Gidan Aro 17*17*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*


Harga Allah ta bawa Musaddiq dariya yanda tai maganar amma Sai ya gimtse yace “Zaki min bayani yanzu, what exactly were you doing in there..? Mai kike cikin d’akin mutumin nan..?”


Zaro idanu waje tai sai kuma tai dariyar yak’e tace “Ban d’aki nake nema kawai sai tsintar kaina nai a wannan d’akin.. Kai kuma fah.. Ba kace min baka shiga wannan gidan ba.. Ya na ganka a cikin gidan.. Kuma da alama ka saba shiga.. Watau dai k’arya ka min kenan..?” Ta k’arashe hannayenta saman kunkumi tana mai tsaresa da idanu tamkar wacce zata kai masa bugu.


“Wait what.. Ke ni nake miki k’arya..?”


Ajidde ta d’an murgud’a masa baki tace “Toh ni bance kayi k’arya ba amma Maiyasa kace min haka..?”


Tsareta da idanu yai dan a yanda ya d’auketa shashasha bai zaci zata iya d’ago zancen da sukai ranan ba.. Ya gyara tsayuwarsa yace “Tsaya ai idan ban mance ba nace  miki inada aboki d’an gidan..”


Ajidde Ta zaro ido Tace “Wannan ne abokin naka..? Ai shine mutumin da ya biyoni ranan..”


Musaddiq ya zuba mata idanu da tsananin mamaki “Toh kin dai aikata laifin kenan.. Na tabbata ke mai laifi ce.. Zaki fad’a mun mai kike a d’akin ko kuma yanzu na shiga cikin gidan na sanar dashi komai..”


Cikin tsananin damuwa Ajidde take rok’onsa “Dan Allah ka rufa mun asiri.. Ka rufa mun asiri kar ka tona mun asiri wajensa.. Idan ka tona mun asiri shikenan bazan bawa matar nan magani ba.. Dan Allah ka barni na gwada sa’an magani na akan matar nan.. Nasan zakaso mahaifiyar abokinka ta sami lafiya..” Ta k’arashe cikin tsananin nuna damuwa.


Musaddiq ya jinjina kai yace “K’warai kuwa nafi kowa so Aunty Nuratu Ta sami lafiya.. Zan rufa miki asiri amma sai kin sanar dani gaskiyar Al’amarin..”


Ajidde ta had’iyi miyau da k’yar tana mai kuma zaro idanu “Zan fad’a maka amma saidai idan zaka mun alk’awari.”


Cikin wane irin yanayi yake dubanta wannan karon. Lokaci guda yananyin nasa ya canza, cikin wane irin kakkausar murya yake fad’in “I thought I’ve already told you.. I don’t make Promises.. Bana Alk’awari.. Ban tab’a cika Alk’awari ba.. Kuma bazan tab’a cika alk’awari ba... Kuma na rasata ne ta dalilin rashin cika Alk’awari na.!” Ya k’arashe siririyar hawaye tana gangaro masa.


Cikin tsananin tsoro Ajidde ke dubansa, idanunta Sun firfito waje sabida tsoro. A hankali Ta soma k’ok’arin jada baya..


“Ina zakije..  Bazaki bar wajen nan ba sai kin fad’a mun sirrinki..” Ya fad’i yana dubanta.


Cikin sauri take girgiza kai “Banida Sirri.. Ni d’in kawai magani nake kawowa..” Tana ida fad’in haka tasa kai zata shige.


Musaddiq yasha gabanta yana binta da wani irin kallo wanda ya kuma haifar mata da tsoro “You are a thief..! Ke b’arauniya ce.. Wancan ranan sata kika so yi masa sai ya biyoki kika b’uya.. Wannan karon ma sata kika shiga d’akinsa zaki masa sai Allah ya kawoni kafin ki ida nufinki.. Now you tell me.. Shin wacece ke.. Mai magani ce ke kokuwa b’arauniya ce.?!”


Idanun Ajidde suka kawo ruwa, Ta soma girgiza masa kai tana fad’in “Dan Allah ka rufa mun asiri wllhi nima umarni nake bi..”


