Doctor Mansoor 17


*Chapter 17*                 

~Rana bata karya saide uwar ɗiya taji kunya, yau alhamis cikin gidan Alhaji Muhammad Dikko cike yake da mutane abokan arziki da ƴan uwa, ƴan uwan Ammi daga Saudiya sunzo domin halattan bikin ɗanta Man, a

Dubai ta siyo kayan auren, sojoji dayawa masu kula da shiga da ficen mutane suna wurin sun kewaye gidan idanunsu akan komai da yake gudana, Amarya Jahad tayi lalle ja da baki ta tayi kyau sosai, jikinta sai shining yake domin Ammi yasa anyi mata dilka, tana zaune akan gado itada su Noor sai kallon masu shige da fice take, murmushin yaƙe take musu, anyi mata gyaran gashi an kame wuri ɗaya, Ammi ma na ɗakinta da kawayenta da ƴan uwa, ta zama busy, Laila na zaune a gefensu kan kekenta na marasa tafiya.


Man yana kwance a gefen Ahmar hannunshi rike da waya yana amsa sakon da ake mishi na barka da yau, tareda tayashi murnan zaiyi aure, sai murmushi yake yana reply, Ahmar kallonshi yayi warce wayan yayi yasa aljihu ya mike zai tafi, ɓata rai Man yayi "dan Allah ka bani"

"bazan bayar ba"

fita yayi da gudu ganin Man yana shirin tashi ya kamashi, da sauri ya dawo baya, Abba ne sukaci karo, "kun fara yarantan naku ko?"

shiru yayi yana dariya kasa-kasa, shiga yayi yace suje su gaisa da bakinshi wanda sukazo daga nesa, saida sukasa manyan kaya kafin sukaje Part ɗin Abba, gaisawa sukayi da abokan Abba ciki hadda Aminin Dady me rasuwa, bayan sun fito Man yaga yanayin Ahmar ya canja, dafa kafaɗarshi yayi tareda cewa "kada kasa komai a ranka Allah yaji kan Dady"

"Ameen Bro"



*Friday 2/june/2023*


bayan an idar da sallan Jumma'a aka ɗaura auren Mansoor da Jahad akan sadaki naira dubu ɗari biyar, cikin gidan cike yake da mutane, Jahad tana ɗaki tayi kwalliya tasa wani farin leshi wanda ya haskota sosai, hannunta rike da waya suna ta hira da Man, wata kawar Noor ce wacce suka saba sosai a school ta kalli Jahad tace "Noor Kamar na san amaryan"

dariya Noor tayi wacce tasha abaya purple hannunta da lalle me kyau ga makeup itama anyi mata, "may be a wayata Kika ga hotonta"

girgiza kai yarinyar tayi "a,a Noor nasan wannan fuskar amma na manta inda na sani, bari dai nayi tunani"

dafe kanta tayi tana tuno inda tasan fuskar, da sauri ta ajiye wayan da tayiwa Man sallama tana sauraran abinda noor suke tattaunawa da kawarta, kanta ta dukar kasa tana aikawa yarinyar mugun kallo, wanda idan tayi maka irinshi da wuya ka kara kwana a duniya, hannu yarinyar ta ɗaga tace "noor"

"na'am minal"


"na santa a jam...."

da sauri Jahad tace "Noor Ammi na kiranki"

fita noor tayi, ɗago kai Jahad tayi da idanunta wanda suka sha bakin eyelashes dogo-dogo da, manyan idanunta ta zubawa yarinyar tana aika mata kallo, murmushi Minal ɗin tayi itama ta maida mata murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarshi, kallon gefe tayi taga Laila tana shure-shure alaman tanaso ta juya, cikin sakin fuska tace "Minal kaita toilet fitsari take ji"

tashi minal ɗin tayi ta ajiye wayarta a gefe ta rike hannun keken Laila tace "wani toilet?"

