Doctor Mansoor 12


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

_Jiddah S Mapi_

*Chapter 12

                 ~Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Man munyi kisa"

cewar Ammi dake zaune a gaban mota tana dafe da kirji, cikin gaggawa suka fito daga

motan, mutanen dake gefe suka karaso, taimaka musu sukayi har saida suka sata a mota, shiga Man yayi yayinda Ammi take kujeran baya tana fifita Hamida, babu abinda yake motsi a jikinta hakan ke tada hankalin Ammi, daga gaba yake kallon yadda take sharan kwallah cikin son kwantar mata da hankali yace "Ammi na stop crying babu abinda zai faru da ita"

"taya zan daina kuka? idan ta mutu fa? munyi kisa fa kenan"

bai kuma magana ba sukaci gaba da tafiya, wani asibiti dake kusa ya kaita don ganin hankalin Ammi a tashe, karɓanta akayi, emergency room aka kaita, Ammi sai safa da marwa take ta kasa zama, Man sai lallashinta yake, bayan 1hr suka fito daga room ɗin wani doctor yace su sameshi a office, binshi sukayi a baya saida suka zauna ya kalli Ammi yace "kece mahaifiyarta?"

jijjiga kai tayi alaman eh, saida yayi shiru kafin daga bisani yace "sai hakuri.."

tashi tayi daga kujeran tace "meya faru?"

"kwantar da hankalinki ki zauna"

zama tayi tana zaro ido, cikin alhini yace "cikin jikinta ya zube sanadiyyan bugata da mota da akayi"

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, zamu iya tafiya da ita?"


"eh zaku iya idan ta dawo hayyacinta zuwa anjima kuje ku ganta"


tashi sukayi su duka sukaje ɗakin, tana kwance da innocent face nata wanda ya kara fari sosai, tana glowing, gashin kanta ta kame wuri guda da ribbon, haɗe fuska yayi yana juya baya, Ammi ta zauna a gabanta ta riko hannunta tana kallon fuskarta, "tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi wannan halitta"


kusan 1hr ta tashi tana salati, hannunta ta ɗaura a cikinta wanda yake mata ciwo sosai, kallon Ammi dake mata murmushi tayi "cikina yana jikina?"


wasu hawaye ne suka cika idon Ammi tace "A,a kiyi hakuri cikin ya zube"

lumshe ido tana hawaye masu ɗumi, shafa cikin tayi tana, cije lip nata na kasa tayi kafin tace "shikenan nayi ciki a sati biyu na rabu dashi kuma"

kallon agogon hannunshi yayi yana ɗan tsaki kaɗan yace "Ammi muje ko?"

riko hannunta Ammi tayi tace "muje mu kaiki gida"

manyan idanunta ta zubawa Ammi kafin tace "banida gida"

wani bakin ciki Man yaji, wai bata da gida, to yawon bariki take?


cikin tausayawa kanta tace "zan biku gidanku koda ƴar aiki ne ku ɗaukeni zan rika yimuku aiki kuna biyana"

harara ya banƙa mata wanda sai a lokacin ta kula dashi, kyakkyawan matashi ne me ji da kuɗi da samartaka, Ammi ta riko hannunta "muje"

fita sukayi saida suka shiga Office ɗin doctor ya basu sallama kafin suka shiga mota, tana gidan baya Ammi dashi suna gaba, jefi jefi take kallonshi baiso zuwan yarinyar gidansu ba, domin babu alaman dariya ko kaɗan a tare dashi, saima haɗa fuska da yake, sun iso makeken Get ɗin su getman ya buɗe musu, Hamida sai rarraba ido take tana kallon gidan, bayan yayi Parking ya fito baiko kalleta ba ya wuce gida, kallon mamaki Ammi ta bishi dashi, kafin ta girgiza kai ta buɗewa hamida mota tareda cewa "sannu"

fitowa tayi suka fara tafiya cikin gidan, kanta ɗaure da farin kyalli irin na wanda sukaji ciwo, domin ta bugu a goshi, hannunta Ammi ta riko suka fara tafiya tana ɗingishi.


yana shiga yaci karo da Jahad wacce tayi wanka cikin riga da skirt na atamfa ta ɗaura kanta tayi kyau sosai, kamar zata faɗi da sauri ya rikota yana janyota jikinshi, murmushi tayi "ina kaje yau?"