“Umarni kike bi.. Umarnin wa..?” Ya kuma tambaya yana dubanta.


Ajidde ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubansa “Zan fad’a maka komai amma zaka yi shiru.. Bazaka fad’a ma kowa komai ba.. Idan har kana so na bawa matar nan magani.. Sannan zaka taimakeni..”


Musaddiq ya jinjina kai yace “Zanyi duk abinda kikace Idan kika fad’a mun komai..”


K’asar wata bishiya suka zauna Su duka biyun, Musaddiq ya dubeta yace “Ina sauraronki..”


A hankali Ajidde Ta soma karanto masa sana’ar da Kyallu ta d’aurata bisa, ta kuma sanar dashi k’udirin kyallu na cewa muddin tazo gidan bata sato masu wani abu ba ga uk’ubar da zata mata.. Wannan dalili shiyasa take k’ok’arin aikata satan da yace tana yi.


Musaddiq ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana dubanta “Toh ita Inna Kyallu bata tinanin watarana a kamaki.?”


Ajidde ta girgiza kai tace “Inna kyallu bata yarda da fad’uwa ba.. Dik abinda zatayi sai ta masa shiri sosai domin kuwa har layar zana ta bani.. Sannan idan aka kamani babu damuwarta dan cewa zatai dama tin can ni b’arauniya ce.”


Musaddiq yace “Ke kuma kin yarda layar zata taimaka miki..?”


Ajidde tai shiru tana dubansa “Ban sani ba..” Ta basa amsa kai tsaye.


Sauk’e ajiyan zuciya yai kad’an yace “Zan taimakeki.. Kuma zamuyi aiki tare.. Aunty Nuratu zata sami lafiya in sha Allah.. Sannan Inna Kyallu bazata fahimci komai ba..”


Tai masa K’uri tana dubansa kaman yanda shima ya zuba mata idanun.


**


Zaune take a uwar d’aki ta rapka uban tagumi tana tinanin rayuwa da yanda Al’amara suke kasance masu tun bayan had’uwarta da Sagir. Tana jin Tabawa da Umma yanda Tabawan ke yab’a wa mahaifiyarta maganganun marassa dad’in sauraro saikace ba d’azu tai masu kaca kaca da gida taci mutuncinsu ba, a rana guda karo na uku kenan kafin yammaci Tabawa ke kawo masu samame.. Wannan shine ake kira K’addara ya riga fata, da ace wani zai iya zab’an k’addararsa tabbas da bata zab’i K’addarar sanin Sagir ba balle har ta kasance dashi. Amma saidai tuni K’addararta tazo da hakan a rubuce. Ji take ta dalilinta komai ke faruwa, duk wasu iftila’i da ahalinsu ke fuskanta itace sababi.. Wasu hawayen masu tsananin k’una suka gangaro mata. A daidai lokacin Umma ta shigo.


Ta jima tana duban Sadiyar kafin ta k’arasa gefe da Ita ta zauna, saida suka d’ibi lokaci babu wanda yace ma kowa komai kafin Umma ta nusa tace “Bana San kina saka damuwa ma ranki Sadiya, cuttutuka sunyi yawa yanzu Sai kije kisa ma kanki hawan jini ko ciwon zuciya a ‘yan shekarun nan naki..”

Sadiya ta goge hawan dake kwance saman fuskarta “Umma Wai ni dan Allah ina dangin Abba suke da bazasu waiwayemu ba.. Umma shin basu san d’anuwansu ya mutu bane bazasu dubi bayansa ba Ko dan albarkacin zumunta. Umma kodai baida dangi ne..?”


