Doctor Mansoor 23


 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    Na

_Jiddah S Mapi_*Chapter 23*                 ~Zaunar da ita yayi ya bata ruwan sanyi a glass cup, da karfi ta buge tana juya kanta, Cup ɗin ne ya faɗi ta tarwatse, cikin lallami yace "nasan kinyi haka ne dan ki kareni daga raini, amma ina me baki hakuri, kwashe glass ɗin yayi ya zuba a dustbeen, dawowa yayi ya janyo ta jikinshi yana shafa bayanta, shiru tayi tana jin zuciyarta yana mata zafi, da baya wajen yau saita caccaka musu wuka, wallahi saide a kamata amma so take tayi ajalinsu a halin yanzu, shima Man shiru yayi yana tunanin hukuncin da zai yiwa Jawad da Noor, har rainin nasu ya kai haka kenan?


da dare Jahad ta sulale ta bar ɗakin bayan Man yayi bacci, Pillow tasa mishi a gefenshi ya rungume ya zata itace, cikin zafin rai take tafiya bata tsaya ko ina ba sai ɗakin Jalal, yana zaune akan sofa cikin bakin kaya da Laptop a gabanshi yana pressing, ture laptop ɗin tayi da karfi ta nuna mishi fuskarta tana huci, murmushi yayi dan yasan marinta akayi, kallon cikin idonshi tayi ranta a matukar ɓace tace "dariya kake? marina fa tayi" juyawa tayi zata fita, tana cewa "yau saina kashe wannan tsohuwar"

rikota yayi da karfi ya janyota ta faɗa jikinshi "calm down Baby Jahad ki rage fishi ki koyi yadda zakiyi control na kanki, tsohuwa ce fa shekaru sun ja, ki kyaleta muyi focussing akan abinda yake gabanmu yanzu haka nasa gidan a kasuwa, Man zaiyi babban kuskure tunda ya amince miki musa gidan a kasuwa, kinga shi zaiyi expecting kuɗin domin yayi business mu kuma saimu fece da kuɗaɗen, Jahad ina son ganin Man cikin tashin hankali da tsoro, ina son ganinshi yana bara a titi"

shafa kirjinshi tayi "kana tare da Jahad kada, rayuwar da suke ciki kaɗai abin tausayi ne, saima mun saida gidan a lokacin zai san ni Jahad ba matarshi bace makiyarshi ce, wacce tazo ɗaukan fansa a gidansu"

shiru sukayi su duka kowa ya fara tunanin abinda ya faru shekarun baya da suka wuce. An shigar da gidan Alhaji Muhammad Dikko kasuwa akan farashin kuɗi naira miyana 80, domin siyarwan gaggawa ne, Ammi da Jawad da kuma shi kashi Man ba su so hakan ba, amma wannan shine may be zai zamo silar arzikinsu, zasuyi business kowa sai samu madafa, acikin kuɗin kuma zasu kai Abba hospital zuwa kasar waje, manyan ƴan kasuwa da masu kuɗi sunce suna so, ganin haka yasa wata hamshakiyar mata me kuɗin gaske ta taya gidan akan Naira miliyan 100 lagadan ba ajalan ba, jin haka yasa suka sallama mata ita kuma ta danka musu kudi ta hannun Mahaifinta sunanta ne akan komai mahaifinta ne ya kai kuɗi ya karɓi takaddu da komai na gidan, Man yaji daɗin wannan kudin yanzu zai gyara rayuwarsu wanda ya ɓaci kuma zai kai mahaifinshi asibiti, sun zauna dasu Ahmar da Ammi sun yanke shawaran yadda zasuyi da kuɗaɗen, a halin yanzu dai kuɗin yana tare da Man ya ɓiyesu a cikin account nashi.


Jahad tsaye a ɗaki sai safa da marwa take hannunta duka biyu ta goya a baya, riga da wando na bacci ne a jikinta fari sal irin silk ɗin nan me less a baki, tayi Parking gashinta da ribbon, tunanin ta yadda zasu kwashe kuɗin su gudu kawai take, ko yau suka samu kuɗin gobe zasu bar kasan nan, fitowa yayi daga toilet waist nashi ɗaure da towel kanshi a jike, kallonta yayi ya watsar, gaban mirror yaje ya kunna drayer ya busar da gashinshi, mai ya shafa kafin ya ɗau rigan baccinshi yasa, kallonta ya kuma yi, cikin sassarfan murya yace "me kike tunani?"

bata jishi ba, hasalima batasan ya fito ba, a hankali ya kuma cewa "tunanin me kike jahad?"

ganin tayi nisa bata hayyacinta yaje wajenta ya tafa hannunshi, firgigit ta juyo ta kalleshi, shafa kanta yayi tare da sa hannu a kasan fuskarta ya ɗago "tunanin me kike?"

hawaye ya cika mata ido da karfi ta rungumeshi, jikinshi yayi sanyi ya fara bubbuga bayanta jin ta fashe da kuka me tsuma zuciya, saida tayi me isarta sannan yace "meya faru?"