da hannu ta nuna mata toilet ɗin baya, turata ta fara, ɗakin mutane sun ɗan ragu, saida suka shiga kafin Jahad ta ɗau jakanta ta mike tana dukar da kai, bata tsaya ko ina ba sai cikin toilet ɗin, time ɗin laila ta juya baya tana fitsari, ita kuma Minal tana tsaye daga bakin kofar, ji tayi an toshe bakinta, waro ido tayi tana ture hannun meshi, juyo da ita Jahad tayi tana mata murmushin mugunta, a kunnenta tace "kin sanni ko? kuma kina shirin gayawa Noor kin sanni?"

girgiza kai Minal tayi, a hankali ta matso da bakinta zuwa kunnenta tace "wai meyasa mutane kuke da baki ne? Jahad Kada unguwar Jambulo tabbas hakane, kenan akwai sirrin da kika sani a tare dani...?"

cikin raɗa take magana, jakanta ta buɗe ta ciro wukan da bata rabuwa dashi, daɓa mata tayi a baya, da karfi ta toshe bakinta ta yadda ba zata iya ihu ba, caccaka wukan ta fara a bayan minal saida ta daina motsi jikinta ya saki alaman ta mutu kafin ta kwantar da gawan cikin sanɗa ta goge wukan da rigan jikin Minal ɗin, maida wukan tayi a cikin jaka kafin ta juya a hankali ta buɗe kofar tafita ta kofan da babu wanda zai ganta.


Laila ta gama fitsari sai ɗaga hannu take alaman ta gama azo a ɗaga ta, ganin babu wanda yazo ga kafanta bazai mike ba ta fara kuka.


Jahad kwanciya tayi a inda ta tashi, a hankali ta rufe idonta kamar me bacci, noor ce ta dawo itada su Ammi sunzo da wani kaya wai ƴan uwan Man ne suka kawowa amarya, karba tayi cikin nutsuwa tace "na gode"

kallon Noor tayi tace "ki hadamin ruwan wanka a toilet zan sake wani wanka kafin nasa kayan"

murmushi Ammi tayi tace "jeki Noor"

ganin toilet a rufe Noor ta fara knocking, babu kowa a ciki, da ihu tace "Ammi kizo ki buɗemin toilet ɗin"

karasowa tayi tana cewa "ke Noor banson ragonta buɗe kofan ne ba zaki iya ba?"

da karfi suka tura kofan, baya noor tayi tana ihu ganin Gawan Minal a kwance cikin jini, Ammi ma a ruɗe ta koma baya, ganin laila tana ɗago hannu tayi dauriya ta shiga ta ɗaga ta, da gudu Noor ta fita waje tana kiran Abba? Yah Man? Ya Ahmar? Ya Sabir? Ya Jawad?"

mutane sai tambaya suke lafiya? hannu take ɗagawa tana cewa "minal"

man da yake sanye da wandon shadda da rigan armless ya shigo ɗakin a rude, harara ya aikawa Noor kafin yace "meya sameki?"

cikin rawan jiki ta nuna hanyan ɗakin tace "Minal?"

"meya samu minal ɗin?"


"An kasheta"

salati mutanen wurin suka fara, atare suka shiga ɗakin dasu Ahmar, a banɗaki sukaga gawan kwance cikin jini, Abba ma ya shigo cikin kiɗima yace "meya faru?"

baya yayi time da yaci karo da gawan, Jahad ta tsaya a gefe jikinta yana rawa idonta yana hawaye alaman itama taji tsoron ganin gawan, samun wata mata tayi a gefe cikin kuka tace "idan police sunzo zasu kwashe duk ƴan gidannan su tafi dasu mun shiga uku"

matar tana jin haka ta ɗau jakanta ta fita, mata suna ganin haka suma suka fara watsewa, kan kace me har an watse a gidan, murmushi Jahad tayi, Abba ya kira ƴan sanda a waya, tasan za suyi bincike domin Abba ya hana kowa ya taɓa gawan sai police sunzo, Noor da take tsaye cikin rawan jiki tana kuka, Jahad ta ɗaga mata hannu alaman tazo, tana ɗaga kafa zatazo, Jahad tasa mata kafa, faɗuwa tayi akan gawan, da sauri Man ya ɗaga ta, Jahad ma tazo tana ɗagata tareda cewa "sannu Noor"

dafe kai Abba yayi yasan koda police sunzo to yaranshi sun riga sun taɓa gawa gashi babu wani shaida a wurin.


