Fulani 4


*4*


SIRLEEM POV.


“Hajiya ina jin kamar ba zan iya jira har Nana ta kare Karatu na aureta ba....!”


Ba Hajiya kadai ba gaba daya kanensa kallonshi su kai. Da Mamaki Hajiya tace. 


“Ban gane ba?”


Ya cika ma bakinsa iska ya busar sannan ya shiga murza hannunsa kamar mai shafa mai. 


“Kawai dai bana iya jira, tana kula wasu bayan kuma kowa a Masarautar nan ya san ni zata aura, sannan ina ganin kamar yan gidansu basa son hadin nan nawa da ita idan abun ya kai wani lokacin za su iya lalata shi”


Ajiyar Hajiya ta sauke. 


“Gaskiya ne, za su iya lalatawa amman zancen tana kula wasu kar ya dame ka kai auren a haka ai zata daina kuma idan ka gani ka rika magana”


“Na ganta da Deen din nan da yake zuwa duba yaran Shattima, na je har Part din su na yi magana babu wance komai karshe ma Hajiya Karama ta taso tana fada ni wai ina takurawa Nana kamar wani ubanta”


Hajiya ta yi murmushi mai kama da dariya. 


“Kar hakan ya dame ka Sirleem kai dai ka aureta kawai komai zai wuce”


Ya kalleta cike da gajiyar jin abunda take yawan nanata masa idan yai mata complain akan Nana. 


“But Hajiya miyasa dole sai Nana? Tsakanin da Allah neman auren nan na saka kaina ne kawai saboda kin tirsasa ni amman ni kaina yarinyar nan bata kwanta min ba, ni kuma na fara gajiya gaskiya ba zan jure daukar wulakanci a gurin kowa ba na fi karfi haka, dan kawai tana yar sarauta ubanta yana sarki mahaifiyarta tana matar sarki yayanta yana dan sarki ba zan dauki wannan wulakanci ba na fi karfin wulakanci a gurin kowa ni”


Ya fada yana daga kafadunsa, Rima ta tabe baki tana ture kofin tea dake gabanta tare da kallon yayan nata. 


“Ni kaina ba son auren nan nake ba, dan dai kawai Hajiya ta matsa ne akan ayi, amman miye amfanin hada alaka da makiyi alakar ma ta aure haba dai...”


Murmushi Hajiya tai ta taso daga kujerar da take zaune ta dawo bayan Sirleem ta tsaya. 


“M2 ba haka duniya ta sanka ba? Kai a yadda kake Celebrity sai kaje ka auri wacce bata kai ba? Ga yar sarauta yar masu naira kuma kyakkyawa yarinya mai kurciya a gidanku? Ba ka lura ba? Maran manyan mutane suna auren yar manyan mutane? A yadda kake sannen a duniya ai kamata yai ace ka auri yarinyar da ta isa gaba da baya, taya za a tashi maganar da kasan zata iya saka Mai Martaba a cikin wani hali bayan gashi kwance ba lafiya? Baka tunani ya takama mu sakawa Mai Martaba da irin hallacin da yai mana? Idan mahaifiyarta matar sarki ce kai ma taka uwar matar sarki ni da Zainabun Jirgi daya ya dauko mu domin dukanmu Mai Martaba muke aure. Ke kuma Rima da kike fadar hakan ai kyautatawa ce wanda yai maka sheri sai ka saka masa da alheri, ba ni da burin da ya wuce na ga Sirleem ya auri Nana a yanzu ku karfafawa dan'uwanku guiwa ba wai ku sare ba”


Ta karasa tana kallon Rima. Sirleem ya juyo yana kallon mahaifiyarsa tasa.


“Amman Hajiya ai ba Nana ce kadai yar sarauta ko yar masu arziki ba, akwai da yawa mi yasa ba zaki bar ni naje da kaina na zabi wacce tai min ba?”


“idan zaka auro yar sarkin Makka, dan arzikinsu da Sarauta ba ka cika min burina ba matukar baka auri Nana ba, idan kuma zaka auri yar sarkin talauci na duk duniya bayan ka auri Nana to ba zai tana damuna ba, ni dai burina Nana ta zama uwargidanka”


A hankali ya aje numfashi yana kallon kanensa wanda shi ma kallonsa yake suna mamakin furucin mahaifiyar tasu. Talba ya ce. 


“Amman Hajiya miyasa?”


