Doctor Mansoor 14

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




    Na

_Jiddah S Mapi_



*Chapter 14*



                 ~Tayata aikin take tana cewa "kinga ai yana cikin damuwa ne shiyasa amma dan Allah ina rokonki kada kiyi mana kallon ƴan iska kinji?"

giɗa kai tayi, tana cigaba da girkinta, fita tayi bayan ta tayata aiki kaɗan, Hamida tace "mukam a garinmu ai ku ɗin manyan ƴan iska ne, bake ba amma mijinki"

girki tayi me lafiya da daɗin gaske ta jera a dining kamar yadda ta saba, sanar musu tayi ta gama, da sauri ta haura sama da ɗan gudunta, laila ce ya fito daga room nata tasa wani riga wanda bai rufe cibiyarta ba da wando palazo wanda yake a buɗe, rigan da faɗi domin ciwon kirjinta bataso ya fame, tana tafiya tana danna waya hankalinta baya nan, tun daga sama Man ya fara kallonta yana jin son Kanwar tashi a ranshi, kallonshi Jahad tayi tana murmushi, a hankali ta mike zata koma ɗaki itama, daidai kan stair ta ɗagawa Laila hannu alaman sannunki, murmushi laila tayi, ba tareda sun sani ba sukaci karo, lokacin kuma Hamida ta fito da kwali a hannunta zata kaiwa Ahmar, tun daga sama Laila ta fara gangarawa kamar yadda Hamida ta faɗi ranan, sai haƙi take tana ɗaga hannu, Hamida ta yasar da kwalin ta bita da gudu, ido Man ya zaro, dama bai jima da fitowa ba, hakan yasa yake zaune a hannun kujera, Jahad tana tsaye ta aza hannu aka tana kwalo ido, da gudu su man suka iso wurin, ɗagata Hamida take shirin yi da karfi Man ya ture ta saida ta kusan buga kanta a bango, Ahmar ne ya riketa, ɗagata yayi sama ganin ta daina numfashi, da mugun gudu ya shiga ɗakinshi da ita, kwantar da ita yayi a ƙasa ya fara danna kirjinta, ganin bata kuma numfashi ba ya kalli Kabir wanda suka haɗa shigowa da Ammi da Ahmar da Shaira da Hamida sai Jahad da Jawad, yace "jakana a drower" ɗauko jakan yayi ya mika mishi, budewa yayi suka fara dubata a tare, Shaira ta juya tana kuka, Hamida ta matso tana bata hakuri da karfi ta tureta tana nunata da yatsa "idan wani abu ya sami kanwata saina kasheki"

shiru tayi "meyasa na fiye mistake? meyasa banida farin jini? haka mamana ta haifeni da bakin jini?"

saida ta fara motsi kafin ya kwantar da ita akan gado, tana buɗe ido ta nuna mishi kafarta da gefen waist nata, a hankali yace "zakiji sauki"


sunyi mata alluran pain killer, fita sukayi baya tayi bacci, kowa yana aikawa Hamida harara, saide ta dukar da kai kawai ta wuce, bayan Laila ta farka ta gagara taka kafarta, kafa yaki motsi, gaban Ammi ne ya faɗi jin abinda Ahmar ya faɗa "Ammi Laila ta samu ciwo a cinyarta da wuya ta samu sauki"

jin maganar ba karamin ɗagawa Hamida hankali yayi ba, da sauri ta matso tace "ya Ahmar ka kara dubawa"

"Hamida Laila ba zata iya takawa ba"

Shaira tayi tsalle ta rike wuyan Hamida tana kuka tana bugunta tako ina, da kyar Jawad ya kwaceta, fita akayi da shaira, Noor kam tana tsaye jikinta yayi sanyi, ta rasa meke faruwa da family ɗinsu daga wannan masifa sai wannan?.


