Doctor Mansoor 5
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*DOCTOR MANSOOR*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 5*
~Sama ya haura saida yayi wanka ya shirya kafin ya fito, hannunshi cikin aljihu yana kallonsu Ammi yace "bari naje gidan Dady"
"saika dawo"
ganin bata wani kulashi ba yaje gabanta ya zauna a kasa tareda sunkuyo da kanshi ya ɗaura a cinyarta, cikin sanyin murya yace "Ammi na kimin addu'a Allah ya shiryeni"
shafa kanshi tayi "a shirye kake Man amma ina kara yimaka addu'a ubangiji ya kara shiryar da kai, kai mutum ne me taimakon jama'a kuma ina alfahari da hakan, nasan ba zaka taɓa cin amanarmu ba, kasa tsoron Allah a lamarinka zakaji daɗi da kuma sauƙin rayuwa"
kyawawan idanunshi ya lumshe yanajin wani sanyi a ranshi, yanajin daɗin yadda Amminshi ta yadda dashi, bata shakku a kanshi ko kaɗan, hakan ba karamin farin ciki yake sashi ba, saida yayi minti 4 a haka kafin ya mike yana kallon Jawad wanda yake ta cin chocolate ɗin da ya kawowa Noor, tsaki yaja kaɗan, ranan da babu abinci yasan Jawad ba karamin rashin lafiya zaiyi ba, don akwai kyakkyawar alaqa tsakaninshi da food, fita yayi daga palour ya nufi cikin gida yana karewa gidan kallo, yau kamar da ɗan datti duk da yanzu bayan mangrib ne amma ai ya kamata gidan ya zama a share komai a kimtse, hannu ya ɗaga ya yafito wani matashi dake gefe "gani yallaɓai"
ya faɗa bayan ya durkusa kasa "tashi"
tashi yayi, "a share gidannan gobe da safe kada naga ganyen flower ko ɗaya"
"to yallaɓai an gama"
tashi yaron yayi zai tafi "am sadiq?
"na'am"
"a matsayin ka na matashi wanda yake da buri zuwa nan gaba, wannan aikin ba zai karɓeka ba, nace ka kawo takaddun secondary ɗinka zan nema maka school sannan idan ka gama zaka samu aiki, amma naga kana baya baya da karatun"
"yallaɓai ayi hakuri dama banson na takura maka ne shiyasa"
"ba komai gobe da safe ka kawomin takaddun"
durkusawa yayi har kasa yana cewa "nagode"
wurin motoci yaje ya ɗau wani fari sol wanda jikinshi yake yalƙi gashi fess, glass ɗin tinted ne, shiga yayi bayan an buɗe mishi ya fita daga gidan, bai tsaya ko ina ba sai hospital nashi, babu ma'aikata sosai domin yau weekend ne, cikin asibitin komai tsaf, da mmaakinshi yazo shiga office yaga wata budurwa a zaune ta haɗa kai da gwiwa da alama bacci ma ta fara, jikin bango Ya ɗan bubbuga kaɗan, a firgice ta tashi tana kallon gefe, jikinta yana ɓari sosai, yarinyar kyakkyawa sosai gashi bata wani bleaching domin bakace tanada hanci sosai, bakinta wanda yake ɗan karami ya fara rawa tana kallonshi da alama magana take son yi amma tsoro ya hanata, hijabin jikinta me tsayi ne pink, takalmin kafarta ya cinye sosai kamar ba budurwa ba, da mamakinshi yaga ta mike ta faɗa jikinshi tana kuka sosai, janyeta ya fara saide ta ƙankameshi taki sakinshi, ganin batada niyan sakinshi, yace "sorry daina kukan ki sakeni komai zaiyi sauki kinji?"
sai a lokacin ta ɗan sassauta rikon da tayi mishi, fuskarta yayi zufa gashin dake gaban goshinta ya kwanta lub sanadin zufan.
bai kara magana ba saida tayi kuka me isanta kafin ta sakeshi kanta kasa tana murza yatsun hannunta, buɗe office ɗin yayi sannan ya shiga, kafin yace ta shigo har ta bishi ciki, zama yayi a kujeranshi kafin ya nuna mata kujaran dake fuskantar nashi, a hankali ta zauna kanta yana kallon ƙasa.