“Saboda ta wannan hanyar ce kawai zan iya sakawa mahaifinka da abunda yai mana”


Gaba daya kanensa mata su uku tashi sukai daga dinning, kaf a duniya basa da makiyiya irin Ammy wato uwargidan Mai Martaba, su kam ba su da dalilin na cewa ala dole sai yayansu Sirleem ya auri Nana ba bayan shi kansa ba sonta yake ba. Da kallo ta bisu tana murmushi kamin ta kalli Talba ta ce. 


“Raheen a kira min Kulu”


Tana fadar hakan ta nufi hanyar dakinta cikin wani irin taku kamar wacce ba zata mutu a saka a kasar ba, tsadadar shaddar dake jikinta sai motsi take tana wani maiko. Tashi Talba yai ya fita domin zuwa kiran Kulu kamar yadda ta Umarta, Sirleem kuma ya ciro wayarsa daga aljihu yana kallon kiran Mansura da ke shigowa wayarsa. 


Gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta fuska babu annuri kamar ba ita ce dazun ta gama dariya ba, a zahirin sarkar gold din dake wuyanta wacce ta sauko har saman kirjinta take kallo a badini kuma zuciyarta na can wani gurin tana wani tunani na dabam,  stool din madubin ta ja ta zauna tana cigaba da kallon kanta abubuwan da suka faru a baya take tunawa, ta dayan bangaren kuma tana kitsa yadda wasu abubuwa za su tafi a nan gaba. Yanayin yadda take motsa bakinta kadai ya isa ya sanar da cewar zance zuci take. 


“Shigo”


Ta fada tana dauke kai bayan an kwankwasa dakin minti uku da suka wuce. Kulu ce ta shigo dakin tana sanye da doguwar riga ta atamfa an mata irin dinkinsu na tsohu kanta lullube da mayafi, gaban Hajiya Bilki taje ta zauna tana mika mata gaisuwa. 


“Allah ya taimake ki ya kara miki lafiya, Sardauna yace kina nemana”


Tashi Hajiya tai daga kan Stool din ta koma saman shimfidarta da ke gefen gado ta kishingida tana kallon Jekadiyar ta ta. 


“Kulu wane Likita ne yake zuwa duba yaran Shattima?”


“Wallahi ban san shi ba ranki ya dade”


Wani kallo Hajiya tai mata. 


“Taya za'ayi kina cikin masarautar ace baki san masu shiga da fita a ciki ba?”


“Ranki ya dade na ga kamar bangaren Ammy ne, ni kuma na fi kula da abunda ya shafi bangarenki ne Allah kara miki lafiya”


“This is nonsense, Ammy da bangarenta ba a cikin masarautar nan suke ba?”


Hajiya ta fada a tsawace har tana tashi zaune fuska babu annuri. 


“Ciki suke Allah ya baki yawan rai, tuba nake”


Cewar Kulu tana kara noce kai kasa. 


“Kina da matsala Kulu, duk abunda ya kamata ki saka ido akai ba kya yi”


“Zan bincika ko waye shi Allah ya huci zuciyar ki ya kara miki lafiya”


“Kira min Jarma”


“An gama ranki ya dade”


Kulu ta mike da sauri ta fice daga dakin ganin yadda Hajiya ta hade rai kamar bata taba dariya ba. Ba a dauki dogon lokaci ba Jarma ya shigo dakin yana sanye da babban riga ga wani uban rawani a kansa, inda Kulu ta zauna ya zauna tana kallonta hankalinsa kwance sai dai har ya zauna ta kira shi ya amsa ta kora masa bayani bata kalleshi ba. 


“Jarma”


“Hajiya”


“Akwai wanda ke son shiga tsakanin Sirleem da Nana”


“A cikin masarautar nan yake?”


Jarma ya tambaya cike da mamaki, sai a lokacin ta kalleshi. 


“Bare ne, yaron da yake zuwa duba yaran Shattima”


Jarma yayi murmushi. 


“Doc Deen? Kar hakan ya damu Salim, wayayyace kawai irin ta yan zamani ke kinsan ai ba zan bari wani ya dauki hankalin Nana ba”


“Idan ma ka ga zai kawo mana matsala ko wasa, aka yi masa sanadi da gidan nan”


“Baki da matsala da wannan Hajiya Salim ya cigaba da neman yarinya babu abunda za a fasa”


Ta dan yi murmushi tana kallon wata doguwar Fulawa dake gabanta. 


