Doctor Mansoor 4
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*DOCTOR MANSOOR*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 4*
~Rubutu ta gani anyi kamar haka
_zuwa ga ƴar uwata Hamida, nice taki Amrah, ki gafarceni nayi miki laifi domin na ɓoye miki wani sirri na rayuwata, nayi hakan ne domin nasan zaki shiga damuwa fiye dani idan kikaji wannan labarin, hakika ni Amrah na kasance mara tunani kuma mara hankali, na faɗa soyayya da wanda ba sona yake ba, nayi nayi dashi ku gaisa yaki yadda, yanayinshi yasa na fara soyayya dashi, ashe shiɗin ba ajina bane, yafi karfina nesa ba kusa ba, saide ban kawo hakan a raina ba tunda masu kuɗi da yawa sun auri talakawa, ban taɓa faɗa miki koda sunanshi ba a niyana saide nayi miki surprised na kawoshi har gabanki ki ganshi, wata rana yacemin mamanshi babu lafiya nazo na gaisheta, ni kuma da rashin tunani sai nace ba komai zanje, na sani umma da Baba sun bamu tarbiyya me kyau basu bari mu fita saida dalili, hakan yasa na saci hanya school na bishi, mukaje gidansu ina ɗan tsoro amma na tuna bashi kaɗai yake zama ba, domin haka ya faɗa min, muna zuwa gidan sai na tadda shi kaɗai ne, Unty Hamida kasa zama nayi nace ya maida ni school, haka yace sai nasha ruwa tukun, da kaina na buɗe ruwan da ya bani nasha, saida na tabbatar goran ba a buɗe yake ba kafin na sha, saide kafin na mike na fara jin marana ya rike, ji nayi kamar bani ba, hijabin jikina na cire tareda kayan jikina, bansan daga ina sha'awa yake tasomin ba, janyoshi nayi jikina na fara kissing nashi, a hankali naga yana murmushi yana shafan duk wani sassa na jikina, saida naji ya fara kokarin shiga na kafin na ɗan dawo hayyacina, da lallami ya fara bani hakuri saida ya aikata abinda babu kyau a kaina kafin na dawo hayyacina, na rasa me zan kira hakan fyaɗe ne? ko ganganci? banyi mishi magana ba kawai na maida kayana, cikin dauriya na fita daga gidan, ina komawa gida umma tayita dukana banyi magana ba domin a lokacin zafi nakeji sosai a ƙasa na, haka dai na fita a hanyanshi kullum yana zuwa kofan school namu ina ganinshi kece bakya kula dashi, kullum da facemask yake zuwa, nice kaɗai na san fuskarshi bayan ni babu kowa, da haka har na samu cikin sati biyu, ranan dana sani shine ranan da period ɗina bai zo ba, naje hospital akace cikine dani, hakan yasa bana iya haɗa ido da kowa a cikin gidanmu, ga zafi ga ciwo, na sameshi har gida nace inada ciki, sai cewa yayi ku zubar tunda babu wanda ya sani, naki yadda da hakan, saida ya faki idona ya bugamin abu a kai, kafin ya kaini ya zubar da cikin ko kuma ince suka zubar da cikin, wallahi tallahi banyi niyan ɓoye miki ba, amma kunya nakeji, kunyarki nakeji, yanzu haka ina wannan rubutun ne domin inaji a jikina ba zanyi rai ba, wannan ciwon cikin yana damu na, ga dukan umma ga ɓacin ran Baba, inaso a matsayinki na kanwata ki ɗau min fansa, idan kinaso nayi alfahari dake to ki ɗau fansar abinda aka yiwa yayarki, bazan faɗa miki Sunanshi ba, so nake ki nemo da kanki, hakan zai nunamin kina sona kuma kina tare dani koda bayan raina ne, dan Allah kada ki manta dani nasan baki da kawaye nice kaɗai kawarki, ki samo wata me nutsuwa ki zama kawa da ita kinji?, amma zan baki wani satar amsa karshen sunanshi ya kare da harafin R_
hawaye ya jiƙa wannan takaddan, babu abinda take sai aikin kuka "na sani fyade yayi miki, ba zaki taɓa yin hakan ba, ɓoye takaddan tayi a cikin kayanta daga nan ta koma cikin gida lokacin inna ta tafi, Baba ne ya tashi shima ya shiga ɗaki, kirjinshi ciwo yake sosai, umma ta zauna tayi tagumi, da haka har suka kara kwana bakwai, a ranan bakwai ne Baba ciwon kirji ya tsananta, mutane sun shigo sun gaidashi, da yamma sosai ya kira Hamida yace ta kawo mishi abinci, ɗauko mishi tayi taga yana ta kallonta, a hankali ta durkusa tace "Baba lafiya?"