"Kayi hakuri na fito da kai ba tareda son ka ba, abin ne ya dameni sosai, na aro wayan wata daga unguwarmu nayi maka text domin bani da waya ka gafarceni"
shiru yayi ya zuba mata ido, yarinyar ta bashi tausayi sosai, gata da nutsuwa gashi da gani tana cikin talauci ba kaɗan ba, murza yatsunta take tana cigaba da kuka.
"Sorry ta yaya akayi har kanin mahaifinki ya miki ciki?"
"mun taso cikin arziki da kuɗi sosai, mahaifina Alhaji Aminu yanada arziki, yana saida motoci wanda yake siyowa daga kasar waje, wata rana muna zaune a gefenshi yana yimana wasa a matsayin mu na yaranshi kanana, kawai aka kirashi a waya cewar motocin da akayi order gaba ɗaya sun kone a jirgi, hakan yasa zuciyarshi ta buga ya faɗi a wurin, tun daga wannan lokaci bashi ya fara hawa kanshi, babu irin abinda bama gani na cin mutuncin masu binshi bashi, yana da ƙani malam bala, shine yake taimaka mana da abinci muke ci, domin yana da aure da yara biyu, wataran sai yace a kaimu gidanshi tunda Babana baya da arzikin dubamu a yanzu kada rayuwarmu ta shiga matsala, bamu kawo komai a ranmu ba, domin Babana ya yadda dashi sosai, mun taso a gabanshi bayan karayan arziki ya samu Babanmu, ashe da manufa ya ɗauke mu nida kanwata, yayi mata fyaɗe har ta mutu ba wanda ya sani, ya ɗauki gawanta ya ajiye a bakin titi ta yadda babu wanda zaisan shine yayi hakan, Babana ya kama ciwon zuciya sanadiyyar hakan, nikuma ya fara bani kuɗi sosai yana jana yana taɓamin jiki, da fari ban yadda ba, saida yace zai kashe Babana kafin na amince ya rinƙa fasikanci dani, idan matarshi bata gida saiya aiki yaranshi yace sai nayi wasa dashi idan ba haka ba saiya kasheni, tun ina yarinya ya koyamin yadda ake wasa da jikin ɗa namiji, da haka ya fara sa yatsa a gabana har na bude, daga nan ya fara shiga jikina, kullum sai yayi hakan koda banda lafiya ne, ban fahimci inada ciki ba saida naga babu Period ɗina, ka dubeni a ƴan kananan shekaruna nasan duk wani abu na jikin ɗa namiji? ka dubeni dan Allah shekara ta fa 20 ne kawai, karatu babu abinci babu, yunwa kaɗai ta isa ta jefani cikin wannan halin, nifa macece....."
kuka ne ya kwace mata, zuciyarta yana yimata zafi sosai, dukar da kai yayi ƙasa yana ɓoye hawayen da suke shirin zubo mishi, saida ya barta tayi kuka sosai har ta sauke ajiyan zuciya kafin yace "miye ribanki idan kin zubda cikin?"
"ribana? Ribana shine mahaifina, idan yaji wannan labarin babu makawa saiya mutu domin zuciyarshi ba zata ɗauka ba, da wani ido zan kalli ɗan dana haifa nace mishi kanin mahaifina shine mahaifinshi? Dr Man dan Allah ka taimaka min dan girman Allah, zan ɓoye wannan abin koda zai zama silar mutuwata na amince ni ɗin na mutu da mahaifina ya mutu"
wani takadda ya mika mata ta karɓa ta karanta, jijjiga kai tayi tace "na amince"
biro ya mika mata, tana kuka ta karɓa tasa hannu, fita yayi daga Office ɗin, kafin ya dawo yace ta sameshi a ɗaya room, fita tayi ta sameshi, hijabin jikinta yace ta cire, "astaghfurullah ya faɗa lokacin da yayi karo da jikinta, Allah na tuba dole kanin babanki ya biki indai haka jikinki yake kuma bakya suturtawa idan kuna tare"
Allah ya bata shape ba kaɗan ba, ga skin nata ba zakace tana cikin talauci ba, domin zaka rantse tana cikin dala, tunda babanta nada kuɗi da ai dole ta zama haka.
