Doctor Mansoor 28

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

_Jiddah S Mapi_*Chapter 28*                 ~Kenan kinada aure Hamida? 

jijjiga kai tayi "kwarai Abba ina da aure"

shiru yayi, kana yace "okay ba damuwa haɗani da mijin naki a waya"

kiran number ɗin Ashman tayi tasa a handsfree ta yadda zasuji, ringing ɗaya ya ɗaga cikin muryan shagwaɓa da sakalci yace "Baby inata missing naki kin tafi kin barni, bakya bani kulawa, banajin daɗin bacci please..." da sauri ta katseshi dan tasan zai iya ɓarin zance tace "sorry inaso ku gaisa da Abba da nake baka labari"


"okay Baby bashi wayan"

mikawa Abba wayan tayi cikin girmamawa, ya amsa yana cewa "Hello"

a zafafe Man ya fara tafiya ba tareda ya juyo ba, ji yake kamar zuciyarshi zata faso kirji ta fito, bama ya ganin hanya, bai tsaya ko ina ba sai ɗakinshi yana shiga ya rufe kofa hadda sa key ya jingina da jikin kofan ya danne jikinshi da karfi, kirjinshi ya buga yana jin wani irin zafi "Hamida da aure?"

wasu zafafan hawaye suka fara bin kyakkyawan kumatunshi, Man meyasa bakada sa'a ne a rayuwarka? na shiga uku, zama yayi a wajen ya haɗa kai da gwiwa ya fara raira kuka.


ɓangaren Abba yana kallon Man ya bar wurin, murmushi yayi domin yasan ba komai yasa ya tafi ba sai zunzurutun kishi, bayan sun gaisa da Ashman yace ya bar musu ita suyi koda 2weeks ne, Man ya amince, hakan yasa Abba yayi murmushi yayi mishi godiya, Ammi rungumar Hamida tayi tace "kima zaton kin ɓata min ne? no ƴa ba zata taɓa ɓatawa uwarta ba"


kankame Ammi tayi tace "Nagode Ammi da taimakon da kika min lokacin da nake prison na gode"


"ki daina godemin domin kema ƴace a wajen"

kallon Abba tayi wanda yaki yadda su haɗa ido dan yasan yayi mata laifi, tace "maimakon kai ta da zakayi me zai hana su Umman nata su dawo nan gidan da zama tunda itama matarka ce"

cikin jin kunyarta yace "kiyi hakuri ki yafemin abinne yazo ba shiri banso kisan abinda man yake aikatawa kisa a ranki shiyasa na ɓoye miki komai"


murmushi tayi tace "ba komai naji daɗin hakan da kayi ka ce rayuwar mutane daga kunci"


hannun Hamida ta riko tace "zauna ba inda zaki sai kinyi 3weeks tare damu, mu kore kewan da mukayi"

zama tayi, Noor tazo ta zauna a gefenta ta riƙo hannunta "untu Hamida dama kina raye? meyasa kika gujemu?"


"ban gujeku ba ina tare daku kune baku sani ba"


"ta ina kike tare damu?"


kallon Abba tayi sannan ta kalli Noor tace "Ina kaka me kula da Abba?"


"eh kin santa ne?"


"ba kowa bace nice"

da mamaki sukace ke kuma?"


Abba ne yace "kwarai itace tazo a matsayin tsohuwa ta rinƙa kula dani, har tasan halinda muke ciki"

laila ma ta zauna a gefenta, Hamida Allah-Allah take taga ummanta da samha tayi missing nasu sosai, Ammi tace "kece kaka?"

jijjiga kai tayi cikin jin kunya.


Jawad yana daga tsaye sai murmushi yake, abu ɗaya ya bashi haushi shine auren Hamida baiso ace tanada aure ba, yaso ta auri ya Man, Ahmar ya kalleta "Mrs tsoro? ki yafe mana"


"ba komai ya Ahmar"


Kabir hannu yasa a kunnenshi ya rike alaman bada hakuri, murmushi tayi ta murguɗa mishi baki "kai fa ba zan yafe ba"


"please unty hamida"

dariya kawai tayi.


Abba da kanshi ya shiga mota shida Ahmar sukaje suka ɗauko umma da Samha basu sanar musu Hamida ta dawo ba kawai Abba yace zasu koma gidanshi da zama, sun tara kayansu a jaka, umma tayi kiɓa ta kara haske ta zama fara sol sosai, ta zama hajiya, samha ma ta zama classic ba wani rashin ji ta maida hankali akan karatu, sun shirya kayansu da taimakon Ahmar, Abba ne yasa makulli ya rufe gidansu wanda yake me kyau ne sosai amma bai kai nasu Man ba, shiga gaba yayi shida umma Samha da Ahmar kuma a baya, bayan sun ɗau hanya Abba suna ta hira da umma, Ahmar ya kalli Samha wacce take aikin murza yatsun hannunta tana kallon gefe, murmushi yayi domin suna yanayi da Hamida, a hankali yace "bakya magana ne?"

ɗagowa tayi ta sakar mishi murmushi nan fa yaga tsananin kama itada Hamida, girgiza kai kawai tayi, yayi murmushi yace "oh madam ɗin ba me magana bace ko dai nice ba'ason yimin magana?"

murmushi ta kuma yimishi, bai kara magana ba har suka isa gida.


Abba ne ya ciro kayansu daga mota Ahmar ya ɗauki na Samha shi kuma Abba ya ɗau na Umma, kallon cikin gidan Samha takeyi tana ganin yadda ya tsaru sosai, shiga ciki sukayi su umma da Samha a baya, a palour suka zauna ammi ta karɓe su hannu bibbiyu, zama sukayi akan sofa Samha sai rarraba ido take, tana ganin Noor tayi mata murmushi, me kama da Unty Hamida.


Hamida ce ta fito daga ɗaki da gudu take tsallaka stair tana kallon umma, mikewa umma tayi cikin tsananin farin ciki da mamaki taje itama da gudu suka rungumi juna, tsalle Hamida tayi ta rungume umma da karfi tana kuka, umma ma kuka ta fara, a hankali ta ɗago kanta tana kallon yadda Hamida tayi kyau ta zama babbar mace, ta murje

"Hamida shine kika tafi kika barmu?"

Umma bada sona bane, ta faɗa cikin kuka.


Samha kanta ta saukar kasa taki yadda su haɗa ido da Hamida, sakin umma tayi a hankali ta karasa wajen Samha, rungumeta tayi tana cewa "kin manta dani kanwata"

kuka ta fashe dashi tana cewa "kiyi hakuri ki yafemin Unty Hamida"


"ki daina faɗin haka, na daɗe da yafe miki"


_Jiddah ce✍🏻_

No comments

Powered by Blogger.