“Waye kika tab’a ji baida dangi Sadiya. Mahaifinku yanada dangi saidai tin lokacin da yace zai aure ni sukayi farrak’u da danginsa.. Iyayensa sun jima da rasuwa sai ‘yanuwan ne suka rainesa. Sunso su aura masa d’iyarsu shi kuma yak’i amincewa yace sai ni yake so.. Tin daga wannan lokaci suka ciresa daga cikinsu sukai rantsuwa babu shi babu su bazasu tab’a waiwayansa ba har abada.. Sadiya mahaifinki ya sadaukar da abubuwa da dama a sabida ni.. Banida kowa a k’asar nan sai shi.. Na shigo k’asar nan a wahalce a matsayin ‘yar cirani.. Kuma na rasa kowa nawa amma mahaifinki shi kad’ai ne ya tsaya min ya taimaka min ya zamto min sutura..” Muryarta ya soma rawa sosai sanda taci gaba da fad’in “Na k’are ina mai masa butulci da raina arzikinsa.. Mutumin da ya sadaukar da komai nasa sabida ni.. Ciki harda danginsa wanda suka guje shi sabida ya zabi ya kasance da matar da bata da kowa a k’asar nan.. ‘Yar cirani data shigo k’asar nan a wahalce.. Shin ki fad’a mun ta yaya bazan ga ba daidai ba.. Ta yaya wacce ta aikata irin wannan butulci zataga da kyau...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana.


Sadiya dake hawaye Ta matso ta rungume mahaifiyarta su duka biyun suna kuka mai ban tausayi.


Cikin zuban hawaye Sadiya ke duban Umma “Umma ki daina fad’in haka.. Bawa baya wuce k’addararsa.. K’addarar ka tamkar inuwarka ce dik yanda ka kaje saita bika sannan idan ka tsaya itama zata tsaya.. In sha Allah zanyi abinda ya dace wannan karon.. Bamuda sauran zab’i da ya wuce na amince da auren Alhaji Isyaku..” Kuka sosai ya kufce mata.


Cikin zuban hawaye Umma ke dubanta lokaci guda take girgiza kai alamun a’a “A’a Sadiya, bazan bari ki sadaukar da rayuwarki da farin cikin ki sabida zunubaina ba.. Nasan bansan yanda zanyi ba.. Amma inada tabbacin Allah bazai bar mu haka ba da sannu zai kawo mana wani mafitan..”


Sadiya tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka gangaro mata “Watak’ila mafitan kenan Allah ya kawo mana Umma. Watak’ila Alhaji shine mafitan angaremu.. Umma idan muka zauna haka bamusan mai Tabawa zatayi gaba ba.. Bamusan ko Malam Aminu zai bar muci gaba da zama a nan ba.. Umma ‘yan uwana nake tunani.. K’anne na nake tunani, bana so suna ganin irin wannan tashin hankali.. Umma abin yayi yawa.. This has to end Umma.. Ni kad’ai ce ya kamata nayi abinda ya dace.. Umma ki sanar da Malam Liman ni Sadiya na amince ya aurar dani ga Alhaji Isyaku... Zan rabu da Sabeera rabuwa Ta har abada.. Bazan k’ara kallon cikin idonta ba.. Watak’ila Wannan shine hukuncina a rayuwa.. Hukuncin abubuwan da nayi ma Abba a lokacin da yake raye.” Ta k’arashe cikin tsananin kuka... Umma ta rungumeta su duka biyun suna masu fashewa da wani irin kuka mai tab’a zuciya.

**


Koda labari ya iski Alhaji Isyaku cewa Sadiya da mahaifiyarta sun amince da batun auren Zo kaga Farin ciki wajensa, jinsa yake sabon ango.. Lallai tarkonsa ta d’anu ko banza zai mallaki wannan kyakkyawan yarinyar da ya jima yana kwad’ayin kasancewa da Ita.. Bayan isha ya shirya tsaf yasha wankansa ya fesa kwalliya da babbar riga ya nufo gidansu Sadiya.


Da k’yar Umma ta shawo kanta tace taje su gaba taji da mai yazo. 

Haka badon taso ba ta zira hijab d’inta ta fito.


Yana ganinta fari’arsa ya k’aru “Assalamu alaki kyakkyawa ma’abociya annuri..” Ya fad’i yana mai k’arasowa.

Sanin darajan sallama yasata ta amsa ciki ciki kanta na duk’e k’asa.. Ta soma k’ok’arin duk’awa da niyyan gaishesa.


“A’a tashi tashi kayanki.. Haba ai saidai ni na duk’a miki Gimbiyata.”


