Doctor Mansoor 13

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    Na

_Jiddah S Mapi_*Chapter 13*                 ~haka take rayuwa a gidan Kabir ya sata a gaba laila da shaira ba sonta suke ba, sai Noor da Jawad suke nuna mata soyayya, Man kam ko kallo bata isheshi ba, Abba yayi tafiya yana bincike akan case na kisan Dady da Momy, Ammi taje wurin aiki, ya rage

yaran ne kaɗai a gida, zaune suke a cikin palour su duka, wasu na game wasu kuma suna kallon tv, Man yana zaune akan sofa yasa kayan shan iska blue wanda ya haska ya kuma fito da kyaunshi na ruwa biyu wato fulani da kuma balarabe, hannunshi rike da remote na game ya buɗe kafarshi, laila na zaune tsakanin kafarshi suna game ɗin tare, dariya takeyi ganin yadda take cinyeshi a game, ita kuma tasa bakin riga dogo mara hannu, fatar jikinta me kyau sosai, Ahmar ya maida hankali akan waya yana chatting, sai Kabir da Jawad wanda suke kallo, Shaira na cin chips, Sabir ma yana tayasu kallo, idan ka gansu gwanin sha'awa, a hankali take taka matattakalar tana kallonsu tun daga sama, murmushin ta me sanyi tayi tana ganin yadda Laila ta kwanta jikin Man suna game, ɗauke kai tayi yanayin shirinsu yana birgeta, inama ace itama tana da ƴan uwa wanda zasu zauna haka, a hankali ta sauko ta nufi kitchen, tayi kyau cikin riga da wando na kanti blue, gashin kanta tayi Parking tasa hula me shara-shara, fuskar Jahad akoda yaushe yana ɗauke da murmushi, haɗa tea tayi me zafin gaske sai ƙamshi yake, a plate ta jera cup ɗin ta nufi wajensu, mikawa kowa ta fara, suna ɗauka suna godiya tareda yaba halinta a zuciyarsu, a hankali taje wurin Man da Laila, mika mishi tayi ya karba yana haɗawa da hannunta ya shafa, da sauri ta janye, mikawa laila tayi ba tareda ta sani ba ta watsa mata a cikin riga, wani mahaukacin tsalle Laila tayi tana murza jikinta, kowa ya ajiye cup ɗinshi ya matso wurinta yana cewa "sannu"

babu bakin magana sai hawaye take tana jin zafi sosai a jikinta, kwaɓe rigan tayi Allah ya taimaka da wando gajere da bra irin me faɗin nan a jikinta, Jahad ta rikice sai hakuri take bata, tana hura mata wurin da iskan bakinta, Hamida wacce ta tashi daga bacci, taji hayaniya ana cewa "sannu" da sleeping dress ɗin daya kama jikinta sosai ta nufi hanyan palour, tana ganin Laila babu riga ga jikinta ya kumbura ta zaro ido da gudu taje wurin, laila tana ganinta ta rungumeta tana kuka "sannu laila" sakinta tayi taje ta ɗibo manja a kitchen, shafa mata tayi a wurin daya kone, a hankali take lumshe ido yau taji zafin rashin magananta da ace tana magana da tayi ihu ko zataji sauƙin raɗaɗin da yake damunta, Man ne ya juya baya ganin rigan baccin dake jikin Hamida, har shatin nipples nata dake a tsaye saida ya gani, cikin zafin rai yace "ke kibar nan"

ta san da ita yake, hakan yasa ta riko hannun Laila suka tafi, Noor ma tabi bayansu, Jawad sai kallon Jahad yake wacce duk ta susuce tana hawaye, bayan sun tafi man ya juyo yana kallon Jahad, hannu ya mika mata alaman tazo, zuwa tayi a tsorace, manneta yayi da kirjinshi yana cewa "ki daina kuka bada saninki bane, zatayi lafiya"

sakin ajiyan zuciya ta fara tana cewa "ku yafeni bada sanina bane"

Ahmar ne yace "ki daina faɗin haka kowa ya sanki da kyaun hali baza kiyi haka da gangan ba"

zama Man yayi akan Sofa ya buɗe kafarshi ya janyota ta zauna a cikin jikinshi, shafa hannunta yake a hankali yanajin soyayya da tausayin yarinyar a ranshi, akoda yaushe idan tsautsayi ya faru saita ɗau alhakin hakan a kanta.


