Furar Danko 1

 


๐“๐ฒ๐ฉ๐ข๐ง๐ ๐Ÿ“ฒ

  ๐Ÿซ— ๐™๐™๐™๐˜ผ๐™ ๐˜ฟ๐˜ผ๐™‰๐™†'๐™Š.....!!๐Ÿซ—

        ๐‘ฉ๐’Š๐’๐’š๐’ ๐‘จ๐’ƒ๐’…๐’–๐’๐’ ๐’„๐’†๐Ÿค™๐Ÿป

๐‘ช๐’‰๐’‚๐’‘๐’•๐’†๐’“ 1

*ุจِุณْู…ِ ุงู„ู„َّู‡ِ ุงู„ุฑَّุญْู…َٰู†ِ ุงู„ุฑَّุญِูŠู…

_Da sลฉnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ฦ™ai._


........ฦ˜arfe uku da mintuna ashirin da biyar jirgin daya taso daga birnin tarayyar Nigeria Abuja ya sauka a *_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT_* da ke a Kanon dabo. Cikin nutsuwa duk wani passenger dake a cikinsa suka fara fitowa. Vvip section ฦ™yaฦ™ฦดฦ™yawar budurwa dake cikin ado mai tsananin ษ—aukar idanun duk wanda ya kalleta ta miฦ™e a hankali tana ษ—an wani ษ“ata fuska tamkar mai jin warin mutane. Sanye take cikin wasu shegun wando da riga da sukai tsananin fidda cikakkiyar surarta musanman ma wandon jeans ษ—in da ya kasance fari tas, an ษ—an faffasashi daga cinyarta da gwiwa har ana iya ganin kalar fatarta. Siririn veil kalar pink mai haske da yay dai-dai da kalar rigar jikinta shima data ษ—an yana a saman kanta ya matuฦ™ar ฦ™awata adon nata da fidda zagayayyar fuskarta, sai bag fara tas da adon stones pick and blue daga gani kasan mai tsada ce. Ga wani shegen takalmin mai tsananin tsini sai dai ya matuฦ™ar ษ—auki ฦ™afar tata musamman da wandon ya kasance baije ฦ™asa can sosai ba kuma yabi jikinta ya lafe luf sai ya bama siririyar sarฦ™ar ฦ™afarta da taji adon stones pink and blue damar fitowa ษ—ar. Yanda ta rufe idanunta da eyeglasses blue ya ฦ™ara saka fuskarta kwarjini da bayyana ฦ™yawunta mai sanyi, sam fuskarta babu alamar wata fara'a, sannan babu kwalliya ko ษ—igo idan ka cire ษ—an lipstick kalar pink mai shining data zizara ma laษ“ษ“anta. A kallo ษ—aya zaka ษ—auka bata san minene ko murmushi ba, sannan zaka iya kiranta da ฦ™abilar kudancin ฦ™asar, dan babu ta inda tai kammani da Hausawa ko yankin arewacin ฦ™asar musamman inda addinin Muslunci keda ฦ™arfi irin su kano. 

          A hankali taja ฦ™aramin tsaki dai-dai tana miฦ™ewa da tura wayarta cikin aljihun wandonta, headphones ษ—in kunnenta kalar pink ta gyarama zama, tare da gilashin idonta sannan ta ciro ledar chewing gum ta ษ“are ta jefa a baki tana ballama saurayin dake ta bayanta kaษ—an harara, tun ษ—azun ya dameta da kallo dan jaraba har zuge labulen da ya rabasu yayi. Bag ษ—inta ta fisga ta ษ—ora a kafaษ—a ษ—aya sannan ta ษ—auka Apple laptop ษ—in ta tana sake jan siririn tsaki ganin shima ya miฦ™e tai ficewarta cikin takunta na ฦดammata marasa jin magana..


          Yanda take taku tsinin takalmin nata na bada wani irin sautin jan magana, ga sautin madaidaicin akwatinta da take gungurawa tamkar a gajiye ya jawo hankalin mutane da yawa gareta. Caaaa idanu da yawa a kanta, wanda basu iya gani suyi shiru tuni sun fara tankawa, wasu ฦดammatan kuwa kishine ya lulluษ“esu, yayinda samari da yawa sukai mutuwar tsaye da ganin wannan ฦ™yaฦ™yฦ™yawar halitta. Ita dai daka ganta kaga cikakkiyar baฦ™ar fata haihuwar Africa sai dai ษ—abi'u da shiga duka ba namu bane. Ga wani shegen ฦ™amshi da duk wanda ke a kusa da ita kaษ—an dolene ya jisa saboda yanda ta bulbulashi kamar ba mace ba. A yanda take juya madaidaita lips ษ—inta a taunar chewing gum ษ—in bakinta kawai dole ya tada hankalin mai kallonta. Dan duk namiji mai tsantseni ya dubeta sau ษ—aya bazai sake yarda yay na biyu ba kodan tsoron ALLAH... 

