Doctor Mansoor 19

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    Na

_Jiddah S Mapi_*Chapter 19*                 ~Meke faruwa nakejin ana kuka anan? muryan mahaifin Maryam ne ya bayyana a cikin kunnuwanta, da sauri ta juya ta saki Momy taje da gudu ta rungumeshi, tureta yayi ya juya baya "meya kawo ki?"

zubewa tayi akan gwiwanta tana kuka sosai tace "Abba na tuba, ka yafemin na tuba, duniya ta koyamin hankali"

bai juyo ba kuma baiyi magana ba, juyawa yayi zai tafi Hamida tace "Abba ta tuba ka yafe mata"

tsayawa yayi ya juyo yana kallon Hamida, hannu ya mika mata alaman tazo, zuwa tayi ta durkusa gabanshi tace "ina wuni Abba"

cikin sakin fuska yace "mun yini lafiya ƴata?"

jijiga kai tayi, cikin sanyin murya tace "ka yafe ma Unty Maryam tanada kyaun hali, itace ta taimakamin tun daga prison har zuwa nan, tasha wahala sosai ka yafe mata bansan abinda tayi ba, amma fushin iyaye yana da tasiri wurin lalacewan yara sosai"


jikinshi yayi sanyi sosai jin ta ambaci prison, Momy cikin tausayi tace "prison? Ya akayi kikaje prison Maryam?.."

hannu Abba ya ɗaga ya dakatar da ita "ba yanzu ba, suje ɗaki suyi wanka suci abinci, zuwa safe zamuji komai"

hannun Maryam ya riko ya ɗagata sama tareda rungumarta yace "kuje ku huta"

cikin kuka tace "na gode Abba"

kayan suka ɗaga zuwa cikin ɗaki, da alama ɗakin Unty maryam ɗinne, kallon ɗakin tayi bayan ta cire mayafin jikinta, bin ko ina take da kallo tana murmushi "Hamida nayi missing ɗin ɗakina hakika duk wacce taki jin maganar iyayenta ba zata kare rayuwarta lafiya ba, ga toilet je kiyi wanka"


shiga toilet tayi ta kwaɓe rigan jikinta tayi wanka, towel ta ɗaura tareda sa dogon hijabi ta fito, kanta a kasa ta iso gaban mirror ta shafa oil, rigan data cire takeson maidawa Unty Maryam tace ga kayan bacci kisa, wani riga dogo silk ta bata, rigan black ne da leshi a baki bakin zuwa kirjin, ba tareda ta cire hijabin ba tasa rigan kafin ta zare hijabin, kallonta kawai unty maryam tayi tana dariya a ranta, Hamida nada kunya sosai, itama wanka ta shiga tayi, fitowa tayi taga Hamida tana ramakon sallan daya wuce ta, bayan ta idar ta kwanta akan sallayan "ki tashi ki hau gado"

tashi tayi ta hau gadon ta kwanta, kashe wutan ɗakin tayi tace "bari naje na duba kannena bazan iya hakura zuwa da safe ba"

giɗa kai tayi domin bacci ya fara cin karfinta, batasan time ɗin da unty maryam ta dawo ba, bacci sosai ya ɗauke ta, ta gaji sosai dan ba karamin tafiya sukayi ba.*Asuba ta gari*


Mutanen gidan sun tashi da farin cikin dawowa Unty maryam, kannenta ne  guda uku Faiz, Zayn, da Manal, kyawawa ne kamar yadda itama maryam ɗin take kyakkyawa, a palour suke zaune suna tambayan maryam ya bayan rabuwa?

Hamida na gefe ta taƙure ta kasa sakin jiki dasu, gani take zasu kyamaceta dan ba kananan masu kuɗi bane, Manal tace "ki matso mana Hamida kinyi shiru"

murmushi kawai tayi, Momy tace "batada yawan magana"


breakfast aka haɗa musu me rai da lafiya, unty maryam tace "tashi muje"

a hankali ta mike tabi bayanta, kan kujeran dining suka zauna, mai aiki ce tayi serving ɗinsu, a hankali Hamida take cin abincin, Maryam ta kalli Momy "banga Ashman ba, ina ya shiga?"


"yayi tafiya sunje meeting, yau zai dawo, baisan da labarin zuwanki ba, sai yazo zai tarar, kinsan yanayin aikinsu sai sun samu hutu zasu samu zama a cikin mutane"


murmushi tayi a fili tace "Captain Ashman, yanzu har ya fini tsawo, kamar ba kanina ba, ina ganin hotonshi a Instagram, ƴammata sai comment suke baya musu reply"


murmushi kawai Momy tayi dan tafi kowa sanin halin Ashman, saida suka ci abinci kowa yayi hamdala Abba ya kalli Maryam "meya faru bayan kin bi mijinki, meya ramar dake kika lalace haka? ina soyayyan da kike mishi? sannan meya kaiki Prison?"


