Doctor Mansoor 6


 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    Na

_Jiddah S Mapi_*Chapter 6*                 ~Samha ki taya Hamida girkin ta gaji yanzu, 

haɗa fuska tayi tana turo baki haɗe da gunguni itakam ba zatayi komai ba, ta yaya za'ace na tayata girki bayan nikam banson hayaki yana ɓatani"


"Oh haba? baki son hayaki ya ɓata ki? ita ɗin ba mutum bace, idan kyaun jiki ake magana kin isa kizo inda Hamida take ne, amma haka take daurewa tanayi muku girki, kune kannenta dan kunga kunada girman jiki shine zaku raina ta"

shiga ɗaki tayi bata ko kula abinda umma take faɗa, dama sun saba haka, da zaran ta fara yimusu faɗa sai su tafi su barta a wurin.


kallon Hamida tayi wacce take aikin tankaɗe gari, "ki cigaba da hakuri"

jijjiga kai kawai tayi taci gaba da aikinta, sauri take ta gama domin ta samu ta kira wannan mutumin so take ya samu number ɗinta.


ta gama girkin ta zuba a flask tayi alwala kafin ta shiga ɗaki, salla tayi bayan ta kwafe number a takadda, saida ta idar ta ɗau wayarta ƴar karama wacce ta kashe tun jiya, kunnawa tayi tasa number a wayarta saving tayi da suna mr R 2, kafin ta latsa wurin kira, ringing yakai uku bai ɗaga ba, ji tayi gabanta ya faɗi, Allah yasa ba wrong number ya bata ba ameen, kusan bugu biyar kafin taji muryanshi yana cewa "hello"

sauke ajiyan zuciya tayi "nice wacce ta karɓi number ɗinka ɗazu"

"okay Hamida?"

girgiza kai tayi kamar yana gabanta, bayan sun gaisa tace yayi saving number ɗinta, ya amsa da ba komai, ajiyewa tayi bayan ta kashe wayan, zama tayi a gefen katifa ta zubawa wuri ɗaya ido, tana jin kewa da tausayin kanta, inama itace ta mutu ba Amrah ba, batajin zata iya cigaba da rayuwa ba tareda yayarta ba, lumshe idanu tayi wasu hawaye masu ɗumi suna bin kykyyawar fuskarta, a hankali tasa hannu ta share tana cigaba da tausayin kanta.*washe gari*


Saida ta gama komai kamar yadda ta saba, kafin ta shirya cikin wani atamfa purple me ratsin baki kaɗan a jiki, bata shafa powder hakan yasa ta gyara fuskarta ta shafa lips kafin ta ɗau hijabinta wanda yake purple ne ɗan karami, jakanta na gefe ta rataya a kafaɗar ta, kallon kanta tayi a madubi kafin ta saki wani sassanyan murmushi, Allah na gode maka da ka yini kyakkyawa, turo karamin bakinta tayi tanajin kamar ta shafa lipstick me color yau, warwar tayi da manyan idanunta kafin ta buɗe jakan kayan kwalliyanta ta ciro wani lipstick me kalan purple, shafawa tayi, ta kuma kallon madubi, sakin murmushi ta kuma yi, tun bayan rasuwan yayarta bata kara shafa lipstick me color ba sai yau, kuma sai ta ganshi kamar sabon abune a wajenta, tunawa tayi da Amrah wacce take yawan shafa lipstick musamman wannan purple ɗin tana son color purple, dungune lipstick ɗin tayi tana jin wasu hawaye masu ɗumi suna sauka kan fuskarta, a hankali tasa hannun ta share tana ɗan murmushi kaɗan "kada kiyi kuka Hamida da yaddan Allah zaki samu wannan mugun, azzalumi ya cuce ni yasa na zama marainiya, ya kashemin yayata, ya Allah wanda ya zubda wannan cikin kada kasa farin ciki a cikin rayuwarta, ya ubangiji kada ka bashi haihuwa duniya da lahira, a matsayina na kanwar wacce aka cuta nake wannan rokon daga gareka ya Allah"

saida ta share hawayenta kafin ta fito waje tana kallon yadda gari yayi haske sosai, batayi sallama da kowa ba ta kama hanyan fita.