jijjiga kai kawai yayi, shiru tayi dan tasan ba lafiya ba "mamana kada kiyi irin abinda ƴar uwarki tayi kinji? ta nunamin ita ɗin nitsatsiya ce ashe ba haka abin yake ba, mutanen duniya suna yimin kallon wanda bashida wayo har yarinya ta zubda ciki ban sani ba"
hawayene ya cika mata ido "tashi kije"
a hankali ta mike ta fita, umma tace taje ta siyo Omo, a hanyan ta na dawowa taga maza sun cika musu kofa, ji tayi kafafunta sun fara rawa, yadda Omo tayi sannan ta karasa tana cewa "lafiya?"
babu wanda ya iya yimata magana saida ta karasa cikin gida taji wai Baba ya rasu, zuciyarshi ta buga, a guje ta fita daga gidan saida mazan waje suka riketa wannan karon asibiti aka kaita domin buge mutane take tana kokarin fizge kanta ta gudu, saida akayi jana'izan malam Umar Arɗo da kwana uku kafin aka dawo da Hamida.
ta susuce ta fita daga hayyacinta, rayuwa ta daina yimata daɗi, yayarta babanta sun tafi a lokaci ɗaya hakan ya haifar mata da rashin cin abinci da kuma wanka sosai, tun daga lokacin Hamida ta canja ta zama kamar kazama-kazama, ko kaya bata fiye sa masu kyau ba, gashinta mai tsayi da cika wanda har gadon bayanta yake sauka shima ya dukunkune ya taru waje guda, sai umma tayi da gaske kafin take wanke mata, hankalinta ya koma kan karatu yi take ba dare na rana, bata da burin da ya wuce ta zama Barrister domin ta kwato ƴancin yayarta, so take tana karatu tana neman wannan mutumin wanda ta naɗa mishi suna Mr R, hakika duk ranan data haɗu dashi ta gama zama a wannan duniyan domin babu makawa zata kasheshi kuma tasan ba za'a barta ba itama kasheta za'ayi, babban takadda ta nemo tana rubuta duk wani suna da ya alakanci kalman R, duk lokacin da taji an kira mutum karshen sunan ya kare da R saita bishi duk inda zaije, ana haka dangi suka fara zancen umma ta auri kanin mahaifinta, da fari taki yadda saida Hamida tace hakan shine rufin asirinsu kafin ta amince domin kula da ƴarta ɗaya tilo wacce ta rage mata a duniya.
saide abin ba sauki bayan ta aureshi yana nuna soyayya sosai wa hamida, saide lokacin data haihu ƴarta Ra'eefa soyayyan duka ya koma kanta, dama bai taɓa samun haihuwa ba, tun daga lokacin da tazo duniya Hamida take ɗawainiya da ita har aka kara haifo wata Samha, tana son kannenta sosai saide bai kai rabin son da take yiwa Amrah ba, haka dai take hakuri tana kula dasu, a kwana a tashi har ta gama secondary nan aka sata a university da taimakon mai unguwa wanda yake alaqa sosai da mahaifinta lokacin da yake raye, tsana sosai kannenta suke nuna mata kamar basu haɗa uwa ba, basa sonta sai izgili da raini suke mata, bata biye musu ga mahaifinsu daya ɗarsa tsoronshi a ranta, baya mata dariya ko kaɗan ga duka idan tayi ba daidai ba, ga tsawa ko acikin mutane ɗari ne zaiyi mata faɗa yadda ya so, aiki yi take ba dare ba rana, a wuri ɗaya take samun sauki shine wurin umma, bata bari wulakanci ya hanata sa hankali akan karatunta na lowyer ba, duk lokacin da ta tuna Amrah da Baba sai taji wani karfin gwiwa, ɓangaren ta da Kabir kuwa itace ta fara taɓoshi ba tare da yasan hakan ba, target ɗin ta ne duk wani me karshen suna da R, haƙika da wanda yayi cikin da wanda ya zubar saita koya musu hankali a nan duniya, domin sun yi kisan kai, kuma hukuncin wanda ya kashe shima a kasheshi, saita gwadawa duniya cewar ita ɗin ba raguwa bace kamar yadda suke gani, Kabir yana haukanshi ne kawai tana kallonshi, baisan wani abu take nazari a tare dashi ba shiyasa take tsokanarshi ba tare da shima ya ankara da hakan ba.