Jawad tashi yayi a wurin ya haura sama ranshi baki, yasan suna ɗakin Noor, shiga yayi bakinshi da sallama, Hamida zaune a gefe hannunta rike da mahuci tana fifita laila wacce take bacci, duk da sanyin Ac saida taci gaba da hura mata ciwon, zama yayi a ƙasa ya riko hannunta, cikin sanyin murya yace "kiyi hakuri Unty Hamida haka ya Man yake"

shafa hannunshi tayi tana murmushi tace "na sani kar ka damu"

Noor tayi shiru a gefe tana kallonsu, ta rasa menene gaskiya, kallonta Jawad yayi ya mika mata hannu, miko mishi tayi ya janyota jikinshi, shafa kumatunta yayi yace "naughty girl ta zama innocent"

dariya tayi "ya Jawad na tsorata ne wlh"

sakinta yayi, ya juya ya fita, Hamida hannu tasa a cikinta tana shafawa, ji take kamar bada gaske cikin ya fita ba, lumshe ido tayi "Allah sarki Jalal" tuno yadda yake kula da ita yasa tayi kewanshi sosai, saida laila ta samu bacci sosai kafin ta fita daga ɗakin hannunta rike dana Noor, Jahad har yanzu tana jikin Man tana rarraba idon tsoro, kitchen Hamida ta wuce taje ta fara aikin girki, Ahmar ne ya shigo yana tayata, tana dariya take shirya komai nata, sai surutu yake mata, saida ta tattara komai ta kai dining kafin tace "toh na gana sauko mu tafi"

saukowa yayi daga kan kantar da yake zaune, "kina kokari"

murmushi tayi suka fito, harara Shaira ta aika mata, tareda Kabir wanda yake kitsa abu a cikin ranshi, saida ta koma sama tayi wanka tasa riga da skirt wanda ya kama jikinta sosai, haka Hamida take bata damuwa da dressing koman kankancinshi sawa take ta mayar normal, shafa mai tayi ta kamo gashinta ta kitse guda biyu irin na asalin fulani, karamin bakinta ta kalla wanda yayi kyau sosai sakamakon lip balm data shafa, a hankali ta jingina kanta da jikin mirror tana tuna yayarta wacce sukayi kama sosai, hawaye taji yana zubo mata, hannu tasa ta share, takaddan da Adda Amrah tayi mata rubutu shi ta ɗauko tana karantawa, tayi missing ɗin ta, badan sun mutu itada Baba ba, da yanzu bata cikin wannan wulakancin, gidannan basa sonta ko kaɗan, ajiye takaddan tayi ta mike tana share idonta kamar batayi kuka ba, fita tayi ta rufe kofar a hankali, hanyar fita ta kama tana tafe tana tuna rayuwarta, gani tayi Ammi tana shirin shigowa ga kuma kasa kamar mai ne, da gudu ta sakko daga up ɗin, time ɗin Ammi ta taka man tayi baya zatayi wani mummunan faɗuwa, da karfi Hamida ta riketa, faɗuwa tayi akan kafarta yayinda ta taimaki Ammi ta mike, salati Ammi tayi jin kafar Hamida yayi kara tareda bakinta wanda ya furta "ahhh kafata"

da gudu Jahad ta karaso tana ɗagata, riketa tayi gam tana shirin mikewa, bayan ta mike ta kuma faɗuwa kasa kanta ya bugu da jikin tyles, da karfi Jahad tace "na shiga uku nayi kisa"

su Ahmar suka zo da gudu suna ɗaga Hamida wacce kanta ya fara jini, Ammi da ihu ta fara kiran Man, fitowa yayi da wando daidai gwiwa a jikinshi ko riga babu, kallon Ammi yayi yace "meya faru Ammi?"

nuna Hamida tayi tana cewa "ta mutu"

Jahad tayi wani ihu ta durkusa a wurin tana cewa "na shiga uku na lalace bada sanina na tureta ba"

cikin zafin nama Jawad yazo wurinta ya ɗagata, da karfi yace "kullum kina cikin mistake ne ke? koda yaushe kika aikata abu sai kice bada saninki ba ke kurma ce ko makauniya?"

ido Laila ta zaro jin abinda ya faɗa, kenan sai kurma ne suke aikata kuskure? a zuciye ta bar wurin, Man yazo gabanshi yana nunashi da yatsa yace "ina gargaɗinka kada ka kuma ɗaga mata murya"

ran Jawad ya ɓaci "saboda ta fini me?"


"ta fika komai"

cikin mamaki Ahmar yace "haba Man meyasa zaka faɗa mishi haka... Hannu ya ɗagawa Ahmar yace "ta fishi komai mana, kada kasa baki a wannan maganan"


da mamaki Ahmar yace "saboda me kada nasa baki? ban kai nasa bakin bane?"


ranshi ya ɓaci kenan suna ganin laifin Jahad ne? 