Iyayen minal sai kuka suke suna jan Allah ya isa ga duk wanda ya kashe musu ƴa, saida police suka duba komai kafin suka ɗau report, tambayarsu sukayi shin akwai wanda suke zargi? 

shiru sukayi, Jahad taje gefen Man a hankali tace "babu wanda muke zargi, Allah sarki Hamida"

da sauri Man yace "eh akwai"


"waye?"


"Hamida, itace muke zargi"

bayani ya basu a kanta, Ammi shiru tayi domin bataso ana kiran sunan Hamida da wannan laifin tausayi take bata, iyayenta suka ɗau gawa suka tafi dashi, domin a gidansu zasuyi jana'iza, Man yana tsaye ya rasa abinyi, kuka zaiyi ko ihu? wani irin baƙin qaddara suke gani a gidansu? 

a ranan Abba ya yiwa kowa booking na jirgi, duk suka watse, babu abinda Jahad takeyi sai kuka, Ammi ce take bata hakuri, tareda cewa ta kwantar da hankalinta an riga an ɗaura aure kada tasa komai a ranta, kwanciya tayi a cinyar Ammi tana cigaba da kuka.


Abba yana daga tsaye kawai sukaji karan faɗuwa, a firgice suka juyo, da gudu duk sukayi kanshi, man ne ya kira kanshi akan Abba yana kuka sosai yace "kar kayimin haka Abba na, Dady ya tafi kada ka tafi ka barmu a wannan halin, ban sanka da yin giveup ba, kai kake bamu karfin gwiwa kada kayi haka dan Allah ka tashi"

Ahmar ma yana tsaye jikinshi sai rawa yake, kuka Man yake sosai, baison komai ya samu Abba bazai iya jura ba, dafa kirjinshi Ahmar yayi jin yana motsi yace "tashi mu kaishi ɗaki"

jiki a mace ya tashi suka kaishi ɗaki, Jahad ce ta rike Ammi ta zaunar da ita domin bataso itama ta faɗi, kayan gwaje-gwaje suka ɗauko nan suka fara gwadashi, blood nashi ne yayi high sosai hakan yasa ya faɗi, ya samu paralyse, kuka Man ya fashe dashi, wani irin masifa ne wannan? ya gommace da shine da wannan ciwon akan Abba, da kyar Ahmar wanda yake daurewa shima ya bashi hakuri, Jawad kam sai tagumi da jiran ranan mutuwanshi shima yake, Sabir kuma sallaya ya shimfiɗa ya fara salla ya ɗaga hannunshi sama yana addu'a, Allah ya daurasu akan makiyansu, Kallon kasa-kasa Jahad take aika mishi, har ya kammala sallan ya ninke sallayan, yana juyowa sukayi ido huɗu, murmushi tayi mishi tana sauke kai kasa, shima ya mayar mata kafin ya juya ya koma dakin Abba.


saida sukayi mishi alluran relief kafin suka kira Ammi ta zauna a wurinshi, palour suka koma kowa yayi tagumi hadda Jahad wacce take share hawaye akai akai, laila sai binsu take da ido, Noor kuma tana gidansu Minal, har dare ya tsaga basu sani ba, Ahmar ne ya kalli Man yace "kuje ku kwanta yaune first night naku don't ruined it"

girgiza kai yayi "banajin bacci"


"amma your wife tana jin bacci kuma kunada bukatar juna a wannan time ɗin, idan ka kasance da ita zaka samu sauƙin abinda yake damunka kaji?"


