Furar Danko 3
๐๐ฒ๐ฉ๐ข๐ง๐ ๐ฒ
๐ซ ๐๐๐๐ผ๐ ๐ฟ๐ผ๐๐'๐.....!!๐ซ
๐ฉ๐๐๐๐ ๐จ๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐ค๐ป
๐ช๐๐๐๐๐๐ 3️⃣
........Da sauri MM Atik ya nufi tasa motar yana sanarma bodyguard ษin sa su bisu. Wani saurayi dake jingine jikin motarsa da ke kusa da su MM Atik ษin ya dubesa. Komai a
gabansa ya faru, dan haka yay murmushi da duban MM Atik ษin. “Ranka ya daษe Bama sai ka wahal da kanka ba indai sanin gidan su Lulu ฦamshi ce. Sai dai zan baka shawara karka wahal da kanka dan ba lallai ka samu yanda kake so ษin ba. Kamarka ma ษan manya daya fito a gidan mutunci ka wuce da ajin wadda ta gama zama gawurtacciyar karuwar turawa tun tana mitsitsiyarta”.ฦaramin murmushi MM Atik Kumo yayi, ya matso kusa da saurayin yana mai girgiza kansa. “Abokina karka damu da son nuna min abinda na gani da idona. Kai dai kawai faษamin inda zan sametan tunda har ka mata irin wannan sanin haka”.
Cikin rashin damuwa saurayin ya faษa masa cikakken adireshin gidan su Lulu ฦamshi. Sosai ya masa godiya ya shige motar da aka buษe masa fuskarsa ฦawace da murmushi......
*_Manseer M Atik Kumo_* kenan. ฦa na farko a wajen Hon. Mustapha Atik Kumo. Babban ษan siyasar nan kuma tsohon gwamnan Kano da ya sauka, a yanzu haka kuma yana ษaya daga cikin ฦดan takarar shugaban ฦasa na wannan zangon da ake kan fara campaign. Sannan shi a karan kansa ma matashin ษan kasuwa ne da kuษi ke kaษa masa gangar lokaci. MM Atik Kumo shegen kansa ne shima a wajen rashin jin magana. Dan duk wani mahaษar marasa ji na ฦดaฦดan manyar ฦasar sune ษoyayyun limamai. Manemin mata ne ฦwararren gaske, dan duk yanda mace takai da iya kame kanta sun san yanda zasu kutsa kai cikin mutuncinta har saita koma jin maganarsu fiye data iyayenta. Mahaifinsa mutumin kirki ne dattijon arziฦi abin alfahari, dan haka yake taka tsantsan akan iya shegensa ba ko'ina yake yarda ya nuna halinsa mara ฦyau ba, idan ma akace maka yana aikata wani abu makamancin hakan zaka iya ฦaryatawa dan ya iya takunsa sosai sosai....
Wannan kenan.
∆••••••∆ ★ ∆•••••∆
Tafkeken gida daya amsa sunansa gida a anguwar Nasarawa GRA drivern taxi ษin yay horn kamar yanda ta umarcesa. Leฦowa maigadin yayi, ganin ba motar gidan bace ya wani yamutse fuska zai farama mai taxi ษin wulaฦanci idonsa ya sauka a kanta. Wani irin rawa jikinsa ya fara da gudu ya koma ciki ya buษe gate ษin. Ko gama parking mai taxi ษin baiyi da ฦyau ba ta ษalle murfin motar ta fice cikin takun nan nata da ke motsa duk wata hallitar jikinta kamar tarwaษa. Abinda zai baka mamaki ko rawa ฦafarta batayi a dalilin matsiyacin takalmin ฦafarta mai shegen tsini. Duk wani ma'aikaci dake gidan da ga kallo ษaya baya sake mata na biyu zakaga ya nutsu cikin tashin hankalin ganinta. Dan halin masifarta da iya taka kowa a duk lokacin da taso buษaษษen abune ga duk wani ma'aikaci na gidan. Duk tsufarka duk ฦanฦantarka zata iya gogeka tas idan ka kuskure mata koda a ฦanฦanin abu ne, tsiranka gareta kawai kada ka shiga shirginta, idan kuma ta saka ka abu yi ฦoฦarin mata a yanda ta buฦata babu kuskure. A duk lokacin da tai tafiya daษi kowa keji a gidan, idan kuma ta dawo zakaga hankalin kowa a tashe. Satin ta biyu kenan da tafiya Abuja wajen ฦanin mahaifiyarta domin yin hutun aiki data samu acan, har addu'a suke ALLAH yasa karta dawo da wuri, sai dai kuma da alama addu'ar tasu bata amsu ba๐ dan gata ta dawo ษin a bazata.
Shigowarta a fusace katafaren falon gidan ya saka duk wanda ke ciki ษagowa ya zuba mata idanu. A tsakkiyar falon ta tsaya tana harare-harare da cika da batsewa kamar wata kububuwa.
“To aunty masifatu, lafiya kika shigo kina kumbura da ga dawowa kuma?”. ฦaya da ga cikin wanda ke a falon ya faษa cikin taษe baki. Kamar mai jira a taษata a fusace ta ce, “Shi ษan uban waye a ฦasar nan da aka aikashi ษakkoni? Miyake taฦama da shi?...”
Kusan a tare suka shiga kallon-kallo, sai dai kafin wani ya bata amsa Dattijo mutumin dake a kujerar zaman mutum ษaya da jarida a hannu ya miฦa mata hannu, “Kinga zo ki zauna naji miya faru Baby na?”.