"Saboda magana ne tsakanin yaya da kani, jini ɗaya"

a firgice Ammi ta juyo tana kallon Man wanda yake shirin janyo Jahad jikinshi, hannu ta ɗaga ta sharara mishi mari me zafi, da karfi ta raba hannunsu tace "Ahmar ɗan uwanka ne jini ɗaya, ita kuma wannan ba kowa bace a tsakaninku, shi kuka Jawad ai kafin kowa sanin matsayinshi"

JAHAD tayi wuki-wuki da ido tana ɓarin jiki ganin abinda yake faruwa, ɗaga Hamida Ahmar yayi ya wuce Man, parking space ya nufa da ita, Jawad ya bishi tareda Ammi, mota suka shiga suka bar gidan, da gudu Jahad ta juya ta haura sama, ɗakinta ta shiga ta fara haɗa kayanta, bazata iya ba, turo kofar yayi, ganin tana haɗa kayanta ya riko hannunta ya fita da ita daga ɗakin, ɗakinshi ya shiga ya rufe, kwace hannunta take tana kuka bai kulata ba, saida ya tura kofar kafin ya janyota zai shiga ciki da ita, da karfi ta kwace hannunta tana shirin fita, mannata yayi da jikin bango yana kallon cikin idonta, a hankali ta dukar da kanta kasa tana cigaba da kuka, wannan wani irin rayuwa take ciki? komai yana ɓaci ta dalilinta? ganin yadda bakinta yake rawa a hankali ya fara matso da fuskarshi zuwa nata, bata ankara ba taji ya haɗa lips nashi da nata, lumshe ido yayi ya fara tsotsan leɓenta na kasa, bata hanashi ba saide har yanzu hawaye basu daina sauka ba, tsotsan bakinta yake yana shafa bayanta wanda ya cusa hannunshi ta cikin riganta, lumshe ido yake yanajin wani tsantsi da laushin fatarta yana shirin kaishi kasa, numfashi yake sauke mata da sauri da sauri, a hankali taji ya fara yawo da hannunshi cikin jikinta, hannunta ta ɗaura akanshi tana shafa suman dake kwance a kanshi, ji yayi kamar zai faɗi da sauri ya zaunar dasu kasa ba tare da ya cire bakinshi daga nata ba, kokarin sa hannu yake akan kirjinta domin Jahad ba karamar mace bace, tana saurin ɗaukan hankalin namiji, tureshi tayi tana kame jikinta wuri ɗaya tareda zaro manyan idanunta tana kallonshi cikin tsoro, baya-baya ya fara yana sauke numfashi domin ba karamin fita daga hayyaci yayi ba, hannu ya ɗaga ba tareda ya kalleta ba yace "am sorry kada ki tafi"

fita yayi ya rufe kofar akanta, ɗakin Ahmar ya nufa, Kabir dake zaune akan Sofa kamar me yin waya ya kalli yanayin da Man ya fito, mamaki abin ya bashi, Jahad ai ba irin wadannan bane to me ya faru tsakaninsu haka? kawar da zancen yayi koma de menene su suka sani.


ɗakin Ahmar yaje ya faɗa kan bed yana murza goshinshi, yana tausayin Jahad yana sonta sosai, bazai iya nisa da ita ba, drower ya buɗe ya ciro wani pills wanda yasan Ahmar baya rabuwa dashi, a hankali yace "sorry bro na faɗa maka magana cikin rashin ɗa'a ka gafarceni"

haɗiye pills ɗin yayi, a hankali bacci ya fara ɗaukanshi.


asibiti suka kaita aka duba kan, ba komai bane ta bugu sosai, duba ƙwaƙwalwa akayi babu matsala, sannan akayi dressing wurin aka ɗaure da farin kyalle har izuwa goshinta, saida aka kwance gashin kanta kafin aka ita dressing wurin, sai sannu su Ammi suke mata, ba abinda take sai murmushi da lumshe ido, Ammi da Jawad ne suka riketa suka kaita mota, Ahmar ke driving sai Jawad a gaba, Ammi da ita kuma a baya, sunyi nisa sosai babu me magana cikinsu kowa da irin tunanin da yake, hannun Ammi ta riko a hankali tana shafawa, cikin sanyin murya tace "Ammi wacece ta tureni na buga kaina a kasa?"

gaban Ammi ne ya faɗi, janyota tayi jikinta tace "ba tureki akayi ba Hamida faɗuwa kikayi, Jahad ba zata taɓa tureki ba kinji?"

