Doctor Mansoor 22

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




    Na

_Jiddah S Mapi_



*Chapter 22*



                 ~Washe kawo mata kari akayi ta kalla sosai, shinkafa da wake ne, bataci ba ta mike ta fita, dama Ammi ta shigo ta gaisheta tun ɗazu, ɗakin Abba taje ta buɗe cikin sanyin jiki da yanayi irin na tsofi, yana kwance idanunshi suna kallon sama, a hankali ta zauna a gefenshi ta riko hannunshi, batasan time ɗin da kuka ya kwace mata ba, cikin tsananin tausayi tace "Abba? kaine ka dawo haka?"

ganin ya tsura mata ido ta cire hulan farin gashin dake kanta, tashi tayi ta kwance lifayan dake jikinta, ya rage daga ita sai riga da wando irin buɗaɗɗen nan black, shiga toilet tayi ta wanke fuskarta sannan ta dawo tana kallonshi, cikin sharan hawaye tace "nice Hamida wacce ka taimaka mata a lokacin da bata da kowa, saide kayimin sharri ba tareda kasan ko nice nayi hakan ko ba niba, na dawo da niyyan ɗaukan fansa sai kuka Allah yasa naga halin da kuke ciki, komai da komai ya kare, an saida komai, an rufe adibinti Man, Ammi wanke-wanke takeyi a gidan mutane, gaka nan kwance akan gado sai yadda akayi dakai, Abba bazan iya juran ganinku a haka ba, kanta ta kifa a cikinshi ta fara kuka sosai, hawaye ne masu zafi suka fara gangara daga idanun Abba, so yake yayi magana ba hali, a hankali ya ɗaga hannu ya ɗaura a bayanta, sauke ajiyan zuciya ta fara har yanzu bata daina kuka ba, ɗago kai tayi tasa hannu tana share hawayen da suka zuba a fuskarshi, cikin shesheƙan kuka tace "zan gyara komai, zan dawo da komai kan hanya, Abba kada ka damu zanyi maganin komai"

magani ta ɗauka daga jakanta ta buɗe tasa mishi a baki, kurɓa yayi ya ɗauke kai, murmushi tayi "zakayi lafiya"

tashi tayi tareda maida lifayan ta shafa sabulu da wani abu a fuskarta, glass nata tasa nan ta fito a matsayin tsohuwa, fita tayi daga ɗakin taje palour ta zauna akan sofa, tunanin yadda zata fara gyara abinda ya ɓaci a cikin gidan take, Jahad ta fito daga ɗaki hannunta rike da champagne da glass cup wanda ta tsiyaya, riga da wando wanda ya kama jikinta tasa light yellow, hula picap tasa a kanta tana tafe tana ɗan waka kasa-kasa domin tana cikin farin ciki, yau birthday ɗin Jalal, da kallo Hamida ta bita tana mamakin meyasa take cikin farin ciki haka?

saida taso tab da ita kafin ta zabga mata harara ta wuce, da mamaki Hamida ta bita da kallo, me hakan ke nufi? Jahad ta palle ne ko ta koyi iyayi?

gyara glass ɗinta tayi saida ta fita kafin ta mike tana binta a baya, Jahad ta lura da hakan, shiyasa ta juya ta koma wani Part ɗin daban bataje na Jalal ba, Hamida ganin ɗaki a buɗe taje ta tura, baya tayi zata gudu ganin wani me kama da mahaukaci zaune a ɗakin ya haɗa kai da gwiwa.


jin an buɗe kofa ya juyo yana kallon ko waye? 

salati Hamida tayi a cikin ranta domin ba karamin kaɗuwa tayi ba, Jalal? meya kawoshi gidannan? shine ya haukace?

dariya yayi mata kafin ya ɗaga hannu cikin sigan hauka yace "ina kwana tsohuwa?"

da sauri ta juya ta bar wajen, meke faruwa? Ya Jajal? meya kawoshi gidannan?.


Jahad tana ganin ta juya ta tafi, ta shiga ɗakin tana cewa "happy birthday to you" cikin waka take faɗan haka, murmushi yayi ya rungumeta nan suka fara celebrating na birthday ɗin shi.