"Kwance yake akan maƙeƙen Bed ɗinshi yana cin popcorn wanda aka sa mishi color blue da yellow, jikinshi sanye da armless riga me kaman vest fari kat, da dogon wandon jins fari, kanshi yasha gyara sosai da alama bai daɗe da dawowa ba, Dr man kenan "sunan da abokanshi suke kiranshi shine Man" matashin likita me tashe ga kyau ga kuma kwarjini sai kuma babban abin wato kuɗi da hutu, kafuwanshi ya daga sama bayan ya kwanta rub da ciki yana kara maida hankalinshi akan Tv inda suka kafa hotonshi a kasa wanda yasha kayan likitoci ya zuba hannu cikin aljihu yana dariya, suna bada biography ɗinshi, saida suka gama kafin sukace Allah ya saka mishi akan taimako da yake a cikin hospital nashi, inda wani mutum ya aika sakon godiya domin mansoor ya taɓa yiwa matarshi tiyata kyauta saboda basu da kuɗi, idan aka bari kuma zata iya rasa ranta, hakika mutane da yawa sun yabeshi, murmushi yayi ya ɗago wayarshi kirar Iphone 14, latsawa yayi a hankali ya nemo number ɗin Kamal.
"ɗan halak yanzu nake ganin bio ɗinka a tv"
"kanajin abinda suka faɗa? positive side ɗina suke ta faɗa babu wanda ya faɗi negative"
dariya sukayi su duka kafin kamal yace "to dama waye zai faɗa? ai duk wacce ta faɗa to ta tonawa kanta asiri babu me aurenta zasuce ta taɓa zubda ciki"
murmushin gefen baki yayi kafin ya ajiye wayan bayan ya kashe, mikewa yayi zai fita yaga wayarshi tana haske alaman kira yana shigowa, bro Ahmar ya gani yana yawo akan wayar tashi, ɗagawa yayi yana dariya kaɗan yace "ya dai?"
ta ɗayan ɓangaren tsaki akayi cikin muryan jin haushi yace "amma kai Man mugun ɗan iska ne wallahi, ina kai ina faɗawa Abba damuwa na? wallahi har kunyar fita nake, gaskiya ka gama dani wallahi"
"to ai ni gaskiya na faɗa kaga babu zancen iskanci anan"
kashe wayan yayi yana dariya kasa-kasa.
Ahmar Yayanshi ne ɗan yayan Abba wanda yake da kanne dayawa, a cikin gidan Ahmar shine babba sai kannenshi, Ahmar shine sa'an Man bayan shi sai kanne kusan biyar, suna shiri sosai domin basu bari alaqansu ta wofinta ba, duk wani sirrin man yan hannun Ahmar, hakan yasa shima Ahmar yake faɗawa Man ɗin sirrinshi, wasu lokutan a gidansu Man yake zama har sai ya gaji zai dawo gida.
