Doctor Mansoor 11

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


    Na

_Jiddah S Mapi_


*Chapter 11*


                 ~Tun da Kabir ya watsa mata itching powder har yau bata kara zuwa school ba, domin zazzaɓi take sosai, kwance take akan sofa tana ɓarin jiki, hakoranta

suna haɗuwa da juna tsabar zafin ciwo ga wani sanyi da takeji, Jalal na zaune a gefe yayi tagumi yana kallonta cikin tausayi, a hankali ta mike ta fara sheka amai, hakan shine yasa jikinta yayi lakwas domin karfinta ya kare, wando ne a jikinta daidai gwiwa da riga baƙi me karamin hannu, saida ta gama aman Momy ta kwashe ta kimtsa wurin, kwanciya ta kuma yi jikinta yana ɓari, maganin ya mika mata yace "gashi ki daure kisha"

girgiza kai tayi, cikin muryan kuka tace "banso amai yake sani ya Jalal"

ajiyewa yayi a gefe ya rasa meyasa bata son magani, gashi Momy ta hana a kira doctor tace zazzaɓi ne kawai, kuma gani yake babu sauki a lamarin ta, a hankali ya matso wurinta yana taɓa goshinta, ji yayi zafi yayi yawa sosai, da sauri ya cire hannu ya mike, ruwan sanyi da karamin towel ya ɗauko ya fara matsewa yana shafa mata a goshi, numfashi ta fara saukewa a hankali saida yaji ta ɗan samu lafiya da rashin zafin jiki kafin ya tashi gashin kanta wanda suka barbaje akan pillow ya tattare wuri ɗaya ya ɗau ribbon mara nauyi ya kame gashin da ita, lumshe ido ta fara a hankali bacci ya fara ɗaukanta, yana kallon kyakkyawar fuskarta har tayi bacci, zuba mata idanu yayi sosai kamar wanda yayi ajiya a fuskarta, kyakkyawa ce ajin karshe batada makusa ko kaɗan a tare da ita, matsalarta shine wannan damuwar da take ciki, koda yaushe kana ganinta kasan tana cikin damuwa, bayan wannan batada wani matsala, jinta yake kamar kanwarshi jini ɗaya, koda yaushe yaga fuskarta tunawa yake da kanwarshi, idanunshi ne suka cika da hawaye da sauri yayi ta maza ya maida, ganin tana zufa yasa hannu yana share mata, saida ta sauke ajiyan zuciya cikin bacci kafin ya tashi yabar wurin, Dady dake tsaye a jikin kofa ya koma baya bayan ya gama ganin duk abinda ya faru, girgiza kai yayi bayan yayi wani tunani a cikin ranshi.


              "Shaƙuwa sosai ya shiga tsakanin Man da Jahad, yarinyar akwai nutsuwa da kamun kai hakan yasa yake sonta sosai, duk time ɗin da zaije hospital saiya leka ya ganta, idan bai ganta ba tayi mishi wannan murmushin nata ba, baya samun nutsuwa ko kaɗan, koda yaje wurin aiki innocent face ɗinta yake gani.


Unty Jahad jikinki da zafi ko na kora Ammi? a hankali ta girgiza kai tana kallon Noor wacce take kula da ita sosai da taji batada lafiya zata fara cewa ko ta kira Ammi, mikewa tayi daga kwancen da take, riga pink mai yankakken hannu ne a jikinta, wandon jikinta ya wuce gwiwa amma bai kai har kasa ba, kanta tayi kitso guda shida manya wanda suka cika kan sosai kuma da alama wacce tayi kitson ta iya sosai, fuskarnan tayi fayau sosai, da alama tana ɗan jin zazzaɓi sosai, hannun Noor ta kamo tana kakalo murmushi tace "kinsan banson allura shiyasa banaso ki faɗawa kowa, haka kawai nakejin jikina yana ciwo, ga kuma gabana yana faɗuwa sosai"

"unty Jahad gara na faɗawa ya Man zai baki magani...."