Man ya fita daga ɗakin yaje ɗakinshi, rufe kanshi yayi ya fara watsi da komai na ɗakin, meyasa abubuwa marasa daɗi suke faruwa? frij ya buɗe ya ciro manyan kwalaben giya ya buɗe ya fara kwankwaɗa, saida ya shanye kwalban uku kafin ya kwanta a gefe ya fara bacci, baison damuwa ko kaɗan ya tsani damuwa gashi kullum zuwa mishi take, bayan kukan jinjiraye da suke hanashi bacci, gashi anyi kisa a hospital nashi, ga mutuwan Dadynsu Ahmar, ga jin ciwon Laila? da wanne zaiji? 


waya Abba ya kira Ammi tana ganin ya kirata da number ɗin Nigeriya tayi Hamdala, bayan sun gaisa bata sanar mishi abinda ake ciki ba yace yana airport, kallon Kabir tayi wanda yake tsaye tace "ɗau mota kaje airport Abbanku ya dawo"

fita yayi jikinshi a sanyaye yaje parking space, mota ya ɗauka ya fita daga gidan, baisan meyasa abubuwa marasa daɗi suke faruwa dasu ba, Allah yasa Abba ya maida komai daidai Ameen, kamar daga sama ya jiyo karan harbi, gudu ya kara domin yaga layin ba kowa, cikin tsoro ya murza ido yana kallon mutanen da suke zagaye dashi suna binshi, jikinsu duk kaya baki da facemask, gudu yakeso yayi suka harbe tayanshi, tsayawa motar yayi cak, da gudu sukazo suka fitar dashi, a motarsu suka sashi, daga nan suka fara gudu, Kabir sai hakuri yake basu, ɗaya daga cikinsu ya manne bakinshi da salatep.


Abba ne a airport sai safa da marwa yake, jikinshi sanye da babban riga yana tunanin ta yadda zai fara solving case ɗin Man, yasan ko kwaro man bazai iya kashewa ba balle mutum, wannan zagon kasa akayi mishi, ganin mai ɗaukanshi bai zo ba har yanzu yayi tunanin kodai goslow yayi yawa, zama yayi a bakin jirgin yana karewa wurin kallo, bini bini yana kallon agogon dake ɗaure a hannunshi.



Ammi ta shiga part nata ta fara shirye-shirye, tasan komai zaiyi sauki idan Abba ya dawo, Hamida ce tayi knocking hannunta rikeda drinks da ruwa domin taga yau Ammi ta wuni da yunwa, zani ta ɗaura na leshi da riga material shigen leshin, babu ɗankwali a kanta domin Hamida crazy ce, haka take bata son damuwa, shiga tayi ta ajiye plate ɗin tace "bismilla Ammi"

saukowa Ammi tayi daga kan bed ɗin ta zauna kasa tareda cewa Hamida "zauna"

zama tayi a kasa itama tana kallon ta, ji take kamar mahaifiyarta ce ita, hannun Hamida ta kamo cikin sanyi tace "na ɗaukeki a matsayin ƴata, kamar yadda su Noor suke a wurina, na kula a fuska kinada rashin ji da tsiwa amma a zuciya ke kamila ce, kinada kyawun hali ga wanda ya fahimceki, ki tayamu da addu'a Allah ya kawo karshen damuwan da muke ciki a gidannan"


"Ina kan addu'a kullum Ammi, sannan insha Allahu komai zaiyi daidai"


"Insha Allah ƴata domin yanzu haka Kabir yaje ɗauko Abbansu a airport kinga shikam zai saita komai"

"insha Allah Ammi komai zaiyi sauki"


"kinga Man ma aurensu zamusa nan kusa shida Jahad"

dariya tayi tace "Allah ya kaimu"

tunawa tayi da yadda ta gansu a ɗaki, abin yaki barin brain nata, tashi tayi "bari naje na gama aikina"


"to Allah yamiki albarka"

"Ameen ta faɗa"


Abba ganin har dare ya fara gashi shiru babu wanda yazo, yakira wayar Ammi yana tambaya ko lafiya? cewa tayi kabir ya tafi tun ɗazu, yace ta kashe wayar, kiran Kabir yayi yanata ringing ba'a ɗaga ba, Ammi ma tayi ta trying shiru ba'a ɗaga ba, tashin hankali, Man ta kira shima wayarshi na ringing bai ɗaga ba, da sauri ta fita ta samu Ahmar tace Kabir fa baije airport ba ana kiran wayarshi kuma a kashe, nan fa mutanen gidan suka taru, Man na ɗaki giya ya sashi bacci sosai.