a haka ya sauka kasa hannunshi da roban popcorn ɗin yana ɗaukan ɗaya-ɗaya yana ci, saida ya zauna akan sofa ya kunna tv, mbc bollywood ya sa inda ya fara kallon wani series da sukeyi امنت وان تحققت yana bin shirin sosai shiyasa baya wuce shi duk time ɗin kallo idan yayi saiya zo babban palour ya kalla, knocking akayi, daga ji yasan Jawad ne domin shine yake bubbuga kofa kamar zai ɓalla, murya kasa-kasa yace "Come in"
shigowa yayi yana nuna fuskar gajiya a tare dashi, a kamanni suna kama da Man saide Man yafishi haske da kyawun fuska, shi wannan akwai kuruciya sosai a tare dashi, hannu yasa a suman kanshi wanda yake a kwance lub kamar na yayanshi, kyaun gashi sun gado ne a wurin mahaifiyarsu, kallo ɗaya yamishi kafin ya maida hankali kan tv, yasan halin Jawad hala yunwa yakeji amma tsabar shagwaɓa shine yaketa yatsina fuska, ganin bai kulashi ba yace "ya Man yunwa"
harara ya aika mishi kafin yace "tom zo ka cini"
shiru yayi yana sosa kai, saida sukafi kusan 5mins ba wanda ya kara magana kafin ya kalleshi yace "ga abinci a dining meyasa kullum saika tambayeni kafin kaci abinci?"
"yadda kake kula dani hakan yasa nake ganin babu abinda zan iya ba tareda saninka ko yardanka ba"
jikinshi ne yayi sanyi domin a kullum kaninshi yana bashi daraja da girma hakan yake kara soyayyanshi a zuciyarshi, Noor ce ta fito hannunta rikeda babban plate an cika da kayan snacks, ajiyewa tayi a gaban Man sannan ta juya da ɗan gudunta taje wurin Jawad, zama tayi a cinyarshi tana cewa "ya Jawad meka kawomin?"
jakanshi ya buɗe ya ciro wani chocolate babba yace "gashi bakya girma Kekam tashi min a jiki naci abinci"
sauka tayi tana turo baki, zama yayi a ƙasa inda Man ke zaune a sama, snacks ɗin ya fara ci, kallon Noor yayi "bani drink"
tashi tayi ta ɗauko mishi wani cool drink, buɗewa yayi ya fara aikawa ciki babu ko jinkiri, idanu Man ya zuba mishi yana mamakin irin ci na Jawad, baya ragawa abinci ko kaɗan, wayarshi ce tayi haske alaman text ya shigo, a hankali ya buɗe yana kallo, sabon number ne hakan yasa ya ajiye a gefe ba tare da ya karanta ba, saida wani saƙon ya kara shigowa kafin ya buɗe yana kallo, number ɗaya ne ya turo sako biyu, karantawa ya fara.
_barka Dr Man dan Allah ina neman taimakonka da gaggawa, ka taimakamin kamar yadda Allah ya taimaka maka, cikine dani kuma ba da sona nayi hakan ba, a halin yanzu mahaifina yanada ciwon zuciya domin karayan arziki ya sameshi tun muna yara ƙanana, gashi yanzu kanin mahaifina shine yamin wannan cikin, na rasa ta yadda zanyi bayani ka gane, dan Allah kamar yadda kake taimakawa mutane nima ka taimaka min, nasan yau weekend ne babu aiki, amma ka taimakamin zanzo har gidanku_
da sauri ya tura mata sakon _no kada ki kuskura kizo mana gida, i will call you ki sameni a hospital bayan sallan isha_
ajiye wayar yayi yana kallon Jawad wanda har yanzu bai daina cin abincin ba, yanzu kam yasa Noor ta ɗauko mishi jellof rice Yana hadawa tare yana ci, janye plate ɗin yayi daga gabanshi, da sauri ya ɗago yana karya wuya, dan Allah ya Man ka bani naci yunwa wallahi"
"bazan bayar ba, baka koshi ne? ko cikinka baya maka nauyi ne?"
Ammi da take saukowa daga stair, tasa wani dogon riga na atamfa jikinshi duk stones ne yana sheƙi, ga fatarta data ke a dirje sai kyalli take kamar ka ɗauke ka gudu, "A,a ya zaka hanamin auta cin abinci? bashi nikam kaine baka ɗau abinci da daraja ba, bashi maza"
cikin ɓata rai da cin magani ya mika mishi, tashi yayi yabar roban popcorn ɗin, dama Ammi ce take ɗaurewa Jawad gindi ai
"eh jeka idan kaga dama kada ka ɗaga wandon ka bari ya faɗi, kaine da kunya a wurin kannenka"
tayi maganan ganin yadda wandon jikinshi yake sauke kamar zai faɗi.
*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849 a turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*
Leave a Comment