Bayan ya zubar da cikin, ya bata kuɗaɗe masu yawa yace ta taimaki rayuwarta dashi, idan so samu ta koma gaban mahaifinta, tayi godiya ba kaɗan ba, kafin ta bar hospital ɗin, ba hanyan gida yabi ba, gidansu Ahmar yaje, babban gidane wanda yafi nasu Man ɗin girma, saide nasu yafi kyau, parking yayi a parking space bayan Getman ya buɗe mishi, unguwar shiru abinka da unguwar masu kuɗi, kowa harkan gabanshi yake babu me shiga harkan wani, manya gidaje ne a layin kamar yadda nasu Man yake, fitowa yayi yana amsa kiran wayan da ya shigo yanzu, shiga ciki yayi yana cigaba da yin wayar, a palour ya gansu sun haɗu duka suna cin abinci, ƙarasawa yayi wurin dining ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun, da kafaɗarshi ya rike wayan yana cigaba da magana da alama shida Dr kamal ne domin hiran yaki karewa, jellof na taliya da wake ya ɗiba kafin ya zuba cowslow da ketchup ya janyo gabanshi, ruwa ya ɗauke na gaban yaron dake faman murmushi domin ganin Man ɗin, kashe wayan yayi bayan sunyi sallama, ɗagowa ya kalleshi yace "Kabir sai girma fa kake kamar wanda ya girmemu kalli har ka fara shirin tara kasumba"
dariya kawai kabir yayi yana cigaba da cin abinci, kallon Ahmar wanda ya haɗe fuska yana tauna abinci kamar baison ci yayi, taɓe fuska yayi "Bro Ahmar lafiya ka wani haɗa fuska haka?"
dama halinsu ɗaya da man shiyasa suke shiri sosai, basu fiye dariya ba saide idan tare suke, ga kuma rashin magana musamman Ahmar, hararan Man yayi ganin yadda yake shirin nuna baima san abinda yamishi ba, a hankali Man ya ɗan mike bakinshi ya kai saitin kunnenshi ta yadda babu me jinsu yace "aure fa kake so kowa ya sani a gidannan gara ka saki fuska ma"
Komawa yayi ya zauna yana cigaba da aika abincin cikinshi, wata kyakkyawar yarinya ce me kimanin shekara 19 ta sakko tana latsa waya, tasa riga da wando wanda ya dameta sosai, gashin kanta ta kame da ribbon gida biyu, rigan pink ne shara-shara wanda har bakin bra ɗin ta saida ya nuna, ribbon ɗin data kama kanta shima pink ne, wandon kuma baki, farace sol ga jikinta yana glowing kallon Man tayi tana murmushi, a hankali ta karaso inda yake ta janyo kujera ta zauna a gefenshi, hannu yasa ya riko hannunta yana mata signal, dariya kawai tayi domin wannan tsokanan ya saba yimata tun tana yarinya, matso da kujeranshi yayi, dab da ita ya zauna har jikinsu yana gugan na juna, wayanta ya zubawa ido ganin tana chatting ya kwace yana kallon fuskarta, turo baki tayi tana kwacewa, kin bata yayi saida ta mike tana kwata, janta jikinshi yake ta hanyar ɓoyewa a bayanshi, zama tayi a cinyarshi tana kwacewa, rungumeta yayi yana dariya "bazan bada ba"
hannu ta haɗa biyu alaman roko, saida yaga ta fara hawaye kafin ya bata, tashi tayi daga jikinshi zata tafi, da sauri ya janyota yana bubbuga bayanta alaman tayi hakuri, saida ta sakko kafin ya ajiyeta akan kujeran, Kabir da Ahmar suna cin abincinsu dama sun saba hakan duk time ɗin da yazo saiya tsokaneta, gashi kuma sunfi shiri.
hannu ta ɗaga tana yiwa Kabir magana, alama tayi mishi da ina headphone ɗinshi, nuna mata aljihunshi yayi, da sauri ta mike tana son karɓa, kin bata yayi, ta koma ta zauna tana cigaba da chatting ɗinta, wannan itace Laila kanwarsu Ahmar ce ta kasance kurma ce, bata magana haka aka haifeta, saide tana jin abinda ake faɗa maidawa ne batayi, duk cikinsu babu wanda ya kaita shiri da Man sai Ahmar, yana tausayinta sosai tun tana yarinya hakan ya kulla shaƙuwa me yawa a tsakaninsu, Laila nada nakasa amma hakan bai hanata samun gata ba, tana samun kulawa sosai a wurin Dady da Momy ga kuma yayunta wanda suke sonta, tana Secondary school itada yayarta Shaira.
