Doctor Mansoor 9

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    Na

_Jiddah S Mapi_*Chapter 9*                 ~girgiza kai take tana hawaye wanda yake tafiya tare da ruwan daya jika mata fuska, karamin bakinta ya koma jawur, manyan idanunta sun kara fitowa, eyelashes nata ya jike sosai, gashin dake kwance a gaban goshinta ya kara kwanciya lub,

mutane sun taru a wurin suna tambayar meya faru? batayi magana ba ta mike ta ɗaga wandon jikinta, ɗaga gawan Ra'eefa tayi ta ɗaura a kafaɗarta ta kama hanyan gida, mutane sai kallon kallo suke abin ya basu mamaki yadda ta iya ta ɗaga ta, ɓangaren Hamida kuma bushewa zuciyarta tayi babu abinda yake kara mata karfi da zafin zuciya kamar kalman R da Ra'eefa ta ambata kafin ta mutu, a halin yanzu idan ta haɗu da mr R saita kasheshi kafin a binne Ra'eefa, bata tsaya ko ina ba sai cikin gidansu, tana zuwa ta tarar da Umma da Baba da Samha a tsaye suna cikin alhini, kwantar da gawan tayi a gabansu ta durkusa kasa tana kuka, hannunta Samha ta rike tana cewa "me ya sameta?"

da kyar ta buɗe baki tace "ta mutu"

mari Baba ya wanketa dashi ya nunata da yatsa yana cewa "aniyarki ta biki"

umma wacce jikinta yake ɓari da sauri ta duba Ra'eefa tana ganin yadda jini ya ɓata dogon rigan dake jikinta, me zan gani? Samha ce ta tayata suka shiga da gawan ciki, dubawa tayi da kyau, nanfa ta tabbatar Ra'eefa ta zubda ciki, da gudu ta fito daga ɗakin tana kiran Baba, cikin tashin hankali yace "menene?"

"malam ciki ta zubar shine sanadiyyar mutuwar ta, tayi irin mutuwar Amrah"

Samha dake tsaye taje da gudu ta shaƙe wuyan Hamida, bugu ta fara kai mata tako ina "dan yayarki ta mutu ta wannan hanyar shine zaki samin kanwata nima ta mutu ta dalilin zubar da ciki? dama tunda naga kina janta a jiki nasan ba abu me kyau bane zai biyo baya, kece kika nuna mata hanyan abortion, kece kika turata Ra'eefa batasan komai ba" 

umma ce tazo tana kwatan Hamida wacce ta tsaya kamar statue tana kallon Samha da take aikin dukanta, Baba yazo ya kwace ta ya janyota a kasa, sai tirjewa take tana basu hakuri, wani bulala babba ya ciro ya fara zabga mata tako ina, ihu take domin ba karamin zafi takeji ba, mutane sun fara taruwa a gidan domin labarin mutuwan ya zaga unguwa, kwatan Hamida akayi da kyar, jikinta ya farfashe fuskarta ya koma jaa, musamman tsinin hancinta wanda yafi ko ina zama jawur, hannu Baba ya ɗaga yace "fita daga gidannan kuma bazan taɓa yafe miki ba, dan kun saba shiyasa kika sa ƴata tayi haka, domin itama Samha a zageta? na rikeki tun lokacin da mahaifinki ya rasu amma shine sakayyan da zakimin? dama shi yasa kike janyo Ra'eefa jikinki a cikin kwanakinnan? kallon mutanen wurin yayi yana nuna ta yace "wannan itace ta nunawa ƴata hanyar abortion, ta dalilin haka ƴata ta mutu domin suna yimata gori wani lokacin kunsan yara da yaranta, kafin ta koyawa Samha na sallameta daga gidannan"

kallon umma yayi yace "idan zaki bita kuma ki bita amma bazata kara dawowa gidannan ba"

