Furar Danko 2
๐๐ฒ๐ฉ๐ข๐ง๐ ๐ฒ
๐ซ ๐๐๐๐ผ๐ ๐ฟ๐ผ๐๐'๐....!!๐ซ
๐ฉ๐๐๐๐ ๐จ๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐ค๐ป
๐ช๐๐๐๐๐๐ 2️⃣
........ฦyakykyawan saurayi ne chocolate color mai cikar kamala da nutsuwa. Baida hayaniya a yanayinsa na zahiri bai kuma da fara'a sam akan fuska. A halittar jiki da cikar kamalar fuska mai nuna barazana ko maฦiyinsa dole ne ya yarda yaci wannan suna na *_Smart_*. Maimakon kallon wadda yaron yay nuni da kira Aunty Lulu sai ya ษaga shi cak ya sauke ฦasa kawai tamkar ma baiji ba. Da gudu kuwa yaron ya nufeta cikin farin ciki da ihun kwakwazo yana mata oyoyo Aunty Lu.
A hankali ta saki murmushi daya ฦara ฦawata ฦyawun fuskarta a karo na farko tana mai tsayawa cak har yaron ya ฦaraso gareta. Yana dab da zuwa gareta ta ajiye laptop ษinta a saman akwatin dake ษayan hanunta ta tarbi yaron. Dai-dai nan MM Atik Kumo da ya biyota ya ฦaraso wajen. A hankali murmushin dake a saman fuskarta ya fara ษacewa, cikin ฦanฦanin lokaci fuskarta ta koma asalin yanda take. Cikin fushi da tsananin ษacin rai ta watsa masa kallon nan nata na raini da wulaฦanci. A fusace ta furta, “Halan kai babu zuciya a ฦirjinka? Nifa a duniya na tsani wasu *_MAYUN MAZA_* wlhy”.
_(Mayun Maza!!!)_ Kalmar tai wani irin amsa kuwwar maimaita kanta a cikin kunnensa duk da bashi aka faษawa ba. A hankali ya ษago fararen idanunsa masu girma karan farko ya saukesu a kanta. Dai-dai nan itama cikin tsiwa ta nuna MM Atik Kumo da yatsanta mai ษauke da farce data ฦara a duk farautan hannuwan nata biyu da ฦafafu. ฦauke idanun nasa yay da sauri wani irin sukar baฦin ciki na tokare ฦirjinsa, a duniya ya tsani mace irinta da zata iya saka kowane irin kaya ta fita kamar yanda take, tun daga samanta har ฦasa babu suffar mace musilma bahaushiya a tare da ita. Siririn tsaki yaja yana sake tamke fuska sai dai kunnensa na garesu.
Itako da bata san yanayi ba yi take kamar zata tsole ma MM Atik Kumo ido da yatsanta data nunashi da shi. A cikin kaushin murya take faษin, “Wlhy! wlhy! idan ka sake gigin zuwa gabana a karo na uku saina wulaฦantaka a wajen nan, mafi munin wulaฦanci, na yaga maka rigar mutunci kuma, danni *_FURAR DANฦO CE, A SHEKARA ANA DAMU BA FARAU-FARAU!!._* Mtsowww ban san damuwa ok”. Fuuuu ta figi hannun yaron da ya tsaya kawai yana kallonsu tare da lap-top ษin ta tai gaba batare data ja akwatin ba.
Babu alamar gargaษin nata ya zafi MM Atik Kumo, dan wani murmushin ma ya saki da bin ฦugunta da kallo a ransa yana maimaita kalmar _(Furar danฦo a shekara ana damaki baki farau-farau)._ Wani shegen yawu ya haษiye yana lumshe idanunsa da suka wani ฦanฦance tare da lashe lips ษinsa.
A gaban motar da Uncle Smart ya ke tsaye taja birki, cikin hucin takaici tai masa kallon sama da ฦasa fuska a yatsine. “Kai kuma malam haka ake aiki a garinku? Kana kallon mutane da kaya bazakaje ka amsa ba!!?”.
Idan motar nan ta motsa to shima da ke jingine a jikinta ya motsa. Wani irin baฦin cikine ya sake turniฦe mata zuciya, “Kai sakarai kai waye da har ina maka magana zaka ษauke mun kai? kan bala'i.....!”
Da sauri yaron ya katseta da faษin, “Aunty Lu! Uncle Smart ne fa! Shi bai san ihu, muma idan zai kaimu school ca yake muyi shiru a mota, kuma Daddy ma baya masa ihu ki bari kem.....”
