Duk Karfin Izzata Complete Hausa Novel


London United Kingdom


  Wasu haɗaɗun samari ne zaune  awani katafaren palo mai girman gaske,Mai ɗauke da manya manya sofa set 2,launin Brown da ratsin milk, gawasu triple staircase ɗaya ta bangaren hagu ɗaya bangaren dama ɗayan kuma a tsakiya daga gefe kuma wani haɗaɗen table ɗin chin abin chine, ga wata makekiyar Tv a gefe guda,palon yaji komai da ake buƙata dan in nache zan tsaya zayyana muku ha'ɗuwar palon nan tofa sae mukare littafin nan a palo kawae, kae dakaga wajen kasan baƙara min dukiya aka narka awajen ba,"zaune suke,shiru ba mai magana " kowa da abin dayake fuskar nan tasu kuwa tamkar an aiko musu da sakon mutuwa " gasu kyawawa sosai kamar larabawa

Farare ne sosai  dukkan su kamannin su ɗaya kallo ɗaya zaka musu kagane yan uwan juna ne amma biyu dake zaune a saman sofa mai zaman mutun 2 nan,sunfi kama da juna sosai dan kuwa kamar an tsaga kara, haka suke suna da dogon hanchi sosai, ga manya manyan ido sai dai abun mamakin kowa dakalar idansa biyu daga chikinsu dake zaune saman sofa guda kwayar idansu ash colour ne biyun dake gefe kuma idan nasu light green ne shikuma ɗayan idan sa baki ne, ga idon nasu manya manya " ga ɗan karamin red lips, ga lallausan bakin saje kwanche a guskar su, sai dai uku daga chikin su gemun su bai da tsawo sosai san nan kuma suna da gashin kai mai tsawo har baya kamar mace.

 "wani haɗaɗen saurayi ne ya sauko daga staircase ɗin tsakiya yana faɗin haba DON yabaku'shiryaba Aryan Aiman yusuf Ahmad me kuke jira

 (nikoh nache daman wayannan turawan sunajin hausane)  

ɗago ido DON yayi  "wadda shi idansa ya kasanche light green ne,yana faɗin "shirin zuwa in kuma Khalid,Akule khalid yace "shirin zuwa Nageria mana ko kun manta gobe za'a ɗaura auren hisham,mike DON yayi yana faɗin "bazanje ba nikam san nan yanufi saman stair ɗin  ban garen hagu,da sauri khalid yajuya daniyar yasha gabansa,Yusuf yamike yarike sa, a'fusache khalid Yajuyo yana faɗin "yusuf kasakeni " Yusuf ya ɗago ido shima dai idan nasa light green gasu manya manya masu kyan gaske yache "aa khalid bazan sakekaba kafasan kokabishi ba chanza magana zaiba saidaima kubata,yakamata ache idan dasabo kasaba ɗan kasan, yaya prince fa idan yayi magana to yayine baya chan zawa, shiyasa muka chanza masa suna daga prince Safras muka maidashi DON, dan in yayi maganafa  it's done angama baya chanza wa "pls yusuf ka kyaleni wlh yau kam dole DON, ya chanza magana haba dan allah ai kobazaije bikin kowaba dole yaje na hisham, saboda tare muka taso gaba ɗayan mu, dukkan mu abu ɗaya'ne chewar khalid "ɗaya daga chikin matasan dake zaune saman sofan ne yamike yache "to ni ma dai ba zuwa zanyi ba, yana gama fadin haka yajuya yanufi stair ɗin  ban garen hagu "a fusache yusuf yajuyo yana binsa da kallo yace what wae Aryan meyake damun kune "ɗaya daga chikin su'ma yasake mikewa yana faɗin to dai kunsan tsakanina da Aryan,  babu ban ban chi, idan yayi abu, nima zanyi idankuma bai yi'ba nima bazan yiba, dan tare aka haife mu kuma tare muke komai, yana kaiwa nan ya juya shima yanufi stair ɗin bangaren dama " kwashe wa da dariya Ahmad yayi, yana fadin amma Aryan da Aiman yan iska'ne wlh anafaman kashe wutar da DON yake kokari kunna'wa su kuma zasu kunna nasu. "akule yusuf yache kaikuma Ahmad menene hakan to ae wan nan ba abun dariya bane,ae ko zakuyi'wa, kowa irin wan nan rashin mutunchin tofa banda hisham, kar'kamanta fa tare muka taso, tare mukeyi duk wani abun daza muyi komai namu iri'ɗaya duk da iyayen mu ba ɗaya ba, katashi muje mushawo kan DON  tukunnan muje musamu yaya Aryan, dan shine matsalar idan yache zaije tofa Aiman mai sau'kine, dan shi duk abun da Aryan ya aika'ta shima ae'katawa zai yi "  kama hanyar tafiya khalid yayi yana faɗin wlh yau DON ya batamin rai haba dan allah " da sauri  Ahmad ya rufe'masa baki da hannun sa yache ya isa yanzu dai muje mushawo kansu dan sulhu muke nema dasu ba faɗa ba "faɗa masa dai chewar yusuf " haurawa saman stair sukayi wani  katafaren  hadadde palo suka shiga "  palan ya tsaru iya tsaruwa komai na chikinsa farine tas harta labulayen suma farare ne tas ga manya manya sofa set ɗaya gawani makekiyar plasma TV dake gefe,babu kowa a palon sae karan AC dake tayi, kai tsaye suka nufi chikin betroom ɗin,"subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangiji jama'a ninaga aljannar duniya,manya manya sofa set ne,set 1 ga wani ɗan karamin table a tsakiya,gefe guda kuwa wani katafaren gado wadda ko mutun 10 zasu iya kwan chiya a kae, daga ɓan garen hagu kuwa kofar dressing room ne,sae kofar toilet kusa da dressing room ɗin, betroom ɗin ya tsaru'ne sosai idan nache zan tsaya zayya no muku tsaru war batroom ɗin nan to zamu kwana mu wuni bamu gama ba"kwanche DON yake akan katafaren gadon'sa dake shin fiɗe da white bet shit,kwan che yake ya miƙe kafar'sa har tawuche gadon tsawo,ya chire rigar sa faffaɗar kirjin nan nasa abuɗe ga wani gashi dark black mai tsantsi kwan che a kan faffadar kirjin nasa, damtsen hannun nan nashi kuwa tamkar zasu fashe,saboda karfi, kamar wani sa'daukin yaƙi,"yana'jin shigon war su Khalid amma ko kallan inda suke baiyi ba
 yusuf ya wuche wajen courting ɗin yasa hannu ya yaye,wata kofar glass ne ya bayyana awajen daga chikin daki kana kallan me a wajen,wajen shaƙa'tawane mai dauke da runfa da kugeru awajen da wata table a tsaki yar kugerun, agefen kuwa wani dan karamin pool ne mai kama da baf ɗin wanka, yana ɗauke ta sky blue ruwa 