Takaici ya turnuk’eta, ta rintse idanunta a hankali tanajin zuciyarta na mata zafi.


“Ki saki jikinki. Kuma ki saka a ranki cewa ni masoyinki ne..”


“Masoyi kuma Baba..? Kodai b’atan kai kayi ne.? Ni ce fah Sadiya k’awar Sabeera wacce ka datse alak’armu da Sabeera sabida banida kamun kai.. Ko ka mance ne..?”


Murmushin da yafi kama da yak’e yai kana yace “Yaro dai yaro ne. Toh banda abinki Sadiya ai ba komai yasa bani k’aunar alak’arku da Sabeera ba Sai dan bana so ku shak’u ku samu kusanci da juna gudun kar randa duk nazo miki da wannan batu nawa da ya jima a birnin zuciyata kice bazaki iya ba sabida k’awance da d’iyata da kuke.. Idan kika cire wanann ni babu wani abinda zaisa na rabaki da Sabeera.. Ki yarda dani Sadiya, ni wllhi ba sabida komai na rabaku da Sabeera ba sai dan kar ta zamto mana cikas a tsakaninmu.. Banaso ta zamto shamak’i ma soyayya ta dake..” Ya d’an nusa yana mai gyara zaman babbar rigarsa “Wato Sadiya na jima Ina k’aunarki saidai bansan Ta yanda zan tunk’areki da wannan batu ba har sai zuwa wannan lokaci..”


Sadiya dake dubansa cikeda tsananin mamaki, dan itakam kunya ma take ji masa, murmusawa tai tace “Sai wannan lokacin ka sami dama. Lokacin da banida wani zab’i da ya wuce na amince da buk’atarka koda ace bana so. Shin ko ba haka bane Baba.?”


Saurin katseta yai da fad’in “Ko d’aya.. Ba haka bane.. Kuma dan Allah ki daina kirana Baba, mud’in  zamu kasance k’ark’ashin inuwar ma’aurata ne, matata zaki zamto nan da kwanaki biyu rak, dan ni asabar d’in nan mai zuwa nake so a d’aura Kinga yau Alhamis ne already..”


A zabure ta d’ago tana dubansa “Asabar mai zuwa fah kace.!”


“K’warai kuwa Amaryata, rashin jan lokacin yafi a’ala, shi dama jan lokaci a aure Baida wani alfanu..”


“Ka sani auren nan da zanyi sadaukarwa ne ga ahalina amma ba don inaso ba.” Ta fad’i idanunta na raurau.


Murmusawa yai yana mai kuma gyara tsayuwarsa “K’warai kuwa nasan da hakan, kuma ina mai tabbatar miki da sannu zaki soni ki k’aunace ni.. Idan har da gaske auren sadaukarwa zakiyi toh kuwa ya kamata ki amince ayi auren nan as soon as possible.. The earlier the better. Sabida ahalinki zasu huta da tashin hankalin Tabawa harma da Malam Aminu.. Bai kamata ayi Jinkiri ba a situation d’in da ahalinki ke ciki.. Bugu da k’ari Nifa d’aukeku zanyi Cak daga garin nan dan ku mance komai ku mance duk wasu tashin hankali da kuka fuskanta cikinta.. Amma ke ya kika gani..? Ki tuna you are doing this for your family.” Ya k’arashe yana mai zuba mata idanu.


Hawayen da take rik’ewa ne suka soma gangaro mata. Ta shiga jinjina kai tana furta “Yes.. Yes I’m doing this for my family.. For the sake of my Family... Zan sadaukar da komai nawa ciki harda Farin cikina sabida Su.. Sabida ni ce duk na ja masu halinda suka tsinci kansu ciki..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.


Juyawa yai yana sakin murmushin cin nasara kafin ya maidoda dubansa gareta “C’mon Baby ki daina kukan nan haka, wllhi har cikin zuciyata nake jin zafin zuban hawayenki.. I promise you kukan ki ya k’are Baby.. Da zaran kin auren zan mantar dake komai.. Zan baki irin rayuwar da kika jima kina mafarkin samu... I’ll spoil you and pamper you kinji Baby na..”