Noor bayan ta dawo daga school tazo ɗakin Hamida ta zauna, kallonta Hamida tayi cikin muryan tsofi tace "kin dawo?"

"eh kaka na dawo ya kika wuni?"


"lafiya kalau"


zama tayi a gefe Hamida tana satan kallonta domin tayi missing nata sosai, shiru tayi kana daga bisani tace "Kaka?"

girgiza kai tayi, "ina missing yayana Kabir kuma ina missing Shaira, ga Sabir ma ya mutu"

a firgice Hamida ta kalleta "wani Sabir?"

tayi tambayan cikin kiɗima, da mamaki Noor tace "kinji labarinshi ne kaka? naga kin tsorata da jin maganar shi?"


nutsuwa tayi "a,a banson jin labarin mutuwa ne ƴar nan, jikokina dayawa sun mutu hakan yasa idan anamin maganan mutuwa sai naji kamar zanyi kuka, amma shi Sabir ɗin rashin lafiya yayi?"


Girgiza kai tayi "A,a kasheshi akayi, a bayan gidanmu aka jefar da gawanshi, Kabir kuma wata ce wacce muka zaune tare da ita a gidannan ta sace shi, bamu san me mukayi mata ba, sunanta Hamida"


jikin Hamida yayi sanyi tace "kiyi hakuri ki daina kuka, kunada tabbacin itace ta sace shi?"


"A,a Abba ne yaga shaida a ɗakinta, kafin ayi wani magana har Unty Jahad ta kira police ta sanar musu, ni har yau ban yadda cewar unty Hamida zata aikata hakan ba, gashi har yanzu babu labarinta tun time ɗin da aka samu matsala a prison, mutane dayawa sun mutu, Ammi taje amma babu Hamida, munyi kuka nida Yah Jawad da ammi dan an tabbatar mana Hamida ta mutu"

kuka take sosai, "yah Man ya fara shan giya, basa shiri da Jawad ko kaɗan kullum cikin faɗa, rannan har wuka ya zaro wai saiya kashe Jawad, gidanmu a lalace yake, Unty Jahad kuma tafi bawa wannan me taɓun hankalin kulawa akan yah man, na lura da hakan ban faɗawa kowa ba saboda ina tsoro"


Hamida batasan lokacin da kuka ya kwace mata ba, batasan haka rayuwa ta koma musu ba, lokacin da taga man saida ta firgita domin duk ya firgice ya fita a hayyacinshi, runtse ido tayi tana tuno lokacin da yake asalin Man nashi, hakuri ta bawa Noor cikin muryan data koya na tsofi, yanzu batada abin zargi sai Jahad, sabida meyasa take bawa ya Jalal kulawa? tausayi? no something is fishy"



a halin yanzu Jahad kokarin saida gidan suke itada Jalal, wannan shine last plan nasu, daga wannan zasu tattara su gudu itada Jalal, Hamida tana kula da Abba tana iya bakin kokari wajen ganin yaci abinci ko yasha magani, hakan yasa jikinshi yana sauki, baya dai magana amma alhamdulillah, Ammi na kokarin zuwa wurin aikatau da take, Jawad yana zuwa aikin gini yana bawa Ammi kuɗi ya fita a hanyar ya Man ya kama gabanshi abinda yake gabanshi shi yake yi, Hamida na kula da duk wani motsin kowa na gidan kuma alhamdllh ta fara gano bakin zaren.



Man, kwance yake akan bed yana baccin safe kamar yadda ya koya yanzu, lulluɓe jikinshi yake da blanket cikin kwanciyar hankali yake bacci, turo kofan akayi Jawad ne wanda ya gaji da rashin fitan man neman aiki dan an rufe hospital nashi, buga jikin gadon yayi, a hankali ya buɗe lumsashun idanunshi ya zubasu kan Jawad, kara maidawa yayi ya rufe yana cigaba da baccinshi, da karfi ya kuma buga jikin gadon "Yah man ka tashi muyi magana"

daga kwancen ba tareda ya buɗe ido ba yace "ina jinka"


"Yah man ya dace ka nemi aiki ai, ka duba rayuwar da muke ciki, Abba da Ammi suna buƙatar kulawa"


"kazo ka bani shawara ne ko gargaɗi?"


