Doctor Mansoor 16
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*DOCTOR MANSOOR*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 16*
~Kwana bakwai da mutuwan Shaira yau aka gama sadaka, gidan har yanzu shiru ne, kowa ka gani jikinshi a mace, Jahad ce zaune a gaban laila tana kallonta cikin tausayi tace "zan sanar miki wani abu a matsayinki na ƴar uwata, dama ɓoye miki ake cewar shaira ya mutu, amma maganar gaskiya shine an kashe Shaira"
zaro idanu laila tayi cikin kiɗima ta fara ɗaga hannunta sama, babu bakin magana gashi babu kafar tafiya, kallon kasa-kasa Jahad ta aika mata a ranta tace "zaki karasa mutuwa da kanki"
ganin tana fitar da hawaye masu zafi ta mike ta haɗa hannu biyu tace "dan Allah kada ki faɗa wa kowa nice na faɗa miki kinji?"
jijjiga kai tayi cikin kuka, cije leɓenta tayi hawaye yana wanke kyakkyawar fuskarta, bargo ta janyo ta rufata dashi har kanta sannan ta fita daga ɗakin, saida ta sauka kasa taga babu wanda ya ganta kafin ta wuce ta part ɗin su Jawad, a hanya suka haɗu tace "ya kake?"
"Lafiya kalau"
har zata wuce sai kuma ta tsaya, cikin tausayi tace "Laila bata shan tea ne da dare?"
"oh na manta tana sha"
murmushi tayi tace "bari na haɗa mata saika kai mata ko?"
shiga kitchen tayi tana tsaki a ranta, hatta tea saida ta kira me koyar mata na wata uku, da kyar ta koya da girki, saida ta haɗa ta fito tana murmushi ta mika mishi, godiya yayi ya wuce domin kaiwa laila shayi, ganin ya shiga tayi sauri taje ta kira Man, yana bacci haka ya mike ya buɗe kofar, bata jira yayi magana ba tace "Ammi bataci komai ba ya dace ka kai mata koda tea ne kuma na haɗa yana kitchen"
tafiya ta fara yana bin bayanta, kallon sama tayi tana murmushi domin tasan abinda ta haɗa, Jawad ne ya fito da gudu yana kiran Abba, Man yace "meya faru?"
dakin Laila ya nuna yace "laila ta sankare" har rige-rige suke wurin shiga ɗakin, Ahmar da su Sabir sun fito, shi Ahmar idonshi a kumbure, tsaban kuka da yayi, da sauri Man ya haura gadon yana duba ta, saida aka bashi abin gwaje-gwaje ya gwada kirjinta da bugun zuciyarta kafin ya ɗago yana kallonsu "ta samu bugun zuciya ne sakamakon jin wani mummunan labari wanda ya tsorata ta, waye ya shigo ɗakinnan last?"
da mamakinshi yaji kowa yace bashi bane, kallon Jawad yayi cikin zafin rai yace "ka sanar mata mutuwan Shaira?"
girgiza kai yayi yace "na yadda nine last na shiga ɗakin amma ban sanar mata komai ba.." mari ya ɗaukeshi dashi, cikin zafin rai yace "kana nufin haka kawai ta sankare? kasan idan ta kara minti biyar ba'a yimata allura ba zata mutu? rai nawa kake so mu rasa?"
hannunshi dafe dakunci yace "kenan ya Man ka yadda zan iya sanar mata da abinda zai cutar da ita?"
"waye last shiga ɗakin?"
"nine amma...." wani marin ya kuma ɗaukeshi dashi har saida bakinshi ya fashe ya fara jini, rike bakin yayi yana kallon Man, bai taɓa mishi irin wannan marin ba, kuma wannan ai ba laifinshi bane, ran man idan ya ɓaci baida sauki, kan Jawad yayi da duka, da sauri Ahmar ya rikeshi yana cewa "haba mana bakada tabbacin shine ya faɗa mata ka kyaleshi dan Allah"
a hankali Noor cikin tsoro tazo ta janye Jawad, rike kunci yayi yana huci, Ammi da Abba suna daga gefe abin ya fara fin karfinsu, Jahad ganin haka tace "da wannan faɗan ai gara kayi mata alluran"
Abba yace "Allah yamiki albarka ya manta ma da alluran"
allura ya ciro cikin zafin rai yayi mata, baiso tasan wannan labarin na mutuwar Shaira ba, saide Jawad yayi gaggawa.