kiran wayar Abba akayi yana ɗagawa akace "da haka zamu ɗauke ku da ɗaya-ɗaya"

kashe wayan yayi yana cewa "Hello"

cikin tashin hankali ya kama taxi ya shiga, Jahad sai kwantarwa Ammi hankali take ta hanyar cewa ba komai fa, 

Abba a taxi ya dawo gida, yana shiga da sallama ya nutsu domin baison hankalinsu ya tashi, da gudu Ammi taje tana cewa "yaya labarin Kabir?"

cikin dauriya yace "ba labari zai dawo ai"

kallon Ahmar yayi ya buɗa mishi hannu, rungume Abba yayi, "ina Sabir?"

"yana ɗaki tunda akayi rasuwan baya yawan fitowa"


"Okay, Ina Laila?"


Shiru sukayi, da mamaki yace "ina Laila?"


"dama taji ciwo ne"


"Ciwo kuma? aina taji ciwon?"


Ammi tace "faɗuwa tayi"


"Aina ta fadi?" Ya faɗa cikin tsawa, domin gani yake suna ɓoye mishi abu, Hamida cikin tsoro tace "bada sanina ba na ture ta"

baiyi magana ba ya wuce sama, kiran layin da suka kirashi dashi yake tayi, basu ɗaga ba har yanzu shiru, Ammi ce ta shigo tana ganinshi tasan ba lafiya.


Man yana kwance yaji kanshi yayi nauyi, buɗe ido yayi yaga time yaja sosai, da sauri ya kwashe kwalaben ya kai frij, wanka yayi tareda alwala yazo yayi salla, buɗe kofar yayi, karo yaci da fuskar Jahad tana mishi murmushi, janyota yake niyan yi jikinshi da sauri tayi baya tace "Abba ya dawo" waro ido yayi tace "yes da gaske ya dawo sannan Kabir yaje ɗauko Abba amma har yanzu ba'a ganshi ba"


"ba'a ganshi ba?"

"eh wlh amma kaje wurin Ammi zakaji daga bakinta"

part ɗin Abba yaje saida yayi knocking ya shiga, kallonshi yayi "ina kake?"


"Ina bacci a ɗaki"


Wanka Abba yayi suka sauka kasa, saida ya duba Laila yaga yadda jikin yake, kira likita yayi daga kasar waje yayi mishi bayani, yace zaiyi iya bakin kokari yazo domin mutumin Abba ne sosai, har yanzu bai daina kiran wayar ba kuma basu ɗaga ba.


Hamida ke serving nasu kowa yayi shiru yana tunani, waye yasawa family ɗinsu ido? 

Jahad da hijabinta domin kunyan Abba take sosai, ganin shirun yayi yawa ya kalli Man wanda yake juya cokali a cikin abinci ya gagara cin koda loma ɗaya ne, kallon Jahad yayi yaga itama tana kallon Man take cikin tausayi tayi tagumi, dama yaji labarin komai a wurin Ammi, gyaran murya yayi yace "Man yaushene zakuyi auren?"

"Abba nikam ko wannan satin"


waro ido Jahad tayi da gudu ta bar wurin domin ba karamin kunya taji ba, murmushi kawai Abba yayi domin shima Man ya bashi kunya, Ahmar ya aika mishi harara, alaman sannu romeo, Hamida na gefe tana yanke farcenta, Abba ne ya ciro wayar yana kara gwada number, ji yayi waya yana kara, da sauri ya kara ɗagawa yana kira kamar da wasa yakuma jin sautin karan kiran waya, tashi yayi ba tareda yayi kowa magana ba ya fara zagaye ɗakunan gidan yana kiran wayar, so yake yaji aina wannan sautin yake tashi, kamar a ɓangaren ɗakin Noor ne, a jikin kofar ɗakin Noor ya tsaya, ya kuma kiran wayan sautin ba daga ɗakin Noor bane a gefe ne, kara kira yayi, da hankali ya maida kanshi jikin ɗakin da yaji karan yafi tashi, tabbas a nan ne, da karfi ya kira Ammi, tareda su Man, yace kowa yazo, haurowa sukayi su duka suna kallonshi, da hannu yayi nuni da kofar fuska ba yabo ba fallasa yace "ɗakin waye wannan?"