"me za'a faɗa min?"

ya faɗa yana karasa shigowa, yasha riga da wando na shadda baki, wanda ya fito da kyau da hasken da Allah ya bashi, kwarjini sosai yake dashi, idanunshi a lumshe kamar kullum, jajayen lips nashi yake taunar na kasa, sajen fuskarshi a kwance, da alama fita zaiyi, Noor ce ta sauko daga bed ɗin ta durkusa kasa tareda cewa "good evening yah Man"

jijjiga kai yayi, fuskar babu annuri kamar ba shine yayi tambaya yanzu ba, Jahad dake kan gado a hankali ta fara janyo hijabin dake gefenta, kallo ɗaya yayi mata cikin rashin fara'a yayi magana "meke damunki?"

a hankali tace "ba komai"

harara ya ɓalla mata wanda yasa taji cikinta ya ɗuri ruwa da sauri tace "kaina da cikina ke ɗan ciwo"

hannu yasa a aljihu ya ciro allura, da sauri ta zaro ido tana kallon Noor wacce take sa hannu a baki tana dariya, kallon noor yayi a hankali ta mike sum.sum ta fita, saida yaja ruwan alluran kafin ya matso yace "tashi"

yarfa hannu tayi cikin tsoro tace "dan Allah yah Man a hankali"

bai wani yi magana ba sai kallon cikin idonta da yayi, wanda yake cike da tsoro, tunda safe yake kula da ita kamar batada lafiya kuma yaji conversation nasu da noor hakan yasa yaje ya ɗauko allura, a hankali ta ɗan mike tana zuge zip ɗin wandon dake jikinta, ɗauke kanshi yayi yana kallon gefe domin wannan yarinyar Allah yayi mata kira ba kaɗan ba, daga sama batada wani kiɓa amma ta hips nata kamar wacce tayi surgery, marabanta da cardy B kawai fuska, tafi cardy kyau sosai ba kaɗan ba, jin yayi shiru tace "kayi min"

juyowa yayi yana kallon yadda ta taƙure tana runtse ido, a hankali ya matso kusa da ita zaisa tayi wani ihu tana rike hannunshi, barinta yayi yana ganin ikon Allah, "kayi hakuri tsoro nake ji"

bai jira ta kuma magana ba ya juyo da ita da karfi, rungumeta yayi sannan yayi kasa da wandon alluran ya ciro yayi mata, ihu tayi tana bashi hakuri ya cire saida ya gama kafin ya saketa, kin barin jikinshi tayi sai kuka harda hawaye, duba time yayi ta hanyar agagon dake hannunshi yaga time ya wuce, zaunar da ita yayi a gefen gado ya janyo pillow ya jingina mata, lumshe ido tayi tana kallonshi yadda yake yin komai a nutse shi yafi birgeta, magani ya mika mata "kisha zuwa anjima idan alluran ya sakeki"

girgiza kai tayi "nagode"

fita yayi yana jin tausayinta a ranshi, badan kiran gaggawa ake mishi ba da babu abinda zai hanashi zama a gida yayi jinyanta, Jawad ya fito daga ɗakinshi yana bin waka wanda takeji ta cikin headphone ɗin dake sanye a kunnenshi, ya sanya riga da wando ruwan ɗorawa kanshi ya taje yayi kyau sosai kamanninsu ya fito da Man, ganin Man ya fito daga ɗakin Jahad abin ya kuma ɗaure mishi kai, dukar da kai yayi zai wuce "Jawad zo nan"

cire headphone ɗin yayi kafin ya ɗan russuna yace "gani"

"ina kake zuwa kwana biyu naga kana jera fita?"


"library nake zuwa ina karatu nida freinds ɗina da Kabir"


"ka tabbata?"

"eh yaya"


"Abba ya sani?"


"ya sani shine ma ya siya mana wasu takaddun"


"okay tashi kaje"

tashi yayi ya tafi, ɗakin Abba yaje yayi koncking, "come in"

tura kofar yayi yashiga bakinshi ɗauke da sallama, Abba zaune akan sallaya yana addu'a, zama yayi a gefenshi yana karɓan addu'an shima, saida ta gama ya kalleshi "Babana ya dai?"

cikin girmamawa yace "ina wuni Abba"

"lafiya kalau"

"ina zakaje naga kayi shiri?"

"ana nemana a hospital ne yanzu"


"to ubangiji Allah ya baka lada, kuskuren da kake Allah ya yafe maka, ina bada kykyyawar shaida a kanka kana bawa al'umma gudumawa, ka ganni nan? mutane suna ganina ibada faɗa, ba faɗa bane gyara nakeyi, ina kokarin na gyara komai ya dawo kan hanya ne, ka rike Allah a koda yaushe ba zaka taɓa faɗuwa ba kaji?"

jijjiga kai yayi yayinda yake murza yatsun hannunshi, akan kafafunshi yake zaune, mikewa Abba yayi yace "zo" buɗe hannunshi yayi da sauri Man ya faɗa jikinshi ya ƙankameshi, "na gode Abba"

saida yaji bugun zuciyarshi ya daina kafin ya saki Abba yace "na tafi"

