Doctor Mansoor 20


 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

_Jiddah S Mapi_

*Chapter 20*

                 ~Hamida kukan me kike? 

muryan Manal taji wacce take tsaye a kanta yana mamakin yadda take kuka kamar zata shiɗe, ajiye pillow tayi ta share idonta kafin ta juyo tana kakalo murmushi "ba komai Manal kawai ina tausayin unty maryam ne kuma na tuno abinda ya faru dani ne a baya"

zama Manal tayi a gefenta tace "bansan abinda ya faru dake ba, ba kuma zan saki faɗamin dole ba, saide zan baki shawara ki manta abinda ya faru a baya"

girgiza kai tayi hawaye yana sauka tace "ba kowani abu ake iya mantawa ba Manal, akwai abinda koda ka manta sai ya dawo maka sabo cikin kwakwalwar ka, Manal zan iya mantawa amma bazan iya yafewa ba, zuciyata zata fashe.."


"ki daina kuka kiyi addu'a Allah ya shige miki gaba, duk abinda zakiyi kada ki manta da akwai Allah wanda yake shirye da karban addu'an bayinshi a koda yaushe, idan an zalunceki kinga zaki iya ramawa ki tashi ki roki Allah kuma kisa a ranki zaki rama, sai kiga Allah ya shige mike gaba, kuka da tunani da hasashe basa haifar da komai sai bakin ciki, dauriya da sa abu a rai shike da kuma addua sune makami sune zasu taimaka miki, sai kin tsaya kin cire tsoro kin daure kafin zaki cimma burinki, tunanin abinda akayi miki zai baki karfin gwiwa amma kuka ba zai gyara miki komai ba"


maganganun Manal sunyi tasiri a wajenta, hakika gaskiya Manal ta faɗa mata wanda ta manta dashi, dole ta nemi hanyar ɗaukan fansa, tasan Man sharri yayi mata dan kawai ya tsaneta, runtse ido tayi tana tuno Jahad wacce take tausaya mata, har ta bata kuɗi a prison, Allah sarki Jahad da Noor da Jawad, ko ina ya Ahmar? shima ya tsaneni, kallon Manal tayi "ba komai na gode da shawara kuma zanyi aiki dashi"


"yawwa ko kefa"


hira suka fara sosai Manal tanada surutu itama Hamida akwai surutu duniya ce tasa tayi shiru, wanke zuciyarta tayi da niyyan zama a cikin gidan, hakan kuma ba zaisa ta daina tunani da nemo hanyan da zatabi domin ɗaukar fansar abinda akayi mata ba, Man nayi nesa daku amma zuciyata tana kusa daku.




"Jahad tana taka tsantsan da Jalal sosai, duk wani hanya da zaiga abinda kishinshi zai motsa duk ta toshe, hatta zama da Man batayi a palour idan tasan Jalal zai shigo, a halin yanzu suna haɗa wani babban plan ne wanda idan sun gama zasu bar gidan"

Kullum da safe ita ke kaiwa Jalal abinci, Ammi tana kula da Abba wanda yake kwance baya iya tashi, magana ma kaɗan-kaɗan yake yi, Man da Ahmar suna iya bakin kokari a matsayinsu na likitoci domin kwato rayuwarshi.


*Monday/june/20*


shirye shiryen breakfast take a kitchen sauran ma'aikatan suna taya ta, bata taɓa yadda wasu suyi girki a gidan idan ba ita bace, hakan kuma tanayi ne domin Jalal girkinta kaɗai yake iya ci, bayan ta shirya komai a dining Kamar yadda ta saba, breakfast ɗin Jalal ta ɗauka ba tareda ta juyo ba tana sauri taga ta kai mishi domin lokaci ya ɗan ja, tare mata hanya yayi yana kallonta, gefenshi tabi zata wuce ba tareda tayi mishi magana ba, kallon rigan jikinta yayi na bacci ne bata cire ba har yanzu, kuma haka take niyan zuwa wurin wannan mahaukacin, kara tare hanya yayi, "dan Allah ka matsa Man sauri nake"