har suna haɗa baki wurin cewa "Hamida"

kallon sama da kasa yayi mata, jikinta ne ya fara ɓari ganin yadda yake mata kallon rashin yadda, cikin wani irin tsananin tsawa wanda yasa har Man saida ya firgita yace "buɗe kofar"

jikinta yana ɓari kamar ba zata iya buɗe wa ba ta buɗe, da kafa ya karasa bangaje kofar ya shiga ciki, wayarshi ya ɗaga ya kuma kiran layin, ji yayi karan yana fitowa ta cikin drower, da karfi ya kuma cewa "ki buɗe"

budewa tayi har yanzu jikinta bai daina ɓari ba, wata ƴar karamar waya ce ta faɗo, ɗagawa yayi yana kallo, saida ya kalla sannan ya kuma kallonta, karɓan wayan Man yayi yana sa number a ciki, kara gwada kira yayi yaga wayan yana ringing, kallonta yayi "ina Kabir?"


a zabure ta ɗago manyan idanunta ta zuba mishi, cikin tsoro tace "Kabir kum....?"

kafin ta karasa ya wanketa da wani zazzafan mari, Wanda yasa tayi juyi ta faɗi akan kafar Jahad, kallon Ammi yayi yana nuna mata wayan, cikin zafin rai yace "kana zaune da munafikinka? wannan yarinyar itace ta sace Kabir, domin da nake airport an kirani da wani number akace da haka zasu rinƙa ɗaukemu ɗaɗɗaya, bayan na dawo ban sanar muku ba, kuma muryan mace naji, bayan na fara kiran layin da suka kirani dashi sai naji ringing Kamar daga gidannan yake fitowa,  ashe a ɗakin wannan yarinyar wayar take, Ina Kabir?"


Ammi sai kallon Hamida take cikin tuhuma, girgiza kai take tana cewa "bani bace, Ammi banyi komai ba"


Cikin zafi Abba yace "ku bincika min ɗakinta gaba ɗaya"

bincike suka fara musamman Shaira da take jin haushin Hamida, a karkashin gado ta ciro wani takalmi gida ɗaya, da sauri Man yace "muga wannan takalmin?"

mika mishi tayi, waro ido yayi yace "ina zuwa"

fita yayi ya shiga ɗakinshi, takalmin daya samu a hospital ya ɗauko haɗawa yayi ya duba yaga iri ɗaya ne, da sauri ya koma dakin yana nuna Hamida "kece kikayi kisa a hospital kenan?"

ido ta kuma waro wa tace "kisa kuma?"

takalmin ya nuna mata tareda yimusu bayanin abinda ya faru duka, hadda video ya nuna musu a wayan, kallon takalmin sukayi duka suka tabbatar da hakan, kafin su kara magana Jahad ta kira waya nunber ɗin ƴan sanda ne, da rarrafe ta matso wajen Ahmar cikin kuka tace "Yah Ahmar bansan me suke faɗa ba"

tureta yayi "dama nasan abinda yake faruwa tsakanin ki da Kabir, amma ai kinsan yaranta ne, bansan kin rike Kabir a rai ba sai yau, Hamida kin bani kunya"

ta rasa kukan ma sai zare ido, wurin Ammi taje tace "kin ɗaukeni a matsayin ƴa kiyi magana banyi komai ba Ammi"

juya baya Ammi tayi don batason ganin Hamida a wannan halin, police ne suka shigo kai tsaye hannunshi rike da bindiga, ruɗewa Hamida tayi tana tsoron police sosai, bayan Man taje ta rikeshi tana cewa "ka taimaka min ina tsoron police banyi komai ba"

wulla musu ita yayi ta faɗa a hannun macen police, handcuff suka sa mata tana girgiza kai tana kuka tareda kiran sunan Man, kallon noor tayi tace "ku taimaka min banyi komai ba, kanina Jawad banyi komai ba wallahi kafi kowa sanin halina"