"ba komai" ta faɗa tana share idonta, baiyi magana ba ganin ta hau gado ta kwanta shima ya bita ya janyota yana shaƙar ƙamshin jikinta, hannunshi ta rike tana murzawa tace "zaka iya min wani alfarma?"


"Ki faɗi koma me zanyi miki"


"Ka yadda dani?"


"fiye da kaina ma"


"to kasha giya yau a gabana"


shiru yayi dan fa so yake ya daina shan giya, bada sonshi yake hakan ba, yana yine idan zai zibar da ciki, yanzu kuma ya tuba ya daina, kara murza hannunshi tayi "zaka sha?"

bai san time ɗin daya girgiza kai ba, "zan sha idan hakan zai baki kwanciyar hankali"


murmushi tayi "na gode da yaddan da kayimin"

zame hannunshi tayi daga cikinta ta mike taje gaban frij ta ɗau kwalaben giya, fara bashi tayi yana amsa har ya shanye tass, ganin ya bugu sosai baya gane inda yake ta durkusa kusa dashi tana riko hannunshi cikin murmushi tace "DR MANSOOR menene pin ɗin bank account naka?"


Cikin muryan buguwa yace "2023"

jijiga kai tayi ta mike ta ɗau jakanta ta ciro bakaken kayan ta, sawa tayi tareda takalmi boot shima baki, bindiga da wuka ta cire tareda haɗawa wuri guda ta zauna a gefenshi, wayarshi ta ɗaga tana murmushi ta tayi transfer duka kudaɗen zuwa account nata, saida taga successful tayi wani tsallen farin ciki tana dariya, kallonta yake ya kasa fahimtar komai "me... kike...yi Jahad?"

yayi magana cikin muryan mashaya, murmushi tayi ta matso gabanshi ta durkusa akan kafarta, waya ta ɗaga tace "Done"

shigowa ɗakin yayi shima jikinshi sanye da kaya irin na Jahad ɗin, ɗaure Man sukayi a jikin gadon da igiya ta yadda ba zai iya kwancewa ba duk yadda akayi, saida suka tabbatar ya ɗauru sannan Jalal ya ciro wani Kwalba a jakanshi, buɗe bakin Man yayi suka ɗura mishi maganin, bayan yasha ya fara dawowa hayyacinshi daga buguwan da yayi, ware idanunshi yayi yana jin kanshi yana mishi nauyi, kallon jikinshi yayi bayan ya gama dawowa hayyacinshi, fizge jikinshi ya fara yana kiran "Jahad!!! Jahad!!! waye yamin haka? banson wannan wasan"


cikin crazy taku wanda take yinshi a duk lokacin da tayi abinda ba kyau ta fara takowa daga cikin toilet inda ta laɓe tana jira ya dawo hankalinshi ta fara takowa tana murmushi, ɗan tsaki yaja "banson wannan wasan ki kwanceni"

murmushi tayi "ba wasa bane"


"Jahad wasa ne ki kwance Ni"


murtuƙe fuska tayi ta koma asalin Jahad nata "nace maka ba wasa bane"


wuka ta ciro daga aljihu ta matso kusa dashi, shafa wukan ta fara a fuskarshi bayan ta zauna a cinyarshi tana kallonshi, muryanta ƙasa ƙasa tace "bari na tashi kada mijina ya ganmu a haka"

kallonta yake cikin mamaki a kuma firgice, waro ido tayi ba tareda ta tashi ba tace "wayyo gashi ma ya karaso"

Jalal ne ya shigo shima yana murmushi, da sauri Man ya harzuka zai tashi, a hankali ta shafa kirjinshi "easy kada ka jiwa kanka ciwo a ɗaure fa kake"

cikin zafin rai yace "mahaukaci meya shigo da kai?"

mari ta wankeshi dashi me kyau sannan ta nunashi da yatsa "kada ka kara cewa mijina mahaukaci"

idanunshi sunyi jawur me Jahad take nufi?

miƙewa tayi tana tafiya jikinta yana girgiza taje gaban Jalal ta rungumeshi tana shafa jikinshi, a hankali ta ɗago kai ta haɗa bakinshi da nata, Jalal ya rike gashin kanta yana bata kiss me zafi a gaban Man, runtse ido yayi da karfi "ki dawo hayyacinki Jahad me kika sha?"

sakin Jalal tayi ta tako zuwa wajenshi, zama tayi a gefe "kana tunanin kowa mashayi ne kamar kai?"