“Daddy babu maganar zama a fara faษa min uban waye shi?, dan sai na wulaฦanta rayuwarsa a gidan nan wlhy, sai yayi dana sanin shigowa gidan nan yin aiki, idan kuma bazaku faษamin ba ALLAH duk wani ma'aikaci da ke a gidan nan yau sai ya bar gidan...”.
Sun san zata iya aikatawa, kaษan daga aikinta kuma babu abinda Daddy ษin nasu zaiyi saboda makahon son da yake mata a gidan. ฦณar budurwar da zata iya kai shekaru goma sha bakwai ce ta bata amsa da “Aunty Lu! Uncle Yousuf ne ya kawo shi, sabon driver ne ko sati biyu ma bai yiba fa, dan bayan wucewarki Abuja da kwana biyu ya kawo shi. Ni kaina baimin ba saboda naga yana da girman kan tsiya, ฦyawun fuskar tasa ne inaga ke ruษarsa bayan baida ko sisi matsiyaci Mtsowww!!.....” Ta ฦarasa maganar a hankali cikin ฦดar sassarfar harshe saboda hararar da dattijuwar matar dake gefen Dattijon nan ta watso mata. Wanda yay maganar farko ne a shigiwarta ya ce, “Wai miya miki ne? Bai je ya ษakkokin ba?”.
“Bamunje ba ta masa ihu. Shiko yay tahowarsa. Kuma na faษa mata Uncle Smart baya san ihu amma tayi” yaron nan da suke tare ya shigo yanzu ya basu amsa yana tuttura baki shi a dole yaji haushin abinda tayi. Duka ta kaima yaron ya ruga da gudu, cikin zafin rai da masifarta tace, “An masa ihun waye shi. Daddy wlhy yau idan banci uban guy ษin nan ba babu zaman lafiya a gidan nan!”.
Cikin sauri dattijon ya miฦe yana girgiza kansa, cike da damuwa ya iso gareta. Hannunta ya kama murya a tausashe yace “Kinga Baby yi haฦuri zauna kisha ruwa ki huta. Ni da kaina ma zan ษauki matakin dan bazan taษa zama da wanda zai saษa miki ba a gidan nan ko wanene shi. Har mi akai akayi wani driver banza can da zai ษata miki rai irin haka. Haba dai cool down my heartbeat ษin Daddynta yanzu zan nema Yousef ษin ma ya dakatar da shi”.
Yanzu kam babu musu ta yarda ta zauna ษin, sauran yaran duk sai suka shiga taษe baki. Hakama mamansu tsaki ta ษan ja a hankali tama miฦe tabar falon. Shiko Daddy ko'a jikinsa ya shiga lallashinta da kalaman ban haฦuri masu sanyaya zuciya gareta tamkar itace uban shine ฦดar. Ruwa ma da aka saka mai aiki kawowa da kansa ya tsiyaya a kofi ya bata a baki. Kaษan tasha ta kauda kai tana faman huci. Sake matsota yay jikinsa ya kwantar mata da kai a kafaษarsa yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa kamar wadda ta fito daga tarnaฦin yaฦin duniya, sai kuma zuwa can ta ษan ษago. “Daddy kar ka kira Uncle Yousuf ษin ban san a sallemsa yanzu, sai na rama abinda yay min. Aikin sati biyu zai min ALLAH sai na wajiga rayuwarsa sannan na masa korar da kare ma sai ya fisa daraja”.
“Babyna in dai hakan zai sa ki huce ina tare da ke”.
“Thanks you sweet Papa..”
Ta faษa tana ษan rungumesa da sumbatar hannunsa sannan ta miฦe, yatsu biyu ta ษaya masa alamar bye ta nufi ษakinta dake acan gefe part guda kamar wata mai aure, sai dai duk a cikin sashen iyayen ne. Murmushi yake da binta da kallo har ta ษacema ganinsa. Bata zauna a ฦayatacen falonta da ya gama tsaruwa ba ta nufi bedroom kai tsaye. ฦaki ne haษaษษen gaske kuma ฦato. Dan bayan ฦaton gado da wardrobe kusan rabin bango da mirror akwai set na kujeru da aka shirya tsaf tamkar falo anan ma, sosai ษakin ya haษu tare da amsa sunansa ษaki kamar na macen aure. Cikin yamutse fuska take bin dattijuwar dake ta saka turaren wuta a burners kusan kashi uku da harara, sai kuma cikin faษa da masifarta ta daka mata tsawa. “Da uwar mi kike a ษakin da baki gama min ba har na shigo....?”
“A gafarce ni Aunty (Duk da zata iya haifarta ta kafama duk wani ma'aikaci dake gidan dokar kiranta aunty komai tsufarsa). Bayi na tsaya wankewa da ฦyau har jikin bangon da kikace”.
Kakkauran tsaki ta ฦara ja da ฦarasa shiga ษakin, saman gadon da aka lailaye da bedsheet mai shegen ฦyau fari tas ta jefa wayarta, itama ta faษa ta kwanta tana mai wargaza fillos ษin da aka gama wahalar tsara mata yanda take so, har ta lumshe idanu ta buษe, a gadarance ta ce, “Kimun farfesun kifi mai yaji da kunun tsamiya, biyar nayi ki haษamin ruwan wanka. Idan kikai min kalar haukan wancan ranar wlhy bazaki gane kanki ba a hannuna fitar min anan banza ฦazamiya sai wani tsamin zufa kike”........✍️
*_Humm nama rasa abin cewa nikam๐ถ๐._*
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at๐
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan๐
09018600202
Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐
09033181070
ฦณan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ษin๐
+22799643131
VIP๐ฅ๐ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*๐ฅฐ
Zafafa๐ซถ๐ฅ
*_ALLAH ya gafartama iyayenku๐ญ๐_*
Leave a Comment