Janye ta suka fara tana tirjewa, har suka fita da ita, mannuwa Ammi tayi da jikin bango tana kuka sosai, man ya jingina da jikin kofar, shiyasa ya tsani yarinyar, Jahad ta matso wurin Ammi ta riketa, kuka Ammi ta fashe dashi yana cewa "banson ganin Hamida a wannan halin, jinta nake kamar ƴar cikina dana haifa, rungume Ammi tayi a hankali ta kaita ɗakinta, kwantar da ita tayi akan bed ta rinƙa bata hakuri har saida tayi shiru, lumshe ido tayi kamar me bacci, a hankali Jahad ta fita, kallon Noor tayi itama ta riko hannunta tace "kuyi hakuri komai zaiyi daidai" 

Shaira ma ta rungume Jahad tana kuka tace "ta nakasa min kanwata, yanzu kuma ta sace yayana?"

bubbuga bayanta tayi tana cewa "sorry"

kaisu ɗaki tayi ta basu ruwan sanyi, duk suka zauna cikin damuwa, Abba ɗaki ya wuce ranshi a cakushe, Ahmar kuka yafara kenan Hamida itace ta kashe musu iyaye? batada tausayi dama? da kyar Man ya bashi hakuri har ya koma ɗakinshi, Sabir dama ba zama yake a gida ba, koda ya tadda labarin ba karamin damuwa ya shiga ba, Jahad ta riko hannun Man wanda yake tsaye ya rasa abinyi, sai dunkule hannu yake, kamo hannun tayi ta kaishi room ɗin shi, kwanciya yayi akan Bed baiyi magana ba sai kallonta yake yana hawaye, kara gudun Ac tayi kafin ta rufashi da blanket, janyota jikinshi yayi ya rungumeta da karfi, bata kwaci kanta ba saboda itama a ruɗe take, hannu yasa yana kwance igiyan rigan dake jikinta, a hankali ta rike hannunshi tace "Allah ya hana hakan, a Kur'ani yace wala tukribuzzina, kada ku kusanci zina..."

da sauri yasa yatsa a bakinta, lumshe ido yayi a kunnenta ya raɗa "ba zina zamuyi ba, zan ɗan samu nutsuwa ne dake kaɗan"

janye jikinta take niyan yi, ya riketa da karfi, kwance igiyan rigan yayi ya fara cusa hannunshi ta kasa, ajiyan zuciya ya sauke lokacin da yaji hannunshi akan breast nata, Jahad jikinta ne yayi sanyi, matsawa ya fara yana lumshe ido, kara janyota yayi sosai kamar zai maidata ciki, a hankali ya ɗaura bakinshi akai, hannu tasa a kanshi da niyan ture shi, sai kuma ta fara shafa kanshi, wani irin feeling ne ya fara taso mishi tun daga kafa har zuwa kwakwalwar kanshi, ta kula idan yana cikin damuwa yafi janta a jiki, shafa bayanshi ta fara, numfashi yake saukewa a hankali yana cigaba da lumshe idanu, ɗagowa yayi yana kallonta, idanunshi sun koma red kamar jan gauta, ga lips nashi sun zama red sosai, kasa kallon cikin idonshi tayi, da sauri ta janye riganta, hannu yasa a kasan fuskarta, saida ya kalli leɓenta na kusan minti biyar kafin ya kife bakinshi akai, wani irin tsotsa yakeyi kamar zai tsinke mata lips, da kyar ta samu ta janye bakinta tana cewa "zan tafi"


"Please kada ki tafi, Hamida muguwa ce shiyasa bana sonta, ban taɓa tunanin zatayi kisa ba, ashe shine dalilin faɗuwarta akan motar mu domin tazo ta cutar dani ne, yanzu bansan inda Kabir yake ba, gashi su Dady sun mutu" rungumeshi tayi sosai tana shafa kanshi, "Jahad na yadda dake, ina sonki, ban taɓa yadda da wata mace ba koma bayan ke, kinada dauriya da juriya, nasan yau aka sanar miki da mutuwar mahaifinki amma kika daure kina tayi mishi addu'a, hakan bai hana kin kula da kowa a gidannan ba, nasan Ammi sunyi sa'an sirika, Jahad kece kika rikemin sirrina, da addu'anki kawai nake iya bacci da dare, nace wa Abba nan da 3weeks nakeso na aureki amince?"