UNCLE A A POV. 


Ya yamutsa shinkafa da waken dake gabansa a kwano yana bata fuska. 


“Anti Rabi sai ayi ta mana wake da shimkafa ba wani canji”


Anti Rabi dake aikin damawa dabbobinta kasari ta yi dariya. 


“Hmm Unclen dinsu wani lokacin iskancin ka yawa yake, wani na can be samu kamar wannan ba amman kai ka raina, da alama dai kana da kudin cin wani abinci shiyasa”


Ya shafa kansa yana yar dariya.


“Wallahi kuwa wata yar marasa sanin darajar naira na samu nai mata na yan talakawa na ci kudinta”


“Ban gane yar marasa sanin darajar naira ba”


Yayi dariya a karo na biyu sannan ya labartawa Antinsa yadda ya yaudareta.


“Amman dai Uncle din yara baka da tausayi”


“Wane irin tausayi kina ganin yarinyar nan kin san yar masu abunce ce karamar yarinyar yar secondary school ta ciro kudi sun kusan 50k ta bani 5k ya maida saura, uwayensu ne barayin Jihar mu ai”


Ya mike tsaye yana ciro kudi, 2k ya cire a ciki ya mikawa Yayar tasa sannan ya maida sauran aljihu. 


“Ni bari naje waje na ci abu mai kyau”


“Ni wannan aikin na ku yana bani mamaki kuma aiki a restaurant amman ba zaku iya cin abinci a ciki ba?”


“Ai wannan mutumen be da kirki ko ruwansa ka sha sai ka biya shi, zaka ci idan kana so amman zai cire a cikin albashinka”


“Allah dai kyauta ni kam ban taba gani ba”


“Ai ina samun wani aikin zan bar na shi Wallahi”


“Allah dai ya kawo rabo mai amfani”


Da amin ya amsa sannan ya fice daga gidan. Abun ka da unguwar mai mutane yana fita abokasa suka fara dago masa hannu. 


“Sai Sardaunan samarin Yola”


Ya nufe su yana dariya. 


“Amman na talakawa”


Ya karasa ya basu hannu suka gaisa sannan ya kara gaba ya siye alalen gwangwani gurin wata ya cika cikinsa a titi. 


Washe gari ma fa yaje restaurant din sai da ya sake tararda Nana a inda ta saba zama, wannan karon ba bachi take ba idonta biyu suna hada ido ta watsa masa harara ta kawardar da kai, a iya ganinta da yake yi a yanzu kam ya tabbatar karya take da tace yayanta ne yake cewa ta jira a nan, ya lura idan ta ga mutane sai ta boye fuskarta kar a ganta haka yai ta aikin raba ma jama'ar da suke shigowa abinci yana kallonta zuciyarsa na karantarta tana tsara masa yadda zai sake samun wasu kudin a gurinta. 

  Sai da ya koma gurin zamansa ya zauna sannan ya dauki biro da takaradar yai rubutu a kai ya dauki bottle water ya nufi inda take ya aje mata takardar a saman tebur din tare da ruwan ya koma ya zauna yana kallonta. 

Tun da ya nufota take turo baki tana harararsa har ya karaso ya aje mata ruwan da takardar ya koma, a zatonta zai ce yau ma sai ta biya kudin zaman dana bachi amman bata ji yace mata komai ba, sai dai ta lura duk abunda yake idonsa na kanta.


“Ni nace ka kawo min ruwa ne”


Ya fada tana turo baki cikin sautin da ita kadai zata iya jin kanta, na kusa da ita ko kuma mai kallonta sai dai yaga bakinta na motsi sai hararar da take watsa masa ta isa ta sanar masa cewar da shi take. Hannu ta kai ta dauki takardar ta jefar a kasa tana cigaba da turo baki ita ala dole ga shagwa6a66iya.


“Ba za a karanta ba”


Daga can inda yake zaune ya gwalo mata ido ya hade rai yana mata alamu da ta dauki takardar ta karanta ko ya daketa, sai ta make masa kafada tana murguda masa baki, sai da ya unkura kamar zai taso ta karaso inda take sannan tai saurin kai hannu ta dauki takardar ta bude. 


