Doctor Mansoor 26

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    Na

_Jiddah S Mapi_*Chapter 26*                 ~Tsayawa yayi cak yana kallonta, ɗan murmushi yayi sannan yace "Kabir ne fa, abokin faɗan ki na school kin manta ni?"


kallon sama da kasa tayi mishi sannan ta watsar tace "sorry I don't know you"


jikinshi ne yayi sanyi ganin yadda ta watsar ta shareshi, yaron da suka watso da kayan ya matso kusa da ita yace "gidanmu ne nan ubana ne ya siya"


matsowa tayi dab dashi tana kallon cikin idonshi, takalmin kafarta me tsini ta ɗaga tare da taka kafarshi, kara yayi sosai, cikin rainin hankali tace "shi uban naka be sanar maka cewar mace ta siye gidan daga hannunshi bane? ta hanyar ninka mishi kuɗinshi sau uku?"


zai buɗe baki yayi magana wayarshi ta fara ringing, yana ɗagawa cikin azaban takun da tayi mishi da takalmi yace "hello Dady?"


yayi kusan minti biyar sannan yace "to Dady"

kashe wayan yayi yana kallon Hamida yace "ranki daɗe ya sanar min yanzu, kiyi hakuri Please dan Allah kiyi hakuri"

ɗauke kafarta tayi tana shu'umin murmushi, kallon ɗayan tayi "zaku iya maidashi inda kuka ɗaukoshi?"


ɗaga Abba sukayi cikin rawan jiki suka maidashi inda suka ɗaukoshi, tafiya ta fara cikin isa da gadara tana taunar cingum tareda gyara zaman space nata, Ahmar ta gani a kwanan da zatayi, da sauri ta ɗauke kai taci gaba da tafiyanta zuwa cikin gidan, Noor tace "Unty Hamida?"

bata juyo ba taci gaba da tafiya saida ta shiga ɗakin Abba taga sun kwantar dashi, waya ta ciro tace "ku kawo"

motoci manya manya cike da furnitures suka tsaya daga kofan, fitowa aka fara dashi suna shigarwa cikin gidan, Hamida na tsaye tana nuna musu yadda za su jera, gado da katifa na kowane ɗaki saida aka canja, babu abinda Ammi takeyi sai murmushi tana kallon Hamida, saida aka shirya komai na gidan ta kira waya tace "Come in"Laila ce ta shigo tana murmushi, tayi kyau sosai tayi kiɓa kuma kafar ta warke, da gudu Noor taje ta rungumeta tana kuka, ɗauke kai Hamida tayi daga kallonsu dan itama ji take kamar zatayi kuka, tana sakinta taje wajen Kabir tayi wani tsalle ta rungumeshi tana kuka, shima kuka yake sosai, Ahmar dake gefe baisan time ɗin da yayi sujadda ba,

Ammi sai share hawayen farin ciki take. 


Laila cikin jin daɗi taje gaban Ammi ta rungumeta, cikin jin daɗi Ammi ta kalli cikin gidansu yadda a rana ɗaya ya dawo yadda yake harma yafi na da kyau, share hawaye tayi "laila?"


"na'am Ammi"


Kabir ne yazo da gudu ya rungumesu su duka jin Laila tayi magana, noor ma tazo ta rungumesu, Ahmar wanda ya kasa rike jin daɗinshi shima yazo, Man ne ya tsaya a gefe yana kallonsu, yasan koda yaje ba zasuji daɗi ba, domin shine silar shigansu cikin wannan tashin hankalin, kallonshi tayi ta kasan ido, cikin ɓata rai tace "Hajiya meyake damun mijin naki?"


"Hamida Abbanku ya samu ciwon ɓarin jiki sakamakon abubuwan da suke faruwa a gidannan"


Kallonta tayi "wacece kuma hamida?"


da mamaki suka kalleta su duka, "kece mana"


"A,a nifa sunana Nihal, na shigo naji kuna kirana da Hamida bansan me kuke nufi ba"


da mamaki a fuskar Ammi tace "Nihal kuma?"


"yeah"


sai yanzu ta kula da wannan tana magana tana sirkawa da turanci saɓanin Hamida wacce take magana da hausa kawai, Noor ma cikin mamaki tace "Nihal? kenan ba Unty Hamida bace?"


"unty hamida? What do you mean? do you know me?"