"Unty Hamida"

cak ta tsaya domin tasan wannan aikin Samha ce, idan ta kirata da Unty to babu shakka tanaso tayi mata wani abinda babu daɗi ne, cikin tafiyan rashin kunya ta karaso wurin tana kallonta from head to toe

"so nake ki wanke min kayana wanda zan fita dashi yau"

bata musa ba ta juya ta koma ciki, kayanta ta ciro daga ɗaki ta watso mata, da sauri ta ɗibo ruwa ta jiƙa omo ta fara wankewa, saida ta gama cikin sauri kafin ta ɗau jakanta zata fita, Samha cikin takun iyeyi ta karaso tana kallonta, 

"unty nikam ba Abba yace ki daina kwalliya ba?"


"wannan ba kwalliya bane haka Allah ya halicceni"


"okay haka nefa, dama an faɗa min keda yayarki kunada saurin nuna ku na Allah ne, saide hakan bai hanaku bin maza kuyi ciki kuma ku zubar ba, haka naji ance wancan ƴar iskan yayar ta..."


Shiru tayi sakamakon wani irin marin da Hamida ta ɗauke ta dashi, har saida jakan hannunta ya faɗi tsabar yadda take huci, bakinta har rawa yake tana jin wani zafi a cikin kirjinta, zata iya juran komai amma ba zata juri a zagin mata yaya ba, Amrah tamkar jinin jikinta ce saboda haka babu wanda ya isa ya zagi jikin jikinta ya zauna lafiya, da yatsa ta nunata tana huci tace "kada ki kuskura ki kara zagin yayata, idan ke baki san darajar taki ba ni na sani, sannan babu abinda ya kawo maganan adda Amrah anan, dani kike magana ni zaki zaga ba ita ba, and mind you ni ɗin yayarki ce ba kanwarki ba"

a zuciye ta fice zata bar gidan.


cikin murmushi Samha tace "oh really? ita nake zagi kece kikejin zafi, wow hakan yayi, to da batason a zageki da bata aikata hakan ba, a yadda naji ma wai itace takebin yaron har gidanshi, may be ba zata iya zama babu namiji a tare da ita ba, kuma ai ta saba zubda ciki wannan ne yayi gardama"


fita tayi daga gidan tana kuka kamar ranta zai fita, adda Amrah why? meyasa Kika zubda ciki? bani da ikon kareki domin gaskiya ta faɗa zubda ciki kikayi, ni kaɗaice na san halinki mutane basu sani ba, ga waɗanda muka fito ciki ɗaya suna zaginki ina ga mutanen waje? tasan kowa yana yimusu kallon marasa hankali marasa kunya yanzu, tana rayuwane kawai domin tana toshe kunnuwanta daga abinda mutane zasu ce, Amrah data fita nutsuwa da rashin faɗa yanzu ganin mara kunya ake mata, balle ita wacce dama ba hakuri ne da ita ba, har ta isa school zuciyarta babu daɗi, ganin tayi laiti ta fara sauri domin kada teacher ya shiga bata nan, a tsakiyar school kowa yayi shiru bakajin komai sai karatun lecturers, a hankali tasa hannu a bayanta tana taɓawa jin wani abu kamar yana tafiya, jin kamar abune da rai yasa tayi sauri tana ɗan janye hijabin gefe, kadangare cewar wata yarinya da take shirin shiga class, wani irin tsalle tayi ta kwaɓe hijabin tana ihu, ganin ta rikice shima babban kadangaren jikinta ya rikice yana neman wurin gudu, shiga cikin riganta yayi tsalle ta fara tana ihu, jakanta ta yasar jasa takalminta ta yasar, ɗankwalin kanta ya faɗi, nan ta fara kokarin ɗaga rigan, kuka take jikinta yana rawa, mutane tsoro suke kowa ya kasa karasowa wajenta, sai tsayawa sukayi daga gefe suna kallonta, 

"Ku taimaka min kadangare zai cijeni"

babu wanda yayi gigin matsowa wurinta, gaba ɗaya ta rikice ta fita daga hayyacinta, ji tayi an ɗau hijabinta ta baya an sanya mata, hannu yasa cikin riganta wanda ya janye zip ɗin da sauri ya ciro kadangaren da yake manne da bayanta, yarwa yayi a kasa tana ganin an cire ta rungume mutumin ba tare da tasa ko wanene shi ba.


