Doctor Mansoor 21

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    Na

_Jiddah S Mapi_*Chapter 21*                 ~Haka rayuwa taci gaba da tafiya, Hamida tana cikin kulawa a gidansu Maryam, Unty maryam ta samu wani wanda yace zai aureta, ta amince da auren domin babban mutum ne wanda Abba ya amince dashi, ta yadda da zaɓin iyayenta, Aliyu ya jima da aika mata saki ta waya, Hamida tana zuwa school Alhmdllh yanzu tana karatu babu me takura mata, saɓanin da Kabir baya barinta ta huta, itace ta fara neman tsokanarshi domin a lokacin bata yadda da kowa me karashen suna da R ba, bayan tayi bincike ta gano Kabir mutumin kirki ne kamar yayanshi, hakan yasa koda yayi mata wulakanci bata damuwa, domin Kabir yanada tausayi duk freinds nashi shike biya musu kuɗin school, kuma ya jasu jiki duk da kasancewarsu ƴaƴan talakawa hakan baisa ya kyamacesu ba, ko ina ka ganshi to suna tare dashi, missing ɗin faɗansu tayi sosai, a halin yanzu ta goge wajen karatun low kamar yadda tasa a ranta tun lokacin mutuwar Amrah, abu ɗaya take fuskanta shine Ashman baya dariya baya sakin fuska sai fishi da harara, hatta kannenshi tsoronshi suke sosai, unty maryam ma wani lokacin tana tsoronshi, Manal idan ta ganshi nutsuwa take sosai bata ko magana sai ya bar wajen, ko kuma ta fara magana kasa-kasa kamar munafuka, Faiz da Zayn suna university a nan Abuja suma karamin tsoron Ashman suke ba, captain yanada kwarjini sosai.


ɓangaren captain Man, tunda yaga yarinyar nan a haka ya gagara samun nutsuwa, daya ganta a cikin gida koda hijabi ne saiya tuna yadda ya ganta ranan, kwance yake akan maƙeƙen Bed ɗinshi wanda yake ɗauke da lallausan katifa da kuma pillow's masu laushi, ya rufe jikinshi da farin blanket idanunshi a lumshe kamar me bacci, a zahiri kuma ba baccin yake ba tunanin yarinyar ya cika mishi konya, knocking akayi da ɗan karfi, saida akayi kusan sau uku kafin aka turo kofar, shiga tayi tana leke tana jin tsoro, dressing tayi cikin pink ɗin kaya riga da skirt na kanti, gashinta ta kame gida biyu kowanne tasa mishi ribbon pink, irin yanda ake yiwa yara, ganinshi a kwance ta tsaya tana murza dogayen yatsunta ɗan karamin bakinta ta buɗe ta zaci yana bacci ne, a hankali tace "yawwa bari na ɗauke wancan zoben na ɓoye ranan da zanje school saina sa a hanya, ai zoben mata ne bana maza ba, kullum ina kallo kuma baya sawa kawai ya ajiye"

cikin sanɗa taje gaban drower ta ɗau zoben tasa a yatsanta, ba karamin kyau yayi mata ba a hankali ta furta "wow zoben ya hasko, Hamida ki ɓoye"

ɓoyewa tayi a hannunta kafin ta ɓoye hannun ta cikin riganta, tafiya take a hankali wai kada ya jiyota, saida tazo gabanshi tace "Momy tace kaje kayi breakfast gari yayi haske sosai"

bata kuma faɗan komai ba ta fita daga ɗakin tana murnan yau ta ɗauke zoben, batasan meya kawo zoben mata ɗakinshi ba kuma tasan bana unty maryam bane, bana Manal bane, ɗakinsu taje ta ajiye a gaban mirror kafin ta fita ya sanarwa Momy cewar ta gaya mishi, taruwa sukayi a dining kamar yadda suka saba kowani safiya, kowa yana cin abinda yakeso, Hamida na tsakiyan Faiz da Zayn tana basu labari kasa-kasa dan Abba ya hana surutu idan sunacin abinci, taka matattakalar yake cikin nutsuwa da kasaita, rigan ball ne a jikinshi da wando dogo, alama yana shirin zuwa ya ɗan buga ball idan ya gama kari, murɗaɗɗen jikinshi ya bayyana ta cikin rigan da yake armless ne, hannunshi rike da cup na ruwan sanyi, da safe shayi ake sha amma shi da ruwan sanyi yake farawa, janyo kujara yayi ya zauna sannan ya ɗan russuna ya gaida Abba da Momy, amsa mishi sukayi ya gaida Unty maryam, itama ta amsa, a tare suke haɗa baki wurin gaisheshi, a dakile ya amsa, janyo flask na abinci yayi, wainar kwai da pitato ya zuba akan plate ɗinshi a hankali ya fara ci cikin nutsuwa, tsit sukayi babu wanda ya kuma magana, Hamida sai rarraba ido take domin ita kaɗai tasan abinda tayi, tunda baiyi magana ba ya manta da zoben ne, ta faɗa cikin ranta, nan ta sake taci abinci sosai, Manal ta tashi bayan tace "Alhamdulillah" zata tafi Hamida ma ta mike tana goge bakinta da tissue, "na gode" ta faɗa musu su duka, wannan ɗabi'anta ne duk lokacin dataci abinci saita gode musu, Abba ya hanata hakan taki bari, saida tayi nisa zata haura sama yace "ki maida zoben da kika sata"

waro mayan idonta tayi atake kuma ta runtse "wayyo Allah ya akayi ya sani? kodai yana da aljanu ne?"