a hankali ya mike ya mikawa Jahad hannu, rike hannunshi tayi ya ɗagata, hannu ya ɗagawa su Jawad, kowa ya tashi ya koma ɗakinshi, ɗakinsu wanda Abba yasa aka ƙawata masu da kyawawan abubuwa suka shiga, komai na ɗakin pink ne da fari, hatta gadon an shimfiɗa pink na bedsheet da fari, sai ƙamshi yake tashi ta ko ina, toilet ya shiga yayi wanka ya fito da towel a ɗaure, kallonta yayi jikinshi a mace domin dauriya kawai yace "je kiyi wanka da alwala"

a hankali ta mike ta shiga toilet, bata wani jima ba ta fito sanye da dogon hijabi domin towel ɗin yayi mata guntu sosai, baiko rufe cinyarta ba, kallonta yayi jikinshi sanye da brown na jallabiya, gaban mirror taje zata shafa mai, saida taga baya kallonta kafin ta shafa, riga mara nauyi ga ciro zata sa, taga ya kura mata ido, ta cikin hijabi ta fara kicinyar sawa, mikewa yayi daga zaunen da yake, kwaɓe hijabin yayi da sauri ta durkusa ta rufe jikinta, rabin kirjinta duk a waje, lumshe ido yayi, ya karbi rigan zai sa mata, da sauri ta ture hannunshi, cikin sanyin murya yace "inada alwala babu abinda zan miki"

barinshi tayi yasa mata rigan sabon hijabi ya ciro daga drower yasa mata, shimfiɗa sallaya yayi suka tada salla, raka'a biyu sukayi kafin ya sallame ya riko goshinta yana yimata addu'a, saida ya gama ya haura gado ya kwanta, baya jin daɗi abinda ya faru ya matukar girgiza shi, ganin halinda yake ciki ta buɗe frij ta ciro snacks da drinks, da kanta ta fara bashi, da fari yaki ci, saida ta nuna ɓacin rai kafin ya fara karɓa, yana hawaye yana taunan abincin, saida ya koshi kafin taci kaɗan ta dawo ta kwanta a gefenshi, kashe wutan ɗakin tayi, shiru bai taɓata ba, yana lulluɓe cikin blanket yana kuka, dariya tayi a zuciyarta a hankali ta matso kusa dashi, hannu tasa ta saman rigan ta ɓalle aninin gaban jallabiyan, shafa kirjinshi ta fara, lumshe ido yayi, matsowa tayi sosai jikinshi, bakinta ta haɗa da nashi, kara lumshe ido yayi yanjin zuciyarshi tana sanyi.


deep romance take mishi wanda bai san ta iya ba, baima taɓa zaton zata iya ba, fitar dashi tayi daga hayyacinshi, a hankali ta mirgina zuwa gefe tana lulluba jikinta wanda ya cire duk kayan dake jikin nata, a rikice yazo wurinta yana janyota jikinshi, bazai iya jura ba, baison tayi nesa dashi, bakinta ta kai kunnenshi cikin shu'umin murya tace "am off, yanzu period nawa yazo"

dira tayi daga kan bed ɗin ta barshi yana juye-juye, toilet ta shiga ta ciro waya tana trying na wani number, hankalinta a tashe domin ba'a ɗaga ba.


tayita kira ya kai sau goma kafin ta kashe wayan ta fito, harara ta aikawa Man wanda ya rungume Pillow da karfi yana sakin numfashi da kyar, sunanta yake kira a hankali, Amsawa tayi kafin ta haura kan gadon ta matso kusa dashi, yana mata daɗi ta ganshi a haka, hannunta ya riko yana ɗaurawa akan jikinshi, da sauri ta janye cikin muryan tsoro tace "bazan iya ba tsoro nake ji"

juya mata baya yayi yana hawaye, yasan ta tsorata dana miji tun abinda kanin mahaifinta yayi mata, zai bita a hankali domin yana sonta sosai, juyowa yayi ya rungumeta suka fara bacci, kulle ido kawai tayi amma ba bacci take ba.