*Washe gari*
Abba ya kirasu bayan yayi musu jajen abinda ya faru, yace auren Jahad da Man zasu ɗaura ranan jumma'a me zuwa, murmushi Jahad tayi a cikin ranta a fili kuma ta dukar da kai alaman kunya, Man yayi murmushi duk da baya cikin yanayi me daɗi wannan labarin kaɗai ya isa ya sanyashi cikin farin ciki, Noor dake gefen Ammi itama taji daɗi, domin Jahad tana kula dasu, tasan ko babu Abba da Ammi zata basu kulawa me kyau, saida sukayi murna su duka kafin yace gobe su Noor su fara zuwa school, laila kuma a wannan week ɗin doctor ɗinta zaizo, kowa yayi farin ciki da hakan, yace Ammi zataje Dubai ta siyo kayan auren nasu, Jahad ta kalli Abba tace "banson komai Abba gatan da kuka nuna min kaɗai ya isheni, kun maidani kamar me iyaye, ku bani kyautar al`kur'ani zanfi jin daɗin hakan"
cikin zuciyar Abba yace "Allahu Akbar Man yayi sa'an mata"
a fili kuma yace "kema ƴace duk abinda za'ayiwa ƴa dole kema ayi miki, yau Lahadi Jumma'a za'a ɗaura aure, ranar litinin amminku zataje saita siyo kayan, saide kiyi hakuri ba za'ayi shagali a bikinku ba, saboda abinda ya faru mara daɗi, sannan Ahmar ka ciro mata dama naso na haɗaku da Man saide naga auren baya gabanka yanzu shiyasa na kyaleka amma zuwa gaba zaka fito da mata nayi maka aure"
kanshi ya saukar kasa yana sosa keya, satan kallon Jahad man yayi, caraf suka hada ido, zata ɗauke nata ya murguɗa mata baki, dariya kawai tayi ta sunnar da kai, sallamansu Abba yayi yana meyi musu addu'a Allah ya kare su daga sharrin makiya, kallon Abba tayi ta kasan idonta a ranta tace "makiya suna tare daku ba zaku taɓa tsira daga sharrinsu ba"
zata shiga ɗaki taji an janyota, har zatayi ihu yasa hannu a bakinta ya toshe, a kunnenta yace "nine"
shiga ɗakin yayi da ita ya tura kofar, akan kujera ya zauna tana shirin zama ya hanata, saida ya buɗa kafarshi yace ta zauna a ciki, ɓata rai tayi tana turo baki, wai bazata iya ba, gyara zamanshi yayi me kyau ya janyota ya zaunar da ita akan kafarshi, kallon fuskarta yayi da sauri ta kawar da kai, matsowa yayi sosai, yasa hannu yana maida mata gashinta wanda ya rufe mata goshi baya, baiyi magana ba sai kallonta yake, tsabar soyayya yanaji kamar ya maidata ciki ya huta, sunkuyo da kanta yayi ya mannata da kirjinshi, shiru tayi tana sauraran bugun zuciyarshi, hannunta ya ɗauko yasa ta cikin riganshi wanda ya ɓalle maɓallin, a hankali ya fara shafa saman nipples nashi, zame hannunshi yayi yana so taci gaba, ganin tana shirin cire hannunta ya kuma mayarwa yana aika mata kallon da ya hanata musu, shafa mishi ta fara ya sauke wani ajiyan zuciya me karfi, idonshi a lumshe yana jin soft hand nata yana yawo a kan kirjinshi, kallon yadda ya lumshe ido tayi, murmushin mugunta ta saki kafin ta matso wurinshi sosai ba tareda ta cire hannun ba ta gama ɓalle aninin rigan, a hankali ta matso da bakinta kan kirjinshi "ahhhh" shine abinda ya furta lokacin da yaji ta ɗaura bakinta akan nipples nashi ta fara tsotsa, runtse ido yayi bai taɓa jin wannan feeling ba sai yau, he feels very good, ganin tana hargitsa mishi lissafi ya ɗago kanta idanunshi har sun canja kala, bakinshi ya kai kan nata a hankali ya cusa harshenshi ya kamo nata ya fara sucking, hannu tasa a bayanshi tana shafawa, ganin yayi nisa a hakan ta ciro wani abu a gefen riganta, a gefen bayanshi ta zana kaɗan tayi rubutun J a wurin, yaji zafi a time ɗin da tayi hakan saide bai kula ba hankalinshi yana kan abinda yake yi, maida abin tayi kafin ta cusa hannunta a kanshi tana kara matso da fuskarshi kusa da nata, saida taga yana shirin barin hayyacinshi gaba ɗaya kafin ta tureshi ta mike daga kan kafarshi, barin ɗakin tayi, murmushi yayi kafin yasa hannu a kai yana maida gashinshi baya, ya lumshe ido, ya rasa meyasa idan yana tara da ita yake loosing control, tashi yayi yana karanta sakon daya shigo mishi, ciki takeso a zubar mata, fyade akayi mata hakan yasa take nemanshi ya taimaka mata, ajiye wayan yayi shifa so yake ya daina wannan abin, domin a halin yanzu sai yasha giya yake iyawa, gashi baya samun ishashen bacci da dare, saboda kukan jarirai da yake damunshi, Jahad ce take ceto shi domin addu'a da take yi, shiyasa ya damu ya auri Jahad dan samun ishashen bacci da kwanciyar hankali ne, kwanciya yayi bayan yasa rigan bacci, tunanin abinda wannan ƴar aikin tayi yake, dama wannan cikin daya zube da gangan tayi hakan, wannan da ganinta ƴar iska ce, idanunta a tsaye kamar ƴar kwaya, shiyasa baison ko ganinta, gata me zubin mayya, zai sanarwa ƴan prison suci mata mutunci sosai, gobe zaije saiya koya mata hankali.