"kina sauri ki kaiwa mahaukaci abinci a haka?"

kallon jikinta tayi bataga laifin hakan ba, tace "ba komai ai shida baya hayyacinshi me zai gani?"

matsa mata yayi domin baison ɓacin ranta kuma gaskiya ta faɗa, tafiya ta fara cikin sauri, knocking na kofar tayi, buɗewa yayi yana kallonta, a hankali ya juya zai koma, cikin fishi, murmushi tayi Jalal rigima yanzu har fushi wai yayi?

shiga tayi saida ta tura kofan kafin ta ajiye plate ɗin, hugging nashi tayi ta baya tana shafa kirjinshi, baiyi magana ba kuma bai hanata ba, cikin shauƙi tace "i miss you so much sweetheart"


janye jikinshi yayi, wurin plate ɗin yaje ya zauna tareda naɗe kafarshi da hannun riganshi, coffee ya haɗa a karamar cup ya fara sipping a hankali baiko kara kallonta ba, lanƙwasar da kai tayi tareda rungume hannayenta tana ɗan taɓe baki, takawa ta fara har zuwa gabanshi, hannu tasa ta kwance igiyan rigan baccin dake jikinta, saukewa tayi zuwa kasa ya rage daga ita sai bra da wani ɗan iskan gajeren wando, wandon irin bomshort ɗinnan ne, matsowa tayi kusa dashi tasa hannu a jikin aninin riganshi ta ɓalle, sauke rigan tayi zuwa kasa kafin ta rungumeshi da karfi, haɗuwan fatar jikinsu ya haifar mishi da kasala da kuma saukowa daga fushin da yake, dama tasan lagonshi idan yana fushi haka take mishi, a kunnenta ya raɗa "meyasa baki zo da wuri ba? banso kina spending time naki a wurin wannan man ɗin you know I really hate him"


"Sorry nima bada sona nake zama kusa dashi ba, kasan ƙaddara ce tazo da haka amma soon hakan zai daina faruwa"

ɗago kanta yayi ya haɗa bakinshi da nata, hot kiss ya fara aika mata, itama tana mayar mishi cikin kewanshi da tayi, hannunshi na yawo a jikinta, Sabir wanda ya kunna ruwan pompo ɗin ɗakinshi yaki zubowa, gashi so yake yayi wanka, bokiti ya ɗauka ya nufi bayan gidan domin ɗibo ruwa a pompo na cikin gida, har ya cika zai koma ciki wani abu yace ya leka ɗakin wannan mad man ɗin domin yaji shiru kuma bai ganshi a waje ba yau, a hankali ya fara takawa domin baison ya ganshi lekashi kawai zaiyi, daidai bakin kofar ya tsaya, hannunshi yasa ya tura kofan yana lekawa, idonshi ne yayi mishi mummunan gani, da sauri ya murza idanunshi yana kara kallonsu, tabbas Jahad ce kwance kasa wannan mad man ɗin yana kanta, jikinshi ya fara ɓari yaso tura kofan da karfi domin a zatonshi ko da karfi ya danneta, turus yayi jin muryan Jahad kasa-kasa tana cewa "i love you so much Jalal, i miss You"

shima Jalal cikin shauƙi da yanke numfashi yace "i love you Jahad"

baki ya buɗe tareda kwalalo idanu waje, rufe kofar yayi a hankali ya juya, bakin pompo ɗin ya zauna tareda dafe kanshi, ji yake kamar mafarki ne ba gaskiya ba, sai furta "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" yake, ya rasa me zaiyi, yasan babu me yadda da zancen idan ya faɗa, Innalillahi Jahad bai taɓa zaton zatayi haka ba, mikewa yayi "dolene na sanarwa ya Man abinda yake faruwa" ɗaukan ruwan yayi, jikinshi har yanzu bai daina rawa ba, ɗakinshi ya kai ruwan kafin ya fito ya nufi ɗakin Man, sallama yayi tareda budewa cikin tsoro, ganin Man tsaye yasa riga da wando bakake, kanshi rufe da hulan rigan dake jikinshi, ya tsaya a bayanshi cikin sanyin jiki da rashin jin daɗin abinda zai faɗa yace "Yah Man zan faɗa maka wani abinda nasan ba zakaji daɗinshi ba, inaso ka biyoni ɗakin wannan mahaukacin yanzu please"