Jawad ya tsaya sai kallo kawai yake, kenan ba Unty Hamida bace?


murmushi tayi "nikam za wuce dad yana jirana a airport zan turo muku doctor ya kula da mara lafiya, na barku lafiya, takaddun gidan zan turo muku gobe"


tafiya ta fara cikin iyawa, Ammi tace "kiyi kwana biyu damu mana Nihal kinada kyaun hali kamar wata wacce muka zauna da ita anan gidan sunanta Hamida, kuna kama da ita sosai da fari mun zata itace, sai kuma mukaga halinku da banbanci Hamida bata sa kananan kaya, kuma batada saurin fushi"


a hankali ta juyo ta fara takowa zuwa wajen Ammi, saida ta tsaya tace "hakan yana faruwa a rayuwa, wani lokacin mutum baida saurin fushi mutane sune suke koya mishi, sannan mom ɗina kafin ta mutu tacemin mu biyu ne ta haifa saide ɗayan ta mutu, farkon zuwa na gidannan sai naji kun bani suna wanda ba nawa bane, hakan yasa naji a jikina kun zauna da wacce take da alaqa dani, wannan yaron"

ta nuna Kabir, "shima yace shi abokin faɗa na ne, ni bama a kasarnan na girma ba, zuwana nigeria baifi 10months ba, na haɗu da wannan a hospital ɗin da mom ɗina ta rasu, ganin babu me kula da ita yasa na kula da ita har ta samu lafiya, banyi tunanin akwai maza a gidan ku ba, na tarar ana yimuku wulakanci hakan yasa nayi searching na duba wanda ya siya mansion naku, na tura mishi kuɗi sau ukun wanda ya siya, ashe akwai maza a gidan, saide duk halin mata ne dasu"

tayi magana tana kallon Man.


rai ɓace ya ɗago yana aika mata harara, wannan kam ba Hamida bace Hamida nada tsoro amma wannan idanunta a tsaye yake, kallonshi tayi ta kasan ido kafin tace "hajiya zanyi kwana biyu saina koma next day"


Dariya Ammi tayi tace "ba komai ƴata ki zaɓi ɗakin da zaki zauna a ciki ko?"


Kallon Ammi tayi ta nuna ɗakin Man da Jahad tace "acan zan zauna"

bata kuma kin abinda zasu ce ba tabar wajen tana takawa cikin isa da nuna wayewa, juyowa tayi tace "Momy na tace mu biyu ta haifa ɗayan ta ɓata, amma an sanar mata ta mutu, hakan ya dameni sosai amma bamuda tabbacin ta mutu"


cigaba tayi da tafiya ta haura sama tana hararan Man ta kasan ido, jikin Ammi ya mutu sosai jin labarin Nihal, tabbas suna kama da Hamida ba shakka su ɗin twins ne, Allah sarki Hamida ta rasu kenan ta tafi ta barsu? share hawaye tayi ta bar wurin kowa yana tsaye cikin mamaki.


Man ya girgiza da jin labarin Nihal shima, kwanciya yayi yana kallon sama abinda ta faɗa gaskiya ne domin Hamida batada tsiwa da wayewa, damuwa ya taru ya mishi yawa, yanzu kenan Hamida ta mutu?

yana cikin tunani yaji wayarshi na kara, cikin rashin jin daɗin jikinshi ya ɗau wayan ya kara a kunne, da sauri ya mike jin ance an buɗe hospital nashi ta dalilin wata wacce tayi magana ta bada makudan kuɗaɗe sunanta Nihal, ya rasa me zaiyi kuka ko dariya? kashe wayar yayi ya mike yana tafiya zuwa ɗakin Ammi, saida yayi knocking kusan sau huɗu batayi magana ba, tura kofan yayi ya shiga yana kallon Ammi wacce take aikin gabanta kawai ba tareda ta kalleshi ba, ta baya ya rungumeta yana hawaye, cikin jin daɗi yace "an buɗe hospital ɗina"

taji daɗin hakan sosai, amma taji haushi domin fa abinda yake aikatawa ba mai kyau bane, cire hannunshi tayi daga cikinta taci gaba da aikinta, dukar da kai yayi yace "Ammi Nihal ce tayi magana kuma ta biya kuɗi"


fita yayi daga ɗakin ya nufi ɗakin shi da Jahad, dama baison ɗakin domin bayason abinda zai kara tuno mishi da Jahad nashi, tana zaune akan sofa tana shan drink a cikin Cup kafarta ɗaya akan ɗaya, knocking yayi tace "come in"

shigowa yayi yana murmushi yace "thank you...."

tashi tayi ta barshi a wajen ta fita daga ɗakin, kallon tafiyanta yayi sosai, wannan Hamida ce, yasan tafiyanta duk da tana canjawa ba zata ɓata mishi ba, saide ai wannan tafi Hamida kyau, kanshi ne ya ɗaure sosai, dole ne ya gano ta.
*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.