shiru tayi tana sauke ajiyan zuciya hawaye yana bin fuskarta, lip nata na kasa ta cije har yanzu jikinta bai daina ɓari ba, a hankali yasa hannu a bayanta yana jin yadda take sauke ajiyan zuciya, hakika ta tsorata sosai, sun kai kusan 10mins a haka, kafin ya cire hannunshi yana cireta daga jikinshi, kara ƙankameshi tayi, bakinshi ya kai kunnenta yace "sorry ya tafi kinji?"

jijjiga kai tayi kafin ta sakeshi, dukar da kai tayi tana murza yatsun hannunta, a hankali tace "na gode"

"nima na gode"

ɗago kai tayi ta kalleshi, da sauri tayi baya ganin yadda suke kama da Kabir, murmushi yayi mata yana cewa "sannu kinji? amma ki rage tsoro shi kadangare baya cizo, kuma iya yadda kika rikice iya yadda zai rikice shima ya ruɗa ki, sannan kada ki kara cire hijabi ko mayafi a cikin mutane ki daure zuciyarki wani lokacin sai ka koyi dauriya kafin kayi dace kinji?"


jijjiga kai tayi har yanzu tana mamakin yadda suke kama da Kabir, karamin bakinta wanda lipstick ya zagaye ya ɓata mata fuska, sai rawa lips nata yake, a hankali yasa hannu a gefen bakinta inda ya ɓaci ya goge mata, sakin murmushi yayi me sanyi kafin yace "jeki class kada kiji tsoron komai, ki jajirce ki cire tsoro kada abu kaɗan ya tsorata ki kinji?"


Girgiza kai take batayi magana ba har yanzu, sai rarraba manyan idanunta take, jakanta wanda ya faɗi a gefe ya durkusa ya ɗaga, sa mata yayi a gefen hannunta, lumshe ido tayi alaman ta gode, hannu ya haɗa biyu alaman ba komai kafin ya wuce, bin bayanshi tayi da kallo, wannan yafi Kabir kyau, kuma ya fishi haske, saide komai nasu iri ɗaya ne kawai de wannan ɗin babba ne kuma matured.


tafi akayi mata a fuska, a tsorace ta juya tana kallon meshi, waro idanu yayi alaman tsoro yace "kadangare wayyo kadangare a rigana, kawo na cire miki, kodai kin samu wani ya cire miki ne?"


ganin tayi shiru tana huci yasan ranta ya ɓaci, taɓe baki yayi "tsa-tsa come on innocent beb, nasan ba zaki yadda wani yasa hannu a jikinki ba, to amma ya akayi lizard ɗin ya fita? ko dai har yanzu yana ciki ne?"


ganin tayi shiru ya kuma matsowa dab da ita yana kallonta, murmushin gefen baki yayi kafin yazo dan kunnenta "kodai nasa hannu na cire ne tunda ni nasa"


ɗago manyan idanunta wanda sukayi jajur tayi tana kallonshi, waro ido yayi shima "ki daina kallona da wannan idanun naki suna tsorani..."


"haka kike so nace ko?"

hannu yasa a gefen hijabinta yana shirin ɗagawa, damke hannunshi tayi da karfi tana huci, "kaine ka sa lizard a jikina?"

"Ofcourse nine, to dama idan bani ba wa kike zato?"


Cikin ɓacin rai ta kuma cewa "kaine kasa na cire hijabina da ɗankwalina kuma nake kokarin cire riga a cikin mutane?"


"Eh mana nine"

sakin hannunshi tayi da karfi kafin ta nunashi da yatsa, tace "kaci albarkacin wanda ya taimaka ya rufeni bayan ka buɗe ni"

juyawa tayi zata tafi da karfi yace "wani ɗan iskan ne ya rufeki?"