"kamar ya gargadi?"

tashi yayi a fusace yace "fita kabar ɗakin nan"


Jawad ranshi a ɓace yace "bazan fita ba gaskiya"

a harzuke ya tashi ya fara jan Jawad ɗin zuwa waje, ganin yana mishi taurin kai ya fara marinshi, Allah ya isa shine abinda Jawad ya faɗa, nan fa ya fara dukanshi bakin Jawad kuma yaki yin shiru, mutanen gidanne suka fara taruwa, Noor tazo tana jan Jawad ganin man yana shirin mishi illa, Jahad na tsaye ta naɗe hannu a kirji tana kallon abinda yake faruwa, ganin man yaki barin Jawad Noor ta tureshi cikin masifa tace "zaka kasheshi ne?"

nan fa ya fara wanke Noor da mari, tana kuka tana cewa Jawad ya tafi, Ahmar baya gida sai Jahad da Hamida, da ɗan sauri Hamida ta karaso wurin cikin dressing na tsofi, ganin abinda yake faruwa ta juya ta kalli Jahad cikin mamaki tace "ke ƴar nan ba zaki rabasu bane?"

girgiza kai tayi cikin kasa da murya yadda ita kawai zataji tace "kema ba kina da hannu ba kaka?"

bata kulata ba taje wajen tana rike Man wanda ya fusata yana aikawa kannenshi duka, ganin ba zai kyalesu ba ta tureshi da karfi, baya yayi ya faɗi tareda ɗagowa yana tunanin ya akayi ta iya tureshi haka da wannan shekarun nata? Kafin ya ɗago ta nunashi da yatsa "jini yafi ruwa kauri, wannan kannenka ne ciki ɗaya kuka fito, babu wani mahaluki wanda zaifi maka su, koda ko matarka ce, wasu suna neman kanne basu samu ba, wasu kuma an rabasu da ƴan uwansu, kai ka samu kuma kake haka? daga yau idan ka sake taɓa ɗaya daga cikin wadannan zaka fuskanci fushina"

hannunsu ta rike suka barshi zaune a wajen yana binsu da kallo, ranta idan yayi dubu ya ɓaci, zasu wuce Jahad ta riko gefen lifayanta cikin sanyin murya irin na shu'umanci tace "kaka kanne basu fi Mata ba, domin abinda na sani a kanshi dayawa basu sani ba"

cikin zafin rai Hamida ta juyo "me kika sani a kanshi wanda basu sani ba? saide ta ɓangaren jikinshi amma ta hali da komai sun fiki sani"


Kwace mayafinta tayi daga hannunta, murmushin rainin hankali tayi sannan ta juya idanunta ta zubawa Hamidan "kwarai haka ne amma ai kinfi kowa sanin mata tafi sanin sirrin miji akan kanne ko? ko ke baki taɓa aure bane a haka kika tsufa"

da wani zazzafan mari ta ɗauke fuskar Jahad, dafe kunci tayi tana mata kallonta wanda idan tayi maka da wuka ka kara kwana a duniya, idanunta sunyi jawur ta ɗago cikin zafi zata rama da sauri Jawad ya rike hannunta "idan kika sake kika rama wannan marin wallahi saina manta ke matar yayana ce"

sakin hannun yayi da karfi, jikin Jahad ya fara rawa hannu take shirin sawa a aljihu ta ciro wuka Man ya mike, riketa yayi ya wuce ciki da ita, juyawa tayi tana aika musu kallon da ba wanda yasan ma'anarshi sai ita, tafiya sukayi zuwa ɗakin Hamida tace idan zasu kwanta su rinƙa rufe ɗakinsu kada wani abun yazo ya faru, haka kawai taji bata yadda da Jahad ba.




Jiddah Ce✍🏻

No comments

Powered by Blogger.