gyara mata ɗankunnen dake shirin faɗi yayi yana cewa "kinyi missing ɗina ne?"

fuskarta tasa a kirjinshi ta ɓoye tana dariya, daɗa rungumeta yayi domin jin ƙamshin dake tashi a jikinta, a hankali yasa hancinshi jikin wuyanta yana sunsuna, da sauri ta ture kanshi tana dariya tace "bari naje cikin gida"

fita zatayi ya riko hannunta da karfi ya kuma janyota jikinshi yana daɗa mannata sosai yanajin kamshinta, a hankali yace "kinyi kyau"

zamewa tayi ta gudu, kallonta ya tsaya yi yana murmushi, haka kurun yake jin tausayin yarinyar, zamanta shiru tana tunani shike ɗaga mishi hankali, hakan yasa yake janta a jiki, yarinyar akwai son addini ga nutsuwa da kamun kai, hakan yasa yaji yana mugun tausaya mata da rayuwar datake ciki, yana cikin tunani yaji muryan Ammi tana cewa "sannu mamana"

ko juyawa baiyi ba, Jahad tsayawa tayi turus tana kallon yarinyar da Ammi take rike da ita, ta tsorata da ganin kyawun yarinyar, wannan kodai balarabiya ce itama? kawar da tunanin tayi ta hanyar zuwa wurin Ammin tana cewa "sannu da dawowa Ammi"


"yawwa Jahad riketa ki kaita ɗakin Noor"

riketa tayi tana cewa "sannu"

man wucewa yayi baiko kara juyowa ba, Hamida murmushi tayi mata, itama Jahad ta maida mata da murmushi, takawa ta fara tana ɗingishi, Jahad na rike da ita suka fara taka matattakalar stair ɗin, kamar zamewa kamar turewa haka taji nan ta faɗi tun daga sama ta fara gangarawa tana ihu, Ammi dake tsaye tana cire mayafinta da karfi ta saki wani ihu tana kiran sunanta "Hamida?"

Jahad zaro ido tayi jikinta yana ɓari tana kallon yadda Hamida take gangarawa kanta yana cigaba da buguwa akan stair ɗin, da gudu Ammi tazo ta rungumeta lokacin da ta gama gangara, kanta yana jini jikinta duk ya farfashe, Jahad ma ta riketa tana cewa "sannu"

"Mannnn"

da karfi Ammi take kiran sunanshi, Abba dake ɗaki ya fito yana tambaya meke faruwa? ganin yarinya kwance cikin fashewan jiki yace "meya sameta? daga ina take?"

ɗagata sukayi su biyu da Abba suka wuce ɗakin Noor da ita, sun bar Jahad tsaye tana kallonsu, man ne ya fito da ɗan gudu yana cewa "meya faru?"

hawayen tsoro ya wanke mata fuska jikinta ya fara ɓari tana nuna stair tana so tayi magana ta kasa, da sauri ya matso ya janyota jikinshi yana bubbuga bayanta, rungumeshi tayi sosai tana kuka, shafa kanta yayi yana cewa "its okay shiii"

sakin ajiyan zuciya ta fara, saida yaga ta nutsu kafin yace "meya faru?"

"Hamida ta faɗi akan stair, bada sanina ba amma a hannuna ta faɗi" ɗaga tafin hannunta tayi cikin tsoro tace "a hannuna ta faɗi"

ganin ta tsorata ya kuma janyota jikinshi yana cewa "shikenan Allah ne yayi zata faɗi a hannunki ki nutsu please"

saida ta nutsu ya riko hannunta suka haura zuwa ɗakin noor, time ɗin har Jawad yaje ɗakin yana zaune a gefe yana kallonta, shigowa sukayi bakinsu ɗauke da sallama, kallon yadda suka rike hannu Ammi tayi raba hannun tayi da karfi tace "ina kiranka tun ɗazu ina kake?"