umma tana kuka tana rokonshi ya bari a gama jana'iza kafin ya yanke hukunci, fafur yaki yadda yace baison ganin Hamida koda a hanya ne, shiga ɗakinta tayi ta ɗibo abubuwa masu amfani tasa a jaka, bata ko canja kaya ba ta fito ta durkusa gabanshi tace "zan tafi Baba saide ka sani wallahi ba nice na faɗawa Ra'eefa ta zubar da ciki ba, hasalima bansan tanada ciki ba, ku gafarceni"

ball yayi da ita saida ta faɗi kasa gaban umma, da sauri umma ta ɗagata, cikin zafin rai yace "idan kika kuma taɓa wannan yarinyar zaki bar gidannan yanzu"

sakinta tayi tana ji tana gani Hamida ta fita daga gidan tana kuka, Samha tana aika mata da kalmar Allah ya isa tsakaninmu dake, umma bata bita ba saboda bazata iya tafiya bataga anyiwa Ra'eefa jana'iza ba, saida ta fita kafin aka fara shirin yimata wanka.


sanyi ake a garin hakan yasa take kare jikinta da hijabin dake lulluɓe da ita, dana ruwa ya jiƙata saida ruwan ya bushe kafin taji sanyin yana kara bin jikinta, bata bar kofar gidan ba saida aka fita da gawa, tana kuka tana kallon yadda Baba yake sharan kwalla, gefe guda tana jin ihun da umma da Samha sukeyi a cikin gida, ji tayi kirjinta yayi nauyi, a hankali ta mike ta bar wurin, hannunta rike da jakarta wanda yafita nauyi, domin ba wani auki ne da ita ba, gashi dama farin mutum yana saurin gajiya, tafiya kawai take ba tareda tasan inda zataje ba, gari har yafara yin alaman duhu, ga sanyi ga yunwa duk sun taru sunyi mata yawa, wani karkashin bishiya take ta zauna tayi tagumi tana kallon mutanen da suke wucewa, saida ta gaji kafin ta mike taci gaba da tafiya ba tareda tasan inda zataje ba, daga gefe ta jiyo anata faɗa kamar ba zata karasa wurin ba sai wani abu yace ta karasa, tana zuwa taga mutane biyu sunata cacan baki, a hankali ta karasa tana kallonsu cikin sanyi, saida suka gama kafin tafara basu hakuri hade da yimusu nasiha ne shiga jiki, a wurin suka bawa juna hakuri, kowa ya watse sai wani mutum wanda yake tsaye a jikin motarshi yana kallon Hamida, murmushi tayi zata wuce yace "ƴata" 

jikinta ne yayi sanyi sosai rabonta da jin wannan kalman tun Abbanta yana raye, a hankali ta juyo tace "na'am ina wuni?"


"lafiya kalau, ina zakije?

shiru tayi dan batada amsa, kare mata kallo yayi yace "naji daɗin sasanta mutane biyu da kikayi hakan ya burgeni, na daɗe ina neman mutum me hankali kamar haka, sai gashi yau Allah ya haɗani dake, idan ba zaki damu ba inaso nayi magana da iyayenki"

hawayene ya fara wanke mata fuska, girgiza kai yayi "no kada ki tsorata kada kiyi kuka, ki faɗamin duk abinda kike ciki"


cikin sanyi tace mishi iyayenta sun mutu, hamdala yayi tunda Allah yasa batada iyaye yanzu ya samu ƴa, dama yanaso ya samu ƴa mace gashi yau Allah ya bashi, buɗe mata mota yayi yace "muje" kallonshi tayi da mayan idanunta tana murza hannunta, murmushi yayi "ki yadda dani babu abinda zai faru"

tana bukatar taimako hakan yasa ta shiga suka ɗau hanya, tafiya yake ita kuma tana zaune ta haɗa kai da gwiwa tana salati a zuciyarta, baiyi magana ba har suka isa wani unguwa wanda yake shiru ne me ɗauke da manyan gini, bai tsaya ko ina ba, sai kofan wani maƙeƙen get wanda tasa Hamida damke jakanta tana kallonshi cikin tsoro, "kada ki tsorata gidana ne"