“Idan kina so zan iya kai ki wani guri inda zaki rika boyewa ba tare da kowa ya sani ba, amman nan ai public place ne kowa zai iya ganinki, idan kin aminta fita waje mu yi magana”


Da sauri ta dago ta kalleshi tana gyada masa kai alamar eh ta amince din, da ido yai mata alama da waje sai ta dauki school bag dinta ta nufi hanyar fita tana waigensa. Sai da tai kusan minti biyar da ita sannan Sardauna ya fakaici idon mutane ya tashi ya fita. Can gefe ya hangota ta juya baya dan kar a ganta sai boye boyen fuska take.


“Ke”


“Ni ba ke ba ni Nana Aisha”


“To ina ruwana da wani sunanki”


“To nima ina ruwana da kai”


Ita ta amsa masa ta shigar da yai mata maganar wato da fada fada, sai yai kwafa ya juya alamar zai tafi ya barta, da sauri ta riko hannun rigarsa. 


“To akwai ruwana”


Ya sake yin kwafa sannan ya kalli security camera dake gurin ya kalleta. 


“Idan kina so zan iya kai ki gidan ku sai ki boya a can idan lokacin da direban ki zai dauke ki yayi sai na dawo da ke”


“Ina zuwa”


Ta fada kai tsaye cike da jindadi, kallonta ya tsaya yi a ransa yana ayyana cewar idan shi barawo ne sai ya sace ta salon alon.


“To ai zamu aro babur da zamu je can unguwar”


“To aro”


“Zaki hau?”


Ya tambaya da mamaki dan be dauka zata yarda ba. 


“Eh”


“To ai kudi ake biya kamin a bamu aron babur din”


“Nawa?”


Tunani ya tsaya yi kamin ya ce. 


“2k kuma a can gidan da zaki zauna sai kin biya kudin zama”


Ta dan bata fuska. 


“Nawa?”


“3k”


“Toh, ai dai ba zaka sace ni ba ko?”


“Eh shekararki nawa?”


“16”


“Amman dai ke wawuya ce”


Ya fada yana dariya a ransa sannan ya juya ta nufi cikin restaurant din, abokinsa Mu'az yai ma magana ya karbi makulin mashin dinsa sannan ya fito ya same ta a inda ya barta.


“Ki fita can titi sai na zo na dauke ki”


Ba musu ta kama hanya a ranta tana jin zafin wawuyar daya kira ta dazun, karasa yai gurin da suke aje abun hawan a gurin ya bude mashin din sannan yasa masa key yai tashi mashin din sannan ya fara tukawa ya fito da shi bakin titi can ya hangota ta boya a kusa da wani shago, karasa yai gurim ya faka mata ta hau yana fara tafiya ta rirrike shi gam ta boye fuskarta a bayansa, kusan sai ta rantse a rayuwarta bata taba hawan achaba ba, iyakarta keke shi ma tana yin wayo Ammy ta hana ta hawa saboda tana mace. 


“Ke dallah sake ni kin wani rike ni kamar yar iska haka zan shiga da ke a unguwar mu kina tabani, ni ba dan iska ba ne ba a saba ganina da mace ba balle kuma ta rike ni”


“To ni ba tsoro nake ji ba ko kuma ni aka ce masa yar iska ce, ni yar iska ce kai ne dai dan iska mai sato yarinyar mutane kaje ka kaita wani guri ta boya”


Ta fada tana turo baki har lokacin bata yarda ta dago kanta ba. Tafiyar ba tai nisa ba ya faka mashin din gefen titi ya sauko ya fuskance.


“Ni ne ma dan iska mai sace yaran mutane? Ai ke ce stupid girl mai guduwa daga makaranta kina boya a wani guri, kuma ba zan kai ki din ba na fasa”


Ya karasa yana dangwararta da yatsansa. 


“Ai Wallahi ba zan sauka ba, zan maka ihun ka yi satar mace”


Yadda ta daddage kan mashin din kamar na gidansu tana watsa masa wani kallo ya sani sarai zata iya iya masa ihun abunda ba halinsa ba, kwadayi yaja masa bala'i, ya san ma it's risk tsayinsu a gefen hanyar dan wani wanda ya santa zai iya ganinta da shi, ba shi da wani option da ya wuce kaita gidansu din ko kuma maidata inda ya daukota. Da farko yayi kudirin maidata inda ya daukota sai dai zuciyarsa na son kudin nata da yake gani kamar na banza a dole ya daure ya cije ya cigaba da tafiyar idan ta riko shi ya buge hannunta har suka kusa isa unguwar sannan yai mata dabara da ta rike karfen mashin din ta sake shi.