"Kiyi hakuri Ammi nayi nisa ne"


"dubata" 

zama yayi a gefe ya kalli Jawad dake zaune yace "ɗauko min firstaidbox"

"bari na ɗauko"

cewar Jahad, cikin rashin fara'a Jawad yace "ni akace na ɗauko bake ba"

ɗauke kai yayi daga kallon da Abba ya aika mishi, fita yayi ya ɗauko, karba Man yayi ya fara dressing wurin yana yana ɗauke kai daga kallonta, yarinyar ba karamin haushi take bashi ba, haka kawai baison ganin fuskarta, saida ya gama yayi mata allurai, wasu bandage ya ɗaura mata a goshi da hannu kafin ya wanke duk wani ciwon da taji, ya rufe da bandage, tashi yayi zai fita "baka mana bayani ba ina zaka?"

cewar Ammi, a hankali yace "nayi mata alluran bacci idan ta tashi zataji sauki"

fita yayi, Abba ma suka fita, Ammi da Jahad suka bisu a baya, Jawad ne kawai ya rage a dakin yana kallon Hamida, haka kawai yaji ta bashi tausayi, gata kyakkyawa da ita, tashi yayi ya zauna a gefenta kan bed ɗin yana riko hannunta, a hankali ta buɗe ido domin bacci bai riga ya ɗauke ta ba, murmushi tayi mishi wanda ya lotsar da gefen kumatunta, a hankali yace "naji Ammi sunce sunanki Unty Hamida?"

jijjiga kanta wanda yayi mata nauyi tayi tana kara mishi murmushi, hankali ya shafa hannunta "Unty Hamida nice to meet you"

bata iya magana sai lumshe ido da murmushi, tana kallonshi har bacci ya ɗauketa.Jahad ɗaki ta shiga ta faɗa kan gado tana tuna yadda Hamida ta faɗi, kuka taji ya fara kubce mata, yarinyar ta bata tausayi, a hankali ya turo kofar yana kallonta, yadda ta rungume Pillow tana kuka, karasowa yayi ya zauna gefenta, batasan ya shigo ba shiyasa bata ɗago ba, karewa bayanta kallo yayi, a hankali yace "tashi muyi magana"

da sauri ta tashi tana share hawayen tana kokarin ɓoye kukanta, murmushi kawai yayi mata, hannunta ya riko yace "zaki aureni?"

da mamaki ta kalleshi da kyawawan idanunta, matse hannunta yayi da karfi yakuma cewa "zaki aureni?"

shiru tayi tana nazarin maganarshi "zaka iya auren wacce ta taɓa zibar da ciki?"

da sauri yasa hannu ya rufe bakinta, cikin kasa da murya yace "banso kowa yaji, nasan bada sonki kikayi hakan ba, Jahad ke mutuniyar kirki ce, kinada nutsuwa kinsan abu me kyau, kinada ilimin addini, ƙaddara ce tazo miki a haka"

wasu hawaye masu ɗumi suka fara wanke mata fuska, tafin hannunshi yasa yana share mata a hankali yace "daga yanzu bazan kuma barinki ki zibda hawaye ba, zan kula dake kamar kwai, zan baki soyayya wanda kika rasa shi a rayuwarki ta baya, i love You so much Jahad"

da karfi tayi hugging nashi tana kuka, "i love You too Man"

wani farin ciki ya mamaye zuciyarshi, saida ya barta tayi kuka me isanta kafin yace "ya isa tashi kije kiyi wanka sai kiyi bacci ko?"

a hankali ta tashi ta wuce toilet, runtse ido yayi yanajin zuciyarshi tana zafi, baison jin kukan Jahad ko kaɗan, tana bashi tausayi sosai, wayarshi ce tayi ringing, cirowa yayi daga aljihu, Bro Ahmar yagani yana yawo a gaban wayan, da sauri ya ɗaga, cikin tashin hankali Ahmar yace sun kashe Dady"

dirowa yayi daga kan bed ɗin yana cewa "su waye?"

"ka kaiwa Abba wayan"

da wani irin gudun da baisan ya iya ba yaje ɗakin Abba, bangaje kofar yayi, time ɗin Abba na rungume da Ammi domin hankalinta ya tashi akan Hamida, sakinshi tayi da sauri, Man baiji wani kunya ba ya mikawa Abba wayan, karba yayi yana mishi kallon lafiya?

karawa yayi a kunne, jin Ahmar yana kuka yace "meya faru?"


"Abba sun kashe Dady"

"What? su waye?"

"wasu mutane da bakin kaya da bindiga kuma sunsa bindiga akan Momy"

kafin tayi magana yaji Ahmar yayi ihu yana cewa "Momy? ki tashi Momy"

cikin tashin hankali Abba ya saki wayan ya fita daga ɗakin, uku uku yake taka stair har ya isa wurin ajiyan motoci, Man ne ya bishi suka tafi tare, da gudu suke wucewa, kallon wayarshi yayi 9:30 na dare, "Abba anya ba risk bane zuwanmu ba tareda ƴan sanda ba?"