Getman ne ya buɗe musu, nan ya shiga, har yanzu bata daina furta kalmar la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimi, parking yayi da sauri aka buɗe musu marfin motar, fita tayi hannunta rike da jakanta tana karewa gidan kallo, tafiya ya fara tana binshi a baya, wani babban palour me ɗauke da kayan more rayuwa suka shiga, wuri ya nuna mata kan wani sofa yace "zauna, ya sunanki?"

a hankali tace "Hamida"

"Okay ƴata hamida ki saki jikinki dani kinji?"

girgiza kai tayi, waya ya ciro ya kira tareda cewa "muna palour"

saukowa wata kyakkyawar madaidaiciyar mata tayi, kayan jikinta kana gani kasan tana cikin kuɗi da kwanciyan hankali, da murmushi ta tari Hamida harda runguma tace "sannu da zuwa"

rungumar mutumin tayi tace "welcome Baby"

dukar da kai Hamida tayi domin taji kunyan ganinsu haka, murmushi yayi kafin yace "kaita ɗaki tayi wanka ta huta, ina Jalal?"

"yana ɗakinshi"

"okay kaita ta kimtsa"

riko hannun Hamida tayi suka fara wuce ɗakuna har suka isa wani ɗaki me kyau, nuna mata toilet tayi "shiga kiyi wanka akwai kaya a wardrobe kinji?"

giɗa kai tayi "nagode"

shiga tayi tana kallon yanayin toilet ɗin, batasan ta ina zata fara baz komai kamar da inji akayi, hawayene ya cika mata ido, da kyar ta kunna wani wuri nan ruwa ya fara malala, hannu tasa tacire da sauri tana daka tsalle, wanna ai ruwan zafi ne, kunna ɗayan wurin tayi taji ruwan sanyi yana taɓa mata hannu, da sauri ta kunna duka biyu ta tara kafin ta cire kayan jikinta ta fara goga sabulu cikin tsoro, saida ta gama wankan ta ɗaura wani karamin towel dake gefe tasa dogon hijabinta ta fito, gaban mirror taje ta shafa wani mai me kamshin gaske, turare ta fesa na jiki kafin ta buɗe drower ta ciro wani riga dogo tasa, mayafinshi ta ɗaura kafin ta murɗa handle ɗin kofar, so take ta bar ɗakin domin sanyi yayi yawa, ga ac ga fanka, fita tayi tana tafiya cikin sanɗa domin har yanzu bata gama dakewa da gidan ba, karo sukaci da wani da sauri ta buɗe baki zatayi ihu, janyota yayi ya toshe bakinta, idanunta ta fitar waje tana nishi da kyar, a kunnenta yayi magana cikin sanyi "Daddy baison ihu"

sakinta yayi yana kallon yadda take zazzare idanu alama ta tsorata ba kaɗan ba, saida ta nutsu numfashinta ya dawo daidai kafin ta ɗago tana kallonshi, da sauri ta ja da baya ganin me mashin ɗin daya ɗauketa ne ranna, cikin tsoro tace "me kakeyi anan Nameer?"

murmushin gefen baki yayi kafin yace "ba Nameer ba Jalal"

wata tambayar take shirin kara mishi da sauri ya wuce ya barta tsaye a wurin, da mamaki fal a fuskarta ta karasa inda taga matar a tsaye, sai yanzu taga kama sosai tsakaninta da Nameer or Jalal, tana isowa ta riketa tana cewa "kinyi kyau ƴata"

murmushi tayi "nagode"

dining ta kaita inda aka shirya abinci kala kala, zama tayi tana kallon yadda ya ɗauke kai yana kallon Tv, saida matar ta tafi kafin ta matso tana cewa "baka faɗamin ba ka sani a duhu"

haɗe giran sama dana ƙasa yayi alaman baison tambaya, shiru tayi ta koma ta zauna.
              "Sorry ya Ahmar za kayi lafiya insha Allah"

Kabir ne zaune a gefen Ahmar wanda yasa hannu a ciki ya rike gam yana hawaye, dama baida dauriya abu kaɗan sai kuka, hankalin Kabir ya kuma tashi da sauri ya kira number ɗin Man, kwance yake akan sofa yana kallon film ɗin shi wato series, gefe guda Noor ce da Jahad wacce take kitsa mata kanta, ɗaga wayar yayi yana magana cikin sanyi "Kabir ya?"