Jin kalaman nasa take kaman Ana hura mata wuta cikin kunnuwarta, babu kunya babu tsoron Allah Wai Baban Sabeera ke jero mata wad’annan kalamai hardasu kiranta Baby.. Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana girgiza kai tace “Wancan rayuwar mafarkin Sadiya ce a baya.. A halin yanzu babu abinda nake so face peaceful world for my family. I want my family to have peace.. Iyakacin abinda nake so yanzu shine peace.. Zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ahalina.. Mafarkina da buruka na sun jima da mutuwa.. An birnesu tareda mahaifina.. Kuma ina neman wani alfarma a wajenka.”


Ya jinjina kai yace “Kin wuce neman alfarma Gimbiyata, abinda kike so kawai zaki fad’a ayi.”


Sadiya tace “Kar ka biya Tabawa har sai randa akazo d’aura aurenmu domin akwai rayuwa akwai mutuwa bamu San mai zai faru kafin ranan ba..”


Ya murmusa yace “Idan dan wannan ne banida matsala. Yanda kikace haka za’ayi Amaryata.. Wllhi na k’agu ki zamto tawa..”


Katsesa tai da fad’in “Ni zan shige gida..”


“A’a tsaya mana..” Yai maganar yana zaro kud’ad’e cikin aljihunsa.


Saurin girgiza kai Sadiya tai tace “Bazan karb’i komai daga hannunka ba.. Na gode..” Bata tsaya sauraron sa ba tasa kai ta shige cikin gida.


Yabi bayanta da kallo zuciyarsa fari k’al, kad’a Kai yai yace a fili “Bari dai naita lallab’a ki har ki shigo...” Yana ida fad’in haka ya gyad’a Kai yana mai kuma Washe baki ya shige.


**


Washe gari sassafe Tabawa tai kiran Asabe mai kayan Koli.


Tabawa ta k’irgo kud’ad’e cikin wanda Alhaji Isyaku ya bata, Ta mik’awa Asabe Mai kayan Koli tace “Kina jina dik abinda na sanar dake haka zaki sanar da matarsa.. Asabe koda wasa kar ki ce ni na sanar dake..”


Asabe Ta jinjina kai tana tura kud’in cikin posar ta. “Haba Hajiya Tabai, indai dan wannan ne ai bakida matsala, da Asabe fah kike zancen..”


Tabawa ta murmusa cikeda jin dad’i tace “Yauwa tawan.. Idan har hak’ata ta cimma ruwa zan k’ara miki wani abu..” Asabe Ta Washe baki cikeda farin ciki.. Tuni ta aza kayanta na Koli aka ta nufi layin gidan Alhaji Isyaku.


Tabawa tabi bayanta da kallo zuciyarta fari k’al. A fili take furta “Alhaji Isyaku kenan ai wllhi bazan bari ka auri yarinyar nan ba, auren nan saidai ayi dani Koda zaka biya masu bashin amma bakada mata sai ni Tabawa. Zan d’aga masu hankali dan ka biya masu bashi sannan zan sa matarka da d’iyarka su d’aga masu hankali suk’i amincewa da buk’atarka bayan ka biya masu bashin..” Tana ida fad’in haka ta bushe da muguwar dariya kafin ta shige gida.


**

Maman Sabeera na zaune parlor tana kallon shirin good morning Nigeria da ake nunawa da sanyin safiya a tashar NTA Asabe mai kayan Koli tai sallama.


Iyatu mai masu aikatau ce ta amsa mata sallamar tace ta jira ta shiga ta tambayi Hajiya idan zata sayi wani abin. 


Asabe tace “Dakata ba saye da sayarwa ya kawoni na ba.. Alhaji na gida Ko ya fice..?”


Iyatu tai jim kafin tace “Ai Jiya Alhaji bai dawo gida ba inaga wajen aiki ya kwana..”


Asabe ta zaro ido waje tace “Bai kwana gida ba..? Ikon Allah Toh ki shiga kice mata magana nazo mata dashi mahimmiya kan maigidanta.”