"kai kake ganin risk akan ɗan uwana da iyalanshi na gommace na mutu"

basu tsaya ko ina ba sai gidansu Ahmar, parking Abba yayi suka shiga ciki, acikin gida sukaga Ahmar da Kabir ɗaure, cikin tashin hankali suka karaso suna kwancesu "ina laila da shaira? Ina kuma Sabir?"


"Suna cikin ɗaki"

da gudu Man yaje yana bubbuɗe kofar, a ɗakin Shaira ya gansu sun ɓuya a karkashin gado hadda Sabir wanda yake zaro ido da yaji an buɗe kofa, jin muryan Man yasa suka fito su duka, Laila ce taje da gudu ta rungumeshi tana kuka, bayanta ya shafa yana kallon Shaira dake matsar kwalla, hannunsu ya riko suka fita daga ɗakin, suna ganin Abba sukaje da gudu, rungumeshi sukayi su duka suna kuka, kallon gawan dake kwance sukayi Laila ce ta faɗi kasa domin itace tafi rauni cikinsu, ɗagata Kabir yayi ya kaita mota, gawan suka sa a motar Abba, su kuma suka shiga motan Dady suka bar gidan, basu tsaya ko ina ba sai gidan Abba, fita sukayi jikin kowa da sanyi, ɗaga Laila Man yayi a kafaɗarshi ya shiga da ita cikin gida, suna su Ammi suna zaune cikin tashin hankali dasu Jahad da Noor, sai Jawad dake kwantar musu hankali yana cewa su nutsu ba komai, da sauri Jahad ta mike ganin Man ɗauke da mace a kafaɗa, kwantar da ita yayi akan sofa Ami tana cewa "lafiya?"

shigowa sukayi da gawan Ahmar, Sabir, Kabir, a palour aka kwantar dasu, Jahad tana gani ta rungume Man tana ɓarin jiki, ba karamin firgita tayi ba, itama Ammi faɗuwa tayi kasa tana ja da baya, da sauri Abba ya riketa yana cewa ta daure, haka suka kwana ido biyu babu wanda ya runtsa, Hamida na ɗaki tana bacci sakamakon alluran bacci da akayi mata.*Asuba ta gari*


an tashi da labarin shahararren ɗan siyasan nan kuma ɗan kasuwa wanda yake neman takaran kujeran governor an shiga gidanshi an kasheshi shida matarshi, labari ya yaɗa ko ina, a gidan kaninshi za'ayi jana'iza da karfe bakwai na safe, karfe shida gidansu Man ya cika raf da mutane sai shirye-shiryen jana'iza ake, Hamida bayan ta farka taga mutane dayawa a cikin gidan duk wanda ta tambaya baya bata amsa, gefe ta samu ta zauna tayi tagumi yana kallon mutanen dake shiga da fita, Jawad ne ya shigo hannunshi rike da turaren gawa, tana ganinshi ta fara murmushi, idanunshi sun kumbura fuskarshi tayi jaa, alaman yaci kuka har ya koshi, da sauri ta mike taje tana cewa "meya faru?"

"yayan Abba ne ya rasu, shida matarshi"

salati ta fara, wucewa yayi ya kai turaren, saida aka shirya komai akayi musu salla, time da za'a fita da gawan saida Laila ta kuma suma, tana tausayin kanta domin itace me lalura a cikinsu, Noor ce ta riketa da Jahad wacce take aikin kuka tun ɗazu, 

gidan yayi shiru kowa yana alhini, bayan an kaisu makwancinsu suka dawo gida, Kabir dayake da neman tsokana gaba ɗaya yayi shiru yana tunani shima, Abba yana lura dasu, aranshi yasa saiya basu farin ciki fiyeda ƴaƴan cikinshi.


haka har akayi kwana uku, nan mutane suka watse, ya rage daga su sai su, Kabir kwance a cinyar Ammi yana kallon slin, kwana biyar kenan rabonshi da zuwa school, sallama akayi yanajin muryan ya ɗago, dariya yayi wanda rabonshi dayi tun su Momy na raye, ganin abokanshi ba karamin farin ciki yaji ba, da gudu ya rungumesu yana cewa "ina kuka shiga?"

cikin kuka sukace "muna kauye munje gaisuwa sai bayan mun dawo mukejin wannan mummunan labarin"

"ku daina kuka ai komai ya wuce"

zama sukayi yana jansu da hira, Man yana tsaye a kan up yana kallonsu, yanajin soyayyar Kabir yana shiga ranshi sosai, drinks aka kawo musu a babban plate, sunki Sha domin mutuwan ya basu tsoro.