“Kai dalla yimun shiru. Shi ษin waye da baza'a masa ihu ba. Shashasha da shi driver mai jiran wata tayi a bashi dubu goma”.
ฦwal-ฦwal yaron yay da idanu kamar zai yi kuka. Ya kalleta ya kalli Uncle Smart ษin da ya ษauke kansa kamar ma bada shi take ba. Itako idanu rufe ta cigaba da zazzaga masa masifa kamar mai jiransa dama. Da yawan mutane hankalinsu ya fara dawowa kansu. A hankali ya raba jikinsa da jikin motar, batare da ya sake mata kallo na biyu ba bayan wanda ya mata sanda take gaban MM Atik ya buษe motar ya shige abinsa, da wani irin ฦarfi ya fisgeta yay reverse ษin daya saka taron fashewa ganin zai takasu, fuuuu ya ษace da ga wajen yay hanyar fita airport ษin baki ษaya..
Tuni wasu da abin ya birgesu suka shiga ฦyalฦyala dariya da faษin hakan da yay ya musu dai-dai. Wasu ko mamakin ฦarfin halinsa sukeyi. Duk da dai tabbas guy ษin ya haษu iya haษuwa, sai dai duk wanda ya kalli uniform ษin dake jikinsa ya san kalmar driver data kirashi da shi kam gaskiya ne. Wasu ko dariya suka shiga kwasa da yaษa mata baฦar magana musamman ganin wulaฦancin da taima MM Atik Kumo da har yanzu yana tsaye a wajen duk da body guard ษinsa da sukazo suka zagayesa shima yana kallon komai.
Lulu da gaba ษaya ta koma butum butumi da wulaฦancin driver ษin nata tuni jikinta ya fara tsuma. Numfashinta har wani irin fisga yake dan ษacin rai, da sauri MM Atik ya matso gareta, yayinda security ษinsa suka fara yima mutane nunin su tafi dan ALLAH. So yake yace wani abu amma wlhy shi tsoronta ma yake ji, bai taษa ganin masifaffiyar yarinya irinta ba, ga azabar kwarjinin tsiya kamar wata babbar mace mai shekarun dattijantaka. Da ฦyar ya iya furta, “Please calm down Babie...”
“Anฦi ai Calming down ษin kai kuma!. Har ni sakarai irin wancan guy ษin mai aikin tuฦi a gidanmu ฦarฦashin ikona zaima wannan walaฦancin? Mi yake taฦama da shi....?” Da sauri yaron nan yace, “To Aunty Lu bana faษa miki Uncle Smart baya son ihu ba ki daina masa...” Hannu ta ษaga zata fallama yaron mari MM Atik ya janyesa da faษin, “Please Babie karki aikata haka”. Idanu ta rumtse da masifar ฦarfi dan kuka ma take jin yana taso mata tsabar baฦin ciki da tuฦuฦin da zuciyarta ke mata duk da kasancewarta mutum mai shegen taurin kai akan abu.. Duk yanda MM Atik Kumo yay ฦoฦarin ganin ta shiga motarsa hakan ya gagara. Dole ya haฦura cikin bodyguard ษin sa yay mata kiran ษaya daga cikin taxi ษin dake wajen da dama su aikinsu ษaukar manyan mutanen. Nanma ฦin shiga taso yi, sai da ya dinga magiya da roฦonta sannan. Kuษin dake a aljihunsa ya ciro batare daya irga ba ya ajiye masa kusan dubu goma. Godiya sosai mai taxi ya dingayi tare da tambayar ina zai kaita. Cikin ษar-ษar ya dubeta, sai ma yaji ya kasa cewa komai ganin yanda take uban huci.. mai taxi da ya fahimci shima bai sani ba ya dubeta ta mirror. “Hajiya ina zamuje...?”
“Gidan ubanka!! Dilla malam kaja mota ban san shiga sharo ba shanu”.
“ALLAH ya baki haฦuri”.
Mai taxi ya faษa yana kunna mota........✍️
*_Kai kai wannan yarinya ta cika jaraba. Anya zan iya kuwa๐ฒ๐? Bara dai muga ko zamu iya cigaba da bin al'amarinta๐๐ค. Nasan dai Uncle Smart ya higa uku yau๐ฅฑ._*
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at๐
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐
09033181070
ฦณan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ษin๐
+22799643131
VIP๐ฅ๐ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*๐ฅฐ
Zafafa๐ซถ๐ฅ
*_ALLAH ya gafartama iyayenku๐ญ๐_*
Leave a Comment