Doctor Mansoor 27

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

_Jiddah S Mapi_



*Chapter 27*



                 ~Kwana ɗaya da tayi a cikin gidan bata kula kowa harkan gabanta take, hatta abinci ba ci take ba saide tasha yoghourt da biscuit tayi ta latsa waya tana taunar cingum, riga kanana take sawa wanda baya wani rufe jikinta, rayuwar turawa takeyi a cikin gidan, ta gyara komai ta kira likita tun daga kasar waje sunzo suna kula da Abba, alhmdllh yana samun lafiya, Ammi kaɗai take yiwa magana hatta Noor ba sake mata fuska take ba, ta maidata school nata na da, Kabir sai kallo yake shiga tsakaninsu shifa har yanzu bai yadda cewar ba ita bace Hamida, Ahmar ma kallonta kawai yake shima bai yadda ba.



Yayi shiri cikin kayan doctor yayi kyau sosai saide ya rame yayi haske, yanada damuwa a ranshi babu me kulashi hakan yasa baya kula kowa shima, rayuwarshi yake cikin kewan Jahad da jin haushin abinda tayi mishi, baya bacci kullum sai kuka, so yake yaga Hamida ya bata hakuri, jaka ya rataya baki a kafaɗarshi yana tafiya cikin nutsuwa, yayi alƙawarin daga yau ya daina zubar da ciki da yaddan Allah, domin ba karamin tashin hankali hakan yasa shi ba, ɗakin Abba yaje ya duba jikinshi, ganin yana samun sauki yayi murmushi wanda ya kara bayyana kyaunshi, juyawa yayi zai fita sukaci karo da Nihal wacce tasha bakin dogon riga buɗaɗɗe, farin fatarta ta fito sosai hannunta rike da cup wanda yake fitar da tururin zafi, Tea ne me zafi ta kawowa Abba, raɓashi tayi zata wuce taga yana kallonta, kawar da kai tayi saida tazo gabanshi tayi kamar zata faɗi ta watsa mishi ruwan zafi a kafa "auch" yayi siririn ihu yana duba kafanshi, murmushin gefen baki tayi kana ta juyo cikin lumshe ido tace "sorry"


kare mata kallo yayi sosai kafin ya fita daga ɗakin yana ɗingisa kafa, Jawad ne ya ganshi yace "sannu"

wuce shi yayi ya shiga ɗaki, a bakin kofa ya tsaya yana kallon Nihal wacce take ɗaga Abba tana bashi Tea a baki, murmushi yayi ya karaso ciki bakinshi ɗauke da sallama, amsawa tayi ba tareda ta kalleshi ba, cikin girmamawa yace "sannu unty Nihal"


"Yawwa" 

ta faɗa tana cigaba da bawa Abba tea, saida ta gama ta mike zata fita taji ya rungumeta, shiru tayi hannunta rike da cup ta zubawa bayanshi Ido, "unty hamida koda zaki ɓata wa mutane dubu ni bazaki taɓa ɓata min ba, na sanki nasan halinki ba zaki taɓa canjawa ba, dan Allah ki yafe mana abinda mukayi miki"

tureshi tayi ba tareda tayi magana ba ta fita daga ɗakin, sai yanzu ya kara tabbatar da cewar wannan Hamida ce, wurin Abba yaje yana kallonshi yana murmushi "Abba wannan Unty Hamida ce?"


Girgiza kai Abba yayi, da karfi ya rungumi Abba yana dariya, alhamdulillah ta dawo.


Man ya fara aiki, yana kula da Aikinshi sosai baya kula mutane baya musu dariya, yanzu rashin magananshi yafi na da, tafiya yake ba tareda ya saurari abinda mutane suke faɗa akanshi ba, ciwo yake dashi a zuciya ciwon abinda Jahad tayi mishi, ba zai taɓa warkewa ba.