"DON pls katashi muna'san magana, da kai ne chewar Yusuf" shiru DON yayi  kamar baiji su ba "hayewa gadon Khalid yayi,yana faɗin  pls prince katashi mana, ko kallan inda suke DON bai yi'ba bare su sa ran zai amsa musu, "haba big bro dan allah to imma bazaka tashi ba,pls kaba mu amsa dan awan nan karan ba shiru muke san kayiba, kanaji koh chewar yusuf " DON dae bai tanka su ba "a fusace Ahmad yace look DON dan Allah kar ka che bazakaje bikin hisham ba wlh idan kayi haka baka kyauta ba,kasani hisham fa jinin mune " dogon tsaki DON yaja atakai che yace in kungama zanchen naku saiku fita kubar'min ɗaki, dan kuna damuna wlh " afusa'che Khalid yafara magana wlh bazamufita mu zakawa iskan'chi to barikaji dole kaje bikin hisham, in bahakaba sai dai kazaba ko,mu kokuma ka kasanche kai kadai "a'takaiche DON yace ae daman ni ka ɗae nafijin daɗin rayuwa  "haka kache koh, baisake che musu ko uppan ba haka sukayita surutun su har suka gaji sukamike suka fita suna fita " DON ya daukoh wata remot ya saita'ta saitin kofar dakin  ya danna remot din jikake lok lok kofar tana kulle kanta,ajiye remot ɗin yayi yajuya yana fiskantar wajen shaka tawan,  

