Doctor Mansoor 10

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


    Na

_Jiddah S Mapi_


*Chapter 10*


                 ~Shiga class tayi tana tuno irin marin da tayi mishi, Allah kaɗai yasan hukuncin da zai ɗauka akanta, Kabir yaki fita a harkanta shiyasa bata daga mishi kafa

yanzu, har aka gama lecture batasan me take ciki ba, saida aka tashi ta ganshi tsaye yana kallonta yana murmushi, abin ya bata tsoro amma ta dake ta kyaleshi tayi wucewarta, bakin get inda mutane suke taruwa taji jikinta yana kaikayi, fara kaikayawa tayi tana jin wani raɗaɗi yana taso mata, cire hijabin tayi tana tsalle tana kaikaya jikinta, rigan jikinta tayi kamar abin yana ciki da karfi ta fara kokarin ɓalle maɓallin jikin rigan, mutane sai gudu suke sun zata wani abin ne, babu abinda take sai hawaye tana dirza jikinta da kasa, wurinta ya karaso ya ɗagata da sauri ta kalleshi bakinta yana rawa idanunta sunyi kalan tausayi cikin sanyin murya da ciwo tace "jikina kaikayi"

Ahmar wani irin tausayi yarinyar ta bashi, watakila tanada matsala ne a jikinta shiyasa kullum yake tashi a cikin mutane, janyeta yayi zuwa gefe inda babu kowa, hijabin ya sa mata, da sauri tace "bayana kaikayi"

a hankali yasa hannunshi izuwa bayanta ya fara kaikayawa, shiru tayi hawaye yana bin fuskarta, saida taji yaɗan ragu kafin ta juya batason haɗa ido dashi tace "nagode" 

tafiya tayi tabar wurin tana kuka kamar ranta zai fita, yana zaune a cikin mota jiranta kawai yake, ganin tana share hawsye kafin ta iso yasa yaji gabanshi ya faɗi, meya sameta? murmushin yaƙe tayi ta buɗe motar tana kallonshi, "ya Jalal kayita jirana ko?"

"meya sameki?"


"kaina ke ciwo"

jan motar yayi suka fara tafiya ba tareda ya yadda da abinda tace ba, saida suka hau kan hanya kafin yace "faɗamin gaskiya meya sameki?"


"kaina ke ciwo ya jalal"

shiru kawai yayi, tsayawa yayi a gefen hanya ya fito ya siyo mata chocolate da biscuit da yawa, ajiye mata yayi tana gani ta ɗauke kai, da mamaki yace "ya dai?"

"ya Jalal bana kwadayin wannan nafison abu me tsami"

kallon mamaki yayi mata kafin ya buɗe ledan chocolate ya fara ci, yana kallo tana dauke kai kamar ƙamshin ne bata so, girgiza kai kawai yayi, saida suka iso mai saida lemo ya tsaya ya siya mata, karɓa tayi ta fara sha tun a hanya, suna isa gida ta ciro ledan lemon ta nufi cikin gida, bata tsaya ko ina ba sai ɗakinta, toilet ta shiga tayi wanka tana tuna abinda ya faru da ita, babu shakka Kabir ne yasa mata itchen powder, tayi niyyan yimishi abinda bazai taɓa mantawa ba, saide yaci albarkacin yayanshi wanda yake taimaka mata a kullum, fitowa tayi kirjinta ɗaure da towel, a gaban mirror ta tsaya tana kallon yadda jikinta yayi jaa duk inda ta kaikaya saida ya nuna shati, koncking ya kumayi jin bata buɗe ba kuma bata amsa ba ya turo kofar, jikinshi sanye da wando wanda ya tsaya a gwiwarshi, da sauri ya juya baya ganinta a haka, itama hijabi ta janyo ta rufa jikinta dashi, saida ta zauna a bakin bed tace "na gama"

a hankali ya juyo yana murmushi yace "na kawo miki magani ne"

da sauri ta kalleshi "maganin me?"