*Washe gari*


ɗakin Abba ya fara zuwa bayan yaje sallan asuba, ganin yana bacci ya zauna a gefenshi yana jin tausayin kansu, Ammi ta shigo tana rike da sallaya "Babana kaine da sassafe nan?"

"eh Ammi"

ya faɗa yana sunnar da kai kasa, murmushi tayi tace "sannunka ina Jahad?"


"tana bacci"


Jahad tana ji ya fita ta mike taje kitchen girki tayi me lafiya na breakfast kafin kowa ya tashi ta jera a dining, ɗakinsu ta koma tasa riga dogo irin jallabiya na mata light green, mayafinshi ta yafa a kanta ba karamin kyau tayi ba, fesa turare tayi kafin ta fito, duk sun tashi suna zaune basuda alaman cin abinci, saida ta kira Ammi kafin suka yadda suka je dining, serving ɗinsu tayi kowa ya fara ci a hankali babu me magana cikinsu, Man ya kalleta yana kashe mata ido, murmushi kawai tayi, Ammi ma cusa abincin kawai take badan daɗi ba, ranta duk a cakushe.


ji sukayi ana hayaniya a kofa, kallon juna sukayi kafin suka mike a tare, daidai Man zai fita wani mutum ya tureshi da karfi, baya yayi zai faɗi, sojoji biyu suka shigo, kokarin fitar dashi suke yaki sai bubbugesu yake yana cewa saiya shiga, Ammi ta ɗaga musu hannu alaman su kyaleshi saida suka barshi tace "meke faruwa?"


"Hajiya wannan mahaukacin ya kai 30mins anan muna korinshi yaki tafiya wai dole saiya shigo"


kallon yaron tayi, matashine sa'an Man, kyakkyawa jikinshi duk ya ɗaure da bakin leda, hakoranshi baki kirin sai dariya yake yana kaikaya kai, hannunshi da wuyanshi duk zanen baki kamar wanda yake dukan kanshi, gashin kanshi duk datti, kana ganinshi kaga mahaukaci, hannu Ammi ta ɗaga mishi tace "sannu"

da gudu yazo zai faɗa jikinta a tare sukayi baya, kamewa yayi wuri ɗaya da alaman hauka a maganarshi yace "sorry Hajiya ba rungumarki zanyi ba abinci nakeso ku bani yunwa"


abinci Ammi ta ɗauko ta mika mishi karɓa yayi ya fara ci, yadda yakeci zakace yayi shekara baici abinci ba, idanun Ammi ne ya cika da hawaye, har zubewa yake a kasa yana kwashewa yanaci, ruwan da suka bashi saida ya lankwasa goran kafin ya fara sha kamar zai cinye hadda gora, kallon Ammi yayi wacce take hawayen tausayi yace "ban ƙoshi ba"

karo mishi abincin tayi ya kara ci yana tsinan na kasa jikinshi yana rawa har ya cinye, da rarrafe yazo zai riketa, Man yace "stop kada ka taɓa ta"

hannu Ammi ta ɗaga mishi "kyaleshi"

jin tsawan da Man ya mishi yasa ya jingina da jikin bango yana zazaro ido alaman ya tsorata sosai, Ammi tace "tashi?"

tashi yayi yana kallon Man cikin tsoro "kada kaji tsoro"

kallon Jahad wacce ta zuba mishi ido tayi tace "nasan akwai addu'a sosai a bakinki, kiyi addu'a ki kaishi guest room ya huta kinji?"

Man yace "haba Ammi ta yaya matata zata kai mahaukaci ɗaki? Idan ya kasheta fa?"


