Daudar Gora Book 2 page 8

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (08)




........Fitowarta kenan da ga toilet da alamun wanka tayo dai-dai da shigowar Jasrah ɗakin. Malikat Bushirat ta zuba mata ƙyawawan idanunta kawai cike da mamakin ganin yanda ta ingizo ƙofar gashi ko sallama batai ba. Jasrah da gaba ɗaya idonta ke lulluɓe da tsantsar ɓacin rai ga dunƙulewa da ɗan cikinta yay waje guda ya ƙulle mata mara ta zube a kan gado yarab. Malikat Bushirat da har lokacin ke binta da kallo ta ƙaraso gareta da sassarfa tana ambaton sunanta. Bata iya ta amsa mata ba har ta ɗagota jikinta.

       “Jasrah! Are you ok?”.

    Ina Jasrah bata iya ta amsata ba saboda yanda mararta ta ƙulle tamau. Hankalin Malikat Bushirat yay ƙololuwar tashi ganin tana jan numfashi da ƙyar. Dole ta shimfiɗeta tai amfani da telephone wajen kiran clinic. Cikin ƙanƙanin lokaci doctor... ta iso, kamar an saita tana shigowa jini na ɓallema Jasrah..


       ★★


      Wannan hali da Jasrah ta tsinci kanta a ciki ya ɗauke hankalin Malikat Bushirat da ga sanin halin da ake ciki akan komawar Iffah sashen Tajwar Eshaan ɗin. Dan kamar wasa jini ya ɓalle mata har sai da cikin jikinta da sukai matuƙar ƙwallafawa rai ita da mijinta (Miran Arshaan) gaba ɗaya ya fita har itama ana neman rasata dan itama hadima Banou ɗin taso taɓata ALLAH dai ya sa tana da sauran kwana a gaba tasha da ƙyar sai dai a ranar kam a asibitin cikin masarautar ta kwana. 

      Rasa cikin nan ya matuƙar ƙona ran Miran Arshaan da ita kanta Jasrahn da sai a washe gari ta dawo hankalinta har take faɗa musu dalilin shigarta wannan hali saboda likita tace musu ɓacin ran da take ciki ne ya janyo ɓarin. Sabuwar tsanar Iffah ce ta baibayesu tare da ɗaukar alwashin a sashen Shahan-shan ɗin da su malikat Haseenat ɗin suka kaita sai sun bita sun halakar da ita. Ita kanta malikat Haseenat ɗin sun ƙullaceta matuƙa dan a ganinsu ita ce sanadin komai. (basu san ita bama tasan anai ba😏).   


      Bayan lafawar halin da Jasrah k ciki ba ƙaramin ɓacin rai Malikat Bushirat ta nuna ba akan jin an maida Iffah sashen Tajwar Eshaan bisa wai umarninsa, sai dai sam bata yarda ba acewarta Malikat Haseenat da Daneen Ammarah ne suka saka shi yin hakan. A wannan gaɓar dai kai tsaye kowa ya fahimci fushin nata gaba ɗaya ya dangana ne ga Malikat Haseenat. Dan a take ta saka a rufe mata likitocin da suke duba Iffah, acewarta sai sun faɗa mata wanda ya sakasu yin shirin. Iya gaskiyarsu sun rantse mata akan su babu ruwansu umarni kawai aka basu. abinda kuma ya samu Iffah gaskiya ne kuma bincikensu ne ya basu da iliminsu. Bata nuna alamun zata saurarensu ba ma balle yarda da abinda suke faɗa ɗin, sai ma sabon bincike data saka akan zaman Iffah kurkuku. Sai dai me hatta jami'an da Malikat Haseenat tasa suke tsaron Iffah sunƙi faɗar kowane sirri, hakan sai ya sake hargitsa mata lissafi ga kuma su Miran Arshaan na tunzurata a gefe da sake munana tsohuwa Malikat Haseenat da komai dake faruwa tana ji amma ko tari taƙiyi balle ta nuna tama san da abinda Malikat Bushirat ɗin keyi. Ta dai aika Yumma (ƙanwarta da take tare da ita) taje ta duba Jasrah a randa tai ɓari...


       ★★.....  ★.....