jijjiga kai tayi, Jawad yana kallonsu ta madubi baice komai ba, har suka isa gida ba wanda ya kara magana, fita tayi tana ɗingishi domin kafarta duk da an gyara har yanzu yana ciwo, shiga gidan sukayi Noor tazo da gudu ta riketa tana mata sannu, a kujeran palour ta kwanta Ahmar ya wuce ɗakinshi, a firgice ya karasa wurin man, wanda yake shirin faɗuwa kasa yana birgima cikin bacci yana ihu, yana cewa zasu tafi dashi zasu kasheshi, bubbugashi ya fara, mekon ya tashi saiya fara rike kanshi yana cigaba da ihu, ruwan sanyi ya ɗibo ya watsa mishi a fuska, a firgice ya tashi yana rarraba ido, da mamakin Ahmar sai yaji yace "ka kiramin Jahad dan Allah, kaji Bro ka kiramin ita, tana ɗakina"

fita yayi yaje ɗakin Man ɗin yayi knocking, ganin da makulli ta waje ya buɗe ya shiga, kanta haɗe da gwiwa tayi shiru har bacci ya fara ɗaukanta, jikin kofa ya ɗan buga yana kiran sunanta, tashi tayi tace "yah Ahmar"

"Man na kiranki"

fita tayi da sauri tabi bayanshi, da mamakinta taga ya shiga ɗakinshi, suna isa ta hango Man akan bed ya rike kanshi yana jujjuyawa, da ɗan gudu ta karasa tana cewa "meya sameka"

janyota yayi jikinshi ya rungumeta da karfi har saida tayi kara, zaunar da ita yayi akan cinyarshi ya mannata da jikinshi yana sakin ajiyan zuciya, a hankali tasa yatsunta cikin gashin kanshi tana wasa dashi, saida ya ɗan dawo normal tace "meya sameka?"

kifeta Yayi akan gadon yabi bayanta, kwanciya yayi a kanta ya kuma rungumeta da karfi yana sakin numfashi, ta fahimci abinda ya sameshi, saide bataso kowa yasan sirrinshi ciki harda ƴan uwanshi, hannu tasa a goshinshi tana yimishi addu'a, a hankali ya fara hawaye, bata daina ba saida ya kuma runtse ido ya koma bacci, blanket ta janyo ta rufashi dashi bayan ta zame jikinta a hankali, Ahmar dake jikin kofa ya kasa tafiya yana kallonsu, saida tazo gabanshi ta dukar da kai zata wuce yace "dakata"

cak ta tsaya tayi shiru 

"Meke damunshi?"


"Mummunan mafarki yayi shine nayi mishi addu'a"

kallon ta yayi da kyau yace "meyasa yake hugging naki haka?"

"Yah Ahmar addu'a yakeso nayi mishi, bakaga danayi yayi bacci ba?"

girgiza kai yayi, a hankali ta juya ta fita daga ɗakin, wurin Hamida taje kanta a kasa tace "ki yafeni"

murmushi tayi "bada saninki bane Unty Jahad ba komai"


Kallon Ammi tayi a hankali ta karaso tace "Ammi na ki yafemin"


"Bakimin komai ba Jahad kada ki damu"

zama tayi a gefe tayi shiru, Abba ne ya kira Ammi a waya tayi mishi bayanin abinda ya faru, wayan ta mikawa Hamida, cikin sanyin murya ta gaida Abba, ya rinƙa yimata sannu tareda godiya, ba Komai kawai ta faɗa, Jahad tana kallonsu har ya kashe wayar.


ranan itace ta haɗa musu abinci tayi komai a gidan, Ahmar zama yayi a gefen Man yana kallonshi, saida yayi bacci me isanshi kafin ya tashi, ido huɗu sukayi da Ahmar da sauri ya janye idonshi ya bar wurin, murmushi man yayi dan yasan sun saba faɗa su shirya tun suna yara, sauka yayi daga bed ɗin ya shiga toilet, sabulai masu kamshi ya goga a jikinshi, saida ya tara ruwa kafin yayi wanka ya ɗaura babban towel a waist nashi ya fito, da sauri ta juya baya jikinta yana ɓari tana zaro ido tareda keɓe baki alaman a tsorace take, cikin harhaɗa magana tace "ka...ka..kasa riga dan Allah"

lalle yarinyar nan ta raina mishi hankali, fuska ya haɗa ba tareda yayi magana ba ya kwance towel ɗin ya ɗau wani wando ɗan karami yasa, baisa riga ba baisa komai ba yace "juyo nasa"

juyowa tayi da niyan sanar mishi abinda ya kawota, ganinshi haka ta tsala ihu ta fita da gudu, kafarta na ciwo haka ta daure tana gudu, saida ta bar part nashi tasa hannu a kirji tana numfashi da karfi, wannan ashe bayan mugunta ya iya iskanci, Jahad ce tsaye a gefenta tace "meya faru?"