karasowa yayi ya zauna a gabanta, hannunta ya rike daidai inda yaga shatin kaikayi ya ciro wani tube daga aljihun wando ya fara shafa mata, kallonshi take yadda yake shafawa yana hura mata iska a wurin, ɗaga hijabinta yayi a hankali ya shafa a hannunshi ya fara shafa mata a baya, lumshe ido tayi saida taga zai sakko cikinta ta rike hannunshi, girgiza kai tayi "zan shafa ya Jalal"

"baki yadda dani bane? ko baki yadda ni ɗin yayanki bane?"

da sauri ta girgiza kai,  ganin zai ci gaba tayi sauri ta mike tana dariya tace "kunya nakeji"

sakinta yayi yace "okay ki shafa duk jikinki zai rage miki zafin"

godiya tayi, saida ya fita ta zauna a bakin gado tana tunani, meyasa yake bata kulawa haka? ta dangana hakan da tausayinta yake, dashi da iyayenshi tunawa tayi da adda Amrah da kuma Baba, wani abinda yake sata kuka sosai shine idan ta tuna Umma, batasan wani hali take ciki a gidan wannan mugun ba, Samha kanwarta itace tayi mata sharri, share hawayen da suka wanke mata fuska tayi "insha Allah zan nemo wanda yayi wannan aikin na tabbata mutum ɗayane ya kashemin yaya da kanwa ta hanya ɗaya, kuma duk ranan daya shiga hannuna sai nayi mishi abinda bazai taɓa ɗauka ba, saina lalata mishi rayuwa"

kanta ta ɗaura a katifar ta fara kuka me taɓa zuciya, a hankali takesa hannu tana toshe bakinta dan bataso kowa ya jiyota, a hankali ya fara tafiya jikinshi yayi sanyi, baison ganinta tana kuka, tausayi take bashi sosai, a window ya tsaya yana kallon yadda take toshe baki tana wani ɗan marayan kuka, koma menene ba karamin abu yake damunta ba, tafiya yayi daga wurin jikinshi a sanyaye, haka Jalal yake Allah ya bashi zuciyar tausayi, tausayin Hamida kesa yake bata kulawa na musamman kamar kanwarshi wacce suka fito ciki ɗaya, tafiya yake yana tunani har sukaci karo da Dady, da sauri ya koma baya yace "sannu Dady"

jijjiga kai Dady yayi kafin ya kalleshi da kyau yana nazarin yanayinshi "lafiya kam?"

"eh Dady"


"to kada kasa damuwa a ranka kuma ka daina tuna baya, domin babu abinda zai haifar maka sai damuwa"

hawaye ne ya cika mishi ido da sauri ya juya yana sharewa, rungumar Dady yayi yanajin kuka sosai, a hankali yace "Dady bazan iya manta baya ba, bazan iya ba, am helpless.."

bayanshi Dady yake shafawa saida ya tsaya da kukan yana sauke ajiyan zuciya kafin ya zameshi, gyara farin glass ɗin dake kwance a fuskarshi yayi kafin yace "kaifa jarumi ne, Jalal ɗina baida ragonta da saurin kuka, jalal ɗina spiderman ne ko?..."

jijjiga kai yayi yana murmushi jin Dady yace spiderman, ya tuna yarantarshi shida kanwarshi wacce take cemishi yaya spider, shikuma yake jin kanshi kamar wani zaki, share hawaye ya kumayi kafin ya rungume dady da karfi yace "Allah ya jikanta da rahma"

"Ameen my son"

sakinshi yayi ya juya zai tafi "ina Hamida?"

"tana ɗakinta"

ya faɗa kafin ya wuce part ɗinshi.