    A hankali ya janye idanunsa da ga kallon inda taken cike da basarwa yana amsa sallamar Doctor Afif da ya shigo ɗakin akan lips. Dr Afif ya ƙaraso cikin ɗakin yana mai rissinawa ya gaishesa, da idanu ya amsa masa kawai alamar ƴan izzar na kusa. Shima Dr Afif ɗin bai damu ba, dan a ɗan zaman jiyyar nan har ya fara haddace magana da idon nan. Gaban gadon ya ƙarasa yana sake rissinawa a cikin girmamawa ya miƙa masa file ɗin hannunsa.

        “Wannan shine file ɗin dukkanin bayanan nata da likitocin suka tattara. Sai dai suna kan sake bincike akan rashin farfaɗowar tata kan lokaci da ya kamata ace tayi tun kwanaki biyu da suka wuce”.

     File ɗin ya amsa batare da yace komai ba, ya ɗan dudduba, sai kuma ya ɗago idanunsa ya sake zubasu kan Dr Afif ɗin. Sai da yaja wasu sakanni kafin ya iya furta abinda ke bakinsa da ƙyar. “Kai mi ka fahimta akan hakan?”.

        Tsaiwa Dr Afif ya gyara yana mai sake rissinar da kansa. “ALLAH ya ƙara maka lafiya da tsohon rai mai albarka ni ina ganin ko za'a sake neman wani ƙwararren likitanne akan al'amurin nata da ya fi waɗan nan ɗin ƙwarewa. A yanda suka san aikinsu bai kamata ma ace sun gagara gano wani ƙwaƙwƙwaran abu guda ɗaya ba har zuwa yanzun, dan dole akwai abinda akai mata, dan bazai yiwu ace ta kasance a wannan halin babu ƙwaƙwƙwaran dalili ba”.

     Ɗan murmushi Tajwar Eshaan ya saki a karo na farko, batare da ya cema doctor komai akan bayaninsa ba ya ziro fararen ƙafafunsa zuwa ƙasa. Slippers ɗin dake ajiye gaban gadon ya saka, murya a dake ya furta, “Zan ganta”. Da sauri Dr Afif yay gaba yana faɗin, “Bismillah ranka ya daɗe”.  

       Gaba ɗaya suka fito a ɗakin da yake tasa jiyyar, shi yana gaba doctor na biye da shi, duk da a jikin ɗakin da yaken ne koma ace ɗakinne kawai aka raba da glass sai ya zam ƙofar shigar sai kayi kamar ɗan taku biyar zuwa shida ne. Anan ɗin ma ƙofar ta gilashi ce, doctor ya buɗe masa yana ɗan ja baya. Sai da ya fara shiga. Tsaye yay a bakin gadon batare da ya zauna a kujerar da Doctor ya gyara masa ba. Sai da ya fara kai dubansa kan na'urorin dake aiki a jikin nata, gadai bugun zuciyarta normal na'urar ta nuna, sai dai nunfashinta baya tare da ita a zahirance. Ɗauke idanun yay da ga na'urorin ya maida a kanta. Lumsassun idanunsa ya tsura mata. Har yanzu tana kwance a yanda yake hangota daga ɗakin jiyyarsa tun ɗazun, tayi wani irin fayau da ita ga uban haske data ƙara. Ƙoƙarin saita yanayinsa da ke neman fallasa kan fuskarsa yayi, batare da yace komai ba cike da basarwa yay wani irin shegen murmushin takaici mai nunin ma'anoni daban-daban da ya saka Doctor Afif yin suman tsaye dan mamaki. Shi baima san Dr Afif ɗin nayi ba, sai ma idanunsan da ya ɗan lumshe yana haɗiye murmushin ya taka a sannu gaban gadon sosai tamkar ba shi ba. Yatsunsa guda biyu ya kai kan jijiyar kanta da tai ruɗu-ruɗu kusan na minti ɗaya, kafin ya janye ransa a dagule ya dubi Doctor Afif. “A cire mata duk wata na'urar jikinta”.