*Asuba ta gari*
Bayan sun gama breakfast shiri yayi cikin riga da wando kanana, wandon jins blue da riga polo yallow, fatarshi luwai-luwai, shafa man gashi yayi a kanshi ya taje tareda gyarawa, idanunshi da yake yawan lumshewa ya kalla ta cikin madubi, cikin idonshi amaikon baki wani kalan blu-blue ne me hasken gaske, yafi kama da Ammi shiyasa yake kama da larabawa, agogo ya ɗaura a hannunshi ya ɗau makullin mota, fesa turarenshi me ƙamshi yayi, ya fito yana amsa call, bakinshi kaɗai yake motsi bakajin muryanshi, taku yake cikin nutsuwa yana sauka daga matattakalar wanda aka ƙawata da tyles, tana zaune akan sofa tana yanke farcenta, ba karamin kyau tayi ba cikin riga da wandon material baki da adon fari a jiki, ido ta zuba mishi tana yaba kyau da haibanshi, hakika wannan shine asalin cikakken namiji, kallonta yayi yana kashe mata ido tareda ɗan turo bakinshi, dariya tayi ta ɗauke kai tana cigaba da gyaran farcenta, saida yazo kusa da ita ya zauna, kanshi ya ɗaura a kafaɗarta cikin muryanshi me daɗin sauraro yace "Baby ki rakani"
wani irin daɗi taji a ranta, dama haka take so hakan zai bata daman ganin duk abinda yake faruwa da rayuwarshi, girgiza kai tayi "a,a Ammi zata hana"
ɗago kanshi yayi yace "no jeki ɗauko hijabi kizo mu tafi na faɗa mata"
tashi tayi tace "tom"
shiga dakinta tayi, saida tasa wuka a jakarta kafin tasa dogon hijabi ta fesa turare duk jikinta, dan tasan dole sai taɓa ta, fitowa tayi ba karamin kyau milk color hijabin yayi mata ba, lumshe ido yayi daga kishingiɗen da yake, saida ta karaso gabanshi tace "muje"
tashi yayi ya riko hannunta, da kanshi ya buɗe mata mota ta shiga gidan gaba, shima zama yayi suka fara tafiya, babu me magana cikinsu, Jahad ta rungume jakan hannunta wanda yake ɗauke da sabon wuƙa a ciki, a hankali ya juyo ya kalleta, ganin tana kallon gefe yace "yau kuma kunyata kike ji?"
Murmushi kawai tayi, ita kaɗai tasan zafin da takeji idan tana tare dashi, hannunta ya kalla, a hankali ya ɗaura hannunshi akan nata ya fara murzawa, shiru sukayi su duka, gabanta ne ya faɗi ganin sun nufi hanyar prison, wani irin crazy kallo ta aika mishi, haɗa ido sukayi da sauri ta kawar da nata domin idan ya kalleta sosai zai fahimci halinda take ciki "innocent Jahad ta zama crazy Jahad, wannan kallon ai saiki tsorata ni"
cikin wani muryan da bai santa dashi ba tace "ina zamu?"
hannunta damke da jakan daidai inda wukan yake, kara kallonta yayi ya tabbatar ko itace tayi magana, bata kallonshi gefe take kallo idanunta a bushe kam, "prison"
"me zamuje yi?"