shiru tayi batason tuna abinda ya faru, saide ya zama dole ta bawa iyayenta labari, cikin sanyin jiki tace "Abba bayan na bijire muku na auri Aliyu pilot, muka koma garin Gombe da zama, yana bani kulawa sosai bayason abinda zai taɓani, ƴan uwanshi suna jin haushin abinda yake min, basa sona ko kaɗan, sharri iri-iri sunyi min a wajenshi bai yadda ba"


share hawaye tayi cikin jan numfashi tace "wata rana ina zaune a ɗaki bana jin daɗi tunda safe, Aliyu ya fita domin zasuyi tafiya me nisa kasancewarshi matukin jirgin sama, karan sautin tafiya naji a cikin gidan, a ɗan tsorace nace waye? babu amsa hakan yasa na kawar naci gaba da kwanciyata, ban ankara ba naji an riko hannayena ta baya, a firgice na wurga kafafuna sama ina kokarin kwatan kaina, danneni akayi da kyar na juya fuskata, wani mutum ne ya rufe fuska da bakin kyalle, na tsorata sosai hakan yasa na fara ihu, ganin zai illatani na fara dambe dashi ina kwatan kaina, wuka naga ya ciro daga aljihunshi, ya nufeni zai caka min, da gudu na ɗau wani kwalban turare na fasa, ganin ya nufeni gadan-gadan kawai na caka mishi a ciki, jini ya fara zuba a wajen dana ruɗe na fara kiran Aliyu a waya cikin rawan jiki, kusan 10miss call bai ɗaga ba, na tsorata ganin mutumin yanata shure-shure, bayan Aliyu ya ɗaga nace mishi nayi kisa, abin mamaki sai naji yayi tsaki, a tsorace nace tsaki fa kayi?

cikin tsawa yace kin kashe saurayinki kuma zaki kirani a waya kinamin kukan banza? cikin rashin fahimta nace me kake faɗa Aliyu?

ki hau online yanzu, cikin rawan jiki na buɗe data, wasu hotuna ya turamin, ina dubawa naga wannan mutumin ne tare dani a kwance kan gado cikin yanayi mata kyau, Abba na shiga tashin hankali ba kaɗan ba, wani tunani yazo min na fara shirin ɓoye gawan na gudu, hakan bai faru ba domin police ne suka shigo gidan, kamani sukayi suka samin ankwa a hannu, Aliyu yana jinmu ta waya yace ku tafi da ita kada ta sake zuwanmin gida bazan zauna da mazinaciya ba.


"nasha wahala a prison shara zasu sani da wanke kaya masu datti, babu wanda yazo dubani a cikin ƴan uwan Aliyu, shi kanshi Aliyu be zo ba, nayi kuka har na gaji, saida na saba da gidan yari kafin aka kawo Hamida wacce take taimakamin a duk lokacin da banida lafiya ko bukatar wani abu, na lura itama sharri akayi mata shiyasa na jata jiki, bayan anyi faɗa muka gudu, nasan inda muke ajiye key na gidan, shine na buɗe muka kwashe kayan, Abba shine labarin abinda ya faru"


Momy kuka take sosai na tausayin ƴarta, Abba ma dauriya kawai yayi domin labarin ya taɓa mishi zuciya, Manal dake gefenta ta rungumeta suna kuka tare, Faiz da Zayn suma da suke maza kuka sukeyi sosai.


Hamida taji tausayin unty maryam sosai, labarinta ya taɓa mata zuciya saide gara ita, akan Hamida wacce aka yiwa sharrin da batasan ma me suke faɗa ba, gyaran murya yayi bayan ya gama jin labarin ƴar uwar tashi wacce sukayi shekara 5 basu haɗu ba, shigowa yayi hannunshi cikin aljihu, uniform ɗin soja ne a jikinshi, cikakken namiji ne kyakkyawa, yafi unty maryam da sauran kannenshi kyau nesa ba kusa ba, fuskarshi babu yabo babu fallasa, kana ganinshi sai ka tsorata domin baya dariya, dogo ne sosai fari ne har ya fara zama yellow, bakinshi ɗan karami sosai, gashin kanshi wanda yasha gyara ba karamin kyau ya kara mishi ba, idanunshi irin na turawa cikinsu brown brown, eyelashes nashi zara-zara, ganin babu wanda ya kula da zuwanshi sun maida hankali kan kuka yace "ya isa"

a tare Zayn da Faiz suka ɗago, ganinshi ne suka sha jinin jikinsu kowa ya gyara zamanshi, Manal sakin Maryam tayi ta koma kujera ta zauna, kanta batayi zaton zuwanshi a wannan time ɗin ba, Maryam ta tashi da gudu ta rungumeshi tana kuka, bayanta ya shafa yana jin zafin abinda ya faru da ita, cikin muryanshi zazzaƙa yace "it's okay unty maryam"

sakinshi tayi tace "an zalunceni Man"

da sauri Hamida ta ɗago ta kalleshi jin sunan da Maryam ta kirashi dashi "MAN" 

ta furta a kasan ranta, batasan maganan yafito fili ba saida Manal tace "ki gaidashi da wuri"

a hankali tace "ina wuni"


baiko kalleta ba yace "lafiya"

zaunar da maryam yayi akan sofa ya kalli Momy da take aikin kuka har yanzu, saida ya lumshe ido ya ciji leɓenshi na kasa yace "Momy why crying? ba gashi ta dawo ba? please banson ganinki kina kuka"


cikin kuka Momy tace "kaga zaluncin da sukayi mata? Man an zalunci ƴata har prison?"


girgiza kai yayi baison ganin kukan Momy hasalima ciwon kai take sashi, Hamida jin sunan da suke kiranshi dashi yasa ta mike cikin dukar da kai tabar wurin, binta sukayi da ido kowa yana mamakin yadda ta bar wurin, ɗakin da aka nuna mata a matsayin nata shi ta shiga, kan gado ta faɗa ta janyo Pillow ta kifa a kanta, wani irin ɗan marayan kuka ta saki tana toshe bakinta da pillow, meyasa take haɗuwa da ƙaddara haka? ta bar Man acan tazo ta kuma tarar da wani Man ɗin?.
*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.