Girgiza kai tayi "no no no ba kowa ke shaye shaye ba, DR MANSOOR MUHAMMAD DIKKO"


"Jahad me na miki kike min wannan ɗanyen hukuncin na san ba halinki bane"


dariya ta kwashe dashi "me kamin? Mansoor tambaya fa kake me kamin?

zan baka amsa amma kafin nan inaso ka amsamin wata tambaya"


Kallonta kawai yake, saida ta gyara zama tace "2/2/2020 shin ka tuna lokacin a ina kake? nasan ba zaka tuna ba, to lokacin kana asibiti ne, kasan me kake yi? ba zaka tuna ba amma zan tunar da kai"


tashi tayi tana safa da marwa ta fara magana cikin hawaye da zafin zuciya.


"Doctor Mansoor 2/2/2020 kana asibiti tareda wata yarinya me kama dani, babu bambanci ko kaɗan tsakaninmu da ita, tsayi, gashi, hanci, ido, baki, duk iri ɗaya ne, nayi mamakin yadda baka gane ni ba a lokacin dana zo Office naka, saide kawai ita yarinyar ta fini haske, ba baka bace fara ce tass, amma babu abinda ya rabani da ita a kamanni"

share hawaye tayi kafin tace "kasan me kake mata a lokacin? ciki ka zubar mata ba tareda kasan miye dalilin cikin nata ba, ta dalilin haka ta faɗi ta mutu, sau uku kana zubar mata da ciki har saida ya zama ajalinta"

da ihu tace "wannan yarinyar ba kowa bace face ƴan biyu na wato JAHAN, nice Hassana Jahan kuka Hussaina ta, mu biyu kawai Allah ya bawa iyayenmu gashi kayi sanadiyyar mutuwar ɗaya, kasan soyayyan dake tsakanina da Jahan? ba zaka sani ba dan baka san mutuncin ɗan adam ba"


"ta dalilin kisan da kayi na uwa da ɗanta hakan yasa mahaifiyata ta kamu da cutan hawan jini kamar yadda kaima nasa mahaifinka yake kwance ko magana baya yi, sanadiyyar mutuwan mahaifiya yasa mahaifina Alhaji Muhammad Kada ya mutu shima, kasan zafin dana ji a raina lokacin? no baka sani ba, Jalal shine masoyina wanda ya yadda dani, hakan yasa ya aureni ya amince zai tayani ɗaukan fansa, bayan aurenmu da Jalal sai na samu ciki, da haka na fara tunanin yadda zanyi da cikin, sai Allah ya turo Hamida wacce Jalal ya tsintso a hanya, daga nan muka sameka ba tareda kasan mu bane mukasa ka cire cikin jikina ka sawa Hamida, Allah yasa yarinyar tana da wayo da kuma sa'a saita ki amincewa taje garin gudu kuka bugeta da mota, lokacin da kuka kawota gidannan ba karamin razana nayi ba amma na dake na nuna ban santa ba, da haka na fara amfani da ita ina aikata duk wani fansa na, hakan yasa ranan da muka sace Kabir na kai wayan ɗakinta tareda takalmin dana bari a hospital naka lokacin da naje na kashe wannan mutumin, Allah sarki Hamida nice na kira police suka kamata ba tareda ta aikata wani laifi ba"


"koda shike ai ɗaukan fansa baya jiran saika samu wanda ya dace duk wanda ka samu kawai kayi amfani dashi, Shaira, Sabir, iyayen Kabir, Kabir, Minal kawar Noor duk nice na kashesu, Kabir ne kawai ya gagara mutuwa na baka assignment ka nemo inda yake cikin 24hrh idan ba haka ba zai mutu, na zubda ciki a wajenka tareda ɗauka dukkan Information na kaiwa ƴan sanda, hakan yasa aka rufe asibitinka, naji daɗin ganinku cikin talauci gashi na sace kuɗin account naka na tura a tawa, wayyo Jahad ke muguwa ce"


"kasan meyasa zan barka ba tareda na kasheka ba? saboda so nake ka rinƙa mutuwa a kowace rana, tunanin Jahad da abinda tayi maka kaɗai ya isa ka mutu ka dawo"


"Mahaifinka ina bashi labarin duk abinda yake faruwa hakan yake sashi cikin shocking yana kuma samun wasu ciwukam fiye da wanda yake ciki, Laila kuma nice na ture ta daga up har Allah yasa jikinta ya shanye, gashi har yanzu tana asibiti ko da sauki ko babu oho, nice nake haɗaka faɗa da Jawad domin yaron ya tsaneni without reason, daga karshe ka rasa wacce take sonku tsakani da Allah wato Hamida, nima gashi zan barka, lonely boy"


Kallon Jalal tayi "baby kana da magana?"


girgiza kai yayi "tunda sweetheart ta gama magana ni ai banda tace wa"

murmushi tayi "i love you Jalal"


"Love You more my crazy Jahad"

*kuɗin littafina ₦300 ne biya ta nan 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta nan 08144818849, turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.