       *_Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiฦ™amshi_* kenan da akafi kira da suna _Lulu ฦ™amshi_ ฦ™yaฦ™yฦ™yawar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da huษ—u a duniya. Itace ษ—iya ta uku a gidansu. Mahaifinta sananne ne da kowa yafi sani da Engineer Isma'il l. Jiฦ™amshi. Babban ษ—an kasuwa ne kuma mamallakin *_Jiฦ™amshi Motors_*. Mawaddat yarinya ce da batajin magana, gata masifaffiyar gaske ta bugawa a jarida. ฦณar gata ce shalele kuma ฦดar shagwaษ“a a gidansu musamman wajen mahaifinsu Engineer Isma'il Ibrahim Jiฦ™amshi da Kawunta Yousuf Ibrahim Jiฦ™amshi. Gatan data samu da rayuwar turai data tashi a ciki ya sata zama fanษ—ararriyar gaske. Ga rashin kunyar tsiya. Dan kowace irin shiga Lulu ฦ™amshi zata iya fita da ita waje ko zama a cikin gida in har ba Uncle ษ—in su Yusuf yana kusa ya tsawatar mata ba. Mawaddat ta samu wadataccen ilimin boko, dan a yanzu haka ita ษ—in lawyer ce mai zaman kanta, duk da dai karatun ma da ฦ™yar ta iya kammalashi saboda rashin jinta, gaba ษ—aya karatunta a ฦ™asar ฦ™etare ta yisa idan ka cire Nursery school datai a Nigeria. Sai dai a ษ“angaren ilimin addini kam fanko ce, dan ko faatiha Lulu ฦ™amshi ba lallai ta kawo maka ita dai-dai ba. Sam bata son harkar talauci, ba kuma ta son talaka. Abu ษ—aya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shine kasancewa da namiji. Ko kai ษ—an uban waye a kuษ—i ko nasabar zuri'a baka ishi Lulu ฦ™amshi kallo ba, dan ko turawan sun buga sun barta kam, hannunka ma yace zai yi gigin zuwa jikinta komai shigar rashin mutuncin da tai zata sauke maka kwando-kwandon masifarta. Ta dai yarda ta shiga club aci uban rawa ayi nishaษ—i tai gaba. Sai sirrintaccen harkar da takeyi da har yanzu babu wanda ya sani a gidansu, dan tana aikatawa ne cikin taka tsantsan da kula, shiyyasa har yanzu babu wanda ya ganota duk da an ษ—an taษ“a samun akasi tsakaninta da Uncle Yousuf dai ya kusa harbota ta kuษ“uta da ฦ™yar.


     Wannan itace Mawaddat Isma'il Jiฦ™amshi (Lulu ฦ™amshi) a taฦ™aice.


         Saurayin nan da suke tare tun daga cikin jirgin sauri yake na son cin mata, duk da yanda take takun nata cike da yauฦ™i da yanga. Wannan ita kaษ—ai ce damar data rage masa, gashi kuma tana neman kufce masa. Tunanin hakan babbar asarace a garesa ya sashi ษ—aga murya wajen faษ—in, 

       _“K! Sarauniyar mata. Son kowa ki dakata mana!!”._

    ฦuษ—aษ—ษ—iyar muryarsa da tsarin adon dake nuna shima ษ—in wani shege ne ya saka mata da yawa tsayawa cak, sai kuma suka shiga juyawa suna kallonsa. Sai dai abin mamaki ita ko nuna lamar ma tasan yanai batai ba tafiyarta take. Ganin ya cigaba da ฦ™oฦ™arin cimmata ฦดammatan da duk suka juya garesa suka shiga taษ“e baki da yatsine fuska. Ko kallo basu ishesa ba sai ฦ™oฦ™arin cimmata da yake yi dai-dai tana ฦ™oฦ™arin isa ga inda motocin ษ—aukar mutane keda hurumin tsayawa. Wani shegen kallo ta watsa masa fuskarta na sake tsukewa.

      Fuska ya marairaice yana mai haษ—e hannayensa waje guda alamar roฦ™o gareta, amma saita ja masa tsaki zata cigaba da tafiyarta. Sake shan gabanta yayi da faษ—in, “Haba mana Babie ki saurareni koda akan abu ษ—aya ne Please. Address ko phone number abeg you”.

           Cike da yauฦ™i da yanga ta furta, “A matsayinka na wa?”.

Duk da yay mamakin jin hausa a bakinta sai ya shanye, cikin murmushi ya ce, “Neighbour naki a jirgi mana beauty!. Sunana MM Atik Kumo. Mahaifina M Atik Kumo sunane da duk wanda ya kwana ya tashi a Nigeria dama ฦ™asashen Africa ya sansh.....”

     “Kai dalla can ka isheni da zance yannn-yannn!! kamar tsohuwar akorukura. Bani hanya kona wanke banzan face ษ—in nan naka zubin alakoro da mari stupid”. Ta faษ—a cikin katsesa da yarfi ta bi gefensa ta wuce. Tamkar gunkin da aka sassaฦ™a domin tarihi haka yay tsaye ฦ™iฦ™am yana kallonta, hakama duk wanda ke kusa da su sai da yay mutuwar tsaye akan abinda tayi. Dan kowa dai yasan wanene sunan MM Atik Kumo, amma yarinyar nan mai zubin yahudawa tai masa wannan yarfin. Kuma ko'a jikinta kamar yanda shima babu alamar zai ษ—auki wani mataki.....


       “Laahhh *_Uncle Smart_* ga Aunty Lulu ษ—in nan”.

   Wani ษ—an ฦ™yaฦ™yฦ™yawan yaro dake saman jibgegiyar mota baฦ™a siษ—ik ya faษ—a yana nunata. Wanda ya kira Uncle Smart dake gefensa tsaye kansa a ฦ™asa da keypad waya ฦ™irar Nokia a hanunsa ya ษ—ago a hankali tamkar mai ciwon wuya.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at๐Ÿ‘‡


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan๐Ÿ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐Ÿ‘‡

09033181070


VIP๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฏ

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*๐Ÿฅฐ


Zafafa๐Ÿซถ๐Ÿ”ฅ


*_ALLAH ya gafartama iyayenku๐Ÿ˜ญ๐Ÿ™_*

No comments

Powered by Blogger.