a tsorace tace "babu" tareda tafiya ta bar wurin, taɓe baki tayi ta wuce part nashi domin ɗauko maganin Ammi, tayi knocking yasan itace shiyasa yace "Yes"

turo kofar tayi, da sauri ta juya baya, ganin daga shi sai towel a waist, hannu tasa zata buɗe kofar ta fita, da sauri yazo gabanta ya riketa, zubawa kirjinshi wanda yake da faɗi ido tayi, a hankali ta lumshe idon tanajin bugun zuciya yana karuwa mata, hannunta ya ɗaga ya ɗaura akan waist nashi yana kallon idonta wanda ta lumshe, dunkule hannun tayi, hannu yasa a waist nata ya matso da ita jikinshi, a hankali ya kai bakinshi kunnenta cikin romantic voice yace "ki shafamin mai"

ba shiri ta zaro ido tace "ni?"

jijjiga kai yayi, ko bazaki iya ba?


"bazan iya ba"

kara matso da ita yayi yana shinshinar wuyanta, cikin kasa da murya yace "haka zakimin idan munyi aure? ki fara koya okay?"

Bata iya mishi musu, asali batada musu sai shiru da eh ko a,a, janyo hannunta yayi ya karasa kan drower gaban mirror ya zauna, hannunta me laushin gaske ya kamo ya matsa lotion ya juya mata baya alaman ta fara, murzawa tayi a hannunta, cikin tsoro da nutsuwa ta fara shafa mishi, lumshe ido yayi yanajin wani irin feeling from no where yana taso mishi, hannunta kamar audiga, cigaba tayi da shafawa, a hankali ya lumshe ido yace "ashh"

da sauri ya damki hannunta yace "is okay"

Yasan idan taci gaba zai iya tabka abin kunya, hannu tasa a baki tana dariya, tsayawa yayi yana kallonta ta cikin madubi, ta ganoshi kenan, tashi yayi zai rikota, da gudu ta fita daga ɗakin tana dariya, lumshe ido yayi yanason ganinta tana dariya hakan yana sashi cikin farin ciki, sa kaya yayi ya ɗau riganshi na doctor ya fita, ba karamin kyau yayi ba acikin riga da wando na shadda sky blue, ya haska sosai, lumsashun idanunshi da karamin bakinshi suna kara mishi kyau sosai, ya gyara gashinshi ya shafa man gashi me kyau, taku yake cike da kasaita, sai ƙamshin turaren shi ke tashi, saida yazo sauka daga up kafin yasa riganshi na doctor wanda ya kuma fito da asalin kyawu da kuma haiban da Allah yabashi, Man ba karamin kyakkyawa bane abin karshe ne shi a kyau, tafiya take tana waka tunawa da garinsu wanda suke zuwa gaɗa da dare, kanta ta ɗaura flask ɗin miya tana lumshe ido tana tuna wakar "ayye ya raye"

ji tayi tayi karo da mutum, da karfi tayi ihu bayan ta juye mishi jar miyan dake kanta, cak ya tsaya yana kallon white rigan doctorn daya ɓaci da jar miya har ya wanke mishi fuska, zaro ido tayi ganin Man ne, huci ya fara yana tunanin me zaiyi mata yaji daɗi? gashi ana jiranshi a hospital akwai operation na gaggawa, kwance ɗankwalin kanta tayi nan take gashin kanta me yawa ya warware zuwa gadon bayanta, da sauri ta fara goge mishi gaban rigan, rigan sai daɗa ɓaci yake, da karfi ya tureta saida ta bugu da jikin bango "wayyo Allah na"

ta faɗa tana rike kanta, rigan ya cire ya watsa mata a fuska, karasowa yayi ya dalleta da wani gigitaccen mari, ihu ta fara, ranshi ya ɓaci sosai bata iya bada hakuri ba kenan?

Ahmar da yayi shiri cikin kayan doctor shima yana da aiki emergency yazo da sauri ya riketa, ganin Man yana shirin zaro sucket, da karfi ta damke Ahmar tana kuka, ganin ya riketa yasa ya haura sama a zuciye, ga fuskarshi sai raɗaɗin barkono yake mishi, wankan dole ya kumayi, kafin ya fito ya canja kaya yasa kanana brown, fitowa yayi hanunshi rike da waya yana basu hakuri cewar gashi nan zuwa, har yanzu Ahmar yana tsaye yana lallaɓanta, sani dogon tsaki yaja kafin ya fice daga gidan, motarshi ya shiga da mugun speed ya bar layin, bai tsaya ko ina ba sai hospital nashi, gaisuwa ake aika mishi yana ɗaga musu hannu, emergency room ya shiga nan suka fara aiki, dama shi kawai ake jira, cikin sa'a suka gama ba tareda matsala ba, dama baya aiki a samu matsala, office ya koma ya zauna, Kamal ne ya shigo ya zauna tare da dafe kanshi, yana sign a takadda yace "ya dai?"