Bata yarda ta dago fuskarta ba sai da ya faka mashin din kofar gidansu ya sauka sannan ita ma ta sauka tana wani kyankyamin unguwar balle kuma da aka shiga cikin gida har wani dage kafa take sama sama kar ta taka kasa. 

Shi yai sallama Anti Rabi dake aikin hada kwado ta amsa masa, ita kam banda aikin bata fuska da karema gidan kallo babu abunda take. Anti Rabi ta bishi da kallo har ya shiga dakinsa Nana na biye da shi ya dauko tabarma ya shimfida mata bakin kofar Anti Rabi. 


“Zauna a nan”


Ta karewa tabarma kallo tana kyankyami. 


“Wallahi ba zan zauna ba, wannan gida duk kazanta ni ba na son nan”


Ya zaro ido


“Kan uban gidan na mu ne duk kazanta? Idan ba ki zauna ba zan bata miki rai”


Ya fada a tsawace amaimakon ta ji tsoro kamar yadda yaran Anti Rabi suke idan yana musu fada ita sai ta make kafada. 


“Wallahi ba zan zauna ba, gida duk datti gidan dokin mu yafi wannan”


“Zan zane ki zan miki bulala”


Ya fada yana nuna mata icen dogon yaron dake gidan, sai ta sake make kafada. 


“Wallahi ba zan zauna ba, kuma ba zan koma can ba, kuma ba zan biya kudin ba”


“Na rantse da Allah karya kika sha”


Ya fada yana buga kafa a kasa dan kudin sune damuwarsa. Anti Rabi ta tashi ta shiga dakinta jikinta na bari ta kwalowa kanen nata kira. 


“AA...”


“Tsaya nan sai na fito”


Ya fada mata bayan ya amsa kiran Anti Rabi, sannan ya nufi dakin ya cire takalminsa ya shiga cikin rada Anti Rabi ta fara masa magana har lokacin jikinta rawa yake dan tsoro ya gama kamata. 


“Ina ka dauko wannan yarinyar?”


“Ita ce wanda na baki labari jiya”


“To miyasa zaka dauko ta ka kawo nan? Kidnapped dinta zaka yi?”


“A'uzubillahi haba Anti kamar dai baki san ni ba? Ce mata zan kaita inda zata boya sai ta biya kudin”


Hannu biyu Anti Rabi ta hada tana rokonsa.


“Dan Allah dan Annabi ka rufa min asiri ka maida yar mutane, karka jamin masifa ka jawa kanta, daga ganin yarinyar nan yar manyan mutane ce, ka duba kaga irin kallo da ake mana a unguwar nan na masu rufin asiri amman ita kallon kazamai ma take mana har da cewa gidan dokinsu ya fi gidan nan kyau ka rufa min asiri ka maida ta karka sake kallonta ma kar sheidan ya sake raya maka wani abun”


“Anti Rabi.... ”


“A a bana son jin komai indai kana jin maganata ka maida yarinyar nan inda ka dauko ta dan Allah”


Juyawa yai ya fito daga dakin, sa cin karo yai da Nana tsaye a kofar dakin da alama labe tai musu. 


“Wallahi ba zan koma ba, sai direbana ya zo kuma ba zan zauna a nan ba”


Anti Rabi ta fito da sauri ta hade hannayenta ta risina har kasa tana rokonta.


“Dan Allah dan ma'aiki ki rufa mana asiri yarinyar nan ki koma inda ya dauko ki”


Ta make kafada daya lallai ita ba zata koma ba.


“Sai idan direbana ya zo”


“Haba Anti ya zaki duka kina rokon yarinya kamar wannan dan Allah tashi”


AA ya fada cike da jin haushin yadda yayar tasa ta risina tana rokon Nana, wanda hakan ba karamin dadi yai ma Nana ba domin ko a gidansu aka risina mata dadi take ji tana ganin an bata girma yadda ya kamata tun da Mai Martaba ba ma haka ake masa. Anti rabi bata bi ta kansa ba ta ce. 


“Yanzu ya kike so a yi?”


“Sai ya duka ya roke ni yadda kikai”


“Ni din? Ashe ko zaki tsufa a tsaye”

AA ya tambaya yana kallonta da mamaki ganin take kokarin zame masa kashin wuya. 