make kafaɗa Man yayi alaman ba zaije ba, girgiza kai Sabir yayi kafin yace "yah Man kaje ka gani da idonka, unty Jahad kwance da wannan mahaukacin, ni kaina banyi zaton hakan daga gare ta ba, ashe cin amanarka take, halin da take nunawa ba shine asalin nata ba, muguwa ce maciya amana"

karasowa yayi wurinshi a zatonshi ko ya girgiza ne da jin maganar, riko hannunshi yayi yace "muje ka gani da idonka"


a hankali ya juyo, da sauri Sabir ya koma baya ganin fuskar Jahad ɗauke da murmushi, janye hulan daya rufe mata kai tayi, a hankali ta fara matsowa wurinshi hannunta cikin aljihun bakin rigan dake jikinta, fuskarta ɗauke da murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarshi, ja da baya ya fara yana kiran "ja..ja.jahad"

ido ɗaya ta kashe mishi kafin tace "yeah nice, baka ƙarasa ba Jahad Kada, ko kuma Jahad mage me kwanciyar ɗaukan rai, ko kuma Jahad kanwar shaidan duk sunana ne"


hannu yasa zai buɗe kofa ya gudu, ji yayi kofar a rufe, da sauri ya juya yana bubbuga kofan ido huɗu sukayi da Jalal wanda yake tsaye a bakin window yasa hannu cikin aljihun bakin riga kamar yadda Jahad tayi.


"Idan kuka taɓani ya Man ba zai barku ba, ku buɗemin kofa na fita"

girgiza kai tayi tana kallonshi cikin murmushi tace "Yah Man? to wa zai faɗa mishi munyi maka wani abu?"

kallon Jalal tayi tana ɗaga gira ɗaya "Baby kaine?"


matsowa yayi ya dafa kafaɗarta "a,a nikam ba zan faɗa ba, saide ko kece zaki faɗa mishi tunda mijinki ne"

kallon cikin idonshi tayi tana turo baki tace "nikam banida wani miji sai kai, kaine farko kuma karshen mijina"

dariya ya kwashe dashi itama ta tayashi kafin ta murtuke fuska ta koma salin Jahad nata na mutuwa ta matso kusa dashi hannunshi ta riko da karfi ya kwace "don't dare touch me zanyi miki illa"

dariya tayi sosai hadda rike ciki, wuka ta ciro daga cikin aljihu ta fara shafawa tana murmushi tareda kallonshi 

"Sabir banso ka mutu ba amma sa ido da sanin sirrina shine zai kasheka"

"baki isa ki kashe ni ba"

"kana da ja ne?"

jijiga kai yayi, ganin tana matsowa ya wanketa da mari, dafa kunci tayi, a harzuke Jalal yazo zai kai mishi duka da sauri ta rike hannunshi tana girgiza mishi kai, sakin hannun tayi ta ajiye wukan a gefe, rigan sanyin ta cire kafin ta ɗaura a waist ɗinta, hannun riganta ta naɗe ya koma guntu, takowa tayi zuwa wajenshi ta kalli Jajal wanda yake huci "tsa tsa tsa Baby calm down, and banso kasa hannu a wannan faɗan please, nayi alkawari idan yafi karfina zan kyaleshi da rai"