ɗan tsaki yaja yace "wallahi aure nake so"

dariya Man ya kwashe dashi, saida yai me isarshi kafin yace "aure? to wa ya hanaka?"

"Umma na mana, wai sai na hakura zuwa 3months"


"to saboda me Umma tace haka Kamal?"


"wallahi ban sani ba, kasan Allah sai nabi bayan gidansu Eeshat nayi mata fyaɗe"

wani dariyan Man ya kumayi hadda rike ciki "to meyasa bazaka iya hakura bane?"


"gaskiya bazan iya hakura ba, domin inada bukata sosa 30years wasa ne.."

da karfi aka banko kofar, wata nurse ce ta shigo tana cewa "Sir wanda aka yiwa operation ya mutu"

a tare suka mike da Kamal suka fita, basu tsaya ko ina ba sai ɗakin da suka bashi, dubashi sukayi suka tarar ya mutu da gaske, kallon Kamal yayi kamar yadda shima kamal ɗin yake kallonshi

"garin yaya?"

ɗaga kafaɗa kamal yayi alaman bai sani ba ai tare suke, kallon nurse ɗin yayi "a kawomin kayan aiki"

shigo da kayan aiki masu yawa aka kawo nan ya fara gwaje-gwaje, saida ya duba gawan da kyau ya kalli duk ma'aikatan wurin waɗan da sukayi tsuru-tsuru cikin alaman tambaya da rashin dariya kamar yadda ya saba yace "poison aka bashi, waye yazo wurinshi?"

nan suka fara musu kowa yana cewa bashi bane, kallon kamal yayi, gaba ɗaya jijiyoyin kan Man ya tashi, fita yayi daga ɗakin, abin mamaki ƴan jarida sun cika asibitin makil, kallon Kamal yayi "waya kirasu?"

"tare fa muke taya zan sani?"


tafiya ya fara zaije office nashi da gudu sukayi kanshi suna aika mishi tambayoyin da ya kusa fasa mishi ƙwaƙwalwa, zufa ya fara ƙeto mishi ran maza ya ɓaci, hannunshi har ɓari yake, wata daga cikin ƴan jaridan tace "yallaɓai Dr munji labarin ka kashe wannan ɗan kasuwan da suke gaba da kanin mahaifinka wanda ya mutu kwanaki da suka wuce, ya samu matsala a cikinshi shiyasa yazo nan asibiti domin ka dubashi hakan yasa ka kasheshi ta hanyar operation"

da wani irin karfi Man yaje wurinta ya kwace abin hannunta ya nunata da yatsa "kije kiyi aure zaifi miki yawon yiwa mutane sharri"


wani ne daga gefe yace "yallaɓai ba sharri bane domin munga hoton gawan, ga ma ƴar mamacin tana zuwa" nunata sukayi tana zuwa da farin riga dogo tana ihu, da karfi ta shaƙe Man tana bugun kirjinshi "ka kashemin mahaifi ka kasheshi?"

tureta yayi ya wuce office ɗinshi tareda banko kofar ya jingina da jikin kofan yana salati, meke faruwa dani? kisan kai? saida ya ɗan nutsu ya ciro waya "a kori ƴan jarida daga nan sannan a kunna cctv Camera a tara duk ma'akatan a office na taro"

kashe wayar yayi, sai bayan kusan 50mins kafin asibitin yayi shiru, daya rufe ido sai yaga yarinyar tana bugunshi, kiranshi Kamal yayi yace "komai is ready"

sun tafi da gawan, fita yayi yaje ɗakin taro, kowa ya hallara hadda masu shara da mopping, ya kasa zama sai murza kanshi yake, fuskarshi yayi jaa sosai, kunna cctv akayi nan aka fara duba abinda ya faru a ranar, baiga komai ba, ɗakin mutumin suka duba basu ga kowa ba, yace a koma baya, kara komawa sukayi nan ma babu wani shaida,   kamar yayi kuka yace "kashe"

bayan sun kashe sun juya zasu fita yace "ku dawo"

dawowa sukayi yace "kunna"

kunnawa sukayi yana kallo yaga mutum da bakin kaya da mopper a hannu, kanshi da nikap, Kara zooming akayi nan yaga takalmin kafar na mace ne, kallon masu shara yayi cikin tuhuma yace "wacece wannan a cikinku?"