"ya Man? ya Ahmar fa baida lafiya tun ɗazu sai juyi yake akan bed"

da sauri ya kashe wayan ya mike, ɗakinshi ya shiga yasa wani riga da wando kanana, makullin motarshi ya ɗaga ya fito, kallonshi Jahad tayi wacce take sanye da bakin dogon riga, kanta rufe da hula me ado, sai murmushi take fuskar babu alaman fushi, cikin sanyi tace "a dawo lafiya" lumshe ido yayi domin hankalin yarinyar yana mugun tafiya dashi, muryanta ba karamin daɗi take mishi ba, musamman idan tanayi kishi addu'a, a hankali ya juyo da shanyayyen idanunshi yace "thanks"

fita yayi Noor tana kallonsu batayi magana ba, wurin motarshi yaje ya fita da mugun speed bayan getman ya buɗe mishi, bai tsaya ko ina ba sai gidansu Ahmar, yana fita ya nufi ɗakin Ahmar ɗin, ganin yadda ya mike akan bed yana danna ciki ba karamin dariya da haushi abin ya bashi ba, ƙarasawa yayi kan bed ɗin yana cewa "Kabir ya jikin nashi?"

"to gashi nan dai"

"Okay kawo ruwa"

tashi Kabir yayi ya fita zuwa palour, Laila yayiwa nuni da takai ruwa ɗakin Ahmar, jijjiga kai tayi, shi kuma ya fita yana kiran waya, mota ya ɗauka me tsadan gaske kafin ya fara driving yabar gidan.


"Kai malam ka nutsu da Allah wannan abu da kake kamar mace? ciwon ciki kawai uban wa ya hanaka aure?"

yana cikin ciwo amma maganan Man ya mugun bata mishi rai, mikewa yayi ya zauna ya jingina da jikin gadon, gashin kanshi ya hargitse idanunshi sun sauya kala sun koma jaa, cije lips yayi da kyar yace "zanci ubanka Man"

dariya ya kwashe dashi harda rike ciki yace "kowa fa yanada wannan ciwon amma ai muna danne wa, kai kuma ka kasa, be a man"

janyo pillow yayi ya jingina, allura Man ya ciro ya fara kokarin yi mishi da sauri ya runtse ido har ya gana baiyi kara ba, yasan da gangan yayi mishi dan suyi faɗa, shiyasa baiyi magana ba kuma baiki ayi mishi ba, saida ya kwanta bacci yana shirin ɗaukanshi yace "kada ka faɗawa Dady Please"

shiru kawai yayi mishi, saida yayi bacci ya rufashi da blanlet kafin ya kama hanyan fita, ganin Laila da cup na ruwa ya janyota jikinshi ya rungumeta ta baya, fuskarshi ya ɗaura akan wuyanta yana cewa "sai yanzu zaki kawo?"

jijjiga kai tayi tana turo baki, karɓan ruwan yayi ya zuba mata a kanta kafin ya fita da gudu, binshi tayi itama tana kuka, Momy dake shigowa ɗakin ta gansu, tsaki tayi kaɗan dan sun saba haka, saida suka zagaye palour bata kama shi ba kafin ya buɗe kofa yana mata gwalo ya gudu, motarshi ya shiga yana jin tausayin Laila a ranshi, text ne ya shigo wayarshi yana dubawa yaga sako kamar haka 

_barka dai Dr Man ina cikin tashin hankali shin zan iya zuwa Office naka gobe da safe?_

baiyi reply ba ya ajiye wayan, babu abinda yake ɗaga mishi hankali yanzu kamar yadda idan ya kwanta yake mafarkin jinjiraye sunzo sun zagayeshi suna kuka, abin tun yanayi kaɗan kaɗan har yafara wuce gona da iri, kawar da zancen yayi har yakoma gida, yana shiga palour yaga Jahad tana salla, saida ta idar ta ɗaga hannu sama tana addu'a, idonshi a kanta har ta gama ta juyo tana aika mishi sassanyar murmushinta, lumshe ido yayi "ina Ammi?"