"Allah ya kiyaye hanya"

fita yayi baije ɗakin Ammi ba dan yasan sallah take, idan ta hau sallaya bata sauka, mota baki kiran benz ya shiga, da kanshi yake driving har ya iso hospital nashi, bai tsaya ko ina ba sai office nashi, zama yayi akan desk ya ciro kwalban giya a cikin drower, kallon jikin kwalban yayi yanajin kamar kar yasha a ranshi, saide abinda take faruwa dashi ya zama dole kafin ya zibda ciki yasha giya, idan ba haka ba rayuwarshi zata galabaita, buɗe marfin yayi, sa kwalban yayi a bakinshi ya shanye tass, wani katon kwalba ya kuma ɗauka ya shanye duka, idanunshi ne suka koma jawur, lips nashi yayi jaa sosai, tashi tayi yana tafiya cikin layi ya ɗau wayar Office yayi dialing number ɗin Dr kamal, ɗauka yayi "ta shigo"

ajiye wayar yayi bayan ya zauna a kujeranshi ya kwantar da kai akan desk ɗin yanajin amai na yunkuro mishi, turo kofar akayi yarinyar da wando da riga a jikinta, wani irin tsaki yayi yana ɗauke kai, irin waɗannan ƴammatan baya tausaya musu ko kaɗan, kalli wani irin shiga da tayi, zama tayi a kujera tace "sunana Nancy"

baiyi magana ba ya mika mata takadda, ɗauka tayi ta karanta, ya ciro biro ya bata, sa hannu tayi tana kuka ta bashi, kallonta yayi sosai da alama christian ce, magani ya bata, daga nan ya cire cikin dake jikinta, saida aka bata gado domin ta kusa mutuwa, barinta yayi a hospital ɗin ya shiga motarshi cikin maye ya fara shirin tuki, da sauri Kamal yazo ya rike matukin yana kallonshi, komawa yayi mazaunin driver shi kuma Man ya zauna a gefe yana shirin bacci, driving ya fara yana cewa "Man kada ka lalata rayuwar ka, ina faɗa maka ka daina wannan aikin zaiyi maka illa"


cikin muryan maye yace "bakada tausayi ne Kamal? baka jin dalilin cikin nasu shiyasa"


"idan ka biye ta dalili ba zaka taɓa dainawa ba, ka daina biye wani dalili kowa da kaddararsa, yanzu kaga idan bakasha giya ba baka iyawa, kuma hakan bazaisa ka bari ba, gashi ba wani kuɗi kake karɓa a wurinsu ba, bafa a gyara ɓarna da ɓarna"


juyowa yayi ya kalleshi yama daɗe da yin bacci, girgiza kai kawai yayi yana tunanin yadda zai shigar dashi cikin gidansu a haka, bubbugashi yayi yana cewa "ka tashi mun kusa gidanku"

idanunshi da sukayi jawur ya buɗe yana kallon hanya, saida suka isa kofar gidansu kafin Kamal ya bashi tukin yace "kodai zamu koma gidanmu ne idan ka warware gobe ka dawo kasan fa halin Abba"

girgiza kai yayi yana shirin tuki yace "ba komai zan iya control ɗin kaina"

horn yayi mai gadi ya buɗe, a hankali yake driving har ya isa wurin Parking, ba tare da yayi parking me kyau ba ya fito, tafiya ya fara yana addu'a kada Allah ya haɗashi da Abba, babban palour dake kasa ya wuce ganin ba kowa yayi hamdala, zai haura sama yaji an janyoshi, baki ya buɗe zaiyi magana ta toshe mishi baki tana nuna mishi Abba wanda yake wucewa hannunshi rike da cup na coffee, shiru yayi saida ya wuce yaji karan rufe kofa kafin ta cire hannunta tana tureshi daga jikinta

"thanks"

da sauri ta juya jin muryan da yayi magana da ita, kamar wanda yasha abu?

ganin ya fara tafiya ta zuba mishi ido yana layi, "Innalillahi me Man yasha? kodai bacci yakeji?"

saida taga kamar zai faɗi taje da gudu ta rikeshi, ba zato taji yasa hannunshi akan waist ɗinta ya kwantar da kanshi kan kafaɗarta bacci yayi a tsaye, janshi ta fara suna haura stair da kyar, Ammi wacce tayi shiri cikin rigan bacci, ɗakin Abba zataje ta gansu, gabanta ne ya faɗi "meya sameshi?"

jikin Jahad ya fara rawa cikin in-ina tace "ya faɗi ne kafarshi taji ciwo"

"aina haka?"