rantse rantse suka fara basu bane, kara kallon kafar yayi yana bin nasu da kallo, tabbas babu ko ɗaya cikinsu, kuma babu shakka wannan me nikab ɗin ne tayi kisan, sallaman kowa yayi bayan ya karɓi video ya tura a wayarshi, rufe asibitin akayi sai bayan kwana uku, kowa ya watse jikinshi a mace, zai shiga mota yaga an farfasa mishi glass, hankalinshi ya kuma tashi, a zafafe ya shiga yana runtse ido, zama yayi a kujaran driver yaji kamar ya zauna akan abu, tashi yayi ya duba, da mamaki yaga takalmi guda ɗaya na mata, wayarshi ya ciro ya duba videon, wannan takalmin shine makashin yasa a lokacin da zaiyi kisan, ɓoye takalmin yayi ya tada motar yabar hospital din, tafiya yake jikinshi yana rawa domin yanaji kota ina ana yaɗa labarin Dr Man ya kashe wannan babban ɗan takara kuma ɗan kasuwa Alhaji Garba, goslow yayi yawa hakan yasa ya tsaya, hangoshi akayi sakamakon glass nashi daya fashe, da gudu aka taru akanshi ana kara jefa mishi tambayar da take neman ruguza mishi lissafi, da kyar ya samu ya tsira a hannun mutanen, da gudu yake tuki burinshi ya iso gida kawai, jikinshi sai ɓari yake, horn yayi da karfi kamar zai fasa kofar, getman cikin tsoro ya leka ya buɗe mishi, da gudu ya shiga gidan har yana bugun get ɗin su, ajiye motar yayi ba tareda ya gama parking ba ya ɗau takalmin ya shiga gida, a palour ya tadda kowa sun zauna sunyi tagumi, Ahmar da rigan likita a jikinshi da alama yanzu ya dawo gidan, Kabir na zaune a gefen Hamida tsabar tashin hankali yama manta basa shiri, ganinsu a haka yasa jikinshi yayi sanyi, da sauri ya ɓoye takalmin a cikin aljihun wandonshi, Ammi tana kwance da alama zuciyarta ta buga, a hankali ta mike zataje wurinshi, Jahad ce taje da sauri tana cewa "kana lafiya?"

hannu Ammi tasa zata rikeshi da karfi ya janyo Jahad jikinshi, saida tayi siririyar ƙara domin ya matseta dayawa, kuka ya saki harda shesheƙa, Ammi tsayawa tayi turus tana kallonshi, bataji daɗi ba, domin ta saba idan yana kuka jikinta yake zama har saita lallasheshi, gashi yau baizo wurinta ba, a hankali ta juya zata koma kan sofa, Hamida tazo gabanta ta rungumeta, cikin sanyin murya tace "Ammi kada ki damu" sakinta tayi ta zaunar da ita akan sofa tana bata ruwa a Cup, cikin tashin hankali ya fara shafa bayan Jahad, kanshi yake cusawa cikin wuyanta, da sauri yasa hannu ya cire ribbon ɗin data kame gashinta dashi, haka yake idan yana cikin damuwa yana son jikin mutum sosai, bata hanashi ba domin tasan ba'a hayyacinshi yake ba, bai bar kuka ba kuma bai bar shafa bayanta zuwa jikinta ba, kamar zai maidata ciki, a hankali takai bakinta kunnenshi tanayi mishi addu'a haɗe da shafa gashin kanshi, da karfi tace "Hamida bani ruwa"

miƙewa Himada tayi ta bata ruwa a cikin Cup cikin girmamawa, ɗagoshi tayi zata bashi ruwan, ya zubawa lips nata ido, zaifi jin sauki idan ya haɗa bakinta da nashi, ganin abinda yake shirin yi, tayi sauri ta kauda kanta, Ammi ta fahimci hakan, Cup na ruwa ta miƙa mishi, turewa yayi yana shirin kara janyota, da sauri tayi baya tana kara mika mishi, karɓa yayi ya kafa abakinshi saida ya shanye tass kafin yaje gaban Ammi ya rike hannunta cikin hawaye yace "banyi kisa ba"

shafa kanshi tayi "na sani kayita addu'a"

Jawad ganin yayanshi cikin wannan halin yasa shima ya fara kuka, Hamida ta matso tasa hannu a kanshi tace "jarumi da kuka? please ka daina komai zaiyi sauki kaji?"

