Doctor Mansoor 29

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

_Jiddah S Mapi_


*Chapter 29*                 ~ɗaki me kyau wanda yake part nashi daban, shine ɗakin da Abba ya bawa umma, Ammi sai murmushi take duk da taji zafin abinda ya faru babu daɗi ace mijinki ya kara aure ba tareda saninki ba, amma ya zama dole ta daure ko dan abinda Hamida tayi musu a rayuwa, gashi tana son yarinyar kamar ƴar da ta haifa a cikin cikinta.


Hamida bin umma tayi zuwa ɗakinta suka zauna suna hira, taki yadda tabar gefen umma gani take kamar zata kuma tafiya ta barta, umma ce tace "bani labarin abinda ya faru, ina kika samu kuɗi har haka? ya akayi kika san Alhaji?"


nan Hamida ta fara bata labarin duk abinda ya faru saide ta ɓoye mata wasu abubuwan domin tasan ran umma dolene ya ɓaci idan taji hakan.Man ya shiga damuwa jin Hamida nada aure, bashi kaɗai ba duk mutanen gidan sun shiga damuwa basu so haka ba.Zaune suke a wajen dining suna cin abinci, kan sai juya cokali kawai yake, Hamida ce ta fito tana waya cikin sakin fuska sai shagawaɓa take zubawa a cikin wayar harda karya wuya, jikinta sanye da riga da skirt buɗaɗɗe tayi kyau sosai domin kayan sky blue ne, zama tayi a kujeran dake fuskantar na Man tana cigaba da waya da alama itada mijinta ne, saida ta gama sannan ta kalli Abba tace "good morning Abba"

amsawa yayi cikin fara'a, ta gaida Ammi kafin ta gaida umma, mikewa tayi ta rungume Noor ta baya sannan tayi mata kiss a gefen kumatu tace "morning my Noor"

amsawa Noor tayi bayan ta juyo ta rungumeta, saida ta saketa kafin taje wurin Samha ta rungumeta ta baya tayi mata kiss a gefen kumatu tace "kin kwana lafiya?"

Samha cikin kewan Yayarta ta juyo ta rungumeta tace "lafiya lau Unty Hamida ina me kara baki hakuri akan abinda ya faru"

"ki daina banso, mun riga mun gama da wannan matsalar"


wurin Jawad raje wanda yayi shiru yana tunani, rungumeshi tayi tana leko da kanta ta wuyanshi, cikin tsokana tace "tunanin wa kake?"

kwaɓe fuska yayi, shifa baison ta tafi yafison ta zauna kusa dasu, hannunta ya riko wanda ta rike wuyanshi dashi cikin shagwaɓa yace "unty hamida yaushe zaki tafi?"


"saura kwana goma, yanzu Ashman yake cewa na koma nanda kwana goma"


"Ohhh yayi missing naki sosai unty hamida"

cewar Noor wacce take kai indomie bakinta, wani kallo da man ya aika mata saida yasa ta ajiye cokalin ta fara ci da hannu.


ji yayi kirjinshi yana zafi, tauna abincin da yakeji kamar maɗaci yaci gaba dayi, ji yake kamar ya kama Noor yayi mata shegen duka.


sakin Jawad tayi, ta rungumi Kabir wanda yake kallon Man yana ganin yadda yake tura abincin da kyar, saida tayi mishi kiss a gefen kumatu kafin ya juyo yana kallonta, kashe mishi ido ɗaya tayi tace "ya dai?"


ɗaukan chips yayi ya kai bakinta, karɓa tayi  ta fara tauna tana murmushi, saida ta cinye tace "karamin" ta kuma buɗe baki yasa mata, ci ta fara hannunta a wuyanshi tana girgiza kafa, sa mata yarinkayi tana tauna tana kallonshi, zama tayi a gefenshi tana bashi labarin abinda yayi mata a school sai dariya yake yana cigaba da bata chips tana tauna


"Kwan" sukaji karan faɗuwan plate daga sama zuwa kasa, kallonshi duka sukayi hadda ahmar wanda yake aikin kallon Samha har ta gagara cin abinci da kyau, cikin fushi ya mike ya bar wajen, saida ya shiga ɗakinshi ya zauna bakin sofa ya rasa meke damunshi, haka kawai yake tsananin kishin Hamida, abinda bai taɓa ji a kanta ba yau yakeji, Innalillahi gashi sai wani kyau da haske take karawa jiya da dare yana ganinta ta fito da rigan bacci a jikinta, so take ga haukatashi, ji yake kamar ya tashi yasha giya saide yayi alkawarin ba zai kara shan giya ba.