tayi magana tana karasowa, da sauri Jahad ta fara janshi dan bataso mahaifiyarshi taga halinda yake ciki, zataji zafin hakan "Ammi kije kawai zan kaishi ɗaki inaga buguwa yayi dan babu jini"


"to ba damuwa ki kaishi sai kije ki kwanta ko mamana"


"to Ammi"

saida ta haura dashi da kyar har tana nishi kafin ta buɗe ɗakin ta jashi har zuwa kan gado, jefashi tayi domin hannunta ya gaji sosai, blanket ta rufashi dashi, takalmin kafarshi ta cire ta ajiye a gefe ta rage wutan ɗakin kafin ta juya ta fita, zuciyarta cike da tambayoyi, zai shiga ɗakin yayanshi kenan yayi mishi bayanin aikan da yah Ahmar yayi mishi, karo sukaci da Jahad wacce take tafiya tana tunani, baya yayi yana kallonta ganin zai shiga ɗakin ta riko hannunshi da sauri ta rufe kofar dan bataso yasan halinda Man yake ciki, saida ta kaishi gefe tace "yana bacci ne"

kallon kin rainamin hankali yayi, sai yau ya tabbatar da abinda yake zargi, sakin hannunshi tayi "ina kaje?"

bai amsata ba ya juya yabar wurin, dafe kirji tayi tana sauke ajiyan zuciya, rolling eyes ɗin ta tayi tabar wurin, ɗakinta ta shiga ta kwanta lub akan Bed tana tunani har bacci ya ɗauke ta.


"Abbansu gaskiya wannan Jahad ɗin tana da hankali zata kula da Man idan sunyi aure, gata da son addini da tarbiyya"


"nima dai haka nake gani amma sai sunyi magana da juna, kada musa su abinda basa so kinsan fa halin yaran zamani"

Abba tayi magana yana karatu, idanunshi sanye da farin glass, Ammi na gefe tana cin ayaba da kankana cikin wani ɗan karamin bowl, suna ganin nutsuwan Jahad ta dace ta zamo sirikarsu

"amma abinda ban gane ba Abbansu shine asalinta ya kamata musan asalinta"


"sanin asalinta ba shine abu na farko ba, su fahimci juna shine farko, idan yaso sai komai ya biyo baya"

shiru tayi dan tasan baison musu.


             "Jalal ganin jikinta babu sauki ya sata shiri ba tareda Momy ta sani ba domin karatu yana wuce ta sosai a school, gashi sai kwanciya take jiki babu karfi, shiri tayi cikin riga da siket na material baki da fari, ko mai bata shafa a jikinta ba ta ɗau bakin hijab guntu tasa, jaka ƴar karama ta rataya a gefe kafin ta fito, yana tsaye a bakin kofa yana jiranta, ganin ta fito haka ya kalleta, murmushi yayi ya riko hannunta suka koma ciki, akan stool wanda yake gaban makeken madubin dake cikin ɗakin ya ajiyeta, hannu yasa ya cire hijabin dake jikinta, kallon kanta yayi wanda uban gashin ya harharɗe ya cunkushe, mataji ya ɗauka ya fara taje mata, tana ganinshi ta cikin madubi, bakin man gashi ya ɗauka ya shafa mata, kara tajewa yayi saida kan yayi laushi ya dawo yadda yake kafin ya kitse mata gida biyu irin na fulani, powder ya ɗauka ya shafa mata, sannan lipbalm da kwalli, lotion ya matsa ya shafa mata a hannu da kafa zuwa bayanta kafin ya maida mata hijabin, turarenta me kamshi ya feshi jikinta dashi sannan ya koma bayanta yana kallon yadda take kallon kanta ta cikin madubi, kana ganinta kasan batada lafiya dauriya ne kawai, wasu hawaye taji suna shirin zubo mata, rabonta da kwalliya tun Amrah nada rai, gashi yanzu tayi kyau sosai, murmushi tayi mishi, rungumeta yayi ta baya "kinada kyau ko ba kwalliya amma kwalliya yana maidaki kamar sarauniya"

lumshe ido tayi ta kuma buɗewa "nagode Yah Jalal"

hannunta ya riko bayan ya rataya mata jakan yace "muje ko?"

tashi tayi suka fita cikin sanɗa ba tareda kowa ya gansu ba, motarshi dama a waje ya barta, saida ta zauna kafin ya shiga suka fara tafiya, da sun haɗa ido sai yayi murmushi itama haka, bai tsaya ko ina ba sai kofan wani asibiti "Sauki clinic"

hannunta ya riko suka shiga ciki, babu ɓata lokaci ya biya kuɗin ganin likita suka shiga, zama sukayi suna fuskantar likita sukayi mishi bayani, jini ya ɗiba suka gwada dasu fitsari, saida suka jima kafin aka kawo result, hannu ya mikawa Jalal cikin murmushi da taya murna yace "congratulations madam nada juna biyu, she's pregnant"

a zabure Hamida ta miƙe tana kallon doctor da kwala-kwalan idanunta jikinta yana ɓari tace "ka kira wanda sukayi gwajin su kara dubawa da kyau ko sun canja result"

kallo yayi da kyau yace "basa canja result Hamida Umar arɗo?"