“Ba zan zauna akan wannan ba”


Ta nuna tabarma sai Anti tace. 


“Idan na dauko miki katifa na shimfida miki a waje zaki zauna?”


Tayi wani abu da kai kamar mai yanga sannan ta amsa da eh. Abun ka da mai nema cikin sauri da kuzari Anti Rabi ta dauko katifar dake kan gadonta ta aje a waje ta dauko zanin gadon data wanke ta ninke ta shimfida mata har da su filo. Sai da Nana ta karewa katifar kallo sannan ta cire takalminta ta hau ta zauna tana kara karewa gidan kallo. 

Anti Rabi ta kuma ta cigaba da hada kwadon da take cikin rashin natsuwa dan ita tsoro ma take kar wani wanda ya santa ko ya san yan gidansu ya shigo ya ganta a gidanta. 

Bayan ta gama ta zubawa AA ko da wasa batai ma Nana ta yi ba dan ta san ba zata ci ba, ita dai tana zaune tana kallon yadda AA yake aikin auna kwadon a bakinsa kana gani kasan yunwa yake ji.


“Gashi nan ba kiba sai mugun ci”


Ta fada a ransa, kamar ya san ta yi maganar sai ya juyo ya kalleta. 


“Za ki ci?”


“Allah ya tsare ni da cin ragin abincinka kazami da kai ma”


Ta fada tana dauke kai, har cikin ransa ya ji zafi ya kalli Anti sai tai masa alama da yai shiru, a iya tunanin Anti Rabi yarinyar tana neman rigima ne ayi mata wani abu taje tace an taba ta babanta yasa a dauresu ita da AA duk kuwa da kasancewar bata san waye uban nata ba.


Sai karfe daya da yan mintuna direbanta ya kirata ya fada mata cewar zai zo ya dauke ta yanzu, sannan ta tashi wanda yai daidai ta dawowar yaran Anti daga makaranta. 


“Ki ce masa ya maida ni”


Ta fada ta sigar Umarni kamar yadda take wa bayin gidansu. Anti  Rabi ta kalli AA dake aikin danna karamar touching dinsa tace. 


“A-A tashi ka kaita”


Ba musu ya mike tsaye ya saka wayar aljihu. 


“Ina kudin zaman da kika yi dana katifar duk sai kin biya”


Ta bude jakarta ta kirga kudin da za su yi 8k ya mikawa Anti.


“Gashi na zaman da nai da na katifarki, ai ba gidanshi ba ne ba katifarshi ba ce”


AA ya saki baki yana kallonta.


“To waya kawo ki gidan? Ki bani kudina malama”


Ta maida ragowar kudin. 


“Wallahi ba zan bayar ba, kai da kace min ma kai dan iska”


Anti ta zaro ido. 


“Subhanallahi AA” 


“Na rantse da Allah karya take wannan yarinyar munafuka ce”


Ya karasa yana kara dangwararta a karo na biyu bayan wanda yai mata a titi. 


“Kin gani ko haka dazun yai min a titi dan yace na taba shi na ki wai sai dai na rika taba shi idan muna kan babur din hadda cewa yai zai sace ni”


Bayan kallon Anti Babu abunda AA yake, gaba daya kunya ta gama rufe shi shi da ko budurwa be taba yi ba yau ace wai yana neman mace ta taba shi, ji yai kamar kasa ta rabi biyu ya shige ciki, Anti ta kasa cewa komai sai kalloshi take da mugun mamaki. 


“Kaje ka aje ta inda ka dauko ta”


Ta masa maganar da sigar da shi kansa ya san ba da wasa take ba. 


“To”


Ya juya sululu ya fice, Nana ta risina ta aje kudin da Anti ta ki karba saman katifar sannan tai mata sallama ta fice. Ko da ta fita har ya tashi babur din ita kawai yake jira, kamar dazun yanzun ma tana hawa ta sake rike shi sai da ya buge mata hannu sannan ta maida kan karfen baya ta boye fuskarta a bayansa. 

Tun da suka kama hanyar bata ji yace mata komai ba, a tunaninta zai mata magana ko yai mata fadan karyar da tai masa a gurin yar'uwarsa amman sai taji shiru. 


“Ni ba zan sake biyoka ba”


“Ki ga ma Uban da zai sake zuwa da ke, ko a restaurant din nan na sake ganinki sai na fadawa shugaban mu yasa an koreki”


Ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ba. 


