Furar Danko 5

 


๐“๐ฒ๐ฉ๐ข๐ง๐ ๐Ÿ“ฒ

  ๐Ÿซ— ๐™๐™๐™๐˜ผ๐™ ๐˜ฟ๐˜ผ๐™‰๐™†'๐™Š.....!!๐Ÿซ—

           ๐‘ฉ๐’Š๐’๐’š๐’ ๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’๐’ ๐’„๐’†๐Ÿค™๐Ÿป

๐‘ช๐’‰๐’‚๐’‘๐’•๐’†๐’“ 5️⃣

_Free pages end_

.......Gidane irin ginin da amma kuma babbane sosai, sannan kuma ko'ina mulmule yake da suminti.  BQ ษ—in yaran gidan maza itace a farkon shiga, sai daga can ciki

iyayensu mata,  baya can ฦ™arshe sashen mahaifinsu Malam Mika'il Idris Mawashi. Sam baya buฦ™atar shiga cikin gidan balle ya tada hankalin mahaifiyarsa, dan haka ya shige nasu sashen na samari. Da ga can ciki ษ—akinsa yake, kasancewarsa tuzurun da duk ya girma sauran ฦ™anensa da basuyi aure ba yasa shi kadai ke rayuwa a ษ—akinsa. Dan a yanzu haka akwaima ฦ™anan nasa da sunyi auren wasu ma matansu har sun haihu, shiko bama ya kula ฦดar kowa balle a saka ran zaiyi. Mahaifinsa yayi faษ—an har ya gaji, hakama mahaifiyarsa har ฦ™wallar ษ“acin rai take akan zaman nasa haka babu aure, babu aiki, babu wata ฦ™waฦ™wฦ™warar sana'a. Shi ba wani iskanci yake ba, ba shaye-shaye ba, ba ษ—aukar magana ba. Amma sun rasa mi yake taษ—e rayuwarsa haka. Duk inda ษ—a nutsatstse mai nagarta yake Aliyu Hydar yakai har ma ya zarta, gashi mutum mai tausayin iyayensa da son tallafar rayuwarsu. Ga tarin ilimin addini dana zamani ALLAH ya bashi, ga addini. Barshi dai da shegen taurin kai ga saurin fusatar tsiya da shiru-shiru, dan ko'a cikin abokai idan ba yaso ba baya fira.

     ฦŠakine ษ—an babba mai ษ—auke da kafet maroon color mai laushi, sai ฦ™atuwar katifa irin wadda ba'a sakawa a gadon nan. Wadrobe mai biyu sai kanta a gefenta cike da litattafan addini dama na bokon, an ษ—an yi teburin karatu da kujerarsa. ฦŠakin babu wani tarkace sannan fes yake ga ฦ™amshi kamar ba ษ—akin namiji ba. Uniform ษ—in da aka sharษ—anta masa sakawa matsayin driver ya cire, a kujerar 2sitter dake ษ—akin ฦ™wara ษ—aya ya jefasu ya haye katifarsa da ga shi sai boxer da singlet yay kwanciyarsa yana furzar da tagwayen huci masu zafi da ษ—aci, dan abinda yarinyar tai masa sam yaฦ™i barin ransa. Sai kuma shigar jikinta da tafi komai ฦ™ona masa zuciya. Haka yake shi ya tsani mace haka. Kai koda atamfa ko lass yaga mace tama ษ—inkin fidda surar jikinta baฦ™in ciki yake ji balle wannan da gaba ษ—aya ta canja suffarta daga hausawan ta koma kamar wata jinin kafirai. Tsaki yaja mai ฦ™arfin gaske ya juya kwanciyarsa yana mai ingije tunanin a ransa. Sai dai duk yanda yaso hakan bai yiwu ba. Al'amurin ma yaฦ™i barinsa yin barcin da yake buฦ™atar yin ko zai samu sassaucin baฦ™in cikin dake sukar zuciyarsa.. Da ฦ™yar ya samu barcin ya ษ—aukesa, baima yi na minti talatin ba akai kiran sallar la'asar. tashi yay da ฦ™yar yana faman yamutse fuska dan a barcin ma harda mafarkinta. siririn tsaki yaja ya miฦ™e ya shiga toilet ษ—in ษ—akin nasa, a gurguje yay wanka da alwala ya fito jin har za'a shiga salla. jallabiya kawai ya saka da turare ya fita kasancewar masallacin a kusan ฦ™ofar gidansu yake, dan baifi gida huษ—u ba ne tsakaninsu....