kwarai nice amma ta yaya nayi ciki?"


kallon tuhuma ta yiwa Jalal wanda yake cike da mamaki yama kasa tashi don tashin hankalin daya shiga, Hamida ciki?

kwalan riganshi ta rike da karfi tana jijjigashi tace "waya min ciki?"

kokarin cire hannunta yake yana cewa "kece zan yiwa wannan tambayar"

da ihu tace "ka faɗamin waye yamin ciki?"

"ina zan sani Hamida?"


likita ya mike yazo yana janye Jalal, a zatonshi murna zasuyi sai kuma gashi suna faɗa? kenan ba ma'aurata bane?"


taki sakinshi domin ba rikon wasa ta yiwa riganshi ba, saida aka yage rigan kafin ta sakeshi, jikinta yana ɓari tace "wallahi tallahi doctor ban taɓa zina ba, ban taɓa sanin wani ɗa namiji ba, kuma zan iya rantsuwa da Alqur'ani, ka taimaka ka gwada cikin ka duba waye yamin"


ganin ta fita daga hayyacinta Jalal ya rikota ya zaunar da ita, "ya Jalal nida nake yaki da cikin haram taya zanyi hakan? me nayiwa Allah yake min wannan hukuncin? me nayi?"

janyota yake shirin yi jikinshi da sauri tayi baya "kada ka taɓani"

shima abin ya ɗaure mishi kai sosai, wa zai tambaya? yasan baza tayi hakan ba.


"Ku nutsu zanyi muku bayani"

cewar doctor wanda ya rasa abinyi shima, bata nutsu ba kawai de tana jinshi, takadda ya ɗauka yace "akwai wasu hanyoyin samun ciki koda bata hanyar saduwa ba, ke kinyi rantsuwa baki taɓa zina ba, hakan zai iya faruwa amma kiyi tunani babu ranan da kika taɓa fita wani ya baki abin sha kikayi bacci? Kuma bayan kin tashi kikaji jikinki ya sauya? domin duk wacce bata taɓa saduwa da miji ba dole sai taji zafi sosai a duk lokacin da hakan ya faru, shin kin taɓajin zafi a kasanki a wasu lokuta? domin cikin sati uku ne"

girgiza kai tayi tana kuka "ko ɗaya ban taɓajin sauyi a jikina ba"


"okay to hanya ta biyu shine an ɗau cikin daga jikin wata aka samiki, ko itaɗin akwai matsala ko tana tsoron haihuwa, ko tanason zibar da cikin yaki zubewa sai akayi amfani dake aka juye cikin a jikinki, kuma akwai kwararren likita wanda nasan shi kaɗai ne zai iya yin hakan?"


wayarshi ce tayi kara da sauri ya ciro daga alhjihu ya ɗaga ya kara a kunne, ji sukayi ya fara salati, mikewa yayi ya ɗauki makullin mota ya fita da gudu, babu abinda yake faɗa sai "Mama?...Mama...gani nan zuwa"

a hankali ta fara silalewa kasa saida ta durkusa akan gwiwoyinta kafin tace "me nayi? me nayi nake samun wannan hukuncin? meyasa sai nice hakan yake faruwa a kaina? meyasa hakan?"


hannu yasa zai riketa da sauri ta bige shi  ta mike a guje ta bar office ɗin, binta yake yana kiran sunanta, ko juyawa batayi ba sai gudu take kamar ranta zai fita, ganin ta fita daga hospital ya shiga mota yana binta a baya, mutane sai kallonsu suke, tayi nisa so take tayi nesa, koda kafa zata iya barin garin a yadda take ji yau, tana gudu yana binta kiran sunanta yake yana bubbuga jikin motar da ɗayan hannunshi, saida tayi kwana ya daina ganinta kafin ta rage kafa, jin karar mota ta kuma ɗaga dogayen kafafunta farare tana kara kaimin gudu, Jalal makalewa yayi a lungu hakan yasa ya gagara fitowa, daidai bakin titi taci karo da wani mota wanda yayi sanadiyar sumanta bata kara sanin inda take ba.

No comments

Powered by Blogger.