Kabir yana kallonta yayi murmushi, tanada kyaun hali, kawai ya saba da tsokanarta ne, Abba ya kirasu video call yace Man ya kwantar da hankalinshi gobe zai shigo nigeria komai zaiyi sauki"


godiya ya yiwa Abba, haka suka zauna shiru, Hamida ta lura basu saba da damuwa ba shiyasa suka zauna haka, Man ya mike zai shiga ɗaki, Noor ta kalli Jahad cikin sanyi tace "Unty Jahad ki rakashi"

Jawad ido ta zuba mata dan wallahi tana tsoron Man, yadda ya zubawa lips nata ido ɗazu, tasan idan ta bishi ba wani kunya ne dashi ba, duk da yana cikin damuwa babu abinda zai hanashi tsotsa, fahimtan hakan yasa Ammi tace "Hamida ta rakashi daga nan saita gyara ɗakin nashi"

dama laila mutuniyar tashi batada lafiya domin bata da riga kirjinta ya kone, Shaira kuma ba shiga harkan mutane take ba, gata da girman kai da raini, jin haka yasa Jawad tace "zan rakashi ba komai Ammi"

Ammi ta lura kishi ne yasa ta amince, rakashi tayi, saida ya shiga ɗaki ta tsaya a bakin kofa tace "bari na koma" janyota yayi da karfi ta faɗa jikinshi, kamar ta sani yatsanshi ɗaya yasa yana zagaye leɓenta na kasa, jikinta ta kwace zata gudu ya kuma janyota da karfi, a kunne ya raɗa mata "ina cikin damuwa ki barni nasha"

gabanta ne ya faɗi, so take ta gudu ya matso da ita sosai, a rayuwa bata taɓa zaton zata kasance da wannan Dr kyakkyawa wanda ƴammata masu ji da kansu yaran masu kuɗi suke crushing dinshi ba, sai gashi Allah ya haɗa jininsu, yasa mishi sonta a zuciyarshi, a hankali ya kai bakinshi kan nata runtse ido tayi, saɓanin shi daya lumshe yana tsotsan soft lip nata, hannunta ya riko ganin tana shirin tureshi, maida hannun yayi baya ya jingina ta da jikin bango yana cigaba da kissing nata, hannunshi ɗaya ya rike gashin kanta, ɗaya kuma ya rike hannayenta duka biyu ta baya, sai numfashi yake saukewa a hankali yana jin wani feeling yana taso mishi, buɗe kofar tayi domin Ammi tace ta kira mata Jahad kamar tasan halin ɗanta, baya ta juya tace "subhanallah" 

ganinsu a haka ba karamin tsorata ta yayi ba, Jahad ta far kwace kanta da karfi ya danne ta, ɗago hannu take tana yiwa Hamida magana, kin sakinta yayi da karfi ta fara buga jikin bangon tanaso Hamida ta juyo, Hamida kuwa ta tsaya sai rarraba ido take ranta ya ɓaci, zasu zo suna iskanci a ɗaki bazasu rufe kofa ba? yanzu miye haka?

a hankali ya zame bakinshi ya toshe bakin Jahad dan so yake ya firgita wannan ƴar aikin, da ɗan karfi yace "ki bari mana muyi Jahad wallahi ina sha'awarki"

da gudu ta bankaɗe kofar ta fita, sai a time ɗin ya saki Jahad yana juya kai kamar bashi ba, hannu tasa ta bugeshi a kirji, idanunta har sun cika da hawaye, fita tayi, ya zauna a bakin gado yana dariya, yanason Jahad har cikin ranshi, bai taɓa jin wani abu akan mace ba sai Jahad, nutsuwa da kyau ga ilimin addini shine yake kara dulmiyar dashi duniyar sonta, Hamida na fita taje gefe ta zauna, Allah ya taimaka babu Ammi a wurin, shiru tayi tana rarraba ido, Ahmar ne ya zuba mata ido yana karantar yanayinta, Jahad ta sakko tana kallon Hamida, so take tayi mata bayani, amma Hamida tayi shiru tana kallonta, Ahmar ya ɗago hakan, abin ma dariya ya bashi kenan Hamida ta gansu may be suna kiss ne, yasan ɗan uwanshi da iyayi koda ya ganta bazai bari ba, a hankali ya mike yaje gefenta ya zauna "madam tsoro what happened?"

"ba..ba..ba komai"

bai kuma magana ba tace "bari naje nayi girkin dare, tashi tayi ta shiga kitchen dafe kirji tayi, "yau naga ikon Allah tunda aurenta zaiyi har anyi musu baiko ba saiya hakura ba? Allah sarki Jahad gaki da kunya Allah ya baki Miji mara kunya"


"ba laifinshi bane Hamida soyayya idan tayi zai tana sa hakan, kinga yah Man yana sona shiyasa yake min hakan".*kuɗin littafina ₦300 ne biya ta nan 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta nan 08144818849, turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.