"gani" ta faɗa tayi shigowa palour, hannunta rike da jaka da alama ta fita ne, zama tayi akan sofa tana kallon Man wanda yake lumshe ido kamar mejin bacci, da rarrafe ya karaso wurinta ya ɗaura kanshi a cinyarta, hannunta ya riko ya ɗaura akan suman kamshi alaman so yake ta shafa mishi, cire hannu tayi tace "Man baka girma baka ga na dawo da gajiya ba?"

ture kanshi tayi tana ciro wayarta daga jaka, kwaɓa fuska yayi kamar zaiyi kuka, idanunshi har sun cika da hawayen rigima, Jahad sai kunshe dariya take, juyowa yayi yana kallonta, a take ta haɗiye dariyan, ƙarasawa yayi wurinta babu zato ba tsammani ya faɗa cinyarta ya ɗaura kanshi, hannunta ya riko ya ɗaura a suman kanshi ya fara shafawa, cak jinin jikinta ya tsaya ya daina aiki, tureshi ta fara tana satan kallon Ammi wacce hankalinta yake kan waya, kin tashi yayi, ganin haka tasa hannu tana shafa gashin dake kwance lub a kanshi, a hankali ya fara lumshe ido, akan sallaya take hakan yasa kafarta ta fara tsami, bacci ne ya ɗaukeshi, sauke kanshi ta fara a hankali tana kallon yadda yake bacci cikin kwanciyar hankali, fuskarshi tayi kyau sajenshi ya kwanta lub, buɗe ido yayi a hankali jin tana shirin ajiyeshi a kasa, dariya tayi ganin ya farka a hankali yace "kaini ɗakina"

rikoshi tayi suka fara tafiya yana ɗan yi kamar zai faɗi domin bacci yaci jikinshi, Ammi tana binsu da kallo har suka haura sama, kwantar dashi tayi akan bed ta mike zata tafi, da sauri ya riko hannunta ya janyota saura kaɗan ta faɗa kanshi, kallon innocent face nata yayi yana cigaba da lumshe ido, a hankali ya ɗaura hannunta a kanshi cikin muryan da baya fita yace "ki shafamin ko zanyi bacci bana iya bacci 2days"

tausayi taji ya bata, a hankali ta fara shafawa tana karanta addu'a a cikin kunneshi, da haka har bacci ya ɗauke shi, zuba mishi ido tayi tana kara ganin kyaunshi wanda ya fito fili, wajen fuskarshi dake a kwance tasa hannu tana shafawa, hawaye taji yana wanke mata fuska ta rasa na menene, janye hannunta tayi, ta rufashi da blanket kafin ta juya a hankali ta fara tafiya, har ta murɗa handle ta jiyoshi Yana cewa "dan Allah ku barni ku daina banson kukan nan"