   

               "Mutanen gidan gaba ɗaya sunyi bacci, bakajin komai sai karan ac da kowa yana room ɗinshi yana bacci, kwance take akan maƙeƙen bed ɗin da aka shimfiɗa mata a cikin ɗakinta, bacci take sosai jikinta sanye da rigan bacci irin silk ɗin nan riga da wando white color, gashin kanta wanda yake da tsayi ta kame da ribbon tasa hulan bacci irin me net, juyi ta fara akan bed ɗin kamar zata faɗi, da sauri ta buɗe ido tana salati, kunna wutan ɗakin tayi a hankali ta mike tana kallon kan frij, ganin babu goran ruwa kamar yadda ta saba yasa ta karasa ta buɗe, babu ruwa, lanƙwasa kai tayi a hankali ta turo baki, yau ta manta ajiye ruwa kuma ruwan frij nata ya kare, tayi sabo da shan ruwan dare, murɗa handle ɗin ɗakin tayi a hankali take tafiya, kallon ɗakin Noor tayi, ganin a buɗe ta shiga, ganin ta kwanta tana bacci akan takaddu ga fuskarta da glass alaman bacci ya ɗauketa ba shiri, Jawad tayi murmushi ta karasa kan bed ɗin ta cire glass ɗin ta gyara mata kwanciyar, kwashe takaddun tayi, blanket ta rufata dashi, a hankali tayi mata peck a goshi, kashe wutan ɗakin tayi ta kunna mata dim light, a hankali ta juya ta fita daga ɗakin, tareda ja mata kofar ta rufe, palourn kasa ta nufa domin ɗauko ruwa, babban frij ta buɗe ta ciro goran ruwa uku ta buɗe ɗaya tasha, sauran ta rike ta nufi hanyan komawa ɗakinta, kamar daga nesa take jin numfashi me karfi, bataso tana shishigi gashi yanzu karfe 2 na dare, sharewa tayi zata wuce sai kuma taji nishi yana karuwa, kamar daga ɗakin MAN take jiyowa, a hankali ta karasa kofar ɗakin, kara kennenta tayi jikin kofar ɗakin, tabbas daga ɗakinshi ne, a hankali ta murɗa handle ɗin bakinta ɗauke da sallama, baya palour amma tanajin sautin shi, ƙarasawa tayi tana addu'a a cikin ranta.


da sauri ta karasa ganin yadda yake birgima a bed ɗin yana zufa, hannunshi yake ɗagawa yana jujjuya kai, zufa ya wanke mishi fuska, gashin kanshi ya barbazu, sai numfashi yake saki da karfi, salati tayi tana riko hannunshi da yake ɗagawa yana motsa bakinshi da kyar, kunnenta ta kai saitin bakinshi a hankali taji yana cewa "ku barni, dan Allah ku kyaleni"

zama tayi akan gadon ta ɗago kanshi ta ɗaura a cinyarta, addu'a ta fara karantowa tana tofa mishi, a hankali ya fara dawowa hayyacinshi, saida taga ya daina birgima kafin ta daina karanto addu'a ta fara kiran sunanshi "yah Man?"

bai buɗe ido ba amma ya daina birgima da zufa, jikinshi taji yayi zafi sosai, sauke kanshi tayi daga cinyarta ta shiga toilet ɗin shi, ruwan sanyi da towel karami ta fito dashi, a hankali ta kuma haurawa kan gadon ta matse towel a ruwan ta fara shafa mishi a jiki, saida jikinshi yayi sanyi ya buɗe manyan idanunshi wanda suka sauya kala suka koma red yana kallonta, murmushin ta me sanyi tayi mishi tana dukar da kai, a hankali ya mike yana riko hannunta, kallon fuskarta yayi kafin ya saukar da idanunshi zuwa kayan dake jikinta, da alama bada shiri ta shigo ba, runtse ido yayi yana tuna mafarkin da yayi, wasu yara ƙanana ya gansu zaune a cikin wani inuwa me sanyi da ni'ima, wurinsu yaje yana yimusu wasa, suna ganinshi suka mike da gudu suka bar wurin, binsu ya fara yana cewa "ku tsaya me nayi muku?"

saida suka kaishi wurin wani rami kafin suka tsallaka shikuma suka jefashi ciki, irin wannan mafarkin ba karamin tada mishi hankali yake ba, wani lokacin baya iya bacci da kyar yake runtsawa, tun abin baya damunshi har ya fara tsorata, a hankali yace "Jahad? na gode"


jijjiga kai kawai tayi tana murmushi, tana jin yadda yake murza yatsun hannunta kamar zai cire su, a hankali ta janye tana shirin sauka daga gadon, da sauri ya janyo hannunta yana langwaɓar da kai kamar zaiyi kuka yace "ki kwana anan please"

waro Ido tayi, ƴar karamin bakinta ta buɗe alaman "kwana kuma?"

jijjiga kai yayi alaman eh, da sauri ta zame hannunta ba tareda tayi magana ba, sauka tayi daga bed ɗin taga shima ya sauko yana shirin binta, a hankali tace "ina zakaje yah Man?"