       A ɗan firgice Dr Afif ya waro manyan idanunsa. Har lips ɗinsa na rawa wajen faɗin, “Ranka ya daɗe na'urorin mam sune ke taimakamana ganin ɗan sauran abinda ya rage yana aiki a tattare da ita. Cirewar zata iya zama haɗari a gareta. A gafarceni idan na shiga hurumin da ba nawa ba”. Kamar ma bai fahimci bayanin doctor ɗin ba ya sake furta, “Nace a cire”.

      Sake daburcewa Dr Afif yay, sai dai bashi da damar cigaba da jayayya duk da ya san bazai yuwu Iffah ta cigaba da rayuwa ba in har babu waɗannan na'urorin. Wayarsa ya ciro a aljihu yay kiran wata nurse da ke aiki a clinic ɗin masarautar, cikin ƙanƙanin lokaci sai gata tazo. Razana tai da ganin mai gayya mai aiki a ɗakin, tuni ta zube gwuyawunta a ƙasa tana kwasar gaisuwa cikin tsumar jiki. Da hannu yay ma Doctor nuni tai aikinta kawai batare da ko ya dubi sashen da take na. Cikin sauri Dr Afif ya ce ta miƙe, shine ya shiga nuna mata yanda zatai komai. Hannunta na ɗan rawa dan kasancewarsa a ɗakun kwarjininsa ya cika ko'ina. Abune kuma da zatace bai taɓa faruwa ba a rayuwarta duk da itama ɗin dai jinin gidan ce. Ta gama janye komai da ga jikin Iffah'r bisa umarnin Dr Afif batare da ya nemo Doctor ɗin da ke kula da ita ba. Shiko gogan na tsaye kamar wani soja idanunsa a kan duk yanda suke komai har aka kammala. Fita nurse ɗin tayi, shima doctor ya koma gefe yana son ganin ikon ALLAH. 

          Kanta ya ɗan rissino a hankali ya kama duvet ɗin gadon ya sake gyara mata, batare da ya dubi Doctor Afif ba ya nufi ƙofar fita yana faɗin, “Ina buƙatar ganin Sayyid Fayzul-haq yanzu nan”.

      “Umarninka shine abin jirana”. Doctor ya faɗa da sauri yana buɗe masa ƙofa.


      ★A mintinan da basu ƙarasa goma ba Sayyid Fayzul-haq ya iso. Cike da girmamawa ya miƙa gaisuwa. Kai kawai ya ɗaga masa batare da ya janye idanunsa da ga kan system ɗin gabansa da yake sarrafawa ba, dan tun shigowarsa ɗakin ita yay zaman sarrafawa. Ɗakin ya cigaba da ɗaukar shiru na tsawon wasu mintuna kamar bashi yasa ai kirasa ba. Sai da ya mula dan kansa kafin ya buɗe baki da ƙyar batare da ya bar abinda yake ɗin ba. “Ina buƙatar ruwan zam-zam, da waɗan nan abubuwan”. Yay maganar yana masa nuni da takardar da ke gefensa batare da ya ɗago ɗin ba dai. “An gama, umarninka shine abin jirana. ALLAH ya ƙara maka lafiya da rayuwa mai albarka”. Sayeed ya faɗa yana matsawa kansa a rissine ya ɗauka takardar. Sai kuma yay masa sallama duk da yasan ba amsa zai samu ba ya fice da hanzarinsa domin gaggauta cika umarnin shugabansa.

        Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa dukkan abinda ya buƙata aka kawosu..


      Ya hana duk likitocin sake taɓata a wannan yinin, sai ma Daneen Ammarah da ya saka aka nemo masa. Tasha mamakin magungunan da ya nuna mata da ganin an cire duk wata na'urar da ke tare da Iffah'r, sai dai yanda ya tsuke fuska babu alamar wasa ya sata shanye duk abinda ke a ranta ta ɗauka abinda ya batan bisa umarnisa. Dan duk da kasancewarsa ɗan ɗan uwanta a yanzu shi ɗin shugaba ne, akwai gaɓar da kuma yake tafiyar da wasu al'amuran a tsakaninsu matsayin shugaba ɗin. Hakan baya damunta, dan kowa ya san ALLAH ne ya bashi, ba dan kuma ya kasƙantar da su a kansa bane ya fifitashi da jarabawar mulkin.........✍️




   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

No comments

Powered by Blogger.