Wanka kawai yayi ya ɗaura towel a ƙugunshi ya fito, fuskarnan a murtuƙe kamar bai taɓa dariya ba, jikinshi da damshin ruwa ya nufi wardrobe ko mai bai shafa ba yasa wani riga da wando marasa nauyi sosai, farare ne daga rigan har wandon, sai agogo fari daya ɗaura, turare kawai ya fesa ya ɗau wayarshi kirar Iphone 14 pro max, da makullin mota ya fita daga ɗakin, ko kallonsu baiyi ba ya nufi hanyan fita, Abba yace "ina zaka bakaci komai ba?"


murtuƙe fuska yayi "zanje asibiti ana nemana yanzu"


"no dawo kaci abinci ko tea ne kasha"

badan yaso ba yaje wurin ya zauna yana harare-harare, umman Hamida ce ta zuba mishi tea me ƙamshi ta mika mishi cikin murmushi, amsa yayi yana kallonta, a hankali yace na gode "umma"

a hankali ya fara kurɓa yana kallon table ɗin dake gabanshi, Ahmar ya lura da abinda ke damunshi kishi ne kawai, dama yasan abokinshi kuma kaninshi da kishi.


yana shanyewa ya mike zai tafi, a hankali ta mike hannunta rike da kwanon stew wanda yake kamshi sosai, yi tayi kamar zata tafi kamar bata sani ba ta juye mishi a riga, waro ido yayi yana kallon yadda rigan jikinshi fari sol ya koma jawur, kallonta yayi ta buɗe ɗan karamin bakinta ta waro manyan idanunta waje, cikin taɓe fuska alaman bada sonta hakan ya faru ba tace "am sorry bada sanina hakan ya faru ba"


juyawa kawai yayi ba tareda ya kara kallonta ba ya kama hanyan tafiya zuwa dakinshi, umma da take kallon duk abinda aya faru ta kalli Hamida cikin ɓacin rai tace "bishi ki wanke rigan"


Ammi tace "barta mana ai bada saninta tayi ba shima baya kula ne"

a hankali ta koma gefen Ammi dan tasan umma zata iya marinta, cikin tsawa umma tace "jeki wanke rigan"

a hankali ta juya ta fara tafiya tana tura baki, saida ta isa bakin ɗakinshi tayi knocking, a hankali yace "yes"

turo kofar tayi ta shigo, da sauri ta juya baya ganinshi babu riga, runtse ido tayi tace "kawo rigan zan wanke"

bai kalleta ba yace "jeki shikenan"

"a,a ka kawo umma na zata dakeni idan taji ban wanke ba"


nuna mata hanyan toilet kawai yayi, a hankali ta tura ta shiga, tana shiga ta jika rigan a cikin ruwa ta shanya bata wani wanke ba haka ta ajiye mishi ta fito zata tafi, ihu tayi ta koma ciki ganin daga shi sai wani ɗan karamin towel a kugu, jikinta har yafara ɓari, me nake gani?

turo kofan yayi bai kalleta ba yaje wajen shower yana kokarin kwance towel din, da sauri tace "me.me.me kake shirin yi?"


"wanka"

ya amsa mata ba tareda ya kalleta ba, buɗe kofar tayi ta fita da mugun gudu har bata ganin hanya, tafiya take tana surutu ita kaɗai "wayyo watarana idan ban kiyaye ba tsirara zai iya yi a gabana"


karo sukaci da Ahmar da sauri tayi baya tace "wayyo Allah"

dariya yayi "madam tsoro tsoron me kike kuma yau?"


"ba komai" ta faɗa tana shirin wucewa, hannunta ya riko ya janyota baya, waro ido tayi "inafa da aure kada ka manta"


"eh na sani kinada aure shiyasa naga kin rungumi Jawad da Kabir kina musu kiss..."


kafin ya karasa tace "dakata Jawad kanina ne kamar yadda Kabir shima yake kanina kada ka alaqanta ni da wani abin na daban"


"nima ban alaqantaki da wani abin ba kawai dai bakimin kama da matar aure bane, har yanzu kamar budurwa nake ganinki"

da sauri ta juya zata tafi ya kalleta da kyau yace "kodai so kike kisa Man a cikin damuwa shiyasa kikayi wannan karyan?"


bata bashi amsa ba ta wuce ta tafi, ɗakint ta faɗa ta kwanta akan bed, a hankali hawaye ya fara sauka a idonta, rungume pillow tayi sosai tana kuka, a hankali tace "i miss you"


"who do you miss?"


share hawayenta tayi da sauri ta tashi tana kirkiro murmushi ta kalli Samha wacce ta tsaya a kanta ta naɗe hannu a kirji tana kallonta, murmushi tayi ta zauna a gefenta ta riƙo hannunta "ni kanwarki ce zaki iya sharing duk wani matsalanki dani, meke faruwa meyasa kike kuka? wa kikayi missing? Man? ko Ashman?"


wasu zafafan hawaye suka kara gangarowa fuskarta a hankali Samha tasa hannu tana share mata cikin tausayawa ta janyota yana cewa "ki daina kuka"


saida tayi mai isanta kafin ta saki samha ta juya mata baya "kiyi hakuri kanwata bazan iya faɗa miki komai ba a halin yanzu"


"ba komai amma idan kin nutsu zanso ki faɗamin duk abinda ya faru"

jijjiga kai kawai tayi.
_Jiddah Ce✍🏻_

No comments

Powered by Blogger.