"binki zanyi Jahad bazan iya kwana anan ba tsoro nake"

komawa tayi ta zauna, yana bata mamaki, a yadda ta sanshi baya tsoro baya fara'a gashi da girman kan tsiya da rashin kula mutane, to amma data zauna dashi sai taga yana da sauki, kodai tausayinta yake? shiyasa yake binta a hankali?

shima zama yayi a gefenta yana jin bacci sosai amma yana tsoron runtse ido, gani yake kamar zasu kara zuwa mishi "zaki kwana?"

shiru tayi, yasan ba zata kwana ba saide ba yadda ya iya ko ɗakin Jawad ne zaije su kwana tare, kafin ya mike harta rikoshi tana lumshe ido alaman ya koma ya kwanta, kwanciya yayi ta lulluɓashi da blanket kafin ta fara karanta addu'a haɗe da rera karatun kur'ani a kunnenshi, kafin wasu lokuta har bacci yayi gaba dashi, tashi tayi ta kashe wutan ɗakin, cikin sanɗa ta fita, a hankali take jan kofar dan bataso kowa yaji kara balle su tashi, saida ta rufe ta juya cikin sanɗa kamar wata ɓarauniya ta fara tafiya zuwa ɗalinta, ido ya zuba mata yana ganin yadda take takawa bataso kowa ya jita ko kuma ya ganta, saida tazo shiga ɗaki sukayi ido huɗu dashi, gabanta ne ya faɗi ganin irin kallon da yake aiko mata, a hankali tace "Jawad"


juyawa yayi hannunshi rike da goran ruwa da alama shi yazo ɗauka, bai kara ko kallonta ba ya wuce zai shiga ɗaki, da sauri ta biyoshi so take tayi mishi bayani  har bakin kofarshi ta iso tana kiran sunanshi, buɗe kofa yayi zai shiga ɗaki da karfi ta riko riganshi ta baya, tsayawa yayi cak saide har yanzu bai juyo ba, kwace jikinshi yayi zai shiga ɗaki ta janyoshi da karfi, bataso ya kwana da zarginta a ranshi, baya yayi sosai zai faɗi da karfi ta rikoshi tana zare ido "Innalillahi" ta furta tareda rungumoshi tana cewa "yi hakuri"

idanun Noor ne ya sauka a kansu, dama tanajin motsi hakan yasa ta fito domin ganin meke faruwa, da sauri ta koma baya tana sa hannu a bakinta domin abinda ta gani ya razana ta, Jawad ne rungume da Unty Jawad? buɗe kofarta tayi a hankali ta shige ɗaki cike da tsoron abinda ta gani, "rigan bacci ne a jikin Jahad? banyi tsammanin haka daga gare ta ba, am 15years old but nasan abu me kyau nasan mara kyau, wannan ba abu me kyau sukeyi ba, zan faɗa wa Ammi gobe da safe" da sauri ta buge bakinta tareda cewa "no..no..no bazan faɗa ba Ammi zatace nayi karya, ya Allah ko dai na faɗawa yah Man?"

kwanciya tayi tana sake-sake a ranta.


zame jikinshi yayi tace "ruwa kaje ɗauka?"

jijjiga kai yayi kafin yace "eh ishi nake ji shiyasa"

murmushi tayi tace "okay good night"

shima murmushi kawai yayi mata ya buɗe ɗakin ya shiga, komawa ɗakinta tayi ganin bai aika mata tambayar zargi ba, kwanciya tayi tana rokon Allah ya karawa gidan zaman lafiya da kwanciyar hankali, 

Jawad yana shiga ɗaki ya fara tunani "meya kaita ɗakin yah Man da wannan lokacin? kuma kayan bacci ne a jikinta"

kanshi ya ɗaure ya rasa me zai fara tunawa, a hankali ya kwanta ya daina jin ishi sai tunani fal a ranshi har yayi bacci.