      Ana idar da salla gidan ya dawo, sai dai maimakon ษ—akinsa yanzu ciki ya shiga ษ“angaren iyayensu. Gida ne da tun a farkon shigowarka zaka iya fahimtar na zaman mace huษ—u ne. Yaran dake kai kawo a tsakar gidan a ฦ™alla zasu iya kaiwa goma koma fiye da haka, wasu sanye da uniform na islamiyya wasu nacin abinci wasu kuma na ษ—an kai kawon aiki. Tsit kake ji duk wani ihu da hayaniyar da gidan ya ษ—auka ya tsagaita, yaran suka shiga gaidashi. Sau ษ—aya ya amsa musu ya nufi ษ—akin mahaifiyarsa kai tsaye. Sun san ba wasa yake da su ba dan haka babu wanda ya damu da yanayin nashi, sai dai sauri-sauri da suka shiga yi na son kowa ya kammala abinda yake ya fice islamiyya kafin ya fito ya sake ganinsu..

         Daga ษ“angarensa kam da mamaki mahaifiyarsa ke kallonsa daga inda take zaune. A hankali ya kai zaune a ฦ™asan carpet ษ—in da aka saka a gaba ษ—aya falon kalar blue. Basu da kuษ—i, amma mahaifiyarsa mace ce mai tsananin tsafta da cikar kamala, tanada haฦ™uri sosai, sai dai bata son raini ko kaษ—an ita, dan kana shiga sabgarta zata tabbatar maka da ita ษ—in jinin zazzagawa ce. 

       “Ammah barka da yamma”.

   Ya faษ—a cikin muryarsa mai sauฦ™in amo da rashin son hayaniya. Maimakon amsa masa gaisuwar tambaya ta jeho masa cikin nutsuwarta da cikar kamala. Dan da yawan halayensa ya samosu da ga gareta ne, duk da ya ษ—akko wasu da yawa ga mahaifinsu ma.

      “Baka da lafiya ne?”.

Gajeren murmushi yayi da ษ—an girgiza kansa. “Lafiya lau nake Ammah, na ษ—an yi barci ne”.

   “Shima wannan aikin an samu matsala kenan? Ya rabba..”

  Ta ฦ™arashe faษ—a a hankali cikin damuwa. Gaba ษ—aya jikinsa sai yay sanyi, murya a sarฦ™e ya ce, “Amma ba matsala aka samu ba karki saka damuwa a ranki. Na dawo da wuri ne dai”.

         Shiru tai tana kallonsa, sai dai har cikin ranta bata gamsu da maganar tasa ba. Ta sanshi fiye da yunwar cikinta akan zurfin ciki, sannan kuma bai iya ฦ™arya ba, ko yaya ya kuskure takan saurin harbosa. Tunda ya fara aikin ko ฦ™arfe biyar na yamma baya dawowa balle yanzu da azhar, alamuma sun nuna tun ษ—azun yake a gidan tunda gashi yace har barci ma yayi. Fitowar ฦ™annensa biyu ฦดammata Maryam da Asma'u masu kama da shi sosai kamar mahaifiyarsu ya katse shirun falon. ฦณammata ne ฦ™yawawa masu tarin nutsuwa da rashin son hayaniya suma. Suma dai ษ—an turus sukai na ganin nasa. Sai kuma cikin damuwa duk suka kalli mahaifiyar tasu. ฦŠauke kanta tai, dan gaba ษ—aya rauninsu da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu. 

     “Yayamu ina yini”

Suka haษ—a baki wajen faษ—a a sanyaye. Kansa ya jinjina da amsawa cike da kulawa, duk ba wani yana wasa dasu bane ko sakewa yana ฦ™aunar ฦ™anensa, sannan suna bashi tausayi da ya gagara tsayawa akan al'amuran su na yau da kullum a matsayinsa na babba namiji a ษ—akinsu tunda mahaifinsu abubuwa sun masa yawa yanzu, ga shekaru ga rashin tausayinsa da ga ฦดaฦดan gidan da kowa ya samu ya tsallake da ga shi sai iyalansa sai uwarsa ne..