Sabir ma matsowa yayi yana fuskantar ta, mari ya kuma ɗauke ta dashi, kara dafe kunci tayi, takai 2mins tana durkushe kafin ta ɗago tareda kai mishi wani mugun bugu a cikinshi, saida yayi baya ya faɗi, hannu tasa ta ɗagoshi ta kara kai mishi wani bugun a ciki, saida jini ya fito daga bakinshi, sakinshi tayi ya faɗi kasa, Jahad ta iya faɗa ba kaɗan ba, tasan duk inda zata buga a jikin mutum yaji ciwo, kafarshi fara takawa da karfi, rike ciki yayi yana aman jini, wukan data ajiye a gefe ta ɗaga, fara shafa jikin wukan tayi tana murmushi, ɗaga wukan tayi sama ta saita daidai cikinshi "Bye Sabir"

daɓa mishi tayi, baki ya buɗe zaiyi ihu da karfi ta toshe bakin, yana shure-shure tareda zaro ido taki sakinshi har saida taji ya daina, alaman ya mutu, da gudu taje wajen Jalal ta rungumeshi, jikinta ya fara ɓari tace "na kuma kisa Jalal"

matseta yayi a jikinshi yana cewa "ki nutsu ki cire kayan nan"

cire rigan tayi da wandon duka, kayan baccinta ta maida kafin tasa wancan a leda ta mikawa Jalal, karba yayi saida ta saita kanta kafin ta buɗe kofan ta leka, ganin babu kowa ta nufi palour ta duba ba kowa, da ɗan gudunta tazo tayi mishi alama daya fito, gawan yasa a cikin akwati da kyar ya fara ja, tana tayashi har suka fita dashi, ɓangarenshi suka kai da nufin anjima da dare zasu fitar waje ba tareda kowa ya sani ba, dawowa tayi bayan sun kai sun ɓoye, zata shiga ɗakin ya janyota da karfi, zaro idanu tayi tana jin tsoro sosai, kare mata kallo yayi sosai yana ganin kamar tana ɗan tsorace, hannu yasa yana maida ganshin kanta zuwa baya, cikin kulawa yace "meya sameki Baby? bakida lafiya ne?"

girgiza kai tayi tana kakalo murmushi "lafiya ta kalau, na ɗan gaji ne, bari naje nayi freshen up"

tayi maganan tana janye jikinta, kara riketa yayi sosai "Jahad duk duniya babu wacce nake so kamar ke, ina kaunarki sosai"


shiru tayi domin batada amsa, murmushi yayi "muje na tayaki freshen up ɗin"

batayi musu ba suka shiga ɗakin a tare, rigan ta cire ta ɗaura towel wanda bai rufe mata ko cinya ba, Jahad tana da diri shine abinda yake kara jan hankalin Man, zata wuce ya janyota ta faɗa kan gadon, zare towel ɗin yayi tana kwace jikinta ya danneta da karfi, sakar mata nauyinshi yayi yana kallon fuskarta, a hankali tace "zanyi wanka"

goga mata sajenshi ya fara a kumatu, lumshe ido kawai tayi, fara aika mata zazzafan sako yayi, itama maida mishi ta fara domin bataso ya zarge ta ko kaɗan, hannu yasa ya kashe wutan ɗakin, kayan jikinshi ya cire idanunshi sun rufe, baijin zai iya barinta yau, kullum tana ja mishi rai ko tsoron yadda zai tarar da ita take bai sani ba, ganin ya fara neman hanya ta tureshi tana kame jikinta, matsowa ya kuma yi sosai yana janyota, a hankali yace "kada kimin haka ina sonki sosai Jahad ki taimaka min"

kwace kanta tayi tace "ina zuwa"

tashi tayi taje wurin deep freezer ta ciro kwalban giya, buɗe wa tayi ta kai bakinshi, a hankali ya fara sha, saida ya shanye kwalba uku kafin ta kyaleshi, ai kuwa bacci ya ɓingire dashi, da sauri ta dira daga gadon ta maida kwalban cikin frij, wanka tashiga tayi, bayan ta fito ta shafa mai tareda sa riga da wando na material ta fita daga ɗakin, burinta shine su fitar da gawan Sabir kafin Ahmar ko Noor ko Jawad su gani, domin taci alwashin koda dukansu uku ne zasu gani saita kashesu, kwantar mata da hankali Jalal yayi cewar zai fita dashi, saide da safe suji labarin an tsinci gawan Sabir, tasan zai iya tunda ya faɗa, ta yadda da Jalal, ba wanda ta yadda dashi a duniya kamar Jalal.