“Ka yi hakuri ba zan sake ba”


Be ce mata komai ba har suka kusa isa, sannan ya faka gefen hanya ya sauka kan babur din ya kalleta. 


“Ba ni 5k dina, kin ga dai taimakonki nai ko? Dan Allah ki bani kudina dan Allah”


Bata ce komai ba sai kallonshi take. Hakan yasa ya koma rokonta ta sigar tausayi yana mata magiya a iya ganinsa idan ta tafi ba ta bashi kudin nan a yayi aikin banza kenan.


“Haba baiwar Allah, ki ji tausayina kin ga nan ni maraya ne ba uba ba uwa komai ni nake yi ma kaina kuma gashi ba wani aiki sai na restaurant dan Allah ki ba ni kudin kinji?”


“Ba kace ba zaka sake kawoni ba”


“Zan sake kawoki, mota ma zan aro ba babur ba kin san ya fi sirri”


Ya amsa mata da sauri. 


“Ka iya mota?”


“Eh”


“Idan kana zo zan iya maida kai direbana sai ka rika kawo ni nan kullum idan lokacin tashina yayi sai ka maida ni gida”


“Da gaske?”


Ya kara masowa kusa da ita. 


“Eh yau zan ce ma Ammy bana son driver din ta canja min wani”


“Kuma zata amince?”


“Eh”


“To kawo wayarki na saka miki number ta idan ta amince sai ki kirani”


Ta bude jakarta ta dauko iPhone yar yayi ta kunna sannan ta mika masa. 


“To sa min a nan”


Da mugun mamaki da kuma dan tsoro ya karbi wayar, how yarinya karama kamar ita ace tana rike irin wannan wayar? Lallai babanta ba karamin barawon kasa ba ne. 


“Waya saya miki wayar?”


Ya tambaya bayan ya saka mata number. 


“Ammy na ce ta siya min bata siya min ba, Ya Shattima idan na masa maganar baya sai ya ce sai na gama makaranta, Hajiya Karama ce ta siya min?”


“Wacece Hajiya Karama?”


“Yayata ce”


“Waye mahaifinki Nana?”


Ya tambaya mamaki na kara bayyana a fuskarsa, har ta bude baki ta bashi amsa sai kuma ta fasa bata son ya san asalinta gudun kar ya tona mata asiri ko kuma ya sace ta. 


“Wani ne ba shi da lafiya ma, baya son mutane idan an yi taro da yawa sai ya rika jin tsoro shiyasa baya fita muma ba kullum ake bari muna shiga ba, ance wai sammu ne wasu kuma su ce jiface amman dai Ammy tace mu daina cewa haka mu rika cewa be da lafiya kawai”


Ya maida wayar a jakarta bayan ta kashe, wannan karon kallon tsoro yake mata sai a yanzu yake fahimtar yaren da Anti Rabi take masa, wata nawa yana kokarin ganin ya canja wayar hannunsa ya siye ko ta 50k amman abun ya gagara, yau sai gashi yaga karamar yarinya da wayar 500k lallai mayan kasar nan ba karamin dadin rayuwa suke ji ba, ya raya a zuciyarsa a take sai yaji ya ba kansa tausayi matuka. 


“How babur na maida ke”


Bata ce komai ba ta bude jakarta ta ciro 7k ya mika masa. 


“Gashi”


Ya kalli kudin be karba ya ce. 


“Wa yake ba ki wadannan kudin?”


“Hajiya Babba”


“Mahaifiyarki?”


“A a Step mother dinta, wani lokacin kuma Hajiya Karama ma tana ni kudi sosai idan ta samu Ya Shattima ma yana bani amman ba sosai ba, sai Ya Sirleem shi ma yana ba ni sosai, ka karba”


Ya kara mika masa, ya dade yana kallon kudin da mugun mamaki sannan ya karba yana tunanin anya ma mutum ce? Ko dai garin shegen son kudinsa ya kwaso aljana? Yanzu akwai yarinya karama mai rabon kudi haka dan bata san zafin su ba?

Ya hau babur din ita ma ta hau baya suka cigaba da tafiya, be yarda ya isa har cikin restaurant ba ya sauke ta a titi ya shiga ciki, ita kam bata ma shigo ciki ba sai ga direbanta ya zo daukarta sai kawai ta shige mota suka kama hanyar gida.


No comments

Powered by Blogger.