"wannan yarinyar nakeso nayi mata gargaɗi"
sauke ajiyan zuciya tayi, saida ta daidaita fushinta da ɓacin ranta kafin ta juyo, hannunshi ta riko wanda baya tuki dashi, tace "kada kayi mata komai kaga karamar yarinya ce kaji?"
baiyi magana ba sai ci gaba da tafiya da yayi, shi kanshi baison ɓacin ranshi domin idan ranshi ya ɓaci babu me iya dawo dashi normal, sunyi tafiya me nisa kafin suka isa prison ɗin, a mota ta bar jakan domin tasan za'ayi cajinsu, basu sha wahalan shiga ba tunda Man sanannen mutum ne, kai tsaye aka kira mishi Hamida, ta rame tayi baƙi, idonta ya koma ciki ciki, tafiya take a hankali ga jikinta duk ciwo, basu wuri akayi suka rage su uku, daga Jahad sai Man, murmushi tayi lokacin da ta gansu, a hankali da muryanta wanda baya fita tace "kun gane banida laifi ko?"
wani irin shaƙe wuyanta Man yayi, ranshi a mugun ɓace ya bugata da jikin bango hannunshi rike da wuyanta, kakarin amai ta fara tana jujjuya kai, cikin zafin nama ya ɗauketa da mari, da kakkausan murya yace "ina Kabir? meyasa kika kashe Shaira?"
ido ta zaro tana janye hannunshi daga wuyanta, ji tayi wuyanta yana bushewa tana bukatan ruwa, bakinta yana ɓari tace "ru..ruwa"
kara shaƙeta yayi "saina kasheki, ina Kabir? wa kikewa aiki? mu mukayi miki?"
ganin ba zatayi magana ba ya buga kanta da bango, har yanzu bai cire hannunshi daga wuyanta ba, Hamida sadaukarwa tayi yaune rananta na karshe a duniya, Jahad dake tsaye a gefe so take ya kashe yarinyar ko zata huta, saide wani zuciyar yace idan ya kasheta wa zaki ɗaurawa sharri duk lokacin da kikayi abu?
da sauri taje tana rikeshi tareda bashi hakurin ya saki Hamidan, kin sakinta yayi, Hamida har ta fara sankarewa Jahad ce ta rungumeshi tana kuka "dan Allah ka kyaleta kada ta mutu, ka kyaleta"
ganin tana kuka yasa ya saketa, baya tayi ta faɗi kasa tana shura kafarta, da karfi ya rungume Jahad yana sakin ajiyan zuciya, badan ita ba yau saiya kashe Hamida saide shima a kasheshi, sakinshi tayi taje tana ɗagata, bakinta yana rawa tace "Unty....Unty...Unty Jahad ruwa"
da gudu ta fita ta karɓo ruwa, zuwa tayi tasa mata goran a baki, sha ta fara kamar tayi shekara bata sha ruwa ba, a jikin bango ta mannu hannunta rike da wuyanta, ciwo yake mata, ga gefen fuskarta ya tashi sosai alaman marin ya shigeta, hulan kanta ya fita, gashinta ya bazu zuwa bayanta da gaban kanta, fuskarta yayi baƙi-baƙi, zama tayi kamar mahaukaciya sabuwar kamu, tayi yarinya da wannan azaban, muryanta baya fita domin mura, da safe ruwan sanyi ake tashinta dashi, tayi kuka har ta gaji, kuɗi Jahad ta ciro daga aljihun wandonta ta watsawa Hamida cikin muryan tausayi tace "ga wannan ki rinka siyan abinda zakici idan kin bawa ma'aikatan zasu siyo miki, naga kinada yunwa a jikinki, sannan ki kula da kanki da kuma bakinki kisan me zaki faɗa kinji?"
bata cikin hayyacinta da rarrafe take kwashe kuɗin da Jahad ta watso mata, hannunshi Jahad ta riko tace "muje dan Allah"
saida suka fita tace "Hamida? ranan jumma'a ɗaurin aurenmu ki tayamu da addu'a Allah ya cireki a wannan halin"
tana magana tana kuka, Hamida bata fahimci komai ba, suna fita wacce take kula dasu ta shigo, ganin kuɗi a hannunta ta kwace duka, ɗaure hannunta tayi ta kaita ɗakinsu, kuka ma ta nema ta rasa, sai kallon mutane kawai take, jikinta yayi jaa tabon cizon sauro.