Hamida na kitchen tana haɗa abinci kamar yadda Jahad ta sanar mata cewar Man ne tayi girki, batajin daɗi amma ta daure tanayi dan tasan itaɗin ƴar aikinsu ce, saida ta haɗa komai dama tana cikin wani riga dogo me yankakken hannu pink ne, sai wani hula wanda ya rufe gashin kanta, ta rame kaɗan sai ta kara zama fara sosai, pink lips ɗinta ya kuma zama pink sosai, goshinta ta cire bandage ɗin sai ciwo da ya rage wanda yake shan iska, babban plate ɗin ta rike tana shirin kai abincin dining, Ido huɗu sukayi da Kabir, baya-baya tayi kamar zata faɗi da plate ɗin tana zare ido, shima abin ya bashi mamaki, meya kawota gidannan? kodai itace sabuwar ƴar aikin tasu? wani shu'umin murmushi ya sakar mata, abokanshi sunayi mishi kallon meya kawota? a hankali ya mike yana karasowa wurinta baya ta fara yana binta, saida ta haɗu da jikin bango kafin yayi dariya yace "princess kece sabuwar me aikin? kinbar wancan gidanne kuma? kodai matar ce ta kamaki da mijinta? anyway welcome to our main house"

tafi yayi, ta ɗan firgita da sauri ta kama hanya zata wuce ya riko gefen hannun riganta, janyota yayi kamar plate ɗin zai faɗi tace "hannun na" karfi ya kara saida ta faɗi, komai ya zube kasa, sakinta yayi ya koma ya zauna akan kujera, Man dayake saukowa akan stair yayi shirin cikin kananan kaya ya hango tana tattare abinci, cikin masifa ya karaso ya ɗagota da karfi, "ke wace irin dabbace da zaki zubar da abinci?"

jikinta ne ya fara ɓari, bakinta har yana rawa "ba..ba"

tsaki yaja dan baison ko kallon fuskar yarinyar, cikin masifa ya juya baya "idan ina gida ki rinka ɓoyemin wannan fuskar taki banson gani"

fita yayi daga gidan yana jan tsaki, murmushi Kabir ya saki, yanajin daɗin yadda man ma ya tsani yarinyar, tashi yayi yabar palour yana waka, abokanshi sun tafi da niyan gobe su dawo, tana kuka tana kwashe abincin, Ahmar ne ya shigo, ya rame sosai yayi haske, riga armless da wandon shadda ne a jikinshi dama yunwa ne ya fito dashi, a hankali yace "meya faru?"

ɗago kai tayi, ganin Ahmar yasa tayi dariya idonta yana hawaye tace "Yah Ahmar?"

murmushi yayi domin ya ganeta, da gudu taje ta faɗa jikinshi, shiru yayi yana mamakin meyasa tayi hakan? saida tayi kuka kafin ya zameta yana murmushi yace "why crying?"

hannu yasa ya share mata hawayen tace "mamanka sun rasu?"


jijjiga mata kai yayi yana cewa "yeah"

"Allah yaji kansu da rahama"

"Ameen madan tsoro, me kikeyi anan?"


a hankali tace "nice sabuwar ƴar aikinsu"

tausayi yaji ta bashi, bai tsaya bincikenta ba yace "okay, muje ki bani abinci yunwa nakeji" a ranshi yaji zafin wannan kyakkyawar wai ƴar aiki?

zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun dining, dama abinci ya rage ta ɗibo ta zuba mishi, saida ya fara ci, ta zauna gabanshi tana kallonshi, ɗago kai yayi ya kashe mata ido ɗaya "ya dai hajiya?"

dariya kawai tayi, Shaira ce ta fito daga room nata tana yamutsa fuska, ganin Hamida zaune da Yah Ahmar da sauri ta karasa, saida ta takata ta yadda bazai gani ba, "washh"

Hamida ta faɗa cikin jin zafi, a hankali ta juya tace "sorry"

shiru Hamida tayi, batasan meyasa suka tsaneta ba.*08144818849*

No comments

Powered by Blogger.