Jijjiga kai tayi itama tana hawaye, kara kafewa yayi a jikinta yace "kar ki tafi sai nayi bacci"

jijjiga kai tayi, a hankali ya zame ya kwanta a cinyarta, hannunta ya ɗago ya ɗaura a suman kanshi yana shafawa, lumshe ido yayi bayan ya cire hannunshi taci gaba da shafa kanshi tana sharan hawayen tausayi.



Kabir wani ɗaki me duhu suka kaishi, baya ganin komai sai duhu, ɗaureshi sukayi bayan sun cire salatep na bakinshi, tun yana basu hakuri har ya daina, kuka kawai yake domin sunyita bugunshi da karkashin bindiga, sauro sun fara cizonshi, fita sukayi suka barshi a wurin, jikinshi duk a fashe.



saida Man yayi bacci kafin ta fita daga ɗakin, Abba ta gani tsaye a bakin kofan, kasa ta durkusa tace "sannu Abba"

"yawwa ƴata kun shirya aure nan da sati uku?"

cikin kunya tace "eh"

"to Allah yamiki albarka, kinyi kokari da kika kira police"

murmushi tayi, yace "tashi"

a hankali ta mike, kitchen taje ta haɗa ruwan tea tasa a plate, ɗakin Ahmar taje, yana kwance akan kujeran dake karamin palour ɗinshi ya kwanta a gadon bayanshi yana kallon slin, Kabir yake tunawa ko yana wani hali? Allah ne kaɗai ya sani, ajiye plate ɗin tayi ta durkusa kasa tace "nasan ni ba kowa bace, amma ina rokonka a matsayina na ƴar riko ka tashi kasha tea ka daina tunani komai zaiyi daidai"

tashi tayi zata fita yace "Jahad ke kowace mana, kinada kyakkyawar zuciya, ba laifin Man bane da ya yadda dake, nikuma wacce nayi shirin yadda da ita, ashe muguwa ce, itace ta sace min kanina? Jahad Man yayi sa'a daya sameki kuma zai aureki, a baya naso Hamida ashe ba da soyayya tazo gidan ba"

a hankali ta dawo, zama tayi a gefenshi tace "ka daina wannan maganan addu'a kawai zakayi"

ɗaukan tea tayi ta mika mishi, karɓa yayi yasha yace "na gode"

fita tayi daga ɗakin, Jawad ta gani zai wuce, a hankali tace "na kawo maka shayi?"

cikin sanyi yace "A,a Unty Jahad bana jin yunwa"

juyowa tayi ta rungumeshi tana shafa kanshi tace "kada kasa damuwa a ranka babu abinda zai kuma faruwa kaji?"

jijjiga kai yayi "ki gafarceni abinda nayi miki"


"babu komai jeka kwanta"

ɗaki ya wuce, kallon ɗakin Sabir tayi tasan shikam ba sai taje ba dama ba son damuwa yake ba, wucewa ɗakinta tayi tanajin bayanta yana ciwo domin ta gaji sosai, rufe kofar tayi da makulli ta ciki, a hankali ta karasa wurin wani akwati ta ciro wasu kaya riga da wando baƙi, kayan jikinta ta cire, kafin tasa wani half vest baki, wando tasa wanda ya ɗameta ya fito da asalin shape ɗinta, bakin riga kamar na sanyi shi ta ɗaura a saman rigan nata, kafin ta ciro wani takalmi boot, sawa tayi ta ciro bakin glass half face daga akwatin, sawa tayi nan take ya rufe mata rabin fuska, hulan kanta ta cire nan ta watso gashin dake cikin ribbon ta ɗaura da lobarin, cingum ta ɓare ta jefa cikin bakinta, gefen jakanta ta buɗe ta ciro wani karamin bindiga piston, taunar cingum ɗin ta fara tana wani irin crazy taku, wanda yasa jikinta gaba ɗaya yake girgiza, daga sama har kasa, stool na gaban madubi ta janyo ta zauna a kai, wata ƴar karamar waya ta ciro tayi kira bugu ɗaya aka ɗaga, cikin dariya da shu'umanci tace "yeah nice JAHAD MUHAMMAD KADA wacce akafi sani da Jahad macijiya, ko kuma Jahad mage me kwanciyar ɗaukan rai, amma zaka iya kirana da Jahad kanwar shaiɗan domin nafi son wannan sunan"