bai juyo ba yasan dai tana tsaye tana shocking, a hankali tace "tom zan mayar"

"ɓarauniya"

ya faɗa yana cigaba da cin abincinshi, jan jikinta tayi wanda yayi mata nauyi ta riko hannun Manal wacce take rarraba ido tana jiran taji dukan da zaiyiwa Hamida, tafiya suka fara Hamida kamar tayi fitsari a wando, saida suka shiga ɗaki Manal tace "meyasa kika ɗaukan masa zobe?"


"wallahi Manal bansan ya sani ba, wayyo Allah yau zansha duka ko?"

jijiga kai Manal tayi, domin tasa halinshi, "saide ki yiwa kanki hukunci kafin yayi miki, haka mukeyi ida mu mishi laifi"


"na shiga uku ni Hamida wani hukunci zanyi?"

"kije ki ɗibo ruwa ki wanke duk motocin gidannan kuma ki tabbatar ya ganki"

hawayen tsoro ya cika idonta hannu tasa ta ɗauko zoben tace "na jawa kaina masifa"

maidawa tayi inda ta ɗauko sannan ta juya ta fita daga ɗakin, kasa ta sauka ta fita zuwa waje, kallon motocin gidan tayi zasu kai tara, runtse ido tayi taje bakin pompo ta naɗe skirt nata daga sama, ganin yana jikewa ta koma ɗaki tasa wando three quarter, riga baƙi me guntun hannu tasa kafin ta fito tana ɗaura kanta da karamin mayafi baki, takalmi ta hango a kofar ɗakinsu Faiz da sauri taje ta cire nata tasa nasu domin bataso ruwa ya jika mata nata, yayi mata girma sosai domin takalmin maza ne, ruwan ta ɗibo ta fara wanke motan, gaba ɗaya ta jika jikinta har fuskarta kumfa ne, motoci uku ta wanke ta rike waist ta gaji sosai, daurewa tayi taci gaba da wankewa.


bayan ya gama wasan ƙwallon kafa daya zame mishi jiki ya ɗau goran ruwa yana sha, hannunshi ɗayan rike da ball yana wasa dashi, hangota yayi tun daga nesa, sai kicinya take tana shirin hawa kan motan, kallon kafarta yayi takalminshi tasa lalle wannan yarinyar, jikinta ya jike da ruwa sosai kamar kanta take wankewa ba mota ba, shikam ya manta da satan zoben da tayi mishi, yasan kuma Manal ce ta sanar mata tayiwa kanta punishment kafin shi, takowa ya fara zai wuce ɗaki yaji yana kara son ganinta, jingina yayi da jikin wani karfi ya fara kallonta, wandon ya mata kyau sosai, daidai gwiwa ga rigan daya ɗan kamata, murmushi yayi ganin har kanta ya jike da ruwa, saida ya kalleta sosai sannan ya shiga ciki, ta wuni tana wankin mota, Momy tace ta bari taki yadda, Unty maryam tana busyn aurenta batama kula da abinda Hamidan tayi ba yau, a gajiye ta shigo palour hannunta rike da soso da brush, har hamma take tana mika tsaban bacci da gajiya, yana daga kan up yana kallonta har ta faɗa kan sofa tana faɗin "wash na gaji"

dariya yayi sannan ya juya ya bar wajen.


*********************

*bayan shekara ɗaya*


komai ya canja a rayuwar Man, an rufe hosiptal nashi sakamakon wani audio da akayi recording aka yaɗawa mutane, hakan ya tabbatar da yana zibar da ciki, case kala-kala aka fitar akanshi, wanda Jahad da Jalal ne suka shirya wannan shirin, Abba yana kwance har yau ba bakin magana, Jahad ta lallaɓa ta sanar mishi an dakatar da komai nasu, hatta busyness nashi an dakatar sakamakon abinda Man yayi, ba karamin kaɗuwa yayi ba hakan yasa bakinshi baya buɗuwa har yayi magana, sai ido kawai, Ammi ta lalace ta rame sosai damuwa ya taru yayi mata yawa, Jalal yana zaune a gidan da sunan ya fara samun lafiya daga ciwon haukan da yake, Jahad har yau bata yadda wani abu ya shiga tsakaninta da Man ba, hasalima ta maidashi mashayin giya na gaske, baya iya zama ba cikin maye ba, gidan ya lalace, Jahad ce take mulki da gidan ba tareda kowa ya sani ba, Noor an cireta daga school ɗin masu kuɗi an maidata government domin rashin kuɗi, Jawad yace ya hakura da karatun sai Allah ya basu kuɗi zaici gaba, Ahmar ne yake taimaka musu, kullum yana cikin kuka da damuwa akan abinda yake faruwa da gidansu, hakan yasa ya rame ya lalace, ma'aikatan gidan duk an sallamesu saboda babu kuɗi, idan kaga Family ɗin Alhaji Muhammad Dikko sai ka zubda hawayen tausayi.