saida suka cinye abinci ya mike ya shiga ciki, ɗakin Ahmar ya shiga ya cire kayan jikinshi ya sanya wani pink na riga armless da wando baƙi daidai gwiwa, sam baison kayan da zai takura shi, kwanciya yayi akan maƙeƙen bed ɗin, pillow ya janyo yana tuna abinda ya faru yau a hospital, ba karamin tausayi yarinyar ta bashi ba, gata da kyau gata da shape amma wannan mugun kanin babanta shine ya zame mata matsala a rayuwa, hakika yana ganin case dayawa amma wannan yafi bashi tausayi abin yayi muni, Ahmar ne ya shigo ɗakin yana cin magani shifa tunda Man ya cewa Dady ciwon cikin dake yawan damunshi sha'awa ce shiyasa yake haɗa fuska yana kin yiwa Man ɗin dariya, amma na ƴan lokota ne, sun saba hakan yanzu kuma zasu shirya, shima Man bai kulashi ba, hasalima janyo pillow yayi ya rungume sosai yana kara dulmiya cikin duniyar tunani, pillow Ahmar ya ɗauko ya maka mishi a fuska, dariya yayi yana cewa "sorry nifa bazan fasa fadan gaskiya ba"
Ahmar yana da kyau sosai domin su Abba ma akwai kyaun fulani a tare dasu, wani lokacin suna yanayi da Man domin sajen dake fuskarsu yayi shige ɗaya, ga kuma hanci da haske wanda kusan ɗaya ne suke dashi, Ahmar sunyi karatu tare da Man shima ya karanci doctor inda yake aiki a wani hospital wanda yake general ne, saide wata shida kawai zaiyi acan daga nan saiya dawo Mansoor Hospital, saboda zaifi daɗin aiki a can, a halin yanzu saura wata uku ya gama aikinshi, shaƙuwa sosai sukayi kamar ƴan biyu haka suke, suyi faɗa su shirya, yana da kanne huɗu, Kabir, Sabir, Shaira da kuma laila, Kabir yana nan university, Sabir kuma yana kasar uganda sai Shaira da Laila wanda suke karatu anan ƙasa nigeria, Momy itace mamansu tanada kiɓa kaɗan kuma batada alaman tsufa sosai.
"Sauri take akan titi burinta ta iso gida domin jikin umma yayi zafi, bata ganin hanya batada burin daya wuce ta ganta a gida kuma a gaban mahaifiyarta a karo na uku bata son ta rasa makusantan ta, ta rasa Yayarta abar kaunar ta kuma rasa mahaifinta, bataso koda kuɗa ya taɓa mata ummanta, karo taci da me adaidaita sahu, hannu ya ɗaga yana zaginta bayan ya fito daga ciki, "horn nake miki tun ɗazu ina kika kai hankalinki?"
cikin muryanta me sanyi tace "kayi hakuri yayana bada sanina nayi hakan ba"
cikin zafi da tsawa yace "bada saninki ba kamar yaya? dubi yadda kika sani naji ciwo"
nuna mata yatsanshi yayi wanda yake fitar da jini, zaro manyan idanunta tayi kafin ta kama gefen hijabinta wanda yake kalan brown ta yaga da karfi, kamo hannunshi tayi ta ɗaure mishi tana cewa "sannu kaji?"