tun yanayi a hankali har ya fara da karfi yana gizge-fizge, da gudu ta karaso kan bed ɗin ta rikeshi, kwace kanshi yayi, yana damke kanshi zufa yana ƙeto mishi, mafarki yake wai jarirai sun rikeshi sun ɗagashi sama zasu wullar dashi, ganin ya firgice yana ihu tayi sauri ta rungumeshi, janyota yayi cikin blanket ɗin yana damketa da karfi, jin kukan jarirai yana yawa yasa y buɗe ido da karfi yana kallon Jahad wacce ta tsorata tana tofa mishi addu'a, da karfi ya rungumeta bayan ya dawo hayyacinshi, saida ya gama nutsuwa kafin ya saketa yana kallon cikin mayan idanunta wanda suke sashi kasala da mutuwan jiki, zame jikinta tayi daga kan bed ɗin ta zauna a baki-baki, blanket ta rufashi dashi kafin ta cigaba dayi mishi addu'a har wani baccin ya ɗaukeshi, tashi tayi ta fita daga ɗakin, ɗakinta ta shiga ta canja kaya domin turaren jikinshi ya shiga jikinta sosai, kuma batason Ammi tayi zargin wani abu.                "riga daidai gwiwa pink da wando fari buɗaɗe tasa a jikinta wanda ya fito da kyawunta, wani ribbon pink ta kame gashin kanta wanda yasha gyara na kwana biyu, ya sauko har gadon bayanta, baby hijab tasa wanda yake fari ne, ta ɗau wani jakan baya me kyau pink, takalmi canvas fari tasa sannan wayarta dake hannunta wanda yake babba ne sosai shima cover pink ne a jiki, kallon kanta tayi ta jikin babban madubin da aka ajiye mata a cikin ɗakinta, murmushi tayi tace "kinyi kyau Hamida" hawaye taji ya taru mata a idanu data tuna Amrah ce take faɗa mata wannan kalman, hakika ta samu komai na more rayuwa a gidan Alhaji Idris, da matarshi Fatima da kuma ɗansu Jalal, kamar iyayenta haka suke kula da ita, wani lokacin har sunfi sonta akan ɗan da suka haifa na cikinsu, wayarta ce ta fara kara, da sauri ta duba taga sunan ya Jalal yana yawo, share hawayen tayi domin baison yaga tana kuka, fitowa tayi tana kakalo murmushi, yana tsaye a jikin kofa ya zuba hannayenshi cikin aljihu yana sakin murmushi, da sauri ta karaso wurinshi tana cewa "sorry ya Jalal"

haɗa fuska yayi "muje"

alama ranshi ya ɓaci, murmushi tayi tana binshi a baya tasan yayi fushi domin bata fito da wuri ba, Momy tazo da gudu ta mika mata goran abinsha tace "kin manta zoɓonki"

rungume matar tayi tace "thanks Momy na, kin sabarmin da shan wannan zoɓon"

dariya tayi tace "bye" fita sukayi suka shiga cikin mota, ya fara driving, kallonshi tayi taga yaki sakin fuska, a hankali ta riko ɗayan hannunshi da baya tuki dashi, cikin sanyi tace "am sorry"

baiyi magana ba, taci gaba da murza hannunshi, saida ya sauket a school kafin yace "shikenan"

dariya tayi tace "bye ya Jalal a gaida office"

lumshe ido kawai yayi yana kallonta har ta shige ciki.


tana tafiya tana tunanin meyasa ya Jalal yake tukin adaidaita? meyasa yayi mata karyan suna? abin yana ɗaure mata kai, tafi taji a bayanta, a hankali ta juyo ji tayi yace "wow kin fara zama big girl, kin samu gidan kuɗi ba dole ki murje kiyi kyau ba?"

batayi mishi magana ba taci gaba da tafiyanta, da sauri ya shari gabanta, wucewa ta kumayi da sauri yace "an koreki a gidanku saboda kin bawa kanwarki shawara ta zubar da ciki har ta mutu? murderer"

kirjinta ne yayi zafi ranta ya ɓaci jin kalman daya jefeta dashi, murderer? wato makashiya? tayi kisan kai kenan?


komawa tayi da baya saida ta tsaya a gabanshi kafin tace "nafi karfin nayi kisa kuma ni banida alaqa da masu zubda ciki, ka daina alaqanta Ni dasu"


"Idan naki fa?"

yayi magana yana matsowa, hannu ta nunashi dashi tace "zanyi maganin ka"

tafa hannu yayi "wow yarinyar ta lashi arziki dole ta fara raina mutane, na faɗa murderer..."

da wani gigitaccen mafi ta rufe mishi baki, hannu yasa ya dafe bakinshi daya fara fitar da jini, cikin zafin nama yace "ni kika mara?"

barin wurin tayi ba tare da ta bashi amsa ba, girgiza kai yayi yabar wurin, gabanta yana faɗuwa amma bata kulashi ba bata kuma juyo ba har ta shiga class.
*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.