dariya ta kwashe dashi cikin maida gashin kanta baya, tace "komai yana tafiya yadda muka tsara, nice fa bana tarko a gagara faɗawa ciki, next 3weeks aurena da DR MANSOOR, wannan yarinyar anyi gaba da ita"

shiru tayi daga bisani tace 

"duk abinda zai shiga tsakanina da Man kawarwa nake, wannan kanwar tashi Laila naga yana sonta a halin yanzu kafarta bata iya tafiya, kuma ina bata maganin rage karfi, ba tareda ta sani ba, domin a zatonta ruwa ne"


"itama Hamida naso kasheta ai tunda na bugeta ta faɗi kasa, saide tanada taurin kai shiyasa na juye komai a kanta, sannan wannan Kabir ɗin idan zai kawo cikas ku kasheshi ku turo gawan gidannan, inason ganin Mahaifinsu cikin tashin hankali, Man ya yadda dani, bai yadda da kowa ba izuwa yanzu, sai na gama lulashi kafin ayimin maganinshi, da gangan nace ku kama Kabir saboda nasan basa shiri da wannan yarinyar gashi na ajiye takalmin a room ɗinta"


"nice na zubawa Ammin mai lokacin data dawo naso ta taka ta faɗi taji ciwo amma wannan me idanun mayun ta taimaka mata, shiyasa ma na yar da ita kasa, kada ka damu a kulamin da company sosai, gidan gona na a rinka ziyarta sosai"

shiru tayi kafin daga bisani tace "ka kula da kanka"


kashe wayan tayi tana kallon kanta a madubi, ajiye bindigan tayi ta fara ɓallawa, cikin raɗa ta yiwa bindigar magana kamar mutum tace "banda bukatar ku, Jahad tana bukatan abu ɗaya ne"

hannu tasa tana dafe kanta, cikin shu'umin murya tace "ƙwaƙwalwa"

wuka ta ciro daga gefen riganta, ta yanke hannunta dashi, nan take jini ya fara zuba, a kan drower jini yake ɗiga tanajin raɗaɗi amma tayi murmushi tace "na rantse da Allan da yayi wannan jinin dake zuba a cikin jikina, saina gama da kowa" tissue ta ɗaga ta goge jinin kafin ta maida wukan cikin gidanshi, jambaki ta ɗauka red color ta shafa a bakinta, kafin ta ciro bakin ayeshadow ta shafa a saman idonta, kallon kanta tayi tana dariya, tashi tayi tana zagaye ɗakin tana taunar cingum "Man!!! Man!!! bazan taɓa ka ba amma zan taɓa wanda zakaji zafi fiye dashi, wani lokacin daka taɓa makiyinka gara ka taɓa wanda idan ya gani sai yaji zafi fiye da kanshi, ribbon ɗin kanta ta kwance da karfi ta durkusa akan gwiwanta cikin jin daɗi tace "nice Jahad  Muhammad Kada, kwarai Kada shine mahaifina, mutumin da baya yawo saida babban kada a hannunshi, hakika inajin bakin ciki ace kamarni ina yiwa wannan gidan hidima a matsayin ƴar riƙo, saide wani lokacin saika rasa wani abin kake samun wani..."




*Kuɗin littafina ₦300 ne biya tanan 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko ki turo katin Mtn ta nan 08144818849, turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.