A mota Jahad tana ta sharan kwalla, saida yayi parking a gefen hanya kafin yayi mata alama da tazo, make kafaɗa tayi, matsowa yayi kusa da ita ya janyota zuwa jikinshi, hannu yasa ya ɗaga hijabin, a kunnenta yace "kukanki yana ɗaga min hankali"
janye jikinta tayi alaman tayi fishi dashi, kara matsowa yayi yana shafa jikinta har yanzu bai huce ba "Jahad!!" ya kira sunanta cikin sanyin murya, ɗago kai tayi ta kalleshi, bakinshi ya haɗa da nata, wani irin mahaukacin sucking ya fara mata, hijabin jikinta ya cire, hannunshi ya cusa cikin riganta, shafata yake kota ina yana numfashi da sauri da sauri, wukan dake jakanta ta ciro ta yadda bazai gani ba, tsaga tafin hannunta tayi tanajin raɗaɗi da zafi, maida wukan tayi tasa hannu cikin riganshi, bayanshi ta fara shafawa da hannunta me ɗauke da jini, kwantar da seat ɗin yayi sannan ya kwantar da ita akai, binta yayi yana cigaba da kissing nata, kokarin cire rigan jikinta yake da karfi ta damke tana kallon cikin idonshi, murya can kasa yace "kibari mana bazan iya jurewa har friday ba"
tureshi tayi da karfi kafin tasa hijabinta, kallon jinin hannunta yayi yace "subhanallah meya sameki?"
matso hawaye tayi "ba time ɗin da kuke faɗa da Hamida bane, shine zan rabaku akwai reza a hannunta zata yanka bayanka saina tare"
zaro ido yayi, "jahad da kin bari ta yankani ai, meyasa zakisa hannu ki tare?"
jan motan yayi zuwa hospital nashi, riko hannunta yayi suka shiga Office nashi, da kanshi ya wanke mata ciwon ya ɗaure da farin bandage, laptop ya bata kafin ya fita daga Office ɗin, yarinyar da sukayi magana jiya itace tazo, dawowa yayi ba tareda ya bari Jahad ta gani ba yasha giya ya fita, saida ya gama aikin ya dawo mata Office a mugun buge, tana ganinshi ta ajiye laptop ɗin tace "Man? meya faru?"
cikin muryan maye yace "Amai"
bai gama ba ya fara sheƙa amai, saida ya amayar duka kafin ya kwanta zaiyi bacci, ganin dare yayi ta ɗagashi sama tasan bazai sani ba tunda baya hayyacinshi, bata tsaya ko ina ba sai motarsu, da kanta take driving, har suka isa gida, getman yana buɗe musu ta hango waɗannan sojojin da Abba ya kawo, yau ma Man ne ya hanasu binsu da sai sun bisu har prison, saida ta zauna suka tafi sallan isha kafin ta ɗagashi ta kaishi ciki, ta kofan baya tabi har ta kaishi Room ɗinshi, jefar dashi tayi akan bed ɗin tana aika mishi wani kallon da ita kaɗai tasan ma'anarshi, a zuciye ta fita daga ɗakin, jakanta na rataye da ita.
cak ta tsaya jin kamar karan tafiyar mutum a bayanta, wukanta ta ciro ta rike tayi ready ta kashe koma waye yake bin bayanta, da ihu tace "surprise" kunna wutan wurin sukayi hannunsu rike da cake na birthday, ba tareda ta bari sunga wukan ba ta maida cikin jaka, juyowa tayi tace "kai Noor ai har kun tsorata ni"
dariya sukayi suka mika mata cake ɗin wanda aka rubuta "happy birthday Jahad"
dafe kai tayi "nikam har na manta yau birthday ɗina ne"
karɓa tayi ta yanka, kowa yasa mata a baki itama tasa musu, Jawad yace "Allah karo shekaru masu albarka"
a ranta tace "babu shekara me albarka a tareda Jahad Kada"
a fili kuma tace "Ameen"
godiya tayi musu tareda nuna musu tana cikin farin ciki, kuma taji daɗin hakan da sukayi mata, ɗakinta ta shiga, ta kira waya "yau birthday ɗina meka shirya min?"
dariya akayi ta ɗayan ɓangaren, "happy birthday Baby"
hira sukayi sosai kafin ta kashe wayan tayi wanka tareda salla tasa rigan bacci ta kwanta bacci.
*kuɗin littafina ₦300 ne biya ta nan 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta nan 08144818849, turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*
Leave a Comment