Hamida na da zuciya, duk yadda tayi ta danne ta kasa, saida ta juyo tana kallonshi wani irin kallo na tsana kafin tace "ɗan iskan da ubanka ya haifa kuma ya raina"


juyawa tayi ta wuce hanyan fita, class ɗin da bata shiga ba kenan, gani take idan ta shiga class ba zata iya zama ba, da kafa take tafiya tana kuka zuciyarta na ƙuna, me tayiwa Kabir da zaiyi mata haka a cikin dubban jama'a? meyasa? wani irin cin mutunci ne wannan?

wallahi saina rama"


har tuntuɓe take domin idanunta acike yake tab da hawaye hakan yasa bata ko ganin hanya, horn yake tayi mata tun daga nesa amma bata jiyoshi ba, saida yazo dab da ita kamar zai ɗauke ta kafin tayi firgigit ta koma gefe tana dafe kirji, dariya yayi kafin ya fito daga motan bayan yayi parking a gefen titi, kallonshi tayi babu shakka shine ya taimaka mata ɗazu, 

"Madam me tsoro tunanin me kikeyi haka? har kina neman ki rasa ranki?"

kokarin saita kanta tayi kafin da ɗan murmushi a fuskarta tace "wallahi so nake naje gida na canja kaya ji nake kamar har yanzu da lizard a jikina"

dariya yayi kafin yace "muje na saukeki"

girgiza kai tayi alaman A,a.


"meyasa? kina tsoron kada na yanka ki ne?"

murmushi tayi "A,a ai da ganinka kaiba me yankan kai bane"

da sauri yace "ni me yankan zuciya ne"

ɗagowa tayi ta kalleshi jin abinda ya faɗa, gira ɗaya ya ɗaga mata alaman eh.


"Muje na kaiki kada kiji komai"

babu musu ta bishi suka shiga motan, tuƙi yake a hankali yana juyawa ya kalleta, kanta a kasa tana kallo farcenta, tsoro take ji sosai amma kamar yadda ya faɗa mata dolene ta cire tsoro ta fuskanci abinda yake gabanta

"madam tsoro ya kikayi shiru"


"sunana ba madam tsoro ba sunana Hamida"

"Oh nice name Hamida, ni kuma sunana Ahmar"

gabanta ne ya faɗi jin karshen sunanshi, mr R? shima da R ya kare?"


"Kinyi shiru" ya katse ta ta hanyar magana, a hankali tace "suna mara daɗi"


murmushi yayi "kin iya wasa ashe"


"Ba wasa nake ba da gaske nake" tayi maganan sounding serious.


"to shikenan tunda sunana babu daɗi ke kam naki akwai daɗi, amma nasan zaki so sunan kannena, akwai Kabir, akwai Sabir, akwai Nameer sannan Laila da Shaira, kuma ina da ɗan uwa wanda nafi sonshi fiye da kannena, domin shi ɗin ɗan kanin mahaifina ne, ina sonshi sosai da sosai kamar na cinyeshi"


"A hankali tace shikuma ya sunanshi"

murmushi yayi "sunanshi Man"


"Umm na gidanku duk sunansu ya kare da kalman R kenan?"

jijjiga kai yayi yana murmushi "mu ɗin special ne shi yasa, shima Man yana da ƙani Jawad sai kanwar Noor"


"Ya isa"

tayi maganan ranta ya ɓaci, da mamaki ya kalleta "meyasa kuma kikace ya isa bakison labarin namu ne? mu ɗin good family ne muna son junanmu, kema zanso ki bani labarinki"


"Kaina na ciwo kayi hakuri sai next time"


"sorry"


ji tayi kamar ta fita daga motan, wani irin rashin hankali ke damunsu? bayan wannan banzan r r r ɗin har mace ma sai sun sa mata wai Noor? Allah ya wadaran wannan zuri'ar.


Bai kuma magana ba domin dama shima ba ma'abocin surutu bane, saida ya kaita kofan gida ta buɗe a ɗan zuciye zata fita "madam tsoro babu sallama"

juyo da mayan idanunta tayi tana kallonshi, "sai anjima mr taimako"

rufe motar tayi da karfi kafin ta shiga gida cikin sauri, a zaure ta zauna, haɗa kanta tayi da gwiwa ta fara raira kuka, ta rasa wani irin tunani ko mataki zata ɗauka, amma ko ba komai Kabir ya cancanci hukunci, dolene ta rama duk wani abinda yayi koda ko baida laifi ne balle kuma shine yake da laifi, runtse ido tayi tana dunkule hannu da karfi, buga jikin bangon tayi da karfi tanajin ranta kamar zai fita, hannu tasa a kanta ta danne da karfi, tunani takeso tayi amma ta rasa wanne zata fara.*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.