Ammi ce zaune kasa tayi tagumi tayi shiru, babban damuwarta shine rashin magana da Abba yake yi, saide ya kalleka ya ɗauke kai kawai, abinci ma a kwance yake ci, gashi sun saida komai na gidan kama daga kujeru har motoci da sauran kayan amfani, Jahad tana ɗaki tareda Man wanda ya zauna yayi tagumi, ya rame shima ya lalace, sai hasken daya kara, da kyau wanda baya taɓa gushe mishi, kallonshi take shima ya kalleta "meyasa kike kallona haka wifey?"

lumshe ido tayi "tausayi kake bani, bansan yadda rayuwarka na gaba zai kasance ba"

matsowa yayi kusa da ita yace "tunda kina tare dani zai zamo da sauki"

a zuciyarta tace "gara bana tare da kai zakafi samun sauki Man"


"Jahad?"

"na'am"


"Meyasa kike guduna?"


shafa kanshi tayi sannan ta janyoshi sosai ya kwanta a jikinta, cikin sanyin murya tace "mu fara settling na komai, kada haihuwa yazo mana ba shiri hakan zai kara dagula lissafi ne, yanzu Abba shine a gabanmu mu nema mishi lafiya kafin komai"

"hakane ina sonki Jahad"


"nima ina sonka"

shiru yayi a jikinta yana tunanin makomarshi, har baison fita ya haɗa ido da Ammi, baison ganin mahaifiyashi a wannan halin, hakan yana raunata shi, zuciyarshi tana karyewa, ga Ahmar wanda idan ya kalleshi sai ya fara kuka, wuri ɗaya yake samun sauki shine Jahad, itace take bashi nutsuwa da kwanciyar hankali, ya yadda da matarshi hundred percent, ba yason wani abun rashin fahimta ya shiga tsakaninsu.Ammi ta fara fita neman aiki saboda itama ta samu matsala a wajen aikinta, cikin sa'a ta samu aikin wanke-wanke a gidan wasu masu kuɗi suna biyanta duk wata, wannan aikin shi yake taimaka mata tana kula da maganin Abba, ba wanda yasan ta samu matsala a wajen aikinta kullum shiri take tace zataje wajen aiki, a tunaninsu can take zuwa, ita kuma idan ta fita saita wuce inda take wanke-wanke, Jahad tasan da hakan domin duk wani motsi na gidan sun sani itada Jalal, tana zuwa wajenshi kullum da dare, sai sun gama abinda zasuyi kafin ta dawo wurin Man.


Ammi ganin bata samun lokacin Abba ta fara neman tsohuwa wacce zata rinƙa kula dashi, anyi sa'a matar da take yiwa aiki tace akwai tsohuwar data sani wacce zata haɗasu ta rinƙa yiwa Abba hidima, tayi farin ciki da hakan tace a haɗata da ita gobe idan ba damuwa.washe gari bayan tazo aiki matar tace ta jira tsohuwar zata zo anjima hakan kuwa akayi, saida ta jira zuwa mangrib kafin ta shigo gidan, lifaya ta naɗe a jikinta irin na tsofi ɗin nan, sai takalmi irin na tsofi na roba, idonta sanye da siririn glass me irin me igiya, ido Ammi ta zuba mata tana ganin wannan ai tafi ƙarfin zama me kula da Abba, zama tayi a gefe tana kallon Ammi wacce ta faɗa duniyar tunani, tafi tayi firgigit ta dawo hayyacinta, cikin muryan tsofi wanda baya fita  tace "na shirya kula da mijinki tareda bashi magunguna na zamani dana gargajiya Allah ya albarkaci nemanki"


"Ameen mama na gode"

tare suka koma gida, ido tsohuwar ta zubawa palour, saida Ammi ta juyo tace "muje mama"

Man ne ya sauko da wani riga wanda ya ɗanji jiki kaɗan, lumshe ido ya yiwa Ammi sannan ya karaso yace "barka Ammi kin dawo?"


"eh man na dawo, wannan itace sabuwar wacce zata rinƙa kula da Abbanku, tanada ilimi akan magungunan gargajiya dana zamani, kuma kaga ina zuwa aiki banida wani lokaci dayawa"

jijjiga kai yayi ya durkusa har kasa yace "ina wuni kaka?"

hannu ta ɗaga mishi "lafiya" kawai ta faɗa, da taimakon Ammi suka karasa cikin ɗakin da Abba yake kwance, hawaye ne ya cika idanun tsohuwar Ammi tana kallonta itama tayi shiru domin su ɗin abin tausayi ne, ɗakin dake gefen na Abba anan aka sauketa, gobe zata fara aikinta.
*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.