Yau ta shirya tsaf domin tafiya, dama kwana biyu tace zatayi, yau weekend kowa yana gida sai kallonta suke jikinsu a mace basa son ta tafi, musamman laila wacce har hawaye take yi a ɓoye, Noor ma tayi shiru tana zaune a gefen Ammi, shiri tayi cikin riga da wando da wani bakin after dressing ta yafa gyallenshi a sama, ta rike jaka da wayarta a hannu, kamar kullum tasa high shoe tana takawa cikin iya tafiya da gadara, wurin Ammi taje ta durkusa, cikin sanyin murya tace "nikam zan wuce Ammi Allah ya bawa Abba lafiya"

shiru Ammi tayi dan bataso ta tafi, itama Hamida dauriya kawai take domin batason barin ammi, ta tuna lokacin da take prison Ammi tana zuwa kawo mata abinci ba tareda kowa ya sani ba, tashi tayi ta rungumeta sannan ta kalli su Kabir da Ahmar da Jawad dasu Noor wanda sukayi jigum suna kallonta, ɗauke kai tayi tace "Laila ki rinka shan magani akan lokaci"

ɗaga wayarta wacce take ruri tayi tana cewa "hello Dady yanzu zan hau hanya by god grace"


kashe wayar tayi tace "na tafi Ammi sai wani jikon"


tafiya ta fara taje wurin handle zata murɗa taji muryan Abba yace "Hamida!!"

tsayawa tayi cak ta kasa juyowa kuma ta gagara fita, kallon Abba sukayi cikin murna kowa ya mike yaje da gudu ya rungumeshi hadda Ahmar da Kabir, Man ma ya fito daga ɗaki jin muryan Abba, da wani irin gudu yaje ya rungumeshi, saida sukayi kuka sosai sannan suka sakeshi, kallon Hamida yayi wacce ta gagara juyowa yace "juyo ƴata"

a hankali ta juyo kanta kasa, batayi expecting Abba zai taka har yayi magana ba yau, ganin ya tsaya yana kallonta taje da gudu ta faɗa jikinshi tana kuka, bubbuga bayanta ya fara a hankali shima yanajin zuciyarshi tana karyewa, basu yiwa yarinyar adalci ba, saida tayi kuka me isanta ta sakeshi tana share ido, hannunta ya riko yace "kiyi hakuri da abinda ya faru ƴata haka ƙaddara yake zuwa, naji daɗi da baki rama mugunta da mugunta ba, sai kika rama da alkhairi, Man yayi miki laifi me tarin yawa ciki harda zubar da cikin ƴar uwarki da kuma kanwarki wacce kuke uwa ɗaya, kiyi hakuri Allah ya baki lada, nasan hakane ta dalilin nemanki lokacin da akace kin mutu a prison, na fara nemanki sama da kasa sai na samu labarin inda gidanku yake, bayan naje mamanki ta bani labarin duk abinda ya faru, Allah kuma ya yiwa kanin mahaifinki rasuwa, suna cikin mawuyacin hali itada kanwarki Samha, hakan yasa na kama musu gida me kyau a cikin gari na basu aikinyi suka samu kyakkyawar rayuwa, ina zuwa a ɓoye ba tareda kowa ya sani ba, ganin ɗana yana da alaqa da halin da suke ciki yasa na auri mamanki ta zamo matata, yanzu haka inada auren mahaifiyarki ina jinki kina kira a waya kullum cewar ko an samesu? nasan kinje gidanku kinga babu su to suna karkashina"


Ammi ta ɗago ido cikin kiɗima ta kalleshi, yana da aure kuma?


Hamida cikin kuka tace "kenan kasan inda Ummana take?"


"tabbas na sani amma bazan kaiki ba har sai kin yafewa Man laifin da ya miki"


"na daɗe da yafe mishi Abba, dama nazo da niyan ɗaukan fansa sai kuma naga abinda Jahad take, hakan yasa naji gaba ɗaya kun bani tausayi shiyasa na kyale fansa ta na fara taimaka muku, amma na yafe mishi"


Man yayi shiru kanshi a kasa, shima yasan baiyi mata daidai ba, inama Abba da Ammi basa wajen daya rungumeta ya roki yafiya, da yayi kuka a jikinta kukan abinda Jahad tayi mishi.


"zan kaiki wurin mahaifiyarki zaki iya auren Man?"


girgiza kai tayi alaman a,a, cikin mamaki yace "meyasa?"


"Inada aure Abba"


da mamaki su Ahmar suke kallonta Aure? yaushe hakan ta faru?


"Captain Ashman shine mijina wanda nake da aurenshi a halin yanzu, bayan na gudu daga prison nida wata mata Unty Maryam ta kaini gidansu a Abuja, sun rikeni hannu bibbiyu sun bani kulawa sosai, nayi karatu a wurinsu na samu aikin lowyer, daga nan suka auramin ɗansu wato ya Man"


gaban Ammi ne ya faɗi, kenan tayi aure? kuma Abba yana da auren Ummanta a kanshi? tashin hankali.





*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.