shiru yayi domin jikinshi yayi sanyi sosai, gata sa siffan masu masifa amma tana da sanyi haka? kallon kayan jikinta yayi da alama tana cikin damuwa sosai"
juyawa tayi zata tafi yace "tsaya na ajiyeki inda zakije"
tana bukatar hakan shiyasa batayi musu ba ta bishi, shiga napep ɗin tayi tana kallon maganin dake hannunta kayan jikinta pink ne wanda take yawan sawa, domin batada kaya, hanya suka kama bayan ta sanar mishi inda zataje, shiru babu me magana cikinsu, wayarshi kirar nokia itace ta fara kara, ɗagawa yayi ya kara a kunneshi yana cewa "Hello"
ya kai minti shida yana maimaita hello bayajin abinda suke faɗa, sai daga baya yace "eh nine Nameer ne"
manyan idanunta ta zubawa keyanshi ta cikin madubi ya kalleta har saida gabanshi ya faɗi, addu'a ya fara domin ganin yadda take aika mishi wani irin kallo, anya wannan ba aljan bace? idanunta ya bashi tsoro ba kaɗan ba, saida ya ajiye wayan yace "lafiya kanwata?" Cikin tsoro yayi maganan, da mamakinshi yaji tace "ya sunanka?"
"sunana Nameer kefa?"
ba shakka tunda ta ganshi taji bata sonshi ashe dalili shine karshen sunanshi ya kare da R, "a wani unguwa kake?"
"ni ba ɗan garinnan bane cirani nazo yi"
kallon fatar hannunshi tayi sai a lokacin taga baiyi kama da masu jan adaidaita sahu ba, "sunana Hamida zamu iya zama freinds?"
"ba komai kanwata"
wani bakin ciki taji, kamar ta shakoshi ta kashe jin yadda yace mata kanwata, bataso sam, bayan adda Amrah babu wani wanda takejin daɗi idan yace mata kanwa, tana cikin tunani har suka wuce kofar gidansu, da sauri tace "anan zaka ajiyeni"
saida ya tsaya kafin ta sauka, kallon biron gefenshi tayi tace "idan babu damuwa zaka iya bani number ɗinka?"
biron ya kalla yace "babu takadda"
da mamakinshi tace "zan iya rubutawa koda a fuskana ne"
kallonta ya kuma yi har yanzu bai gama yadda wannan mutum bace.
hannunta ta mika tace "rubutamin anan"
a tsorace ya bata biron ta fara rubutawa yana faɗa, saida ta gama tace zan kiraka idan na shiga gida nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bayyana maka gaskiya dani gaba ɗaya, tana faɗan haka ta juya ta fara tafiya cikin nutsuwa da kamun kai har ta shiga gida, jan mashin nashi yayi zuciyarshi cike da wasi-wasi.
Umma a kwance kan tabarma, da sauri ta karasa gabanta ta ɓare maganin tareda ɗibo ruwa ta bata, sha tayi tana cewa "Nagode Hamida, kin damu sosai ciwon kai ne fa kawai"
"umma bazan iya jure rashinki ba, Adda Amrah da Baba sun tafi sun barni banso kema ki tafi"
"Ki daina wannan maganan ga kannenki anan suma nasan sun sonki"
kauda kai tayi domin tasan babu so a tsakaninsu, Samha ce ta fito tana mika da alama bacci ta tashi, kallon Hamida tayi tana yamutsa fuska itama ba laifi tana da kyau saide ko rabin Hamida bata kai ba, "ina abinci?"
"yanzu zan girka"
kawai ta faɗa tana mikewa, umma kuwa kawar da kai kawai tayi, batajin daɗin abinda suke yiwa yayarsu amma batada bakin magana domin mahaifinsu zai cika ta da zagi, kumaya daki hamidan hakan yasa take yin shiru domin yin magana ma zai iya kara haifar da gaba tsakaninsu, Ra'eefa ce ta shigo, jikinta sanye da wani Atamfa wanda akayi ɗinkin fited gown, ya kamata sosai har shatin pant nata yana ɗan nunawa, kanta tayi kitso ta watso gashin waje, dama tana da gashi sosai, domin umma suka biyo, hannunta rike da katon waya tana latsawa tana cin cingum, kallon umma tayi "sannu mama ya jikin?"
"da sauki, amma wannan shigan ya dace dake a matsayin ki na musulma?"
tura baki tayi ta shige ɗaki, batason wannan wa'azin wallahi, Hamida girki ta fara tana kallon duk abinda suke yi, Allah ya sani bata ɗaukesu kanne ba a halin yanzu, domin abinda suke gwada mata a cikin gidannan.
*Biya 300 kacal domin samun cigaban littafin 08144818849*
Leave a Comment