Iyatu ta dubeta da mamaki amma sai ta jinjina kai tace “Shikenan.” Lokaci guda ta shige ta nufo parlor ta tadda Maman Sabeera ta sanar da ita abinda Asabe mai Kayan Koli ta fad’a mata.


Mamaki ya cika Maman Sabeera jin Wai magana Asabe tazo mata dashi kan mijinta. Ta nusa tana tinani kafin taceda Iyatu “Kice mata Ta shigo.”


Iyatu ta jinjina kai kafin ta fice yin iso ma Asabe.


Jim kad’an Asabe ta shigo d’aikeda kayan Kolinta, ta nemi waje daga k’asa ta zauna tana gaida Maman Sabeera.


Maman Sabeera Ta dubeta da mamaki tace “Asabe kikace yau ba talla kikazo ba.. Toh wani magana ne ya kawo ki kan maigidana.?”


Asabe Ta d’an Tab’e baki tana ‘yan waige waige tace “Hmm ai Hajiya abinda nazo dashi yau yafi k’arfin talla.. Amma Hajiya jiya Kinsan yanda mijinki ya kwana..?”


Da tsananin mamaki Maman Sabeera ke dubanta ganin basu saba irin wannan batu ba, iyakaci ta shigo da kayan kolinta ta tallata ta fice. Amma yau Asabe tazo mata da batu mai girma. 

Girgiza kai kad’an Maman Sabeera tai “Ban.. Fahimceki ba Asabe.. Mai kike nufi..?”


Asabe ta kuma gyara zama tana duban Maman Sabeera “Hajiya wllhi wllhi abinda zan fad’a miki Sai ya firgitaki.. Idan dai har bakisan yanda mijinki ya kwana jiya ba kuma bakisan da wa ya kwana ba ni zan sanar dake dan na sani..”


Zuciyar Maman Sabeera yaci gaba da bugawa cikin sauri, mijinta ya saba kwana cikin Abuja idan dare ya masa sabida tsananin holdup da cinkoson Abuja yakan sa wataran ya kwana ga yanda k’asar Ta koma babu tsaro,  wataran yakan  ce aiki ya rik’esa zai kwana cikin Abuja da safe ya dawo. Amma koda wasa bata tab’a saka ma ranta cewa mijinta na ha’intarta ba tuni ta kyautata masa zato tinda ma kafin ya kwana cikin Abujan Sai ya kirata ya sanar da Ita cewa zai kwana aiki ya rik’esa gudun Karma zargi ko abu mai kama da haka ya shiga tsakaninsu. Cikin rashin yarda da batun Asabe Ta mik’e tana nuna ma Asabe k’ofa “Kinga Asabe tashi kawai ki fice.. Kafin ranmu gaba d’aya ya b’aci.. Tashi ki fice min a gida ni bana shiga gulma da gutsiri tsomen unguwar nan.. Tashi ki fice min a gida kuma kar ki sake dawowa idan da irin batun nan zaki Zo..”


Asabe Ta murmusa tace “Hajiya wllhi Allah na rantse miki da Allah daren jiya mijinki na unguwar nan kuma nasan da wa yake tare.. Ni ganau ce ba jiyau ba, na gansa da yarinyar nan Sadiya kuma yau kusan kwanaki uku kenan yana zarya k’ofar gidansu.. Ina mai tabbatar miki d’aukanta yayi suka fice suka kwana tare.. Ai dai Kinsan wacece Sadiya a unguwar nan Sadiya Sady Pretty da tai k’aurin suna wajen rab’an maza masu abin duniya.. Toh ta fad’o kan mijinki zata k’wak’wale abin hannunsa.. Dan wllhi jiya tare na gansu kaman zai mata sijadda dan biyayya..”


Bibbiyu Maman Sabeera ta soma gani, hazo hazo da wani irin duhuwa ne suka gifta k’wayar idanunta. A yayinda Sabeera da fitowarta kenan daga kitchen rik’eda mug dik taji tattaunawarsu a kunnuwanta.. Wani irin k’ara ta saki had’ida sake mug d’in dake hannunta ya watse saman tiles..


No comments

Powered by Blogger.