki sake Assad Ke dubansa yana kuma juya ‘yar k’aramar Doguwar takardan mai d’aukeda address d’inmu.. D’an girgiza kai kurum yai kafin ya shige ya d’auki hanya...


**


-Star lake street, Maitama_



Tsaye tayi saman kan matar dake kwance saman gado wacce idanunta Ke bud’e tarau saidai gefen jikinta guda tamkar a shanye yake, bakinta dake karkace miyau na fitowa.. A tak’aice dai kallo guda zakai mata ka fahimci matar tana cikin tsananin jinya ne...


A hankali matar dake tsaye kanta ta duk’a tana mai ci gaba da k’are mata kallo, lokaci guda ta saki murmushi tana mai ciro tissue paper dake ake gefe cikin kwali ta shiga goge mata miyau d’in dake fitowa daga cikin bakinta. Lokaci guda take furta “Na shafe tsawon shekaru ina jinyar kishiya.. Shin zan samu riba nan gaba..? Shin hak’ata zata cimma ruwa.. They say everything in life has a price, Nuratu.. Could this be my punishment..?” Tai fasali tana mai duban matar wacce ta kirata da Nuratu kafin ta saki murmushi tace “No wait.. How could this be my punishment bayan ni ban aikata komai ba.. Kece kika aikata mun komai Nuratu.. Kece kika d’auke komai daga gareni.. A baya ked’in matar d’an uwan mijina wacce na miki lak’abi da kishiyar Dinga sannan Hausawa sunce ita d’in tafi zafi..  Kin kasance wacce tafi soyuwa cikin dangi musamman wajen Inne Mahaifiyar mazajenmu..” Ta k’arashe maganar tana mai disposing used tissue paper d’in kafin ta d’auko wani tana mai kuma goge wanda yake gangarowa, lokaci guda take ci gaba da furta “Nayi zaton idan mijinki ya mutu zaki fita daga rayuwarmu.. Zaki koma yanda kika fito.. But then I was wrong.. Ashe mutuwar mijinki ba komai zai k’ara mana ba face kusanci da juna..” Kukanta ya k’aru sanda taci gaba da fad’in “Kin aure mun miji Nuratu.. Kin aure mun miji bayan naki mijin ya mutu.. Kin zamto shalele mafi soyuwa a wajen mijina.. How could you.. Ta yaya zaki aikata mun haka..? Ta yaya Nuratu..” Tasa hannu tana goge hawayen da ya wanke mata fuska kafin taci gaba da fad’in “This is what you deserve.. Keda mijina bazaku tab’a kasancewa ba balle har Kuji dad’in yin rayuwar aure tare.. Bazan tab’a bari hakan ta kasance ba Nuratu.. Ked’in bazaki tab’a warkewa daga wannan ciwo ba.. Kar ki mance da furucina... Dama na gaya miki gidan mijina tamkar GIDAN ARO yake a wajenki... Babu Ke babu sukuni balle samun natsuwa a cikin gidan mijina.. Na fad’a miki aron gidan na baki na d’an wani lokaci.. Zaki fita daga gidan domin kuwa akwai babban shiri da nake miki.. Zaki fice daga wannan gidan  kaman yanda na miki alk’awarin cewa shid’in GIDAN ARO ne a wajenki..” Tana kaiwa nan ta kece da wata irin dariya hawaye na fito mata.. Saida har dariyar nata ya koma tamkar kuka kafin ta kifa kanta gefen majinyaciyar tana kuma sakin kuka mai ban tausayi.


K’amshin turaren mijinsu da yaima k’ofofin hancinta sallama ya tabbatar mata cewa shid’in ne ya shigo.. Nan fah ta dad’a narkewa tana sakin kuka mai ban tausayi..


No comments

Powered by Blogger.