      “Babu wata damuwa ko?”.

   Kai suka jinjina masa alamar babu duk da sunada buฦ™atu, sai dai sun san koma sun faษ—a tayar masa da hankali kawai zasuyi tunda bashi da shi. Abincin da akai gidan kason ษ—akinsu da aka kawo suka zuba masa, tuwon shinkafa ne da miyar ganye dai-dai ฦ™arfin talaka mai rufin asiri. Ya jima yana kallon tuwon bayan fitar su Asma'u har sai da Ammah tai masa magana sannan ya fara ci dan yunwa yake ji sosai, yau baya jin ko karin kummalo ma yayi, sai ruwan shayi da ya zame masa jiki ko yaushe bai rabo da shi a flaks da ya sha...........✍️


        *_Humm rikitata-rikitata kenan. Masu karatu ina faษ—a muku Bama a fara komai na fa, dan ko shimfiษ—ar labarin bamu kammalaba balle shiga cikinsa. Littafin FURAR DANฦ˜O...!! Labarine da yazo muku da nashi salon na musamman. Babban abinda ke addabar al'ummar mu a wannan lokaci a cikin gidajenmu da ma wajen gidajenmu da rayuwar ฦดaฦดanmu mata da maza dama na gidan aure duk ya taษ“o fiye da inda kuke zato._*


    *_Ga dai Uncle Smart a matsayin drivern Lulu ฦ™amshi, yarinyar ฦดar ฦ™walisa mai tsananin wayewar rayuwa. ฦณar gata kuma ฦดar hamshaฦ™an masu kuษ—i. Uncle Smart matashin saurayi ษ—an talakawa dake cikin jarabawar rayuwa kala-kala. Ya taso cikin gida mai yawan zuri'a da kowa kansa ya sani. Shin ta ina muke tunanin labarin waษ—an nan mutane biyu zai kamanceceniya da juna?_*


_Minene abinda Lulu ฦ™amshi ke ษ“oyewa na rayuwarta?_


*Minene ke faruwa a rayuwar Aliyu Hydar (Uncle Smart) da ke taษ—e rayuwarsa da ga cigabansa?*


_Baku ba, hatta da ni kaina ina son sani. Dan haka ku garzayo domin kasancewa da ZAFAFA BIYAR ษ—in nan naku abin alfaharinku. ฦณan amanarku, akoda yaushe labaransu masu gamsarwane a gareku._


*_Ki daure a matsayinki na mace mai kima da daraja, musulma da ta san muhimmancin hakki da son cigaban nata kasuwancin ko aiki kizo ki saya domin karanta halak ษ—inki, karki bari ki ษ—orama kanki nauyin da zaki iya yin kaico da sakacin ษ—aukar watarana saboda ruษ—i da ษ—aukar komai a ba komai ba ฦดar uwata._* 


_ALLAH ya ฦ™arama rayuwa albarka, duk wanda ya tsare domin ALLAH shima ALLAH ya tsare masa kasuwancinsa ko aikinsa. Alkairin ALLAH ya kai gareku a duk inda kuke a duniya masoya. Muna sonku irin trillions ษ—in nan. Duk wanda ya somu domin ALLAH shima ALLAH ya soshi haka shi da zuri'arsa baki ษ—aya. ALLAH ya gafartama iyayenmu da duk al'ummar musulmi baki ษ—aya๐Ÿ˜ญ๐Ÿ™๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜❤️❤️❤️❤️๐Ÿ˜˜_.


Garzaya ki biya naki kar a baki labari gasu nan da ษ—umi-ษ—uminsu suke๐Ÿ‘‡๐Ÿ˜€๐Ÿ˜˜.

    


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at๐Ÿ‘‡


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan๐Ÿ‘‡


09018600202


Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐Ÿ‘‡

09033181070


ฦณan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ษ—in๐Ÿ‘‡


+22799643131


VIP๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฏ

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*๐Ÿฅฐ


Zafafa๐Ÿซถ๐Ÿ”ฅ




*_ALLAH ya gafartama iyayenku๐Ÿ˜ญ๐Ÿ™_*

No comments

Powered by Blogger.