    *Washe gari*


kamar kullum haka yauma suke zaune a dining domin yin breakfast, Abba da Ammi suna kujeran dake kusa da juna, Jawad da Man suna zaune a kujera kusa da juna, kujera ɗaya ne a tsakiyarsu, Noor ta zauna tayi shiru tana tuna abinda ta gani jiya da dare, gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, Jahad ce ta fito tana sanye da hijabi guntu purple, dogon rigane a jikinta baki wanda yayi kyau sosai ya karɓi jikinta, a hankali ta karaso cikin takun nutsuwa ta durkusa kasa ta gaida Abba da Ammi, cikin fara'a da sakin fuska Ammi ta amsa saɓanin Abba da amsa da "lafiya" kawai yaci gaba da cin abincinshi, dama ba mai dariya bane shi, a hankali ta mike, Noor tana kallonta jira take taga aina zata zauna, idan a gefen Jawad ne zarginta ya tabbata, Jawad dake kallonta ta kasa yana jiran yaga ina zata zauna idan a gefen Man ne ya tabbata da abinda yake faruwa tsakaninsu, hankali ta zauna a kujeran dake tsakiyansu tana murmushin ta wanda baya rabuwa da fuskarta a koda yaushe, 

Noor ji tayi gabanta ya faɗi, da gaske ne abinda ta gani ba gizo idanuwanta ke mata ba, meyasa ya Jawad zasuyi haka?


Jawad dake kallonta yaga ta mikawa Man cokali tana murmushi, ba shakka ta tabbata abinda yake zargi, Man karɓa yayi ya fara cin abinci ba tareda tunanin komai ba, kallo ɗaya Abba ya yiwa su Noor yaga yadda suke jujjuya cokali a cikin abinci, shima Jawad haka sai juya cokali yake, wannan karamin bakin nashi me shegen cin abincin tsiya yau kam baici komai ba, da alama akwai abinda ke damunsu.


"kuci abinci"

ya faɗa ba tareda ya kara wani kalma ba suka fara cin abincin, hatta Man yana mugun tsoron Abba balle su Jawad da Noor wanda suna ganinshi kamar wuta, saida ya koshi ya yagi tissue ya goge bakinshi, mikewa yayi "Alhamdulillah"

ya faɗa kafin ya wuce room ɗinshi, wanka yayi ya shirya cikin kananan kaya riga blue da wando baƙi, yayi kyau sosai musamman daya taje gashin kanshi ya gyara, sajen fuskarshi ya kwanta lub, agogo ya ɗaura a tsintsiyar hannunshi, kafin ya ɗau riganshi na doctor yasa a saman dressing ɗin, kyau ya kara fitowa fili, turare me ƙamshi ha fesa, dama shi ma'abocin son kamshi ne, wayoyinshi da car keys ya riko a hannu, taku yake cike da isa da izza haɗe da kwarjini, kana ganinshi kaga cikakken namiji me ji da karfi da kuma samartaka, an kirashi zaije yayi theater shiyasa ya tashi daga dining da wuri, a nutse yake tafiya yana ɗan raira waka cikin harshen turanci, saida yazo palour yace "na tafi"

kallon Jahad Ammi tayi tace "tashi ki rakashi"

Jawad ne ya kalleta ganin ta mike ya zuba mata ido yana nazarin yarinyar, ya rasa gane ina ta dosa, Noor ce ta zubawa Jawad ido tana ganin yadda yake kallon Jahad, yau kanta ya kulle a gidan, abincin da takeci ji take batasan inda yake tafiya ba, da mamaki ta kalli yah Man wanda yake murmushi, idanu ta kai kan Jawad wanda yake kallonsu sosai, a ranta tace "Noor kina da positive mind".


*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849 a turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.