"Jahad tana da ilimin Kur'ani ba zai taɓa ta ba tasan Addu'an da zatayi ba kamar kai ba"

hannu Jahad tayi mishi alama da muje ko? 

itama a tsorace take amma ta dake, tasan akwai wuka a gefen wandonta zata iya caka mishi idan ya kawo mata hari, domin ita a koda yaushe a shirye take, gaba ta shiga yana biye da ita, ɗakin babu nisa tsakaninsu, nuna mishi tayi "ga ɗakinka"

dariya yayi mata ta kuma kallonshi sosai,  zata juya ya riko hannunta ya janyota cikin ɗakin, rufe kofar yayi da karfi ya mannata da bango, shaƙe wuyanta yayi da karfi, zatayi ihu ya toshe bakinta ya cire hakorin dake sakale a bakinshi, hannu yasa a aljihu ya ciro tissue ya goge fuskarshi, ido ta zaro, cire hannunshi yayi daga bakinta, da karfi tace "JALAL?"

jijjiga kai yayi, cikin kakkausan murya yace "eh nine"


Kallon kofa tayi cikin tsoro tace "Meya kawo ka nan? kanaso ka tona mana asiri ne?"


danne ta yayi da karfi yace "cikin plan namu babu auren wannan yaron, meyasa kika aureshi? saina kasheshi yau ɗinnan"


hannu tasa ta toshe bakinshi "kayi magana a hankali Jalal ka zauna zanzo anjima"

shafa bakinta ya fara yana matso da fuskarshi zuwa nata, lumshe ido yake yana so ya haɗa bakinshi da nata, da karfi ta tureshi "nace maka zan dawo anjima ka zauna ina zuwa"

zata fita ya kuma janyota da karfi, a kunne ya raɗa mata "ba zaki tafi ba sai nayi abinda nakeso"


tureshi tayi "kada su biyo baya Jalal"

"Kin fara tsoro ne? Jahad Kada batada tsoro, Jahad ɗin dana sani bata shakkan kowa"

"ba zaka gane ba..."

bakinshi ya haɗa da nata, da karfi ta runtse ido tana jin yadda yake shan tongue nata yana haɗawa da leɓenta na kasa, itama tayi missing nashi hakan yasa ta kyaleshi saida yayi me ishanshi kafin ya kai bakinshi kunnenta saida ya tsotsa kaɗan yace "da fatan baya miki irin haka?"

jijiga kai tayi cikin tsoro "bayayi"

sakinta yayi, yace "jeki kuma anjima ki dawo"

da sauri ta buɗe kofan ta fita.




"Kiyi hakuri ki kyaleni kaina yana ciwo"

buga kanta matar take da kasa domin Hamida taki yadda ko taɓa ta tayi, da kyar ta kwaci kanta ta hanyar ɗaukan wani babban dutse ta kwala mata akai, rike kanta tayi wanda ya fara fitar da jini tace "ni kika buga?"

jikin Hamida yana rawa ta kawar da tsoro ta kara ɗaukan wani katon dutse tace "na buge ki kiyi abinda zakiyi, kuka duk wanda ya kara shiga harka na bazan taɓa barinshi ba, a baya kin zalunceni bazan bari yanzu kici galaba a kaina ba, duk wanda ya zalunceni saina rama"

matar ta tsorata domin idanun Hamida ya koma jaa, jijiyoyin kanta sun tashi, jikinta har rawa yake, jan jiki tayi ta koma wajen kwanciyarta, daga yau ta daina shiru, itama saita rama duk wani abinda kayi mata, fansar ran Adda Amrah dana Ra'eefa dana Baba, saita ɗauka, zuwanta prison sharrin da akayi mata saita rama, da karfi ta furta "kota halin kaka"..





_anan na kawo karshen free page, kuyi making payment domin samun complete, doctor Mansoor fa yanzu aka fara, Albishirinku ina masu son littafin YARIMA JUNAYD tareda DR MANSOOR? to ki biya naira 500 kacal domin samun littafan duka biyu, littafi ɗaya 300 littafi biyu 500 duka complete ne, idan kuma kinason littafi uku ne 800 littafin MUTUNCINA shima complete, kumin magana ta nan 08144818849 domin samun karin bayani nagode ina muku fatan alkhairi_

No comments

Powered by Blogger.