Hamida tana zaune a gidan kowa yana nuna mata soyayya tayi kyau cikin kwana uku kacal, ta murje fatarta ta kara kyau ga kuma haske, saide kana ganin fuskarta zakasan tana cikin damuwa akwai abinda yake damunta a rai, Abbansu Maryam yasa a nema mata school ta ɗaura daga inda ta tsaya, tayi murnan hakan, saide batajin zataji daɗin wani abu koma bayan ganin Man cikin tashin hankali da kuncin rayuwa kamar yadda ya sata, Captain Ashman babu abinda yake shiga tsakaninta dashi sai gaisuwa, wani lokacin ya amsa wani lokaci kuma ko kallonta ba zaiyi ba, suna hutu shiyasa yake zaune a gida, badan haka ba shi ba ganinshi ake ba, yau talata tanada lecture da safe, tunda ta tashi asuba tayi salla ta fara gyara ɗakinta da Manal, saida ta shirya komai ta kimtsa kuma ta goge kafin ta shiga wanka, gashin kanta me tarin yawa da tsantsi ta wanke da shampoo me daɗin kamshi, sabulai masu gyara jiki tayi wanka dasu, sai lumshe ido take dan ƙamshin sabulun yana mata daɗi, tunawa da tanada lecture yasa ta watsa ruwa me ɗumi a jikinta, brush tayi sannan ta kalli inda suke ajiye towel, ganin babu babban ta dafe kai "oh ni Hamida ina kuma na ajiye babban?"

da karfi tace "Manaaal? ki bani babban towel, jin shiru ta tabbatar bata ɗakin, zaro karamin pink towel ɗin tayi tana kare mishi kallo, turo ɗan karamin pink lips nata tayi "wannan ai ko cinyata ba zata rufe ba"

ɗaurawa tayi taga bai rufe ba, "ashap ai na sani"

ganin lokaci yana kurewa ta kalli jikinta ta jikin madubin bayin, Allah ya bata farin fata, sai glowing take kamar ƴar wasu masu hannu da shuni, kallon santala santalan cinyoyinta tayi ta cikin mirror, "Hamida kinyi kiɓa"

ta faɗawa kanta kafin ta murɗa handle ɗin kofar ta fito cikin sanɗa, tana da kunya sosai bataso ko Manal ta ganta a haka, ganin bata ɗakin yasa ta saki jiki taje gaban mirror ta ɗau handrayer ta jona, fara busar da tulin gashinta tayi saida ya bushe me kyau kafin ta shafa mishi hair food, sheƙi ya fara sosai, ɗaga hannunta da take shi yakesa towel din kara janyuwa zuwa sama, hakan ya kara bayyana cinyoyinta wanda suke ta sheƙi, man baby oil ta shafa domin batason mai me kama jiki sosai, kuma baby oil yana karawa jikinta laushi, juyawa tayi zata je wurin wardrobe ta ciro kayan da zata sa, ido huɗu sukayi da captain wanda yayi suman zaune akan stool na gefen gadon, hannunshi rike da katon takadda da alama akwai abinda ya kawoshi, wani irin ihu tayi ta durkusa kasa tana kare jikinta, tattaro nutsuwa yayi sannan ya murtuke fuska cikin muryanshi da yake magana kamar me koyon magana yace "banson shashanci kisa hannu anan inji Abba"

tana gani ya ɗauke kai yana miƙa mata ta gagara tashi, sai kare cinyoyinta take, tsaki yayi jin bata karɓa ba tareda ya juyo ba cikin tsawa yace "ki karɓa mana"

da rarrafe ta janyo hijabin dake sakale a gefen gadon tana kallonshi har tasa, tashi tayi ta karɓi takaddan, biro ta ɗauko tasa hannu kafin ta mika mishi, fita yayi daga ɗakin ba tareda ya kuma kallonta ba.


ajiyan zuciya me karfi ta sauke tareda dafa kirjinta, ba karamin tsorata tayi ba.





*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.