 Su yusuf kuwa suna fita dakin, DON ɗakin, Aryan suka nufa wani ɗan corridor suka bi ɗan tafiya kaɗan sukayi suka shiga palo Aryan, komai na palan iri ɗaya ne dana DON sai dai na Aryan ash colour ne babu kowa a palo kai tsaye betroom ɗin sa suka nufa,da sallama a bakinsu suka shiga, Aryan yana zaune yana aiki a laptop shikuma Aiman na kwanche yana latsa waya " chikin ladabi da neman sulhu yusuf yafara magana wai me hakane bro,baikamata muyiwa hisham haka'ba,pls kar kuche baza kuje ba " daga Aryan har Aiman ɗin ba wan da ya tanka yusuf " akule yusuf yakuma chewa pls wai meyasa ku keyin hakane dan Allah " yusuf idan fa yaya Aryan ya yarda zaije nima wlh zan je, amma in bazai jeba takin takalmi babu inda zanje nima chewar Aiman " juyo Yusuf yayi yana kallan Aryan da ko kallan in da suke su bai'yiba  bro dan allah kar kache bazakaje ba' dan wlh ko bazakaje bikin kowa ba ya'zama dole kaje na hisham dan kuwa hisham yazama tam kar jinin mu ya'zama tamkar ɗan uwan mu,a'fusache Aryan yajuyo' yana faɗin  "kasan dai bani da yayan daya wuche DON koh to ko bikin shi ake bazan jeba " a'fusache khalid yache wai meyasa bakuda hali mai kyau ne dan allah, daurin aurefa kawai zakuje,"shiri Aryan yayi bai sake tan kasu ba yachi gaba da aikin sa " yusuf kuwa kallan Aiman yayi yace bro zo muje waje muyi magana

 palon suka fita, yusuf yayita lallaɓa Aiman har ya yarda zai bisu "kowa ya nufi ɗakin sa dan shirin tafiyar, 

shir'yawa sosai sukayi suka fito suka haɗu a babban palo,"to bari na tambayo mana Aryan sae muyi using jet nashi koh chewar yusuf ya karisa maganar yana hayewa stair ɗin yanufi dakin Aryan, a kwanche ya same sa yana latsa waya, harara Yusuf ya wunga masa kafin yache zamuyi anfani da jet naka "batare da ya kalle'sa ba yache adawo lfy "  juyawa yusuf yayi yafito, yasa mu su Khalid a palo suka jera zuwa waje motochi 4 suka ɗauke su zuwa Airport, Khalid Yusuf, suka shiga mota ɗaya Aiman Ahmad suma motar su ɗaya, saura moto chi 2 kuma sojoji yaran Yusuf ne a chiki, a jere motochin suka chera da matsakai chin gudu suka miƙi hanyar fita daga gd, da sauri security dake bakin gate suka wan gale  katafaren gate ɗin, a hankali suƙa danna han chin moto chin waje,suna fita su ka karawa motochin gudu, sosai suke sharara gudu chikin kan kanin lokachi suka isa Airport, suna isa suka tarar an gama shirya komai su ka ɗai ake jira su tashi, basu wani ɓata lokachi ba suka fito daga motochin,suka nufi jet ɗin Aryan suka shiga suka zauna ba wan da yache da ɗan uwan sa kala kamar an musu zuwa dole karfe 7 na safe jirgin nasu ya ɗaga suka lula a sararin, sama'niya sai babban birnin tarayya Abuja Nigeria

Jirgin su na sauka a Airport na Babban burnin ta'rayya, dan kara dan karan motochi masu numfashi ne sukazo ɗau kan su, wan ɗa a'kallah yawan motochin zasu kai 8 ga kuma motochin 5 na sojoji abaya " wasu jib ga jib gan sojoji guda 4 ne suka diro kasa daga samar motar su fiskar sun nan babu annuri ko kaɗan riƙe suke da manya manya Gun a hannun su, su na takawa irin takun jaruman maza,suka nufi su Yusuf, da sauri biyu suka tare bayan su biyu kuma suka tare gaba, Yusuf kuwa sae taku yake kamar wani sa dauki,har suka karisa wajen motochin,da sauri sojojin dasu gaban su suka fara buɗe musu kofar motochin, Khalid da Yusuf suka shiga mota ɗaya Aiman da Ahmad kuma suka shiga mota ɗaya,hannu sojojin suka ɗaga suka sara wa Yusuf san nan suka rufe kofar motochin,da gudu suka juya suka nufi nasu motar, sauri sauri suka motochin key, da matsakai chin gudu suka bar Airport ɗin,suka miki shin fi ɗadɗiyar titi gudu suke shararawa sosai har suka kusa chikin anguwar wuse 2 bakin wani katafaren gida na alfarman kae kaga ganin gidan kasan ya tsaru,suna karisawa bakin gate ɗin suka rage gudun motochin nasu, wani soja dake zaune kan plastic chair ne ya taso da sauri ya wan gale musu katafaren gate ɗin, kusa motochin chikin gida sukayi kai tsaye parking space suka nufa suna kashe motochin sojojin suka fito da sauri suka buɗewa su Yusuf kofar motar, a nitse suka fito,jingina da jikin motar Yusuf yayi yana bin gidan da kallo,gidan part 4 


DOWNLOAD HERE

No comments

Powered by Blogger.